NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

“Swt hrt ke kuwa kukan me kike yi”
“My man..dole nayi kukan farin ciki saboda Abu 3”
“Menene wanna?
“Na farko ka warke Wanda har na cire tsammanin sake xama kusa da kai kamar ynxu na dauka na rasaka har abada kaga kuwa farin ciki ya zama dole”
“Hakane rahamar ubangiji kenan baya karewa ..uhmm na 2”

“Na 2 kuma adu’oin da ka jera tabbas duk macen da ta samu irin wannan aduar a bakin mijinta toh lallai tayi dace a duniya babu kamarta..kaga Allah yana amsa aduar miji ga matansa kaga dole nayi murnan samun wannan Alhamdulillh ko ynxu nabar duniya nayi dace”
“Uhmm…Ayshata kenan.. Allah ya miki albarka, idan har ta hanyar kyautatawa miji ake shiga aljannah toh na daga kafata..Allah ya baki jannatul firdaus..tabbas kin cika alkawarin da kika dauka na cewa komin tsanani komin wuya komin dadi kina tare dani bazaki barni ba har abada,
[2/21, 2:41 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
68
By Reefat yahya

Mr president ya cigaba da cewa
“Tabbas da ace duk matan duniya halayensu irin naki ne da lallai zaman lfy xata dore a kowane gida ..Allah ya miki albarka Allah ya barmin ke har a gidan aljannah”
Ya kara kankameta yana me kuka shuairat ta kwantar da kanta a kirjinsa tana jin bugun xuciyarsa , a hnkli ta daga kai tace
“Mr president kawo kunnenka “
Ba musu ya kai kunnensa dai2* saitin bakinta a hnkli ta furta
“Am pregnant”
???????????????????????? ya xare ido sai kuma ya fara hawaye ya rungumeta gam a jiki yana kuka tamkar karamin yaro
“Haba my man..me abin kuka a ciki ? Kai da zakayi farin cki “
“Kuka ya xama dole Ayshata..bansan wane irin farin cki nake bah tabbas babu abun bautawa da gaskiya sai Allah kuma Muhammad manxonsa ne..Allahu Akbar! Allah mai ikon komai da kowa..yau ni Suleiman matata tana dauke da ciki? Allah nagode maka ..dama da rabon xan sake ganin jinina a doron kasa ..Allahu Akbar”
Haka mr president ya cigaba da sambatu Dakyar shuairat ta lallaba shi ya daina kuka har ya bata tausayi..eyya mr president????.daga nan ya tashi ya wuce bayi ya daura alwala ya fito ya fara nafila yana godiyarsa ga ubangijin talikai, shuairat ta kwanta a gefe tana kallonsa tana jinjina masa sabida ya kasance daga ckn bayi masu nuna godiyarsu ga ubangijin da ya haliccesu..bacci ne yayi awon gaba da ita a yayinda mr president kuwa yacigaba da nuna godiyarsa ga ubangiji.


Shukrah tana xaune a falo sai hura hanci take tana cika tana batsewa bash ya fito daga dakin bacci ya kalleta sau1 ya kawar da kai gefe yana mmkin wasu halaye irin nata ..
“Wllhi ina kan bakata, idan har bazaayi tafiyan nan dani bah toh sai dai kaima ka hkura don bazan yarda da wannan salon yaudaran bah..uhmm inaji ina gani ka dauko wata can ka tafi da ita turai da sunan zakuje duba jikin mahaifinta salon kuje kuyi soyayya a can koh..toh ban amince bah'”
Sai ynxu ya juya ya kalleta sosai ya girgiza kai yace
“Wai dama haka halinki yake ne shukrah? Kodak kin fara bin xugin kawaye ne? 4Allah’s sake shukrah ina matsayin mijinki mu haifi waleed amma ace har yau baki yarda dani bah? Yaushe zaki daina zargi na ne..bayan kinsan cewa aure da zargi babu kyau”

“Kaga malam..ni ba jahila bace da zaka min wa’azi ehen, bazaka fake kana min dadin baki bah kawai ka fito fili ka gayamin aurenta zakayi ba sai ka tsaya yin wani kame2* bah”
“Allah sarki..yau kuma ni nake kame2* shukrah! Lemmi ask u..idan ina son umaima wai tsoronki zanji? Ko kina tunanin cewa idan ina son aurenta wannan haukan taki xata hanani yin abunda nayi niyya?”
“Koma menene..tafiya ce baxa ayi bah “
Ran bash ya baci sosai gskiya shukrah ta canza amma dole ya ja mata birki ( mata a kiyaye..wannan kishin hauka ne kuma hakan yake kara tunxura miji har yayi aurenda be shirya yi bah Allah yasa mu dace ameen).
Ya tashi kai tsaye dakin umaima ya wuce fuu..shukrah tabi bayansa, umaima tana kwance bash ya shigo tare da sallama ta gyara zaman ta kenan shukrah ta shigo kamar wata zakanya????????????(Wa ya gamin anti rabi ana kishi????)
Bash yayi banza da ita yace
“Umaima hop kin gama shiryawa cos jirgin 8pm zamu bi”
“Na gama but yaya I tot tare zamu tafi dasu sultan da gran mah”
“No..I change my mind mu 2 kawai zamu tafi su kuma jirgin 7am na safe zasu bi , zamu jira su @ Beijing”
“Ok..Allah ya kaimu”
Basuyi aune ba sai ganin shukrah sukayi ta makure umaima a jikin gado tana huci ta fara magana
“Shegiya munafuka..wllhi mijina yafi karfinki kije can….
Bata karasa ba taji saukan mari Tass! A fuskarta ba shiri ta sake umaima ta juya tana kallonsa tmkar a mafarki wai yau bash ne ya daga hannunsa ya mareta? Hawaye ne Suka cika mata ido a hnkli Suka fara sauka
“Shine ka mareni? Ak..kan ..akan wannan yarinyar? Baban waleed?
Ya runtse ido ckn jin zafin abunda ya aikata.shukrah ta juya tabar dakin shi kuwa ya jingina da bango kansa na kallon kasa, umaima kam tayi Kim..tmkar gunki ta rasa me xatayi tabi bayan shukrah ko kuwa ta tsaya gun bash? Shiru ya ziyarci dakin a hnkli ta karasa kusa dashi

