NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

[2/21, 2:29 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABANKASA????
2
By Reefat yahya

Bayan sallar magariba iyalan suna zaune suna shan fruits yayan shuairat ne ya fara magana” baba dama a wajen aikinmu ne an bani gida,shine nace tunda baby tayi graduating y not mu koma Abj tare da Ku gaba daya” yayi kyau Allah ya kara budi ya muku albarka ” ..yeee xan koma Abj da xama , hapie me” shuairat ta fada da karfi tana murna.” Ohh yar nan yaushe zaki girma ne? Mama tana kallon diyar tata ” ke de kin Faye takura wllhi, kin sa mata ido sosai ba dama ta sake Sam a gidan nan” hmm malam kai de baka son jin laifinta Ku kuka shagwaba ta ai” shuairat ta wani tura baki ta tashi daga inda take ta koma kusa da babanta..” Dama nasan mama tafi son yaya kullum tana hantara ta ” murmushi sukayi yayan nata ya jawota kusa dashi yace” yi hkri baby mama na sonki, duk sunfi sonki ma a kaina kuma kinga nima ina sonki koh” kai ta gyada masa tana jin dadi.” Dama ina son maka xancen aure, ka girma babana u r 35 now ya kamata ka ajiye family ” hakane baba insha Allah xanyi kokari Ku tayani da adua ” ba komi Allah ya sanya alheri ya baka mace tagari” ameen ” se kuma Ku fara shiri ina so ko jibine mutafi sabida 3days aka bani ” Allah ya kaimu ” haka Suka cigaba da hira ckn walwala da son junansu.


Da safe bayan sunyi kari shuairat ta dau wanka ckn wasu pepalace darkblue n red ta saka yankunne red tayi kyau sosai dayake ita wankan tarwadace se kalar kayan sun mata kyau, tana xaune kenan shukrah ta shigo tare da sallama kayansu iri daya itama tayi kyau sosai ta gaisa da mama sannan Suka shige dakin shuairat.” Ke mutuniyar xan tafi Abj’ ???????? shine har wani dadi kike ji? Bayan zaki tafi ki barni nan hawaye ya cika idon shukrah, ” so sorry bestie nah kinsan baxanso rabuwa da ke bah but yaya ne yace xamu koma can tareda su baba da mama kiyi hkri pls” nan Suka rungumi juna shukrah kam se hawaye itama shuairat ta fara nata kukan an rasa mai rarrashin.ya shigo dakin tare da sallama…gurus!ya ja ya tsaya ” lafiyanku kuwa? Kun shige daki se kuka kukeyi kamar wadanda aka aikowa sakon mu2wa” yaya shukrah CE bata son intafi in barta kuma nima bana son rabuwa da ita” hmmm lallai rashin duka na damun Ku , if not haka kawai hmmm” yasa kai ya fice yaje yana sanarwa mama, tana dariya tace ” kadan ma ka gani in har shukrah da shuairat kam alamarinsu se Allah” tsaki yaja cike da jin haushinsu ya wuce falon baba.dakyar mama ta lallabasu Suka shirya xuwa makarantar su.tun a bakin gate aka rubuta da many an harufa FEDERAL POLYTECHNIC MUBI wato makaranta ta gwannatin tarayya dake can mubi jihar Adamawa,Nigeria. Makarantar ta cika makil da jamaa yanmata da samari, iyayen dalibai ga yara kanana da dai sauransu. An fara gabatar da taron daga karshe anci an sha mutane sun fara komawa gidajensu a yayinda dalibai Suka cigaba da daukan hotuna.shukrah da shuairat suna tsaye a gefen wasu masu daukan hoto, kamar a mafarki se ga saurayin da Suka hadu jiya yana murmushi ya karasa tare da sallama ” wato don kinsan xan kiraki shine kika kashe wayarki koh? Ohh har ga Allah ita ta manta dashi kuma dama bata damu da rike waya bah murmushi tayi tare da cewa”no ba haka bane” bayan sun gaisa nan ya gabatar da kansa a matsayin yana son shuairat kuma har ga Allah yana sonta da aure yace sunansa Abubakar Ahmed imam, shuairat tace xatayi tunani a kai daga nan sukayi sallama ya tafi suma Suka koma gida.da dare shuairat ta kasa tabuka komi se kuka takeyi tun mama na rarrashinta har ta gaji ta daina kulata, shukrah ma sun zo tare da innarta sunyi koke kokensu dakyar aka rabasu.haka makota Suka dinga shiga suna musu sallama , baccine ya saceta bata farkaba se da asuba.tayi sallah tare da wanka a daddafe Suka karya daga nan Suka kulle gidan. Ckn mota ma shiru tayi ta jingina jikin mama, baba yana gidan gaba yaya kuma shi yake tuki Suka dau hanyar xuwa Abj……

