ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Gaida Mahaifin nasu sukayi cikeda girmamawa kana ganinsu kaga yaran dakeda tarbiya dakuma natsuwa. Cikin so da kauna ya amsasu yana tambayan kowa ya aiki sanan suka wuce masallaci, itakuma kayan Baba su files da wasu yan tarkace tafito dasu daga motan sanan tai cikin gida.

Sama tayi direct zuwa lafiyayyen hadadden falon Baba, ijiye kayan tayi sanan tajuyo tabude kofa ahankali, ganin Mama tsaye abakin kofan kaman ita take jira daman yasa takarasa fitowa tareda maida kofan tana rufewa tana kallon fuskan Mama dake kallonta tana murmushi, harara Mama ta watsa mata tace “ba murmushi nace kimin ba, quietly go to that kitchen kidafa sabon abinci wanda za’aci agidan nan this night tunda wanda aka dafa dake da kawayenki kun cinyeshi tatas” dan turobaki tayi dan wlh tagaji ahankali kaman zata rushe da kuka tace “Mama maisa Ladidi bata dafa wani ba wlh nagaji school fa naje” cikin fushi sosai Mama tace “are you stupid Umma? Inba so kike na makeki ba kiwuce yanzun nan kafin raina yabaci kije ki daura abincin daza’aci this night, I am talking to you kina gayamin Ladidi tadafa, kin zaci sabida ke nadauki Ladidi aiki kokin dauka jakace ita batasan ciwon kanta ba dazata zake tai girkin gida keda kawayenki kuzo kutasa abincin agaba ku cinye tas, yanzu ina gayamiki kije ki daura wani kina neman kawomin gabli da ba’adi, to the kitchen my friend!” Mama tadaka mata tsawa kaman zata kurma ihu tawuce hawaye sun cika idanunta tass tai kasa, harara Mama tabita dashi sanan takada kai kawai tawuce tashiga dakinta.

Kitchen din tashiga tamaida kofan da mugun karfi tarufe kaman zata Balla kofan sanan ta jingina da kofan tana maida numfashi takai kusan 5min sanan tawuce ta kwaso kayayyaki tashiga shirin hada girki.

