NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

Mama tayi jugum ta rasa ta ina xata fara ita dai har ynxu mamaki take kan wannan lamarin dakin mijinta ta wuce nan ta sanar dashi halin da ake cki don shima ya sakko daga fushin da yake kan xancen Karin auren..tare Suka dawo dakin yana nan xaune ya buga uban tagumi take tausayinsa ya mamaye xukatansu baba ya rike hannunsa ya fara magana
“Haba babana…kayi hkri ka daure shi namiji da juriya aka sanshi , kuka baxai warware matsala bah pls stop crying”
Yasa hannu yana share masa hawayen ya cigaba da cewa
“Meyasa tun da dadewa baka sanar dani cewa kana sonta bah..but kaga ynxu is too late don…
“Pls baba is not too late..pls do somtin bana son rasa ta ka taimakamin”
Tausayi sosai ya basu..baba yace
” is ok toh..stop crying zanyi magana da shi daddy ok”
Kai ya gyada masa yana goge hawayen da Suka bata fuskarsa, haka Suka cigaba da lallaba shi dakyar yayi shiru ya daina kukan da yake, baba yace masa ya tashi ya koma gidansa firr yaki yace musu a nan xai huta xuwa yamma bayan kuwa tunda ya dawo ko gaisuwar arxiki bata hadashi da shukrah bah.

washegarimasu aikin gidan mr president sun dafa abinci kala2* sun gyara ko ina a ckn gidan se qamshin tyraren wuta da airfreshners Ke tashi a can kitchen kuwa qamshin girkine..gidan yayi fes ya kara kyau shuairat tayi wanka ta shirya sultan da salman ckn kaya masu kyau se xuba qamshi suke , umaima tayi wanka tayi kwalliya ba laifi tana bin shawarar da shuairat ta bata.mr president kuwa fararen kaya ya saka har da babban Riga shuairat tana xolayarsa wai surukai xasu xo gaisuwa su mr president an tsufa..murmushi kawai yayi har ynxu de baya ckn walwala wannan ma don shuairat tana yawan jansa da magana ne tana son ganinsa ckn farin cki.
10am jirginsu ya sauka mr president tare da driver Suka je airport ckn jin dadin ganin Dan nasa ya karasa sukayi huggin din juna daga can gefe kuma wani dattijo ne tare da dansa ba sai ka tambaya bah mr president ya gane cewa surukin nasa ne, ckn girmamawa Suka gaisa daga nan Suka shige mota driver yaja Suka wuce gida.kyakkyawar sauka aka musu bayan sun ci abinci Suka koma falo daga nan shuairat ta shigo tare da salman da kuma sultan.. har kasa ta sunguna Suka gaisa da daddy da kuma mahaifin yaron shi kuma ya gaisheta ta amsa ckn sakin fuska ta tashi xata koma cki daddy yace
“Ah..ina zaki kuma, munxo Neman auren ya’rki ai kema magana ta shafe ki don haka yi xamanki “
Babu gardama ta xauna a can nesa daddy ya karbi salman yana masa wasa sultan kuwa yana manne da mahaifinsa.shuairat tana Satan kallon yaron yana da kyau ba laifi Amma be kai basheer Nash girma da kyau duka… Daddy ya kira umaima a waya babu bata lokaci ta fito ckn natsuwa ta gaisa dasu gaba daya daga nan ta koma kusa da shuairat ta xauna daddy yace
“Kuje Ku tattauna Ku daidaita kawananku..gashi Ann sunansa ismaeel “
Umaima tayi shiru bata ce komai bah, shuairat ta xunguri kafarta ba tare da wani ya lura da hakan bah nan umaima ta tashi tana wani nokewa wai a dole kunya take ji..falon baki Suka nufa tana gaba yana baya ta bude musu ta nemi kujera ta xauna suna mai fuskantar juna.
Yabi ta da ido tanada kyau sosai shikam ya amince da zabin iyayen nasa ita kuwa tana satar kallonsa ba laifi yana da Dan kyau Amma ko kadan baki burgeta bah hasalima haushinsa take ji don shine silar rabuwarta da Rabin rayuwarta wato basheer!
“Umaima.. Sunana ismaeel kamar yanda kika sani, nayi makaranta nayi degree ina aikine a NPA dake can Lagos”

“Aw..daz gud Allah ya taimaka”
ta kirkiro wani murmushn da bai kai har xuci bah..ba karamin daurewa take bah har take kulashi tana yin hakan ne don bin umarnin shuairat..
“Dafatan xaki bani hadin kai mu xauna lfy don faranta ran iyayenmu”

“Ohh..kana nufin tilasta maka ake son yi..kenan baka son auren?
“No..ba tilastani akayi bah, bin umarnin iyayena ne “
“Just tell me idan kana da wacce kake so kada ka boyemin”
“Ah.ah nidai na amince da auren ki domin kin kwantamin a rai..u have all d qualities dat I want”
Murmushn karfin hali take masa wani sa’in kuwa ta faki idonsa ta watsa masa harara karar bude Kofa da akayine ya jawao hankulansu umaima tana daga kanta sukayi ido 2 da bash ????????????????????????

