NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

“Anti wllhi jinin yaki tsayawa kuma Dr ya gayamin cewa pills na tsarin iyali da nayi amfani dasu su Suka jawomin wannan matsalar”

Tayi shiru da alama tana sauraron me ake gaya mata daga dayan bangaren sai kuma tace
“Ni ba wannan bane matsalata..cewa yayi dakyar idan zan sake haihuwa saboda mahaifar ta lalace”

“Innalillahi wa innailaihi raji’un..abunda bash yake nanatawa kenan.hawayene ya fara gangarowa bisa kuncinsa ya runtse ido, shukrah ta cigaba da cewa

“Idan yaji wannan maganar nasan sakina xaiyi..kuma wllhi iyayena ma zasuyi fushi dani, pls anti ki taimaka min yau ya zanyi? ..wayyo Allah na wllhi sharrin shaidan ne da kuma fa….
Bata karasa ba taji takun mutum a bayanta ckn hanzari ta juya Suka hada ido ya bita da wani mugun kallon da bata ganin irinsa bah????????????????
Wani gumi take hadawa ga fuska chabe2* da hawaye ba shiri ta sake wayar hannunta ckn raxana…….

…nima na ajiye tawa wayar

Hmmm ya bash zaiyi da ita?
Sakinta zai yi ?
Wane mataki zai dauka?
Ku biyoni…Lov u all????????
[2/21, 2:41 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
81
By Reefat yahya

Hawayene yake gangarowa a fuskar bash ya durkusa a gaban shukrah yana kuka yace

“Shukrah me na tsaremiki a Rayuwa …wace irin tsana kike min da har yasa bakison hada jini dani..wane irin laifi na aikata da nayi deserving irin wannan punishment din tell me plsss…”
Ya karasa maganar yana kuka me ban tausayi shukrah ta xauna dabas a gabansa ta cigaba da kukanta tace
“Yaya don Allah ka yafemin nasan na aikata laifuka da dama a gareka amm…

Bai bari ta karasa ba ya dauketa da wani wawan mari xuciyarsa se tafarfasa take nan ya tashi yabar dakin..shukrah ta cigaba da rusa kuka ta nadamar abubuwan da ta aikata masa itakam fatee ta cuceta kuma laifinta ne daga haduwa da mutum a watsap se ta biye mata ta rusa farincikin gidanta..kuka sosai takeyi tana jawa fatee Allah ya isa ( ni Reefat nace ..ohh dama ke bakida tunani ne kawai daga haduwar watsap…mtsww???????????? duk masu biyewa kawayen banza haka zasu kare ..Allah ya tsare mu da sharrin mugayen mutane)
Bash yana fita ya shige motar sa ya hada kai da guiwa yana kuka tamkar karamin yaro , ya share minti 30 yana kuka sannan ya fara kiran sunayen ubangiji ya dan samu sauki a ckn xuciyarsa daga nan yaja motar be tsaya koina ba sai gidan mahaifinsa.ya fito ckn sanyin jiki ya karasa ckn gidan waleed ne ya rugo da gudu ya fada jikinsa yana cewa

“Oyoyo Abba Nah “
Murmushn karfin hali yayi nan kuma ya tuna da zancen shukrah ya jawo yaron ya kankameshi sosai a jiki nan hawaye ya malale fuskarsa , mama CE ta fito daga daki tana Neman waleed turus…taja ta tsaya bata taba ganin dan nata ckn wannan halin bah .tayi gyaran murya tace

“Waleed kaje daki ka jirani ina xuwa”
“Yawwa mama..zaki bani sweet koh”
“Ehh..je ka xauna banda kiriniya gani nan xuwa ynxu xan kawo maka sweet har da chocolate”

Yaron ya hau tsalle nan ya sake uban nasa ya ruga aguje xuwa dakin mama , bash ya xauna kasan carpet yayi shiru ya kasa furta komai.mama kuwa ta juya xuwa dakin mijinta ta kirasa tare Suka fito bayan sun zauna baba yace
“Ni bazan nemi jin matsalar ka bah..koma menene kayi kokari ka kasance mai juriya da jajircewa, shi zaman duniya iyawa ne kuma mai hakuri shi zai dafa dutse har yasha romonsa..Dana! Na dade da gane cewa kana ckn matsala tun ba yau bah na lura da ramar da kakeyi nasan kana ckn damuwa kwarai da gaske kuma naji dadi da ka iya rike sirrin aurenka alhamdulillh ..hakan na nuna cewa ko bayan raina xaka iya rikemin iyalina”
Ya dan ja dogon numfashi sannan ya cigaba da cewa

“Nasan damuwar tsakaninka da matarka ce sabida baka rasa komai na rayuwa bah..don haka ina mai baka shawara ka cigaba da Hakuri wata ran zaizo karshe koma menene matsalar kayi kokari ka shawo kanta”

