NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

“Dad bana son ganinka pls leave”

“Baby am so sorry let me explain pls”

“Explain wat just go”
Babu irin lallarshin duniyan nan da mr President beyi ba Amma firr taki sauraronsa haka ya hakura ya koma bangarensa da damuwa fal a ckn ransa.
Umaima ta aika a kira mata bash an shaida mata baya gari haka ta yini jugum xuciyarta na tafarfasa tana jin kishin wannan yarinyar da ko sunanta bata rike bah.


Shukrah CE tare da bash suna hira ckn kwanciyar hnkli ya tmbayeta irin kayan da take so a saka mata ckn akwatin lefe , an sanya ranan auren nasu nan da wata1 ya kai mata tsarabar turamen zani 2 da lace da kuma gown se sabuwar wayar Samsung galaxy da turaruka da mai da sabulu masu kyau da sadan gaske.

“Nagode sosai yaya Allah ya kara budi”

“Ameen matata”
Ta sunkuyar da kai ckn jin kunya
“Aw kunyata kike ji?
“Nifa bana jin kunyarka”

“Toh ki daga ido ki kalleni”
Murmushi tayi ta sunkuyar da kai hmmm masoya.
Haka Suka kasance suna hirarsu irinta masoya daga karshe Suka rabu ya mata sallama domin gobe xe koma Abj, kamar baxasu rabu bah shukrah har hawaye take ????????ahh abun ba sauki an kamu) dakyar ya lallabata ta daina kuka sannan ya koma gida da shirin tafiya.

Tana kwance a falonsu idanunta a lumshe tana tuna kalaman mr President mama CE ta shigo ta xauna a gefenta

“Ya’r baba tashi ki xauna magana zamuyi”

“Ina jinki mama”
“Menene gaskiyan alamarin dangane da magananki da shugabankasa “

“Mama wa ya gaya miki?

“Ina xaune gaban TV na gani da idona kin fito kinyi magana”

“Mama…nifa ba komi tsakaninmu kawai dai…”
Sai kuma tayi shiru ta kasa magana.

“Kawai me? Shuairat kibi a hnkli mutumin nan ba saan aurenki bane mu talakawa masu rufin asiri Muna…

“Pls mama nace miki ba komi tsakaninmu”
Daga nan ta tashi ta koma dakinta ta kwanta ta rasa me ke mata dadi a duniyar ko wane hali mr President yake cki oho! Ko ya zasu kaya da umaima oho! Haka ta kasance har bacci yayi gaba da ita.

A bangaren mr President ma hakan ta kasance ya kwanta yana ta tunane -tunane wayarsa CE ta hau ruri dum …xuciyarsa ta buga don ganin kiran mahaifinsa

“Dady nah”
“Boy ya kake “
“Alhamdulillh ya gida ya momsi “

“Gata kusa dani lfyanmu kalau, na bugo ne don tabbatar da news da gani”

“Ohh dady is just…
“Son am happy zanzo next week sai ka nuna min gidan iyayenta idan Ya’r gidan mutunci CE sai a fara maganar aurenku koh”

“Damm…dammm! Kirjinsa ta buga innalillahi ya zaiyi da wannan kwamacalan

“Boy kana ji Nah, am so proud of u, kayi tunani mai kyau ai xamanka haka nan ba dadi “

“Dady….
“Don’t worry boy na fahimceka momsi tana gaisheka sai anjima takkia of urslf” garam ya kashe wayar
Mr President ya rintse ido yana maimaita innalillahi lallai rayuwarsa tana ckn matsala Allah ne kadai xai fiddashi.ya rufe ido nan ya hango shuairat yana siffanta ta, doguwa CE siririya bata da hasken fata tana da dogon hanci da karamin baki tana da dogon gashi baki wuluk don ko ta daura dankwali rabin gashin nata a waje yake.tana da kyau dai-dai gorgodo toh amma ya zaayi ya aure ta? Babba da shi ? Yasan zai Iya haifanta don koda ta girmi umaima ma baxe wuce da shekara ko 2 xuwa 3.
To Amma wacece ita? A ina ta samu tarihin rayuwarsa? Shin auren nasu zai yiwu? Ya umaima xata yi idan taji xeyi aure? Kodai ya fito ya karyata labarin?
Shin idan yayi haka ya kyauta? Tambayoyin da ya fara jero wa kansa kenan ya kasa samun amsarsu.

Hmmmmmmmmm muje xuwa Reefat CE xata amsa muku wadannan tambayoyin..
Drop ur comments Lov u all????????????

