NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

????????????lov u all
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
45
By Reefat yahya

Da misalin Karfe 9 na safe masu aiki sun gama gyara komai na gidan sai qamshin air freshener ke tashi an jera abinci kala-kala a dinning table.building din dakuna 4 a sama da babban falo a tsakiya da dinning table mai kujeru6 sai kuma dakuna 3 a kasa da kitchen da kuma dinning mai kujeru 10 ga wani tangamemen falo da kujeru duma2 har set 4 kai kayan more rayuwa dai an narkasu a wanga falon.
Shuairat tayi wanka tayi ado ckn wani uban leshi Wanda zai kai 100k golden n lemon green da milk color ta saka yan kunnen gold mai tsadan gaske tayi kyau sosai tana tsaye a gaban dressing mirror tana kallon kanta yanda ta chanza tayi kyau sosai, anti mairo ta shigo dakin itama ckn uban kwalliyarta tana murmushi tace
“Wow my baby is looking gorgeous kinyi kyau sosai I wish Mr president zai ganki yanzun nan”

“Tnx anti” ta fada tana murmushi anti mairo ta rike hannunta Suka bar dakin sai kuma ga sauran yan uwan nata sun fito kowacce ckn ado na alfarma tare da kawayenta anti mairo na gaba tana rike da hannun shuairat Suka fito sai zuba gaisuwa ake musu wani Dan building Suka nufa me karen kyau .
Sun shigo tare da sallama wani makeken falo ne a cike makil da jamaa mata zalla gasu nan birjik kowacce tasha ado tana ji da kanta ckn faraa aka karbesu daga nan aka fara gaisuwa.

Bayan kowa ya nitsu anti mairo ta fara magana
“Ga ya’rmu nan mun kawo muku sai Ku riketa da amana idan tayi abunda ba dai2 bah a nusar da ita ko kuma a sanar damu saboda karama ce , Allah ya basu zaman lfy da zuria dayyiba”

Gaba daya falon aka amsa da ameen .sai ynxu na lura da wata dattijuwa mai kyaun gaske kamarsu daya da Mr president tunda aka shigo da shuairat se murmushi take a hnkli ta fara magana

“Insha Allahu zamu riketa hannu2 Allah ya basu zaman lfy da ya’ya nagari”
“Ameen” aka sake amsawa daga nan aka kai shuairat kusa da wannan matar Suka gaisa ta rike hannun shuairat cike da so tace “ya’ta Allah ya miki albarka kiyi hkri nasan zaku zauna lfy insha Allah “

Bayan wani lokaci kowacce tana Dan tufa albarkacin bakinta tare da musu fatan alheri daga nan aka fara daukansu hotuna sai kuma kyaututtukan da shuairat ta samu na ban mamaki wato turamen zani ne da lesuna sai kuma kdade mai dumbin yawa kai sunga abun arzki kam daga karshe Suka koma bangaren ta.kowa yana yabawa dangin Mr president da irin karamcin su.

Wani bodyguard ne ya shigo ya sanar dasu cewa Mr president na son ganin shuairat tayi shiru bata CE komai bah anti mairo CE ta jawota xuwa daki ta kara fesa mata turarurruka iri2 sannan ta kara powder da lipstick tace mata
“Saura kije kina wani nokewa , feel free mijinki ne”
Murmushi kawai shuairat tayi tana mamaki halaye irin na anti mairo daga nan ta sauka zuwa kasa inda bodyguard din yake jiranta daga nan Suka wuce ckn mota ya kaita bangaren Mr president.
Sau daya ta taba zuwa amma yau taga komai ya canza mata an sake fenti da furniture’s da komi a bakin kofa bodyguard din ya tsaya ta karasa.
Bata sameshi a falon farko bah don haka ta wuce personal falonsa ta shigo tare da sallama yana zaune ckn manyan kaya yayi kyau sosai ko don ta kwana2 bata ganshi bane oho ya amsa ba tare da ya daga fuskarsa bah yana danna waya da alama wani yake son kira ta nemi waje ta zauna suna fuskantar juna. Shiru sukayi sai kuma ta tuna cewa ynxu itace kasa dashi nan kuwa a hnkli ta furta

“Ina kwana ur xcelency”
Wani kayataccen murmushi ya sakar mata duk da cewa baya kallonta sannan ya amsa ckn wani salon ji da kai

“My first lady kin tashi lfy”
“Lfy alhamdulillh”
“Hw was ur nite ya bakunta”

