ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL
ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Takai kusan 20min takasa motsi sanan ahankali ta tashi zaune da kyar kafin tamike tsaye ahankali tajuyo tana kalllon yanda suka bata kujeran, turobaki tayi ahankali murya chan kasa tace “Ya Aliyu Yamin mugunta kuma zan rama” store tawuce tadauko sabon tissue da ruwa awani bowl tazo ta gyara kujeran tsaf sanan tamaida komi yanda yakamata kafin ahankali tawuce sama tana tafiya ahankali, dakinta tashige tai wanka lafiyayye da ruwan zafi sanan tafito shiryawa tayi cikin wani nude abaya mai kyau bata daura dan kwali ba tabar gashinta ahaka sabida yakarasa bushewa sanan tasauko kasa tunkafin takai dinning taganshi zaune yasa wasu simple kaya na zaman gida farin riga da 3quater na polisawa yanacin sandwish datayi ga cup na shayi agabanshi, daukekai tayi tawuceshi tadauki plate tabude warmer da chips keciki tadeba da egg tadauki cup tazuba shayi duk yana kallonta sanan tahada a tray tadauka zata wuce tashi yayi sanan yasa hannunshi ahankali yakarbi tray ya ijiye kan table yawani jawota jikinshi yace “mekike shareni fushi kike dani dan nai breakfast dake anjima fa zanyi lunch sanan inyi dinner in the night” fashewa da kukan shagwaba tayi tana makemai kafada dasauri yay dan dariya yace “Okk sorry wasa nake, zauna kici abinci kusada ni to” yay maganan yanajan kujeran kusada ita, ahankali tazauna shima yazauna yadauki fork yadebi Irish din yakai bakinta, ahankali takecin abincin harta cinye sanan suka tashi tare suka wuce kitchen wanke plate din yashigayi itakuma tahau dauramusu kayan abinci bai iya komi kan harkan kitchen ba ko plate din saida takara wankewa, banda bare bari da dauko abu da mikamata babu abinda yakeyi saikuma chan ya rungumeta yay kissing nata yadauketa everything, ita mamaki takema why does Aliyu loves her this much kaman basune sukai fada dazun nan ba love lives here.
Wuraren 1 tagama komi suka jera a dinning yawuce mosque itakuma tawuce sama dantai wanka tai salla.
Tana cikin shiryawa taji ana bude gate wani murmushi tayi jikinta har rawa yake takarasa shiryawa cikin wani Riga da skirt na atampa red daya amsheta takafa dauri.
VIPs we are almost roundRing up
7️⃣9️⃣
Kallon kanta tayi amadubi tayi kyau bana wasa ba Amarya sak, jan baki tadauka red tasaka daya karama fuskanta kyau kaman yaune ranan bikinta sanan ta feffesa turare taijiye sanan tajuyo tafito tana murmushi jin hayaniyan su afalo, ahankali tashiga saukowa daga stairs tana tafiya ahankali falonta cike makil dasu, dan Baffa ya tattara su gabaki daya yace suje su dubo kanwarsu Ya Hafiz, Su Ya Hassan, Ya Manaf, Mu’az Maheer, da matayensu dakuma Batool dake kallonta tana murmushi cikeda don Khairy ganin yanda takara kyau, tana saukowa hannunta tasa ta ture kan Batool tareda turo baki irin kallonfa, sanan tawuce wajen Anty Asiya matan Ya Hafiz datafi saninsu wani irin fadawa jikinta tayi tanajan gyalenta tana rufe fuskanta tace “Anty ni kunya nakeji wlh gasu matan Bros” fizge gyalenta Anty Asiya tayi tace “dalla tashi ki gaisa dasu ga Aysha matan yayan ku Zayn” ahankali Ummulkhairy takalleta kaman yanda Aysha itama ke kallon Ummulkhairy da aka kusa bikinta da mijinta yarinyar kan akwai kyau ga diri, gatanan so adorable she don’t even know how to explain it, hannu Khairy tamata waving tace “sannu da zuwa ina yini, ina Ya Zayn” dan murmushi Ayshu tayi tace “gashinan” inda Ayshu tamata pointing takalla Ya Zayn na zaune kan one sitter yana danna waya kaman bashi adakin, dauke kanta tayi dasauri ganin Aliyu zaune kusada kujeran dayake kai yana kallonta, ahankali tace “Ya Zayn sannu da zuwa ina yini” anatse batare daya kalleta ba yace “how are you Ummulkhairy”? Ahankali tace “fine, sanan takalli sauran matan su Ya Manaf ta gaidasu” kafin ta tashi taje wajensu Ya Manaf babu kunya kaman Yar yarinya ashagwabe tafada jikin Ya Manaf tana kankameshi tana tattaka Mu’az da Maheer tana murmushi, cikeda masifa Maheer yace “Ya Manaf kaga tana takani ko” dariya akai afalon, gwalo tamai tace “Ya kufadamai yanzu na girmeshi nai aure ko” yunkurowa yayi kaman zai daketa tai ihu tana kankame Ya Manaf, duka dakin akahau dariya banda Zayn dake abinda yakawo yake dawaya ko kadan baiso yazo ba tursasashi Baffa yayi, shida Aliyu basa fada ko yima juna wani kallo and at the same time shida Aliyu are not friends and don’t think they can ever be.
