NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

A can bangaren Mr president kuwa wasu turawa ne Suka zo tayashi murnan auren da yayi maza 3 da mata 2 dukkansu manyan mutane ne masu fada a ji a can kasar England daga fadar sarauniya Suka zo don haka Suka nemi ganin amaryar tasa Mr president ya daga waya bayan ya Dan fita daga dakin da aka sauke bakin nasa layin shuairat ya kira ringing 2 ta daga
“Hello ur xcelency”
Wani yarr…yaji a jikinsa dakyar ya saita kansa yace

“Ki shirya baki nayi kuma turawa ne suna son ganinki”

“Eyya…Mr president y not su bari xuwa dare Allah na gaji ynxu bacci zanyi”
Tayi maganan ne ckn wani salon shagwaba murmushi yayi shi kadai yasan ma’anar yace

“Ok sorry ki huta zuwa daren sai ki shirya koh”

“Ok tnk u my dear”
Nan ta kashe wayar ya tsaya Jim…tmkar mai tuna wani Abu sai kuma ya nanata kalamanta na karshe “tnk u my dear” nan ya sake yin murmushi haka nan tun jiya yake jin kansa ckn wani nishadi daga nan ya koma gun bakin nasa ya basu hakuri cewa amaryar tasa tana tare da baki sai zuwa dare zasu gan ta haka Suka cigaba da hirarsu.
Bash da john suna zaune a waje John ya juya ya kalli bash yace
“Aboki Mr president fah ya fada tarkon son yarinyar nan ba kadan bah”

“Me ka gani john?

“Haba …kana ganin yanda muka samesu dazun”

“Hmmm…next tym zamu hana kowa zuwa bangaren Mr president sai da izininsa cos yanzu yana da iyali bai dace ana shiga anyhw bah”

“Yes haka zamu yi”
Daga nan sukayi shiru shi kansa bash yana mamakin kalan soyayyar kanwar tasa da Mr president hmmm…mata kenan zasu maida tsoho yaro.

Shuairat kuwa tana zaune a falo har bacci yayi awon gaba da ita se bayan azahar ta farka tayi sallah sannan ta fada wanka, wani material pitch color ta saka dinkin buba da zani ta saka danyar gwal mai kyau ta fesa turare se qamshi ke tashi. Dinning ta wuce masu aiki suna tsaye a gefe aka zuba mata rice n chicken ta fara ci a hnkli tmkar bata so sai wani yauki take. wata mata ta shigo tare da wani Dan yaro nan kuwa ta gane sultan ne nan ta sake fuska tana faraa sun karasa falon ta musu tayin abinci matar ta jawo kujera ta zauna shuairat ta rike hannun yaron tace

“Boy zo mu ci tare” ba musu sultan ya karasa gunta ta daurashi a kafa nan ta fara bashi a baki suna ci suna hira masu aiki kam se yaba halayenta suke nan da nan anty khady ma taji son shuairat ya shige ta don ba haka tayi tsammanin ganinta bah ta dauka shuairat irin matan nan ne masu girman kai da wulakanta mutane.sunyi hira sosai bayan anty khady ta damka mata amanar sultan nan kuwa ta karba ckn jin dadi Suka rabu akan anti kadi xata koma yau.

Haka shuairat ta kasance tare da sultan tana biye masa duk abunda yake so shi zatayi sunyi game sunyi kallo sunyi karatu haka Suka kasance har lokacin sallan la’asar nan ma tare sukayi sallar shuairat ta masa wanka ta canza masa kaya sannan Suka tafi bangaren momsi( Maman Mr president )

Love u alll????????
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
47
By Reefat yahya

