ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Ahankali Zayn yace “Abba kayafemin I am so sorry” murya chan kasa Baffa yace “shiiiiiii Zayn i understand you Allah yasa hakanne mafi alkhairi, kana ina”? Murya chan kasa tace “ina wani hotel ban sami flight ba yau saida safe” anatse Baffa yace “dare yayi yanzu dan haka forget about tafiyan nan gobe dasafe kadawo gida kajini, I am not angry with you one bit hakama Baffan ka shima he’s not, so kadawo gida kadauki komi amatsayin kaddara inda Ummulkhairy matarka ce da Ammi n ka bata isa taraba Auren nan ba, so it’s okay, kadawo gida inaso kafito dawata yarinyar ka aura idan wacce mahaifiyarka keso ne to idan ma ba ita bane duk daya kaji” gyadamai kai yayi ahankali yace “thank you Abba” murya chan kasa Abba yace “don’t cry again good night son” ya katse wayan.
6️⃣0️⃣

Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.

wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp

This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️

Jirgin karfe 6 nasafe Dad da abokinshi sukabi aka wuce da Aliyu Oman.


Dukansu adakin sun makara sabida yanda akai bacci late jiyada daddare, Ummulkhairy tafara bude idanunta wuraren 8 nasafe, saman dakin tabida kallo komi nadawo mata sabo she can’t believe ita Amarya ce and tana gidan iyayen mijinta Aliyu anan ta kwana, tashi zaune tayi ahankali tana kallon Batool da Amal dake shargan bacci sanan ahankali tamike tsaye tawuce bayi, shiga tayi ta maida kofan tarufe sanan tabude tap wanke fuskanta tayi takalli madubi tai wani irin fresh fatarta tayi da sulbi sulbi yakeyi tsabagen dirzan gyaran jikin da aka mata tarame babu abinda yarage ajikinta banda boobs da hips, ijiyan zuciya tasauke ahankali sanan tadauki brush sabo dake dakin tadauro alwala tafito daga bayin ganin Batool zaune yasa tashimfida dadduman dake dakin tadauki hijabi tasaka tai salla.

Koda ta idar zama tayi tai shiru tana tunani, Aliyu kawai zuciyanta keso yagani tabashi hakuri, tsayawa akanta Batool data fito daga bayi tayi tace “tashi kije kiyi wanka ki shirya” gyadama Batool kai tayi sanan tamike tsaye ahankali tana kallon Amal dake bacci still sanin bata salla yasa tawuce bayi batare data tadata ba.

Wanka tayi tafito daure da towel set na akwatin da Baba yamata Batool tashigo da daya shigo daga cikinsui sanan ta ciro mata wani lafiyayyen lace ja, shiryawa tayi da taimakon Batool duk wanda yaganta saiya kara kallonta, mayafi Batool takawo mata tayafa mata aka sanan ta feffesa mata turare tace “fita kije ki gaida Gwaggo tana falo” Gyadamata kai Ummulkhairy tayi sanan tabude kofa ahankali tafice tanabin corridor dake kamshin turaren wuta sanan tadaga labule tafito falon, Gwaggo na zaune afalon kan daya daga cikin jerin kujerun dake falo 3sitter tana burga wani lafiyayyen fura a kwarya, Meena na zaune kusada ita itama tasaka atampanta mai kyau sosai, ganin Khairy yasa tawani irin ijiye wani empty kwaryan dake hannunta wanda tarike tana jiran Gwaggo tagama ta tsammata tadauke kai, kaman ance Gwaggo ta waigo sabida kamshin turaren da jikin Khairy keyi ganin Khairy gaban corridor kanta akasa kana ganinta kasan kunya takeji yasa tawani washe baki tana kallonta tace “jama’a kuzo ku kalli Matar jikana Ali Gadanga kusar yaki” dan gajeren tsaki Meena taja mara kara tana kara dauke kai kaman taga kashi, ahankali Khairy takaraso gabanta sanan ta tsugunna har kasa akunyace tace “Gwaggo ina kwana” dungure kan Meena Gwaggo tayi tsabagen dadi tace “dan gidanku kalli yanda ake gaida manya ba irinku ba da kullum kedamuna da kud moni daga tsaye kuna shanyemin jini masu bakin hali, tashi tashi kinji diyata Allah ya lullubeki da albarka, zauna kenake dama ma fura zo zauna nan kusadani ke Meena matsa mata” gyara zama Gwaggo tana kara matsa mata girgiza matakai Khairy tayi akunyace tana kokarin zama akasa dasauri Gwaggo tace “kul karki zauna akasa, sokike sanyi ya shigeki kina amarya, zauna nan kan kujera kusadani kiga, matsa mata Meena” tai maganan tana tunkude Meena wani mugun kallo Meena tama Gwaggo kaman ta maketa sanan ta tashi fuuuu tafice daga dakin Gwaggo tabita da harara tace “kinga bakin hali yan gidan nan ko dukansu haka suka gaji Wanan bakin halin daga wajen ubansu, zauna kiga” zama ahankali Khairy tayi kan kujeran Gwaggo itama ta gyara zama da kyau sanan takarasa kada furan tamika mata tace “ungo sha kena dama mawa” ahankali tasa hannayenta biyu takarba tana murmushi sanan takai bakinta takurba furan kadan dadi sosai tadade bataci abinci hakaba tass tashanye furan Gwaggo nawani irin murmushi sanan takarbi kwaryan tace “kawo nan kiga banson kiyi komi, ko sauro banson ya cijeki zan taya Aliyu kula dake harsu dawo daga kasan waje” kallon Gwaggo Khairy tayi dan batagane metake nufiba hakan yasa Gwaggo tace “yauda sassafe aka tafi dashi kasan waje sabida zuciyanshi ba lafiya Baban shi yakaishi wajen wani abokinshi likitan zuciya kidinga ma mijinki addu’a kinji In sha Allah zaiji sauki” gyadama Gwaggo kai tayi ahankali tana kokarin rike hawayenta dan duk itane dalilin Wanan rashin lafiyan nashi.