Bash yayi shiru ya jingina da kujera yana nazarin kalamn mahaifin nasa sannan ya share hawaye Muryar mama yaji tana cewa
“In banda shashanci matarka CE zata sa ka kuka kamar wani karamin yaro? Ai nasan dama zaa rina don ni kaina shukrah ta fara nunamin rashin kunya bare kai…dama Allah yayi ka shiru2* ba dole ta hau kanka ta xauna bah..tirrr! Allah wadai da mijin da zai xubda hawayensa saboda mace”

“Haba Fatima..ke da xaki bashi hakuri ki gyara tsakaninsu Amma kuma kina…
“Ah-ah Alhaji..abun ne da ban haushi wllhi, dubi yanda yaron nan yake zubar da hawaye tamkar wanda ya rasa iyayensa..toh wllhi bazan lamince hakan bah, don kawai ina zuba ido bana magana? Wllhi hakuri na ya kare dole na dau mataki akanta”

Baba yayi murmushi yace
“Kai mataa..halinku da tunaninku duk iri daya wllhi..toh in banda abinki Fatima kinsan me ya shiga tsakaninsu ne da har kike ikirarin daukan mataki?”

“Koma menene ai nasan ba karamin Abu bane zai sashi kuka irin haka”
“Wannan duk ba matsalar ki bace ..kuma babu ruwanki da maganar”
“Ya zakace babu ruwana a cki..dana ne fah?
“Sannu masu da’ ..”
Bash kam haushin kansa yakeji meyasa zai dagawa iyayensa hankali? Nan yayi gyaran murya yace

“Baba ..mama..Ku gafarceni maganar bata kai haka bah..ni aure nake son karawa ina Neman amincewar Ku”
“Dakyau yarona..Allah ya maka albarka , haka ake son namiji ya kasance mai xuciya ba wai ka xauna da mace daya tana wulakanta ka bah..haba ga mata nan birjik. …gaskiya naji dadin wannan zancen”
Mama CE tayi wannan furucin ckn jin dadi ta juya tana kallon mijin nata ya watsa mata harara yace

“Yanzu ke idan nace zan kara aure zaki amincene ?
“Aure? Hmmm..Alhaji kenan! Ya kake magana kamar karamin yaro”
Maganar taso bashi dariya ya gimtse yace

“Toh ni ban amince da auren bah..matukar kika dage kuwa nima auren zan kara”
Yana gama fadin haka ya juya yabar falon mama ta bisa da ido ta tabe baki tace

“Kaji dashi..masifaffe kawai”
Nan ta maida hankali gun bash tace
“Kana jina koh…matukar ka tabbatar da cewa baka jin dadin zama da shukrah toh ni na baka dama ka kara aure, domin bazan shiga hakkinka bah..mu muka hada aurenku da shukrah kayi biyayya bakayi gardama bah don haka yanxu ina baka goyon baya ka auri duk wacce kake so..Allah ya tabbatr da alkairi ya kuma xaba maka mace ta gari “
Yaji dadin kalamanta sosai yace

“Nagode mama insha Allah zanyi yanda kika ce…ke dai ki cigaba da min adu’a”
“Ba damuwa tashi kaje ..Allah ya maka albarka ya baka nasara akan abunda kayi niyya..Amma pls ban amince maka da sakin shukrah bah, duk irin laifin da maka kada ka kuskura kace zaka mata saki kaji koh”
“Nagode mama insha Allah zan kiyaye..Amma kina ganin baba zai amince kuwa bayan ya nuna baya so”
“Barni dashi zai sakko ne ..kaidai ka cigaba da Neman auren naka zan tayaka da adua”
“Ok Nagode mama “
Daga nan ya tashi ya shige dakinta sai ynxu yaji sauki a ckn xuciyarsa , abinci ya nema yaci sannan ya fara hira da waleed yana biye masa sunata shirme.

*saura kwana 2 tafiyar tasu sun gama duk wani shirin da zasuyi umaima sai xumudi ake don kuwa tana matukar son kasar China …da dare mr president da shuairat Suka je yin sallama da iyayen shuairat , a falo Suka tarar dasu a zaune suna kallon news har ynxu baba yana fushi akan maganar auren bash..bayan sun gaisa mr president ya sanarda baba zancen tafiyar da zasuyi baba yace

“Ohh..ni bello! Mutanene sai yawace2* yau kuna nan gobe kuna can..wai Baku gajiya ne”
Dariya sukayi shuairat tace
“Baba yaushe mukayi tafiya? Tun bayan dawowarmu daga hong Kong fah babu inda muka sake xuwa”
Baba ya jefa mata wani irin kallo yace
“Watannin salman nawa? Ba uku bane ko hudu..bayan komawarki gidan kunje Lagos ..yola..mayo..maiha..mubi..kano ynxu kuma zaku tafi kasace sunkai biyar”
Dariya sosai suke yi shuairat tace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button