ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL
ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Dawani kalan sauri direban keke napep din yafito yaci Kwalli a idanunshi yana sanye da Yar singileta daya koma brown tsabagen datti da jeans passengers shi maza biyu suma dake baya duk suka fito yana kallon yanda bayan keken shi yay condemn, sauran motoci sukuma sunata wucewa abinsu tunda dai Allah yakawo sauki hatsari ne da babu wanda yaji ciwo to su karata chan anata wucewa ta gefensu.
Saida mai keken yagama duba kekenshi tass yakalli yanda duka kwan fitilan dake bayan keken suka faffashe sun fadi akasa sanan ahankali yadaga kanshi yakalli glass din gaban motan ranshi amugun bace yana kallon Umma dahar lokacin takasa motsi sai numfashi datake maidawa ita kadai tasan yanda cikin jikinta ke rawa, kafinma mai keken yay magana daya daga cikin passenger yace “durun uwanchan amman matar nan yar bala’in rainin wayau ce Auwal, muna tuki abinmu lami lafiya tazo ta dakan mana keke tamana Wanan uban asaran sanan ta zauna hankali kwance a motanta batama fitoba balle ta duba asaran datayi mana ba”……..
Wani hadadden hilux baka dakana ganinta zaka gane da security personnel ne ke gudu akan titin, ganin titin is congested go slow yasa yashiga rage gudu yana kalle kalle, wani kyakkyawan saurayi ne ke tukin motar yana sanye da kayan yan sanda, daya bala’in haska farin fatan jikinshi, ahankali yake tuki yanabin titin da kallon ganin yanda motoci suka cika hanya tam ga daga chan gefe gefen titi haka ya hango accident akayi tsakanin keke da wata mota dayaba iya ganin cikin motan cus tinted glass ne, ga masu keken sun fito suna duba keken su uku kana ganin yaran kasan irin rascals dinan ne, dan tsaki yayi ahankali sanan ya gangara gefe yay parking motan shi, murya chan kasa tace “I hate this job Dad!” sanan ya kashe motan yafito yanadan yatsine fuska tareda maida kofan motan nashi yarufe..…..
Cikin wani kalan bakan zuciya mai keken da aka kira da Auwal da idanunshi sukai jajir danshi kadai yasan wuyan dayasha kafin yasami keken nan mezaicema mutanen dasuka bashi haya, cikin fushi ya nuna Umma dake kallonsu kuri ta glass din gaban motan da yatsa, irin warning dinan yama kasa magana tsabagen zuciya, hakan yasa ahankali Umma takai hannunta ta zare sitbelt sanan tabude kofan motan tafito ahankali jikinta na rawa tana kallon gaban motanta itama dayama bare yay kacha kacha saikuma bayan keken dashi ma ya baci wutan duk ya mutu sun faffashe sun fadi, sanan takaraso ta inda suke tsaye nesa dasu zata bude baki tai magana Auwal mai keken ya tare mata numfashi yace “ke dan ubanki dame kike takama agarin nan dazaki min condem din adaidaita sanan ki zauna cikin motarki batare dakinma fito kin duba barnan dakikayi ba balle kibani hakuri..” sosai kirjinta kewani kalan dukan uku uku hakuri tai niyyan tabashi amman yanda yazagi Babanta yasa taji ranta yabaci, cikin fushi tana kallonshi itama right in the eye tace “karka karayin kuskuren zagin ubana again inba hakaba wlh saina wanka maka mari, besides ma kai agidanku ba’a koyamaka kaduba hanya kafin kashigo ciki ba eh”? Cikeda wata kalan bakar zuciya Auwal yana kallonta da idanunshi da ita kanta taga bala’in dake cikinsu yace “ni kike gayama magana?” Dakewa tayi dudda kirjinta kaman zai tsage tace “ai kai kafara, dama ance idan Yaro bai koyi tarbiya agida ba zai koya a titi, dan haka from today karka kara ganin mutum kai kuskuren zaginshi ko iyayenshi” kafin ma Auwal dake dunkule hannu yay magana passenger sukace “ke wai kinada hankali kuwa kin bugemai keke kinmai asara bazaki bada hakuri ba” wani mugun kallo tamusu tace “kune marasa hankali bani ba, kuma hakurin bazan bayarba kuyi yanda zakuyi” tai maganan zata