NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

“Daddy wata alfarma nake nema”
“Fadi bukatarki ya’ta”
“Daddy xancen auren nan da xaayi ina ganin gara a hakura “
“Sabida me?
“Umm..umaima bata son auren tana da wani Wanda take so”
Dariya yayi sannan ya juya yana kallon mr president Wanda tun da Suka fara maganar bai sanya bakinsa a cki bah..daddy yayi murmushi yace
“Wato mijin naki ne ya turaki koh”
Shuairat tayi saurin girgiza kai tace

“Bahaka bane daddy, kawai gani nayi umaima…
“Aysha!
“Naam daddy”
[2/21, 2:42 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
90
By Reefat yahya

Daddy ya cigaba da maganarsa
“Aysha kada ki biye ma mijinki , shi boko yasa a gaba idan na biye masa cewa xaiyi sai ta gama masters b4 ya aurar da ita”
“Daddy bahaka bane..dama
Hannu ya daga mata nan tayi shiru da bakinta..yace
“Zancen aure babu fashi , kuma na fasa jiran ta gama makarantar ma..bari Alhajin ya shigo”
Shuairat xata CE wani Abu baban ismaeel ya shigo tare da sallama daddy yace a kira ismaeel a waya su taho da umaima.
Yana can xaune a falon har ynxu babu umaima babu labarinta wayarsa ta hau ruri mahaifinsa ne ya daga yace
“Ku samesu a falo”
Daga nan ya kashe wayar ta tashi ya wuce falon da suke.ya karasa cki tare da sallama bayan ya xauna daddy yace
“Ina umaima?
“Uhm..tun dazu ta tafi, wani uncle waye..uhmm
Shuairat tayi carab tace
“Lahh..har ynxu basu dawo bah..dama ni nace suje ta xabi kalan furniture’s da take so ita da uncle bash”
Idanunta Suka fada ckn na mr president ya harareta tayi Sauri ta tashi tsaye tace
“Bari na kirasu daddy ina zuwa”
Daga nan ta fice bata jira jin amsar su bah.
Bangaren baki ta fara xuwa tana nemansu taji murya kasa2* a dayan dakin nan ta tura kofar fuska a murtuke ta samesu suna xaune suna hira ckn kwanciyar hankali harara ta watsa musu tare da cewa

“Sai ku nuna ma duniya akanku aka fara soyayya”
Umaima ta tashi ta karasa kusa da ita
“Lfy mom sultan”kwafa tayi tare da cewa
” zaku gane ai ..kixo ana Neman ki”
Jikinsu yyi sanyi bash yace
“Sisy any progress?
“Wane irin progress..Abu yana Neman tabar barewa”
“Wat hpn”
“Muje dai kuji da kunnenku”
Daga nan ta juya tayi tafiyar ta umaima da bash kuwa sunyi jugum kowannensu yana tunani daga bisani Suka wuce falon.
Bayan kowa ya xauna daddy ya fara magana

“Ismaeel ina fatan babu matsala”
“Ba komai Abba mun daidaita mun amince da juna”
Ckn Sauri umaima ta daga kanta sukayi ido 2 dashi ta sake sunkuyar da kan, daddy ya cigaba
“Masha Allah..dama haka muke son ji Allah ya muku albarka”
“Ameen” kowa ya amsa banda bash da umaima
“Ynxu tunda sun fahimci juna ni na saka rana nan da wata 1 “
Tare Suka hada daga kai suna kallon juna babu Wanda ya lura dasu sai mr president ya kawar da fuskarsa tamkar baisan meke faruwa bah..hawayene Suka fara gangarowa a fuskar umaima ba shiri ta tashi tabar falon baban ismaeel yace

“Meyake damunta Alhaji naga kamar kuka take yi”
Murmushi daddy yake w
Sannan yace
“Babu komai nasan ta tuna da mahaifiyarta ce”
“Ka tabbata..? Kodai bata son auren ne”
“Ko kadan ..nasan tunowa tayi da marigayiya zainab Allah yajikan ta yasa ta huta”
“Ameen”
Haka Suka cigaba da hira bash ma barin falon yayi ya koma bangaren baki ya xauna ya buga uban tagumi yana Neman mafita.
Jirgin yamma su daddy Suka bi Suka koma Lagos mr president ma hankalinsa yaki kwanciya sai ynxu ya fara jin tausayin Ya’r tasa shi da kansa yaje har daki ya sameta yana bata hakuri dakyar ta daina kukan da take.