Aliyu na zaune inda yake yana kallonta yanda take wasa da yayyinta he could see love and care tareda dukkansu, she’s so happy, dan murmushi yayi yasauke ijiyan zuciya baiso yadameta gashi ko ruwa basu bama bakinsu ba hakan yasa yatashi yawuce yay hanyar dinning, tureta Manaf yayi batare dakowa yaji maganan suba yace “is this how u make mijinki work for you agaban guest naki Ummulkhairy”? Yay maganan yana kallon hanyar kitchen dayaga Aliyu yashiga ciki, girgixamai kai tayi dasauri sanan ahankali ta tashi tawuce kitchen itama, tana shiga daidai yagama saka bottle water a wani fine tray, murmushi tayi tai wajenshi dasauri ahankali tace “sorry Ya Aliyu” dan juyowa yayi yakalleta kaman mai nazarin abu, maida marfin fridge din yayi yarufe sanan ahankali yadaura tray din kan saman fridge din kafin yakai hannunshi kan waist dinta yawani jawota dab dashi yana kallon fuskanta, faduwa gabanta yashigayi tana kallonshi da idanunta dasukai zuruu, hannunshi yakai yakama habanta yana kallon lips dinta yace “wayace kisa Jan baki wasu maza nagani” rawa lips dinta yafara zatai magana yahada bakinshi da nata yashiga kissing nata saida ya shanye janbakin tass sanan yasaketa ahankali muryanshi haryadan shake yace “jeki dauko babban mayafi” gyadamai kai tayi batare datai musu ba tawuce tafita daga kitchen din tai sama mayafi tadauko tayafa sanan ta sauko a kitchen din tasameshi yakama zuba drinks da ruwa a 2 different manyan trays, tare suka dauko suka fito falon dashi suka kawo suka ijiye, sanan suka koma dinning kulolin abincin datayi suka kawo nan falon da plates sanan aka zazzauna aka faracin abinci ana hira akasa tana zaune kusada Ya Aliyu da dakanshi ya zubamata abinci, he’s so caring and possessive of her dakowa dake falon yalura da hakan.
Saida suka gamacin abincin tahada all the plates zata daukan Aliyu yace “is too heavy Pickle, go with the cans” yay maganan yana kwasan plates din falon yay tsit, itakuma tadauki gorunan abubuwan shan tadaura a tray tawuce dasu kitchen, tare itadashi sukai clearing wajen Manaf sai murmushi yake dan yasan ko’ina Mama take this is what she wanted for Khairy namiji dazai sota yakuma kula da ita tasami hakan awurin Aliyu, fita mazan sukayi zuwa mosque yin asir hakan yasa ta kwashe matan sukai sama zuwa dakinta dansuyi alwala, Anty Asiya yakama hannunta zuwa wani daki daban tashiga da ita tareda kulle kofa hakan yasa tace “zauna Ummulkhairy” zama Khairy tayi ahankali tana kallonta, Anty Asiya tace “how are you” murmushi tayi tace “fine” murmushi itama tayi tace “Ummulkhairy I am happy for you Allah yabaki miji mai sonki, lura dake dakuma kulada ke haka kigodema Allah” dan murmushi tayi akunyace, Anty Asiya dake kallonta tace “Ummulkhairy mijinki nada jarababben kishi and he’s so possessive of you kinga yanda yake kallonki dakina wasa da Maheer kuwa” ahankali tace “haka yake Anty Asiya” anatse Anty Asiya tace “kidena bari yana correcting naki on certain things, koyaya kukai baki kidena fitowa haka babu mayafi kinji, please Khairy take care of your marriage life kinji” Gyadamata kai tayi ahankali jin kukan little dake wajen Batool yasa tace “ohh Noo tafara, Khairy pls tafasamin ruwa kadan nahada mata madara, bantaho da ruwan zafi ba” dasauri Khairy ta tashi tace “tom” itama Anty Asiya ta tashi tafito tashiga dakin Khairy da Batool da baby keciki, itakuma Khairy tawuce kasa zuwa kitchen babu kowa afalon dudda an idar da salla a masallaci basu shigo ba.