Yan aikin Mami ne suka shigo da manya manyan kulolin abinci zasu ijiye a falo tace “tafin musu dashi chan dakin Amarya” wucewa cikin sukai sa abincin, ahankali Gwaggo tace “tashi kije kiyi Kari ki kwanta ki huta anjima kawayena zasuzo su ganinki kinji” gyadama Gwaggo kai tayi sanan ahankali tace “nagode Gwaggo” wani irin washe baki Gwaggo tayi tace “ohh Allah yabani mai mini godiya, gantalallun yaran gidan nan kome zan musu babu godi bare nagode, yimaza jekiyi Kari ki kwanta kihuta Khairiya Allah yamiki albarka” wucewa ciki tayi tana dan murmushi.

Da rana kawayen Gwaggo tsofaffi su kusan goma sukazo gidan damai kidan kwarya, wasu tsofaffin wakoki suka dingayi suna sa Khairy rawa sai dariya ake kafin daga baya su bata gift nasu, buhun gishiri, goruba, aya dasauransu sai dariya ake sanan suka tafi wajajen 6.

Bayan sallan isha’i mota yazo zai tafi da Batool da Amal Khairy tai kuka kaman me hakanan tana gani suka tafi babu yanda ta iya aka barta ita kadai agidansu Aliyu danma Gwaggo na sonta kaman tahadiyeta da abin duniyan sun mata yawa.


Shigowa yayi falon Ammin nashi ahankali yana sanye da jumper na faran shadda yayi kyau saidai yadan rame da ita kanta Ammin tagani but she knows he will be fine, tashi Baffa yayi babu yabo ba fallasa yakalli Ammi dabasa wani good times yanzu sosai saidai yamaida ita yace “muje ko” gyadamai kai tayi tana murmushi sosai ta mike juyawa Zayn shima yayi sanan suka fito Mmotan Baffa suka shiga Zayn najan motan Ammi na nuna hanya harsukakai gidan Aminiyanta dasuke kira da Hajiya Kwangila.