Safe journey Alh bello maiha n co
[2/21, 2:29 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABANKASA????
3
By Reefat yahya

Yamma lis …Suka shigo birnin tarayya Abj wohoho shuairat tayi kallo kam har ta gaji domin shine karo na farko da ta fara xuwa garin. Anguwan kubuwa Suka nufa a dai-dai wani gida yayi parking, ya sauko rike da makulli ya bude kofar sannan ya dawo yaja motar Suka shiga. Gidan madaidaici mai kyawun gaske flat ne guda 2se karamin bq.flats din kowanne 3bedrum ne, ya bude musu dayan flat din dakuna uku da falo a tsakiya se kitchen a gefe kowane daki da bayi a ciki abun de gwanin shaawa masha Allah.nan ya nuna musu dakunan, master bedrum ne na babansu se kuma dakunan da suke kallon juna daya na mama daya na shuairat. Kowannensu ya shige dakinsa , yaya kuma ya fita nema musu abunda xasu ci.dakin gwanin kyau gado ne madaidaici se dressing mirror ga kuma wardrobe a gefe se kuma kofar shiga bayi.shuairat ta fada gadon ckn tsananin jin dadi, ta shiga bayin tayi alwala ta fito tayi sallar azahar da laasar .yayantane ya tura kofa tare da sallama ya ajiye mata Leda yana murmushi yace” my bae ki ci abinci ki huta koh wannan shine dakinki hop u lyk it, akwai kaya a wardrobe idan akwai abinda kike bukata ki sanar dani koh” ckn tsananin murna ta tashi ta rungumesa tace “tank u my guy bana bukatar kmai, kaima kaje ka ci abinci ka huta nasan ka gaji ” murmushi yayi sannan ya juya ya bar dakin.
Ta bude ledar fried rice ne da peppe chckn a ckn tek away se kuma hollandia drink mai sanyi , bata yi wasa ba ta hau ci har taji ta koshi sannan ta haye gado ta kwanta tare da yin hamdala.
Wayarta CE ta hau ruri shukrah CE ke kiranta , sun Dade suna hira daga karshe sukayi sallama nan bacci yayi awon gaba da ita.


D next day mama CE ta share falon ko ina fes ta xuba humra a falon ko ina qamshi ke tashi tana son kunna turaren wuta Amma basu da gawayi n abun basu da electric burner.yayan shuairat ne ya shigo tare da sallama bayan sun gaisa yace” mama baki huta ba kina wahalar da kanki ina baby ne ta barki kina ta shan wahala” karka damu sharace kawai nayi kuma mutuniyar taka bacci ma takeyi”
” lallai mama shine idan kin tashi se kice muna shagwaba ta, bayan kema baki son ki sata aiki” murmushi kawai mama tayi ya cigaba da cewa
” yawwa batun girki kuma ku huta koda na 2 weeks ne xaa dinga kawowa daga gidan shugaban kasa”
” anya xaayi haka kuwa?
“Karki damu mama ba komai, yanxu bari in fita in sama mana abun kari” daga nan ta ya kai ya fice.
Shuairat tayi wanka tayi kyau sosai ckn kananan kaya Riga da dogon wando tayi parking gashin kanta da farin ribbon dama wandon nata fari neh kuma pencil ne, rigar kuwa 3qtr gown ce white n orange ta saka orange fashion earings tayi kyau sosai.ta tsaya a gaban madubi tana kallon kanta tayi murmushi tace” Ayshat Bello u ar not soo btiful but I knw dat u ar perfect” ta juya ta bude wardrobe din ….
” wooowww! Ya ilahi wannan duka kayan nawa ne? Ya Allah nagode maka , yaya bash I Lov u sooo …much ” tana magana tamkar yana wajen.bayan ta gama shirmenta ta dauko wani karamin gyale ta yafa sannan ta fice xuwa falo.mama da baba suna xaune suna kallon BBC ta gaishesu daya bayan daya sannan ta koma kusa da babanta ta xauna ” baba!
“Naam yata “
” baba kaga kayan da yaya ya siyamin kuwa?
” yayanki Dan albarka ne Allah ya kara mishi budi , nima haka na tarar da sababbin kaya a dakin da nake yace min duk nawa ne” haka nan Suka cigaba da yaba halayen basheer har ya dawo ya samesu .sunyi ta xuba godiya sannan Suka ci abincin da ya kawo musu, daga nan ya musu sallama sannan ya tafi aiki.haka Suka yini gidan shiru shuairat tayi kallo har ta gaji tayi bacci, da rana ma abinci aka kawo musu lafiyayye daga gidan shugabankasa.
Basheer bai dawo ba se bayan magariba shi ya taho musu da abincin dare daga can gidan, bayan ya huta Suka hadu suna hira a falonsa har xuwa tym da xasu kwanta kowannesu ya koma dakinsa.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button