NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

Shiru sukayi dukkansu biyu daga karshe shuairat ta tashi zata fita yace
“Ina zaki ?
“Uhmm..falo zan koma can xan kwanta”
Wani irin kallo ya watsa mata ba shiri ta dawo ta xauna
“So kike ki tonamin asiri ko me? ..as from today ki tattara kayanki ki dawo nan da xama”
Ckn Sauri ta kura masa ido ya kada kai yace
” yes! Ki dawo nan mu xauna tare kinga babu wanda xaiyi magana koh, oya ki hau gado ki kwanta ba sai kinje falo bah”
Ba musu ta cire hijabinta ta hau saman gadon ta kwanta a gefe tayi aduointa ta shafa sannan ta rufe ido tana son bacci Amma ta gagara she is not comfortable.
Mr president kuwa ya tashi ya fada bayi ys watsa ruwa sannan ya fito ya saka kayan baccinsa ya fesa turare sannan ya kwanta a gfenta bata rufe da bargo ba ya kura mata ido na yan dakika sannan ya dauke kai.baccine yayi awon gaba dasu can tsakiyar dare ta mirgina ta koma kusa dashi ta kankame shi gam wutar dakin a kashe yake, ckn bacci mr president yaji alamar mutum a jikinsa a hnkli ya bude ido ya kunne side lamp tana baccinta ckn kwanciyar hnkli ya kura mata ido tana sauke numfashi a hnkli tayi masa kyau sosai ya juya zai kashe wutar ta Dan motsa nan ya koma ya kwanta a hnkli shima ya kara rungumarta.
Da asuba ita ta fara tashi a hnkli ta zame jikinta daga nasa ta fada bayi zama tayi a ckn bahon wanka tana lumshe ido tana tuna halin da ta farka ta gansu a cki, tana mamaki ya akayi hakan ya faru? Dakyar ta daure tayi wanka tare da yin alwala ta fito har ynxu baccin yake ta tsaya Jimm…hannu tasa a gefen fuskarsa tana shafawa a hnkli take ya bude ido tace
“Morning… Tym din sallah yayi”

Daga nan ta tada sallah tayi nafilfilu sannan tayi sallan asuba ta xauna tana Jan carbi ya fito ya gabatar da sallah haka Suka kasance har rana ta fito shuairat ce ta nade sallayar ta xauna a gefe tace
“Ina kwana”
“Lfy ya kike”
“Lfy alhamdulillh”
Da tashi ta kama hanyar fita dakin
“Ina zaki ?
“Nayi wanka Xan je dauko kaya a…
“Dawo ki xauna xaa kawo miki”
Ba musu ta koma kan gado ta xauna tana wasa da yan yatsunta.
Falo ya nufa bayan yan mintoci ya dawo ya shige bayin da alama wanka zaiyi.motsi take ji a falon ta fito don ganin waye ne ga mamakinta akwatunan ta aka jera da sauran kayayyakin da ta mallaka a dakinta , wani dakine da yake kusa da na mr president a can Suka shigar da kayan sai kuma mata masu aiki Suka shigo Suka gaisheta sannan Suka shige dakin take Suka ajiye komai inda ya dace Suka gyara dakin se qamshi ke tashi daga aka hada musu abinci a dinning.
Tsarin dakin ya birgeta kwalliya ta fara yi bayan ta gama ta saka wasu material masu kyau daga nan ta yafa veil ta wuce bangaren da momsi take Suka gaisa se kuma daddy shima ya fito ta ritsina ta gaida shi.sultan ya fado mata a rai a hanya Suka ci karo dashi yana ganinta a guje ya fada jikinta yana cewa
“Anty ina kika je nida jummai muka kwana jiya” ( jummai ya’r aiki CE)
Tana shafa kansa tace
“Sorry boy muje kayi brkfast koh”
Daga nan Suka wuce bangaren mr president don karya kumallo.

Bayan kwana4 su daddy sukayi sallama akan cewa zasu koma , momsi kuwa ta ajiye mr president da shuairat tayi musu nasiha sosai akan zaman ta kewar aure daga nan Suka fara shirin komawa.