Babban gidane sosai ga ma’aikata ta ko’ina suna parking a compound din wata mata wacce kibanta kenan kaman na Ammi bakinta hakoran makka guda hudu na gold sama biyu hakiran kasa biyu tafito cikin shiga na alfarma tareda mai gidanta wanda yakenan business mogul Chanchangii kenan, karasowa sukayi matan tawani rungume Ammi tace “barka da zuwa aminiyata, ina yini Alhaji” tai magana tana gaida Baffa dake gaisawa da mai gidan cikin mutunci sanan takalli Zayn da kanshi ke kasa ahankali yace “ina yini” cikeda fara’a tace “surukina Zayn Oya dan Allah kushigo kun tsaya anan” tai maganan tana kama hannun Ammi sukai ciki shikuma Zayn yagaida Baban daya rungume shi cikin ao sanan akai cikin gida, wani lafiyayyen falo suka shiga aka zazzauna yan aiki suka shiga kawo kayan kwalama shaaaaa kafin sugama suwuce.
Cikeda natsuwa Baffa yay gyaran murya yace “Alhaji to ga d’ana nan Zayn, da izininka inaso idan ka aminta dashi kabashi permission na neman yarka, idan sunga juna sun aminta da juna sai mufara maganan aure ko” wani kallon juna da Ammi da Hajiya sukayi sanan suka kama hannun juna suna murmushi, Alhaji yace “Alhamdulillah Alhamdulillah, naji dadin hakan kuma ina fata Allah yatabbatar mana da alkhairi kira Aisha wife” tashi Hajiya tayi tai sama sanan Alhaji yace “sunan Y’ata Aisha, a UK tai karatu tayi Mass com, Aisha nada kirki dakuma hankali da girmama na gaba da ita” ahankali Baffa yace “Masha Allah”
Wani hadadden daki Hajiya tashiga ganin wata yarinya zauna gaban madubi tasaka hadaddun kaya tajuya ma kofan baya yasa tace “wai dan gidanku Aysha bazaki sauri ba maisa bakijin magana ne namiki alkawari zakiso Zayn” hawayen idanunta tashare ahankali tace “Momy ni Zayn din danakeso daban dan Allah ki karamin 1month na nemeshi yana nan Abuja kinji” fizgota Mom tayi tadagata ciked masifa tace “wlh zan kwada miki mari nizaki maida karaman mutum ga yaro chan da iyayenshi afalo da babbanko kinki fitowa dau gyalenki jor” ahankali tadauki gyale zata yafa karba Mamanta tayi tayafa mata tana murmushi tace “kinga yanda kikai kyau kuwa wuce muje” yakama hannunta saukowa falon sukayi, tunda suka fara saukowa Zayn ke kallonta idanunshi kur akanta jiyayi zuciyanshi na bugawa fat fat fat ahaka har suka karasa saukowa kasa kanta nakasa tace “ina yini Abba, Mom ina wuni” daga Baffa har Ammi murmushi sukayi ganin yarinya mai natsuwa gata kyakkyawa gatanan fara kaman Zayn din, murmushi Ammi tayi sosai tace “Zayn tashi kuje garden ku zanta mu muna nan muna namu na manya” dasauri Hajiya tace “kai shi Garden Aisha” tashi tayi ahankali kanta akasa hakama Zayn shiya fara gaba suka fita tana biyedashi kanshi akasa har zuwa garden suna shiga garden yawani irin fizgota da mugun karfi baki tabude zatai ihu yadaura hannunshi kan bakinta yana mannata da bango yana wani irin huci ware idanu tayi gabanta na mugun faduwa ganin Zayn Zayn data dade tana nema, hannunshi yazare daga bakinta yanunata da yatsa yace “how dare you Ayshu” wani irin murmushi tayi tanaji kaman zuciyanta zai fito sabida murna tace “Zayn” da yatsa yanuna ta yace “listen to me kome zaki fadama iyayenki kifada musu baki sona karki sake kibari ahada Auren nan dan bazaki taba jin dadin aure na, i can’t marry a girl datasan namiji awaje” wasu hawaye masu zafine suka zubomata murya chan kasa tace “Bantaba son wani namiji kaman ka ba Zayn” yana kallonta in the eyes yace “amman kuma kika bama wani chan virginity naki” jitayi zuciyanta yamata zafi, ahankali tace “I regretted everything, I had sex once u were the second sex danayi in my life dan Allah that shouldn’t be a barrier to aurenka Ya Zayn idan bansameka amatsayin miji ba I can die” dauke kai Zayn yayi yawuce kawai yaje yazauna rayuwan shi babu abinda kemai dadi but he just feel Allah ne ke kamashi, he has been a bad boy, yaci mata daban daban turawa yasha shisha gashinan yanzu the only woman daya taba samu bai sameta ba, look at yarinyar da Allah yahadashi da ita his life is ruin.
6️⃣6️⃣

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button