Sun shigo falon tana tare da wasu mata su 2 nan shuairat ta gaishe su sannan ta zauna a gefe momsi kuwa wani irin dadi taji don anty khady ta shaida mata komai fuskarta dauke da murmushi ta fara Jan shuairat da hira tana tambayarta ko ta taba zuwan mayo belwa can Adamawa haka dai Suka cigaba da hira shuairat ta sake kadan suna hira sultan kuwa yana makale da ita, aka kawo musu fruits da drinks dakyar shuairat ta dau apple kwaya1 tana ci wannan ma saida momsi ta bata rai ne ta nuna mata cewa ta dauka nan gidan su ne ta daina jin kunya ta sake jikinta nan ne shuairat take tmbayar ina umaima aikuwa momsi ta zayyana mata daga biri har wutsiya sannan ta Dora da nasiha kan cewa tayi hkri da halayen da zata fuskanta gun umaimA haka dai Suka cigaba da hira har magrib sannan ta koma bangaren ta tare da sultan , bayan sunyi magrib da isha ta dibawa sultan abinci yaci ya koshi ta kunna masa cartoon yana kallo har yayi bacci nan ta daukesa ta kaisa dakin barcinta daga nan ta fada wanka.tana fitowa ta tsara wani uban kwalliya sannan ta fito da wani hadaddiyar dinner gown silver da duwatsu a jiki sai shinning suke ta sanya rigar mai dogon hannu pencil hand ya dame hannunta haka nan rigar dai-dai da jikinta ta saka wasu English diamond mai uban kyau ta daura wani red net daurin step har 6 tayi kyau sosai ta saka takalmin Vinci red color ta rike clutch purse din shima red ga red lipstick tayi kyau sosai woow….ta fesa turaren laylatul sahr da musk- almudhakkr se kuma far away , bleu feeling, diable bleue, to nyt , mekako Miami, Cuba , touch me da kuma esabella Curie.☺☺☺ turare 10…hmmmm qamshi kam baa magana ita kanta tasan ta hadu sosai.wayar intercom na dakin ne ya fara ruri ta daga wata mai aiki CE take sanar da ita cewa Mr president ya turo mota yana bukatar ganinta nan ta ajiye wayar ta kurawa fyskarta ido a ckn mirror tace

“Wow…yarinya kinyi kyau but hakan ya dace ta fita ne ko ta yafa gyale? Ahhh….turawa ne bata son su mata kallon bakauyiya don haka red net din ta dauko wani ta yafa sannan ta daurashi ta baya tayi kyau sosai????????????????.
A hnkli take takawa har ta fito falon ba kowa duk masu aikin sun koma bangaren su sai masu gadi a waje ta Tarar da bodyguard din ????????????gaba daya Suka zuba mata ido dakyar ya saita kansa ya bude mata gidan baya ta shige daga nan ya ja motar .

Bangaren saukan baki sukayi parking ya bude mata kofa ta fito tana takun kasaita ta hadu da yayanta yana fitowa murmushi ta sakar masa sannan ta wuce ya tsaya galala yana kallonta har ta bace masa da gani yana tsaye yana mamaki shi kadai. Suna zaune a dinning area da alama ita ake jira Mr president ne yake fuskantar kofa tana shigowa ya kasa dauke idonsa a kanta tmkar a mafarki haka ya ganta kurrr ya ajiye ido ya kasa motsi tana murmushi ta karasa kusa dashi ta mika masa hannu nan ya tashi yana rike da hannunta gaba dayawa turawan sun shagala da kallonta basu taba ganin bakin fata kyakkyawa irin shuairat bah.Mr President ne ya katse musu tunani ta hanyar cewa

“Pls meet my wife mrs Suleiman”
Murmushi shuairat ta sakan musu sannan tace

“Hello everyone” tare da mikawa matan hannu sun gaisa ckn faraa sannan Mr president ya jawo kujera kusa da nasa nan ta zauna tare da cewa

“Tnk u Darling”
Ckn wani tsiga tana fari da ido Mr president kam se kallonta yake tmkar wata sabuwar hallita nan shuairat ta fara musu barka da xuwa tare da basu hakurin rashin xuwanta akan lokaci, haka nan ta sace zukatansu hira sosai sukeyi ckn harshen turanci Mr president in banda murmushi babu abunda yake shuairat ta bashi mamaki sosai nan da nan Suka fito da wayoyinsu aka fara daukan selfie an dauketa tare da Mr president ma sunyi kyau sosai nan aka fara turawa a instagram da Facebook ana taya Mr president murna. Daga karshe Suka gabatar da kyaututtukansu diamonds golds da dalolin amurka shuairat de tasha kyaututtuka da dama har wajen 12 sannan kowannensu ya koma masaukin sa shuairat ta tashi zata tafi Mr president ya rike hannunta sai kuma ya rungumeta gam a jiki, mutuwar tsaye tayi ta kasa motsawa Sun share minti 3 ckn wannan hali dai2 nan john ya shigo don kulle kofa aikuwa a 360 yabar bangaren ya tsaya a waje ya rike kai yana maida numfashi . Mr president ya motsa bakinsa a hnkli yace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button