Love u all….????????
[2/21, 2:40 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
57
By Reefat yahya

Shuairat tana zaune a falo tana danna wayarta da alama chatin takeyi mr president yana office ynzu saura masa 1yr regime dinsu ya kare cos an fara shirye-shiryen zabe na gaba ana son ya fito Dan takara shikuwa baya so yace mulkin ya ishesa haka.
Umaima CE ta shigo ckn gadara da nuna isa ta zauna a daya daga ckn kujerun ta kalli shuairat da wani irin kallon raini sai kuma ta fashe da dariya, shuairat bata juya ta kalleta bah ta cigaba da chatting dinta
“Ke munafuka bakiji shigowata bane bazaki gaisheni bah”
Nan ma bata kulata ba kawai shuairat taji wani wawan mari a fuskarta dankari ko iyayenta basu taba wanka mata mari irin wannan bah..ba tare da dogon tunani bah ta daga hannu ta rama dai-dai nan mr president ya shigo falon
“Subhanallah Aysha meke faruwa”
Nan umaima ta rike kunci ta fashe da kuka sannan ta fada jikin mahaifin nata tana rusa uban kuka mr president yabi shuairat da wani irin kallon tuhuma ransa ya baci kwarai da gaske shuairat ta kawar da fuska gefe..
“Aysha wannan shine amanar da na danka miki? Dama zaman da kukeyi kenan idan bana gida ko nayi tafiya…

“Dad wllhi kullum se ta mareni ta kuma zagi iyayena , ba hali inyi magana cos babu Wanda xe yarda…dad don Allah ka bata hakuri idan wani laifin na mata kuma don Allah ta daina zagin mom ….
Ta karasa maganar ckn kuka ran mr president ya kara baci sai tafarfasa xuciyarsa ke yi shuairat tace
“Mr president…..
Hannu ya daga mata alamar baya son jin komi daga gareta daki Suka wuce yana rike da hannun umaima se kukan munafurci take yi.ran shuairat ya baci tayi mamakin rashin adalci da aka nuna mata ido da ido, dakinta ta wuce ta fada kan gado tana rusa kukan bakin ciki.
Yinin ranar tayishi ne a dakinta abinci ma bata fito ta ci bah mr president kuwa ya lallaba umaima ta koma bangarenta tana jin dadin abunda ya faru ko a banza ta shiga tsakaninsu Ashe dai dad yana sonta.
Mr president ya dawo da dare yana cin abinci ya jira fitowar shuairat Amma shiru babu labarin ta ladi ya kira yace a kira shuairat ta fito taci abinci nan ladi ta shaida masa cewa bata ci abincin rana bah kai ya gyada ya koma dakinsa zama yayi akan gado ya fara tunani tabbas baiyi adalci bah kamata ace ya tsaya yayi bincike Amma Sam ya rufe ido ya nuna yafi son ya’rsa hakan babu adalci Sam.a hnkli ya taka xuwa gaban hotonsa da Maman umaima yana shafa hoton yace
“Zainab ki gafarceni Tabbas na zauna lfy dake Amma ban taba jin sonki a xuciyata kamar yanda na fara jin son Aysha bah, na yarda da maganarki idan abubuwan da kika fada min a baya hakane toh lallai na fada tarkon so…ckn kankanin lokaci namanta dake ya daina yawan tunawa dake ya daina xubar da hawaye a kan rashin ki…am sorry”

Hawayene Suka fara gangarowa yana lumshe ido yana tunanin cewa dama haka so yake? Tunda yake a rayuwarsa bai taba shiga yanayi irin na ynxu bah..lallai yayi nisa ckn tarkon so yana son Aysha bazai iya rabuwa da ita bah.nan ya juya ya fito direct dakinta ya nufa ya tura kofar a hnkli tana kwance ckn wasu kananan kaya skinny jins da red top gashin kanta a ya rufe mata fuska…wow???? mr president ya tsaya tamkar statue shi bai taba ganin kyawunta irin na yau bah, bata San ya shigo bah ta juya kenan Suka hada ido tayi saurin kawar da kanta gefe a hnkli ya taka xuwa kan gadon ya xaune a gefenta

“Look Aysha! Am sorry ..nasan banyi adalci bah I shul have…
“Me laifin ka ? Don ka nuna ka goyi bayan ya’rka? No..ko kadan I din blame u, am just…
Bata karasa ya rungumeta gam a jiki hawaye na malala a fuskarsa wani ajiyan xuciya tayi itama kuka Mara sauti takeyi
“Am so sorry my lady..pls kada kiyi fushi dani , muje kici abinci koh”
Ya sassauta rungumar ya daga kansa yana kallonta a hnkli yasa hannu yana share mata hawayen da suke fitowa ya sake cewa
“Am sorry pls…
“Is ok! Nima ka yafemin kuma…

“SHhhhh…bakiyi laifi bah ki kwantar da hnklinki now let’s go n eat”
Ba gardama ta tashi hannunsu sarke da juna Suka fito falo bata damu da kayan da suke jikinta ba don tasan cewa babu Wanda zai shigo a wannan lokacin.a dinning area Suka xauna kan kujerun table din suna fuskantar juna ya xuba mata abinci ya tura a gabanta ta fara ci a hnkli tabbas taji yunwa ba kadan bah, suna ci suna kallon juna a haka har Suka gama sannan Suka koma daki sun fara shirin bacci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button