“Yaya bash kayi hkri laifina ne da nazo gidanka..na hanaku kwanciyar hnkli am sorry”
Hannu ya daga mata ya juya yace
“Ki shirya ynxu xamu bar gidan nan”
Daga nan dakinsa ya wuce ya shiga bayi ya watsa ruwa gaba daya ransa a bace yake , ckn kankanin lkci ya gama shirinsa ya dauko wani Dan karamin jaka dakin shukrah ya shiga tana kwance rub da ciki tana kuka Mara sauti waleed kuwa yana gefe sai sharar baccinsa yake ckn kwanciyar hnkli.
Ya karasa kusa da ita yace
“Am sorry..nayi kuskure ki yafe min ni zan tafi kiyi hkri”
Daga nan ya ajiye mata rafar yan 1k ya juya ya fara tafiya har ya kai bakin kofa ya tsaya cak! Yace
“Ki gyara kwanciyar ki Allah yana fushi da masu irin wannan kwanciyar”
Daga nan ya tura kofa yayi ficewarsa shukrah ta cigaba da kukan da take.umaima ta fito da jakar kayanta ta sanya a mota bash ya ja Suka wuce gidan iyayensa don yin sallama dasu.


   Shuairat ta caba ado tana xaune a gaban mirror mr president ya fito daga wanka bayan ta taimaka masa ya kimtsa Suka fito falo sai kallonta yake ya lura cewa tana ckn nishadi yau ya juya yace

“Nana Aysha !
“Sir! ta amsa tana murmushi, saida yayi dariya sannan yace
“Sir! Kuma? ..anyway na lura dake yau tun safe kike ckn nishadi ko meyasa?
“Hmmm..ba komai fah haka nan nake jin kaina ckn annashuwa “
“Kin tabbata?
Kai ta gyada tace
“Na tabbata sir!
“Hmm..ke din ne somtymz u r amazing, kuma am sure u ar hiding somtin baki son gaya min koma menene dai nasan gud news ne”
Murmushi kawai tayi bata CE masa komai ba tana duba agogon hannunta , bayan 30min aka kwankwasa kofa shuairat ta mike a hnxarce ta bude kofan tare Suka hada baki wurin cewa
surprise!!!
????mr president ya tashi ckn tsananin mamaki yana binsu da ido..ko a mafarki bai taba tunanin ganinsu a wannan lokaci bah..
Bash, umaima, sultan, momsi, daddy da kuma baban shuairat.. Wow wani farin cki ne ya lullubesu wen last Suka hadu irin haka…

Muje xuwa????????????
[2/21, 2:41 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
69
By Reefat yahya

Gaba dayansu Suka dugunxuma ckn falon mr president kuwa murna ne har ya rasa ina zaisa kansa ya kankame daddy kamar xai shige jknsa momsi tana dariya, sultan kuwa da gudu ya fada jkn shuairat yana cewa
” I rily miss u mom Nah”
“Miss u mor my son”
Mr president ya raba jkinsa da na daddy ya jawo sultan ckn sauri yana cewa
“Boy kayi a hnkli kada ka ji wa kaninka ciwo”
“Wane kanin dad?
Ba sultan kadai bah ..duk wadanda suke ckn falon sun maida kallonsu ga mr president shi kuwa ko a jikinsa ya cigaba da cewa
“Sultan mom tana dauke da ckn kaninka very soon zata haifa mana baby koh”
“Wow…da gaske dad? Am so happy nima na huta da gorin frenz dina a skul “
Daga nan sultan ya koma gun shuairat ya sake kankameta ckn hanzari mr president ya sake rabasu shuairat kam kunya yasa ta bar falon ya shige bedroom.
Momsi da daddy kuwa wani farin cki ne ya lullubesu umaima ma haka , daga nan Suka zauna aka gaisa har ynxu shuairat bata fito bah momsi tana hararar mr president tace
“Kaga rashin kunyarka yasa ka korarar min ya’ ko gaisawa bamuyi bah..anyway Allah ya raba lfy ya Baku zuri’a dayyibah”
“Ameen momsi nagode”
“Hooo..dad ko kunya babu”
Umaima CE ta fadi hakan gaba daya Suka sa dariya bash kam sai faman murmushi yake haka nan baba shikuwa yana son ganin ya’rtasa.momsi CE ta tashi ta nufi dakin a hnkli ta tura kofar shuairat tana xaune tayi jugum momsi ta rike mata hannu suna fuskantar juna tana murmushi tace
“Allah ya miki albarka ya’ta nagode sosai da irin kulawar da kike bawa dana Allah yasaka miki da gidan aljannah ya sauke ki lfy ya albarkaci abunda zaki Haifa”
Sunkuyar da kai tayi ckn tsananin jin nauyinta momsi ta cigaba da cewa
“Tabbas kin zame mana alheri a Rayuwa ..kin dawo da farin ckn mu , kin cancanci yabo a garemu mun gode Allah ya saka.tashi muje ki gaisa da mahaifinki nasan yana bukatar ganinki”
Ba musu ta tashi Suka fice xuwa falo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button