****bayan kwana 2 bash ya kwanta zazzabi ya rufeshi ya tare a gidansu yaki komawa gidansa , kullum shukrah tana xuwa dubansa ko kallo bata ishe sa bah.gashi umaima ta kashe wayoyinta gaba daya hnklinsa a tashe yake mama tana masa nasiha akan ya rungumi kaddaara Amma Sam baya sauraronta ya xama kamar wani xautacce daga karshe ya tashi ya shirya ckn kananan kaya yayi kyau sosai duk da ramar d yayi ya fada sosai , mama ta shigo dakin rike da magungunasa ckn mmki ganin yana fesa turare da alama fita xaiyi tace

“Babana ina kuma xaka je ..kaida baka da lfy”
“Na warke mama..”
“Toh ina xa ka?
“Zanje ganin umaima domin wayoyinta a kashe suke, xan duba ko lfy”
“Lfy kalau suke dazu munyi waya da Ya’r uwarka da akwai wani Abu ai kasan xata gaya min”
“Naji…Amma nikam sai naje”
Daga nan ya xare makullin mota yyi ficewarsa.
Umaima tana xaune a dai2* windon dakinta taga shigowar motar bash nan kuwa da gudu ta fito har tana tuntube masu aiki sai kallonta suke bata kulasu bah tayi hanyar last floor na kasa a bakin kofa Suka ci karo turus yaja ya tsaya…sun Dade sun kurawa juna ido daga bisani yayi karfin hali yace

“Meyasa zaki kashe min waya?
“Uhmm…dama
dama me? Just tell me dat baki damu da halin da muke cki bah, kina nan ckn kwanciyar hnkli ni ko ina fama da jinya”
Wato Kalmar da tafi tsana kenan a ce duk son da take masa Amma se ya goranta akan shiyafi damuwa da ita….
Idanunsa sun kada sunyi ja yace

“Umaima nasan kina sona Amma tsoronki ya hana ki fito fili ki nuna musu cewa baki son auren ni kike so ki aura y??
Kuka ta fara Mara sauti ya harde hannunsa a kirji ya tsaya yana kallonta daga bisani yace

“Mafita xaki kawo ba kuka bah pls”
ta cigaba da kukan
“Haba mana bby u knw I hate doz tears ki bari pls bana son ganin ki ckn wannan hali”
Ckn Muryar kuka tace

“Toh Bb ya xanyi..wane mafita xan kawo ? Ni gaba daya kwakwalwata ta toshe na rasa samun mafita kuma next week ance xaa kawo lefe”

“Wat??????????? next week? U know wat umaima kawai ki kira yaron ki CE masa baki sonsa kina da wani daban , daz d only solution”
“Bb ar u sure it’ll work?
“Am very sure baby Nah try it”
“Ok muje na dauki phn dina yana can daki”
“Ok lets go”
Daga nan ta shiga gaba yana biye da ita a baya Suka haura xuwa sama don daukar wayarta.

Shin xata kira ismaeel kuwa??
Zai amince da bukatar tata??
Hmmm…muje xuwa
Lov u all????????
[2/21, 2:42 PM] Reefat: ???? NI DA SHUGABAN KASA????
91
By Reefat yahya

A hanyarsu ta xuwa daukar waya Suka ci karo da shuairat tabi su da wani irin kallo sannan tace
” dad naki yana son ganinki ynxu”
Gaisawa sukayi da yayan nata sannan tayi wucewarta sum sum umaima ta tafi falon baban nata yana xaune da jarida a hannusa ta shigo tare da sallama ta nemi waje ta xauna
“Gani nan dad”
“Ki shirya gobe zaku wuce Dubai shopping Ke da Aysha”
A hnkli ta daga kanta tana kallonsa sannan tace
“Dad…
“Bana bukatar jin komai daga gareki tashi ki tafi Allah ya Baku xaman lfy”
Kuka ne ya kubce mata da gudu tabar falon a hanya ta hadu da bash yana tsaye ya jingina da bango da alama ita yake jira..
“Lfy my bby “
bata iya furta masa komai bah ta wuce bangarensu a kujera ta fada tana kuka mai ban tausayi bash ya shigo ckn tashin hnkli ya xauna kusa da ita ya fara magana ckn kwantar da murya
“Bby kullum ina gaya miki bana son wannan kukan naki amma baki ji pls stop it”
Haka ya cigaba da bata baki dakyar ta sagaita kukan ta sanar masa abunda yake faruwa shiru basheer yayi yana jin wani radadi a ckn xuciyarsa ya rasa ma wani mataki xe dauka daga nan ya tashi ya fita ba tare da ya furta ko kalma daya bah.
Umaima ta cigaba da kukan da take bash kuwa bai tsaya ko ina bah sai gun mahaifinsa wani sabon hauka ya tada musu mama kam se kuka take tana tausayawa dan nata , suna lallabashi tamkar kara tunxura shi suke baba ya rasa ya zayyi kawai ya fice ya koma dakinsa ya xauna. Mama ce ta cigaba da rarrashinsa dakyar ya tashi ya ci abinci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button