juya jitayi an wani irin fizgo bayan riganta fut tadawo baya hartana turgeda kafa sabida heel din data saka, wani irin bari jikinta yadauka tana kallon Auwal daya fizgota ganin yadaga hannu zai kaimata mari yasa tawani irin kwala ihu tareda kai hannayenta biyun tana kare fuskanta, shiru taji batare dataji saukan Marin ba akan fuskanta, hakan yasa ahankali kaman wacce tai sata ta shiga janye hannunta daga kan fuskanta tana nishi sama sama sanan tabude idanunta da kyau tana kallon gabanta inda su Auwal mai keken suke, wani mutum tagani dogo fari kal sanye da kayan yan sanda yasha gabanta yana rikeda hannun Auwal daya kawomata mari ya murde, dudda bataga fuskan mutumin ba dan yabata baya but she could see yanda bayan shi keda fadi, gawani kalan bakin suma dake kanshi sun kwanta suna kyalli sosai zuwa shi wajen yasa wajen yadauki kamshin dayakeyi. Daga Auwal har passengers din duka tsurewa sukayi suna mutumin, cikin wata kalan kakkausan murya yace “how dare you raised your hand zaka daki mace akan titi, are u mad!” Yadakamai tsawa yana murde hannunshi da kyau ihu Auwal yayi jin azaba yace “officer dan Allah kayakuri bazan karaba, wlh bugemin mota tayi opisa” cikin muryan nan nashi nabawasa yace “and u dare to lift your hand up zaka daketa, cause she is a woman, and she is helpless, alone! Inda kanwar kace fa? U deserve to sleep in jail dukan ku the three of you” sosai suka shiga bashi hakuri, tun tana kallonsu tanajin mesuke fadi har taji kanta nawani irin juyawa kaman tanajin jiri, bugawan da kirjinta keyi yay multiplying da kusan dari hakan yasa gently tajuya tana daura hannayenta akan kirjinta tana kokarin ta saita numfashinta dake mata wuyan kamawa tana kokarin tafiya kawai tafiyan taji ya gagareta wani irin zubewa tayi jikin motan, Karan faduwanta da bugewa da motan datayi yasa dawani irin sauri dagashi harsu suka kallo inda take, ganin yanda take nishi tana beating chest nata tana kokarin numfashi at the same time tana kokarin tashi tsaye yasa dawani irin sauri yasaki Auwal yay inda take.
???? ALKAWARIN ZUCIYA ????
✍????M SHAKUR
7️⃣
Ganin Officer yasaki Auwal yay wurin yarinya datake abu kaman mai aljanu yasa suka juya da gudu suka shiga cikin keken su suka ja suka bace atitin saurama kadan sukara wani hatsarin Allah ya kiyaye.
Ahankali ya tsugunna agabanta yana kallonta from head to toe, this is the first time yake kallon fuskanta ganin yanda take fitarda numfashi da kyar yasa yashiga bin jikinta da kallo kota bugene koko tai sustaining any internal injury ne,or something else but babu any sign ajikinta, ahankali yasake maida idanunshi kan fuskarta yana kallon yanda take breathing not knowing exactly what to do, da kyar ta iya bude idanunta tana nishi kaman zata mutu, dishi dishi take gani sosai but she could see mutum akanta yana kaman yana kokarin karantan wani abu, gently taga pink lips dinshi na motsi kaman magana yake mata amman batajin komi, tashi yayi da sauri ganin kaman something is stopping her from breathing maybe tanada blockage a airways dinta, bude gaban motan yayi ya cire jakanta dake wajen ya wurga kujeran mazaunin direba sanan yadawo inda take zaune akasa, ahankali yasa hannunshi yakamo kafadunta sanan gently yadagata yadauketa yakai ta gaban motan yasata aciki yamaida kofan yarufe sanan yazaga ta dayan bangaren direba da sauri daidai ana kiran sallan magrib yabude kofa yana kallon yanda take wani irin dambe da numfashinta da kyar ta iya bude idanunta ta kalli jakanta daya wurga mazaunin direba dayake kokarin daukewa zai zauna ganin haka yasa dasauri yadauki jakan yashigo motan tareda bude jakan cikin zafin nama yashiga ciro abubuwan ciki, kayan shafa, kudi turare wayanta sai daga dan lungun jakan yaga inhaler.