ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL
ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Ganin inhaler yasa dasauri yadauka yana kallon jikinshi sai chan yadaga kanshi yakalleta, ganin yanda take mimmika tana juya idanu yasa yacire Marfin inhaler dasauri yamika mata ahankali yace “You are asmatic” yanda take nishi yasa tama kasa karban abun da hannunta ganin haka yasa yakai bakinta yamakala mata yana kallon fuskanta cike da tausayi cikin muryanshi dabakaman ta dazuba very soft dashi yace “try and breath in, gently” yay maganan yana kallon idanunta dakokadan basa buduwa da kyau dudda hawaye baya gangarowa but dogayen eyelash dinta were completely moist ga gajerun hawaye dasuka tsaya wajajen idanun kana ganinta kasan tana wahala, ganin eyes dinta nakokarin closing rup gashi takasa jan inhaler yasa ahankali yakai hannunshi kan soft cheek dinta ya bubbuga sau biyu yace “ke open your eyes” dan kadan tabude idanunta ta kalleshi dudda bamata ganeshi sosai sama sama taji muryanshi yace “breath in, breathhhh” kaman wani abu yashigeta wani kalan karfi taji yazo mata taja inhaler, jin wani sanyi har kasan kirjinta yasa dasauri tadaga hannunta bamatasan tadaura akan nashi ba tawani irin kama inhaler da hannunshi da kyau tana shaka da sauri sauri. Har cikin brain dinshi yaji wani yirrr jin hannun yarinyar akan nashi, ahankali yake kallonta tana shakan inhaler tana sauke ijiyan zuciya tana dan natsuwa idanunta a lumshe har lokacin kaman tai bacci.
Almost 10min sanan numfashinta ya daidaita tadena motsi jikinta ko’ina yay relax, ahankali yashiga yunkurin janye hannunshi daga nata gently tabude idanunta, dudda garin yay duhu but baihanata ganin fuskanshi ba sabida hasken motocin dake gittawa ta gefensu, ganin dan sanda wanda she is sure wanda yay saving nata from those guys ne yasa dasauri tasaki hannunshi hakan yasa shima ya janye hannun nashi yakoma mazaunin direba yazauna da kyau, ahankali yace “how are u feeling now”? Ahankali tajanye inhaler, kafin murya chan ciki datai sanyi sosai sabida yanda batada karfi ajikinta tace “I am okay” kallonta yasake yi ganin yanda take zufa tundaga goshinta har wuyanta, calmly yace “can you drive back home”? Batare data kalleshi ba ta girgizamai kai tanajin wani abu na tokaremata wuya she try to swallow it takasa sai kawai tadaura hannayenta kan fuskanta tashiga kuka sosai mara sauti jikinta ko ina narawa, cikin kuka sosai tace “I can’t drive” bata tabajin tsoro kaman nayau abinda ma yasa tai having attack kenan, Binta da kallo yayi yanda take kuka tarufe duka fuskanta da hannun yace “call your family to come and pick you up then” yay maganan yana mikamata wayanda daya cirosu daga jaka dazu, ahankali ta hadiye kukan sanan tasa hannunta ta share fuskan nata tass kafin ahankali tajuyo tasa hannunta takarbi wayan dayake bata, taba wayan tayi ganinshi amace yasa ahankali kaman mai tsoron magana tace “banida chaji tamutu wayan” shiru yayi yana kallonta, yanabin hannunta datake fidgeting da kallo, yadade ahaka sanan gently yakai hannunshi ya murza key ya kunna motan batare daya kalleta ba yace “where is your house”? Kallon hanya tayi dudda gabanta nafaduwa amman hakanan taji takasa kin fadamai, ahankali tace “Wuse” dan juyowa yayi yazubamata idanunshi dasauri tasauke kanta kasa tana kara kankame inhaler dake hannunta, murya chan kasan makoshi yace “where at wuse” ahankali tace “Ademola adetokunbo way, gidanmu nakan hanya” jan motan yayi da bala’in gudu dayasa taji wani kalan mugun tsoro yashigeta yana sharara uban gudu akan titi kaman babanshi ne mai hanyan, har sukakai wuse din, zuwa layin sanan tanunamai wani dankareren gate din wani gida, karasawa yayi yay horn, lekowa mai gadi yayi ganin wata rubabbiyar mota da duk gabanta tai dameji yasa yafito daga gate din yazo wajen motan ta side din direba daidai police