Saida akai Isha’i sanan Baba da su Manaf suka shigo gida, afalo suka tarda Mama zaune gaidata duk sukayi, Mama ta gaida mijin nata zama duk sukayi, Maheer yace “Mama me aka dafa yunwa nakeji” ahankali Mama tace “Khairy na kitchen tana girki, itada kawayenta suka cinye duka abincin da aka dafa tass shine yanzu dannace taje tadafa wani abincin take kumbure kumbure” dan murmushi Baba yayi yana duba wayanshi ganin yanada miss call, cikeda kufulewa Maheer yace “wlh Mama Allah zan zane yarinyar nan, duk randa takawo kuchakun kawayenta tashiga kitchen tamusu girki da kanta ba abincin muba” cikin fushi shima Mu’az yace “ni I don’t even know wani kalan brain Khairy keda shi, ni tunda nake bantaba ganin wacce takai Khairy yawan kawaye ba, kawayenta sunfi dari biyu, tamaida mana da gida nanne majallisar kawayenta ai gobe Saturday Allah sa takawo mana wata gidan nan wlh daga ita har kawar saina kakkaryasu” Baba daduk ke jinsu yana taba wayanshi wayan ya ijiye yakalli Mama yana murmushi sanan yakalli su Maheer yace “ku kyale yarinyar nan she’s just a small girl, idan making friends makes her happy so be it, abincin gidan banike siyaba taita kawo kawayenta sunaci is no big deal, and you wife” yajuyo yakalli Mama yace “idan abincin gida da kawayenta keciki ki kara yawan abinci since kinsan yarki mai mutane ce, ta yanda zasuzo suci su koshi sanan muma muzo muci okay” tabe baki Mama tayi tace “daman babu wanda ke bata yarinyar nan saikai kacigaba” Mama tai maganan da fushi dan murmushi Manaf da tuntuni baice komiba yayi ganin yanda ran Mama yabaci yace “Mama kudena making issue out of this small thing please bagashi yanzu tana kitchen tana dafa mana wani ba, is just friends ta tara bawai wani bad hali ko dabi’a takeyi wanda yaran yanzu sukeyi ba Mama, please ku kyaleta, she’s still a small girl, inda ace bata gama secondary school dawuri ba da har yanzu bamata shiga university ba ballema tazo hartana final year, ku barta please Mama ahankali zata gyara” murmushi sosai Baba yayi yanajin maganan da Manaf keyi, Manaf nada dabi’unshi sak, ga hakuri ga iya tafiyar da gida gashi da halin manyanta halin Baba, amman Mu’az da Maheer jin kansu suke kaman sa’onnin Ummul Khairy. Baki Mama tabude zatai magana aka bude kofan kitchen din aka fito Khairy ce tadauko wani hadaden warmer, ko kallonsu batayi ba sai uban turo baki take tawuce zatakai warmer dinning Baba yace “zo kawo kulan nan Umma anan falo zamuci” ahankali tajuyo tazo Mu’az da Maheer sai uban ballamata harara suke tana karasowa ta ijiye kulan Baba na kallonta yace “yauwa sannu da aiki Yanmata na” Maheer dake kallonta yace “yi sauri kije ki kawomin plate dina da fork” dasauri ta kalleshi da manya manyan idanunta harara ta watsamai wani irin mikewa tsaye yayi kaman zaiyo kanta dasauri tai baya tareda dan sakin ihu. “Wayyo Ya Manaf kaganshi ko” hararanshi Manaf yayi batare dayay magana ba hakan yasa Maheer yakoma yazauna yana kwafa, Manaf yakalleta yace “go and bring the plate and serve us” gyadamai kai tayi tajuya tana turo baki daga Baba har Mama suka bitada kallo, bata wani dade ba tafito dauke dawani babban tray da plates spoons, bottle water da drinks ke kai sanan takawo tsakiyan falon, sanan tabude kulan wani kamshi ne yadaki hancinsu tadafa wani lafiyayyen taliya da nama, zuzzubama kowa tayi sanan ta tashi, Baba yace “ina zaki zauna kici naki” ahankali tace “nakoshi naci shinkafa dazu, wanka zanje nayi Baba nagaji” “jikiyi yarinyar kirki” wucewa tayi sama sukuma sukahau ci, saida Maheer yajuya ganin hartama shiga dakinta yasa yajuyo yace “at least she’s good in one good aspect, wato girki” murmushi Baba yayi yakalli Mama yace “akwai wacce zata zauna da Wife bata iya girki ba ballema yarta” murmushi kawai Mama tayi batacemai komiba, saida suka gamacin abincin tsaf sanan Maheer ya kwashe komi yakai kitchen kafin su tashi suma iyayensu sallama suka wuce side dinsu.

Tashi Baba yayi yana kallon Mama datai shiru yace “please kidena sa zancen shirmen Khairy aranki, is just like what Manaf said at least friends kawai ta tara bawani mugun hali ba” dan ijiyan zuciya ta sauke sanan ahankali tace “Alhaji still yawan kawaye basu da amfani wlh” ahankali Baba yace “I promise duk randa nai sensing wani bad behavior kokuma wani abu nida kaina zan rabata dasu, please this matter of her friends shouldn’t be an issue again ok” Ahankali Mama tace “ai shikenan dama kaine ke bata Umma ai” Mama tai maganan tai gaba abinta binta yay abaya yace “wifeyyy common” bata biyemishi ba tabude kofar dakinta ta shige, murmushi yayi kawai aranshi yace “I will handle u later” sanan yay hanyar dakin Khairy, knocking yayi ahankali tareda kiran sunanta. “Umma” jin shiru yasa ahankali yabude kofan dakin, dakine nai kyau dakana gani kasan dakin Yar gata ne anyimai Fenti pink dakuma design na flowers everywhere, tana kwance kan lafiyayyen gadonta mai kyau tana sanye da dogon gown na bacci tana bacci hankali kwance ga dakin uban sanyin AC tachure alamun sanyi takeji, karasowa gaban gadon yayi yace “Umma Umma, mamar ki dake fada ita batasan rashin jin maganan ta kika daukoba” yay maganan yanajan bargon gadon yarufa mata sanan yadau remote don AC yarage AC sosai kafin ahankali yajuya ya kashe wuta sanan yarufe mata kofan yawuce dakin matarshi!!!!
???? PROMISE OF THE HEART ????