Muje xuwa
[2/21, 2:42 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
89
By Reefat yahya

pals need ur pryrs pls…Allah ya biya min bukatata idan alheri ne ….Lov u all

Fuskar basheer babu annuri ko kadan ya hada girar sama da ta kasa yana kallon umaima ismeel ya juya don ganin me umaima take kallo bash kam ko kallo bai isheshi bah gun umaima ya dosa ckn wani irin murya yace
“Ina son ganin ki ynxu”
Ya juya xai tafi tayi karfin halin cewa
“Uncle bash ga ismaeel nan , ismaeel dis my uncle basheer”
Kafin bash yayi magana ismaeel ya tashi ckn girmamawa ya mika masa hannu babu yanda ya iya dole ya mika nasa nan Suka gaisa daga nan bash yayi gaba abinsa umaima ta tashi tamkar wata munafuka ta kirkiro murmushn dole tace
“Amm..yi hkri pls 10 mins ina xuwa”
“Olryt no p”
Daga nan ta fice yana nan tsaye a bakin kofa daga waje sai cika yake yana batsewa tana fitowa bata kula dashi bah kawai jin an fisgo hannunta yasa ta firgita ta juya Suka hada ido dashi idanun nan nasa sunyi ka kamar jini ze fita da karfi yake Jan hannunta bai tsaya da ita bah se ckn dakin baki ya wurgata saman gado ita kam tsoro ya cika xuciyarta don bata taba ganinsa ckn wannan yanayin bah nan kuwa hawaye ya fara fitowa a idanunta ta fara kuka Mara sauti ..wani wawan tsawa ya daka mata seda na fadi a kasa???????? ckn daga murya ya fara magana

“Shiru! Shiru nace.. Just keep quite my fren, ina can ina rashin lfy xan rasaki Ke kuma kina nan hnkli kwance kuna soyayya koh”
“BB am…
Hannu ya daga bai bari ta karasa maganar bah ya cigaba da cewa
“U have notin to say umaima.. Kin nuna min halinku na mata halin yaudara da cin amana n …
“Dakata ..kaima ka nuna min halinku na maza halin rashin hakuri da kuma mugun zargi, did u even kia to ask me ya akayi na xauna ina magana dashi…da xan so wani baxan xauna na bata shekaru da dama ina xaman jiranka bah ..dama Ku maza haka halinku yake, excuse me pls”
ta tashi xata bar dakin bash yayi Saurin rike mata hannu ta kwace sannan ta gyara tsayuwa fuskarta na kallon gefe jikinsa ya mutu da jin kalamnta shikam kishi ya rufe masa ido har ya fara ganin tmkar soyayya suke da ismaeel musamman idan ya tuna murmushin fuskarta a wannan lokacin da ya shiga ya samesu..Muryar umaima ce ta katse tunanin da yake

“Idan baka da abun fadi ni xan tafi cos na bar bako shi kadai”
Yayo kanta kamar xai cinyeta yace
“Baki da hnkli ne..wai meyake damunki ne har kina xancen wani bako a gaban idona”
Ta marairaice fuska

“Bb is risky fah..idan daddy yaje nemana bai sameni ba fah ?
” sai yazo nan ya sameki ..kinga daga nan xai San lallai baki son auren n am sure baxai miki auren dole bah”
Haka dai bash da umaima Suka kasance daga karshe ma xama sukayi suna ta hirarsu irin ta masoya sun manta da wani ismaeel a can.
Ismaeel yana xaune yana danne2* a wayarsa bayan yan mintuna ya duba agogan dake daure a hannunsa ta share 30 mins bayan kuma tace 10 mins anyways.. Ya gyara kwanciyarsa a kujera ya cigaba da danna wayarsa.a can falo kuwa suna hira ckn faraa , wayar baban ismaeel ne yayi ruri daga nan ya daga ya fita waje shuairat ta gyara xama tace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button