“Lfy kalau”
“Daz grt, dama na kiraki ne ina son jin nawa zaa sallami frenz naki”
Shiru kake ji ta rasa me zata gaya masa yaji shirun yayi yawa don haka ya daga ido ???????????? masha Allah haka ya furta a ckn zuciyarsa dama yarinyar nan haka take da kyau? Wow..she luks soo…btiful” carab Suka hada ido a dai dai lokacinda shuairat ta daga kanta , kowannensu yayi saurin dauke kai zuciyoyinsu ne ke harbawa.Mr president ya daure yace

“Kinyi shiru”
“Uhmm…gskiya nima bansani bah just give dem…

“No first lady! I hate dat word “bansani bah” ki gayamin pls”
Nan ma tayi shiru sai kuma ta tashi ya bita da ido har ta kai bakin kofa yace
“Ina zakije kuma muna magana”

“Uhm…zanje gun anti mairo ne”

“Zakije ki tambayeta nawa ya dace ?
Murmushi yayi yana tunani shi kadai cewa lallai akwai yaranta a tattare da ita
“Ok dawo ki zauna tunda baki sani bah lemmi tink on my own” ba gardama ta koma ta zauna yana danna waya can ya kara a kunne yace
“Ka tura sakon da na baka jiya ?
Ok yes ka hada duka ka basu a ckn gida “
Daga nan ya kashe wayar ya maida kallonsa gareta sun kurawa juna ido can shuairat ta kauda fuskarta yana Murmushi sannan ya fara magana

“Aysha ynxu idan aka baki mukamin first lady haka zaki dinga yi?
Ta daga kai ckn rashin fahimta yace

“Yes! Wat I min is dai komi sai kin tambaya ? Bazakiyi on ur own bah?
Ta zumbura baki tace

“Ni…ni nace a bani first lady ne dama”
A hnkli ya taka xuwa gabanta ya sunguna idanunsa a kanta suna fuskntar juna shuairat ta sunkuyar da kai tana wasa da warwaronta yasa hannu ya daga habarta Suka kurawa juna ido yace

” ke matata CE dole zaki koyi yanda zaki gudanar da wasu harkokin on ur own , u have to fight Aysha”
Bash ne tare da wani bodyguard Suka shigo tare da sallama ganin halin da Suka tarar da ogan nasu a ciki ne yasa Suka bar wajen shuairat kuwa kunyane ya kamata haka nan Mr president ma nan da nan ya tashi ya koma kujerar da yake da ya zauna ya dannawa bash kira a waya Suka shigo Suka sanar dashi cewa yayi baki daga England nan ya tashi Suka fita tare shuairat kuwa bodyguard Suka rakata ta koma bangaren ta.

????????????????????????lov u all
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
46
By Reefat yahya

Ta shigo bangarenta kawayenta suna mata tsiya Hafsat tace
“Ohhh shuairat an kasa hakuri a jira mu koma mana”
Ummi tayi dariya tace

“Gane min hanya dai da ana nokewa wai tsoho zaa aura ba zancen love gashi nan tun baaje ko ina bah an fara lumewa”
Suka fashe da dariya Suka shewa anti mairo ta shigo tana dariya tace

“Rabu dasu baby nah love kam kowa ma yana yi sai Wanda bai samu bah , Ku kuwa Ku tashi Ku tattara mu bar musu gida ynxun nan”

Suna dariya se kuma Suka hau godiya abun arzikin da Mr president ya aiko musu kowacce an bata kaya lace super da kuma Holland se kudi 120k shuairat kam mamaki ne karara a fuskarta sai kuma ta share zancen haka nan su haj mairo ma an basu kudade Masu yawa daga nan ta sake Jan kunnen shuairat akan zaman da zatayi a gidan tare da koya mata wasu dabarun sarrafa miji Wanda ba sai na fada bah???? nan sukayi sallama shuairat ta fara hawaye haj mairo tace kul..karki bata kwalliyanki daga nan motoci Suka kwace su sai gida aka bar amarya daga ita sai halayenta sai kuma masu aiki.
Sama ta haura sai ynxu ta samu damar karyawa tea ta hada sannan ta Debi chips kadan da kwai ta zauna ta cinye tas sannan ta dawo falo ta kunna TV MBC ta kama tana kallon film din “triple X” yan uwan Mr president ne Suka shigo sun Dan taba hira daga nan Suka shaida mata cewa yau zasu wuce Adamawa wasu kuma Kano wasu kd da kuma Lagos, cin-cin doughnut da cake ta diba musu da turarurruka masu yawa ta basu suna godiya Suka tafi. Haka masu aikin Suka shigo Suka gabatar da Kansu nan ma ta kawo musu abubuwa iri2 suna yaba mata Suka koma bakin aikinsu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button