Vote: waye jarumi/jarumarka a ckn wannan littafin umaima” mr President” shuairat” basheer” shukrah”
Wane page yafi burgeki/burgeka….sai naji daga gareku
[2/21, 2:38 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
22
By Reefat yahya

Bash ya shigo falon umaima tare da sallama dawowarsa kenan daga Adamawa ya samu sakon nemansa da take tana kwance tayi nisa ckn tunani ya sake maimaita sallama a karo na biyu ta tashi xaune tana ganin bash ta fashe da kuka.
Ckn rudewa bash ya karasa kusa da ita
“Lfy miss umaima?
Ta cigaba da kukan bata saurareshi bah ya rude sosai ya xauna dab da ita yana bata baki dakyar ta tsagaita kukan ta fara magana

“Kai kadai ne ka ragemin a duk fadin garin nan Kaine zan Iya fuskanta in gaya maka duk wata matsalata bani da kowa a ynxu se kai”

“Meke faruwa ? Ina dad naki”
“I hate him bana.

“Shhhh….hannu yasa ya toshe mata baki yana girgiza kai

“Don’t ever say dat pls, mahaifinki duk laifin da ya miki he don’t deserve dis”
“But bana sonmu ni da Kani Nah baya kulamu yafi son budurwarsa”

“No! Yana sonku kece baki fahimcesa bah kuma wancan yarinyar ba abunda yake tsakaninsu she is a reporter”

“Hmmm basheer kenan! Amma de baka kalli news ba koh? Yarinyar da ta fito da bakinta tace sun Dade suna soyayya”

“Waat? No! No! Umaima I tink…shit! Ya buga kujera da karfi take launin idanunsa sun canza
“Basheer ya na ganka wani iri? Any problem?

“Ba komai kaina ke min ciwo”
“Sorry bari na dauko maka magani”

“No! Am ok” xuciyarsa na tafarfasa shin meyasa shuairat xata yi haka?

“Bash ina kaje an cemin kayi tafiya?

“Uhmm..Adamawa naje wllhi”
“Really ! Dama kai Dan jahar su dad ne, no wonder yake sonka”Murmushi yayi yace

“Haka ne!
“Ehh…dad yana sonka sosai”

“Abunda nake so dake shine ki kwantar da hnklinki nasan dad naki yana sonku sosai batun yafi son wata duk be taso bah , nasan akwai wani boyayyen alamari dangane da yarinyar nan Amma xan bincika da kaina xan gano koma menene”

“Ok bash nagode” nan ta kwantar da kanta a kafadarsa tana hawaye wani irin shock da be taba ji bah haka nan yaji wani irin Yarr..a hnkli yasa hannu yana share mata hawayen tana yin ajiyar xuciya
Mr President da yayi niyyar shigowa gun umaima ya juya a hnkli ya koma bangarensa yana jinjina hnkli irin na bash yaji ya kara son bash har ckn ransa yaron ya burgeshi.

A hnkli umaima ta fara bacci ba tare da ta sani bah bash ya kura mata ido sosai yana kallon kyakyawar fuskarta tabbas loneliness yana addabar ta bata da Wanda xatayi hira dashi don bai taba ganinta da kawaye bah kullum ita kadai take rayuwarta sai kuma kaninta sultan, mahaifinsu is always busy bayi da lokacinsu se masu aiki ne ke kula dasu yaji tausayinta sosai yayi alkawarin zame mata Dan uwa Wanda zai rage mata kadaici.

Ta share awa2 tana bacci bash kuwa yana xaune ya gaji Amma baya son ya tasheta , a hnkli ta bude ido tayi mamakin ganin bash sai kuma ta kalli agogo karfe 4 da minti5 ckn mamaki ta juya

“Basheer u mean tun dazu kana xaune haka?
Murmushi ya sakar mata yace

“I promise to b wit u always”

“Nagode but hw can u” mamakine a fuskarta tana kallonsa nan ya tashi tsaye

“Am going now, duk tym da kike bukatar gani na am always available “

Bai jira amsarta ba ya fice yana murmushi
Umaima kam se mmki take yi ynxu haka ya xauna har na tsawon 2hrs ? Allah sarki nan taji wani irin sonsa ya mamaye ta tana murmushi tana tuna fuskarsa dama ta Dade tana Neman Wanda xe kasance tare da ita sai gashi Allah ya kawo mata bash a lokacin da tafi bukatarsa.
Hmmmm…..akwai aiki!!

Bash be tsaya ko ina ba sai gidansu dakin shuairat ya wuce tunda bata falo yayi saa mama ma bata falon maybe tana dakin babansu don tare Suka dawo.
Tana kwance tana game da wayarta ya shigo tare da sallama

“Hey ango ansha kamshi”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button