man din na saukar da glass din motan kasa kafin ma yay magana hango Khairy yasa dawani irin sauri cikin farin ciki yace “Khairy!” Dawani irin gudu yakoma cikin gida daganan gate sukaji muryanshi yana ihu yace “Alhaji tadawo ga Ummulkhairy nan” yay maganan yana bude gate din da duka karfinshi tsabagen murna, wani irin mahaukacin lafiyayyen gida ne mai bala’in kyau, ga mutane wanda kallo daya yamusu yasan iyayenta ne duk a tsaitsaye, barinma matan wanda ya kyautata zaton itace mahaifiyar yarinyar ce idanunta sunyi ja, saiga yayyinta daduk yagani rikeda waya a hannunsu da alamu ita suke kira, yanayin yanda yaga damuwa tattare dasu kuma duk motan suke kallo yasa baimayi wajen parking space din dayaga an tanada a compound din gidan ba yayi gabansu inda duk suke tsaye sanan ya kashe motan, duk suna tsaye suna kallonsu kafin ya Manaf shiya fara motsi dasaurinshi yakaraso bangaren mazaunin direban yabude kofan yana kallonta, ahankali yabude motar yafito yana kallon su Baba, cikeda girmamawa yakaraso gaban Baba dake kallonshi kuri batare dayay motsi ba dagashi har Mama cikeda natsuwa yace “Barkanku da dare Alhaji, nadawo da yarku gida ne, she had an accident akan titin Apo itada keke napep, ina cikin mota ganin hold up I had to step out naga what’s happening nan naga hatsari akayi motanta yadaki na keke napep ga masu keken su uku about to beat her because she couldn’t apologize, I step in nahana su, I was about arresting them naji faduwanta akasa breathing somehow, I had to let go off the keke guy and reach out to her, at first nadauka ciwo taji kafi daga baya nagano she’s asmatic bayan naga inhaler ajakanta, bata dade da regaining senses nata ba, ganin she can’t drive, I try to make her call family ta but wayanta akashe I had to ensure her safety dan yarinya ce kuma is not safe for her tadawo gida dakanta, saisa nadawo da ita, here is the car key” tunda yake maganan daga Baba har Mama da yayyinta da ita kanta Khairy da Manaf yafito da ita daga mota kanta nakan kirjinshi tai lamo kallon police man dinan dako rufamata asiri baiyi ba take, like babu an atom of lie a maganan shi.
Kafin Baba yay magana cikin tsananin bacin rai da damuwa Mama tace “Alhaji kaga abinda Khairy keyi ko, wai Khairy kadai na haifa aduniyan nanne da ita kadai kebani ciwon kai, ga maza yayyinta har uku da sune yama kamata suyi rashin ji amman basuyi sai ya mace ce keyi, yanzu inda wanan bawan Allah this kind hearted officer ya ceceta ba da Allah kadai yasan mezai faru, Allah kadai ne zai sakamai da alkhairi, inda ace bai taimaka mata ba kunsan kalan dukan da masu keken nan zasuma Umma eh, wlh……” dasauri Manaf yace “Mama please we are not alone here” cikin fushi sosai Mama tace “abinda kukeyi kenan dagaku har mahaifinku saisa Khairy duk ta baci haka, zaki gamu dani Khairy” tama Khairy wani mugun kallo taredayin kwafa sanan tawuce ciki fuuuu cikeda bacin rai.
Dan murmushi Baba yayi sanan yasa hannu yakarbi car key dayake bashi anatse yakai hannunshi yakama na officer cikeda murmushi yace “thank you, nagode nagode, I can’t even thank you enough, Allah yamaka albarka for saving Ummulkhair, nagode officer, Allah yamaka Albarka” gyadamai kai ahankali yayi yace “saida safen ku bari natafi” dasauri Baba yace “bari Mu’az yakaika wajen motanka please is late” dasauri yace “a’a Alhaji, dare yayi, yazauna agida I can manage, saida safen ku” yay maganan yana juyawa zai wuce dasauri Baba yace “youngman, I mean officer” jin Baba yakirashi yasa ya tsaya tareda juyowa yakalli Baba, ahankali Baba yace “baka fadimin sunanka ba” dan jim yayi yana kallon Baba kaman bazaiyi magana ba sai chan yace “sunana ASP Aliyu Hydar Zango” gyadamai kai Baba yayi yace “Allah maka albarka Aliyu Hydar” murmushi kadan yayi tareda juyawa yana tafiya one one kaman Gwarzo yawuce yafita daga gidan.
???? ALKAWARIN ZUCIYA ????