 ALKAWARIN ZUCIYA ????


    ✍????M SHAKUR 

6️⃣

Wajajen 3 aka wuce da Amarya Kano, ita kanta Khairy saida tadanyi kuka cus Besty tabata tausayi, bayan an wuce da ita tama Maman su sallama tawuce dan zuwa chan gidan dasukai party inda motanta yake a pake, ahankali take tafiya ta bala’in gaji sabida rawan dasuka sha, ita kadai kemagana tace “yanzu inda Baba yabarni da hardani za’akai Zainab Kano, gashi akwai more event a Kano” dan murmushi tayi ita kadai tace “Allah kaimu bikina wlh 2 weeks zaayi ana event hmm” dan murmushi tasakeyi tace “nidako saurayi banda shine nake planning biki na” ahankali ita kadai tace “saikace wata mara farin jini, inada samari dayawa but duk mazan Nile ne, basu hadu ba gasu yan rainin wayau saisa i don’t even talk to them” tai maganan tana murguda baki daidai lokacin ta iso wajen motan, ahankali tace “I want to marry hadadden namiji, classic , handsome, miji dat will make mata jealous of my catch” tsayawa chak tayi takalli motan gabanta yadan fadi, saikuma chan tace “don’t be scared Khairy you have to show Baba u can drive sabida yabarki kidinga jan motarki” tana maganan tabude gaban motan tashiga tazauna tana sauke ajiyan zuciya sanan tamaida kofar motan tarufe kafin ahankali tace “Ohhkay let’s see” sitbelt tasaka still gabanta nafaduwa bata taba tuki bafa kawai tasha ganin yanda akeyi sanan Maheer idan tashiga mota dashi yana nuna mata yace “kihaka kihaka this and that” ahankali tace “Bismillahir Rahmanir Raheem” sanan ahankali takunna motar gently gabanta na dum dum tashiga yin reverse kadan kadan kana gani kasan wacce bata iya tuki bane acikin motan nan sanan ahankali taja motan tana tafiya ahankali wani irin murmushi tayi cikeda jin dadi tace “see ba gashi nan na iya ba ina tuki perfectly like a pro” Ahankali takejan motan feeling a bit too sad sabida su Mama basu Bari takai Zainab ba ahaka hartakai gate din estate din tasa kan motarta tafice tana kalle kallen main road din gabanta na faduwa, ganin motoci kowa na zuba gudu na wucewa yasa sabida irin karfin hali irin nata tasa motan ta shige cikin titin sanan tafara gudu Adan hankali, ganin tana gudu kan titi smooth babu wani tangarda yasa tai murmushi tace “wlh na iya” sanan tawani kara uban gudu tana murmushi, ko kadan bata lura dawani keke napep dake bullowa daga wani layi da mahaukacin gudu ba kawai danno kan keken shi yayi batare dayama kalli titin ba rawa jikinta ya dauka dudda da akwai tazara kadan tsakaninta dashi amman sabida yanda jikinta ke rawa tanason takara kara rage gudun datake kawai ta danna sauri before the blink of an eye jikake kwarap!! Motanta yadaki bayan keken da bala’in karfi tacigaba da tura keken gaba jikinta nawani irin rawa tama kasa taka burki. “Innalillahi wa innailaihi raji’un” tafadi arude kaman walkiya sanan ta ci wani mahaukacin burki dayasa dabata saka sit belt ba data buga kanta a siteri, ganin motan ya tsaya chak yasa dawani irin sauri ta murza key ta kashe motan gabaki daya tana wani irin sauke ijiyan zuciya da sauri dasauri tana kallon keken dake manne da gaban motanta zufa nawani irin keto mata daga goshi takasa ko motsi still in shock.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button