NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

“Ba haushinsu nake ji bah…haushin kaina naji ni na cuci kaina “
“No…kaddara ce babu Wanda ya isa ya hanata afkuwa so just take hrt ki yarda da kaddarar ki kuma ki godewa tunda kin samu kina da daya , wani har ya koma ga mahallicinsa ma baxai samu ikon ganin jininsa don haka yana da kyau bawa ya kasance mai yawan godiya a duk halin da ya tsinci kansa a cki”
“Maganar ki gskiya ce Nagode Allah bar xumunci”
Shuairat ta cigaba da kwantar wa shukrah hankli umaima ta shigo kallo daya ta musu ta dauke kai tayi wucewarta.haka Suka cigaba da hira har lokaci sallah yyi Suka gabatar da sallah tare da cin abinci, umaima bata fito bah don haka shuairat ta ynke shawarar duba ta.
Tana kwance a dakinta ido 2 shuairat ta shigo tare da sallama cki cki ta amsa tamkar bata so shuairat tace
“Ki fito ki ci abinci” “na koshi”
“Lfynki kuwa..so kike ki kashe abunda Ke cikin ki da yunwa , tashi maxa ynxun nan”
“Allah ni nace miki bana jin yunwa”
Shuairat ta tabe baki tayi ficewarta shukrah kuwa tana ganinta ta hada rai shuairat ta koma ta xauna ta fara magana ta ga shukrah na amsawa kamar bata so , umaima ce ta fito fuska a hade ta bude fridge ta debo ruwan sha shuairat tace
“Haba umaima…ya xaki sha ruwan sanyi a ckn halin da kke cki “
“Haka nake so”
Tayi shiru tana mamakin wannan sauyin ckn kankanin lokaci ta juya gun shukrah itama ta hada rai nan shuairat ta gane matsalar ta tashi tsaye ckn masifa tace
“Nifa baxaku maida ni er iska bah…kowacce ta hada rai toh wllhi ni ba munafuka bace ga fili na bar muku kuyi abunda kuka ga dama”daga nan ta haura xuwa dakinta mr president yana kwance ta shigo ckn bacin rai yana kallonta yace
“Wa ya tabo min my lady”
“Mtsww…aikin banxa, nema suke su mayar dani munafuka wllhi karyansu”
“Su waye? “Umaim da shukrah man”
“Aw…kice min aminiyarki da ya’r ki matan yayanki”
Wani kallo ta jefa masa tare da cewa “meaning” “meaning notin ..kedai ki bi a hnkli” haushi taji nan ta fada toilet se cika take tana batsewa mr president kam dariya ta basa ya girgixa kai yace “oh Aysha ba dai rigima bah”
Har dare basu sanyata a ido bah har xuwa lokacin da bash yaxo daukarsu shukrah ta shiga gidan gaba ta xauna umaima tare da waleed Suka xauna a baya, ta cika tayi fam a haka Suka karisa gida.

Bayan kwna 3 da xuwan su shuairat momsi da daddy Suka kawo musu xiyara a wannan Daren umaima ta haifi kyakkyawar erta mace murna a gun bash baa magana shukrah kam kuka ta kwana yi a wannan Daren. Haka en uwa Suka yi ta xuwan Barka.

????????
[2/21, 2:43 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
100
By Reefat yahya

last page

Ranar suna yarinya taci sunan maman umaima wato zainab anyi shagali sosai mai jego sun sha hotuna tare da en uwa da abokan arxiki a gidan mijinta ta xauna aka hadata da wata tsohuwa ta xauna da ita , bayan 2weeks shuairat taje gidan iyayenta da gidan shukrah da kuma umaima sukayi sallama wannan karon tare da sultan xasu koma hakan kuwa akayi jirgin yamma Suka bi sai Delhi.

1yr leta …shuairat ta kammala degree nata dama kos din shekara 2 ne tayi ynxu ta fara masters sultan yana js2 salman kuwa yana da shekara 2 da rabi ya gara girma yayi wayo sosai sai shegen surutu muryarsa radau babu maganar da be iya bah .mr president ya bude wani kamfani a nan Delhi na sarrafa gwalagwalai???? a China kuma yana da kamfanin sarrafa motoci , idan aka zo gida Nigeria kuma abun baa cewa komai don babu inda zaka shiga ka kira sunansa a ce da kai baa San shi ba..yayi kaurin suna yana da kamfanoni da dama ga gidajen mai da sauransu.bash Ke kula masa da harkokinsa na Nigeria se bayan wata 1 yake xuwa , umaima ta sake haihuwa namiji ta Haifa aka rada masa Suleiman suna kiransa Abbas zainab kuma Ummi ake kiranta.rayuwarsu ta kasance ckn so da kulawa umaima ta gama tana kula da daya daga ckn kamfonin mahaifin nata dake Abuja arxiki ya bunkasa babu harkan talauci shukrah ma mijin nasu ya gina mata katafaren boutique tana harkar kasuwanci ckn kwanciyar hnkli a jarida ta samu labarin an damka fatee tana gidan yari a can Kaduna.
Shuairat na kwance a kasan kafet ga katoton cki Wanda xai kai wata 6 idanunta a lumshe suke da alama bacci take ji mr president ya shigo ya xauna kusa da ita
“Pls my lady ki tashi bana son kina kwanciya a kasa ko so kke ki cutar min da ya’
Harararsa tayi tace “wato ni idan naga dama na mutu koh..dama ai Ku maxa haka kuke kunfi son ya’yan Ku fiye da komai mu mata…
“Pls not again Aysha ba haka nake nufi bah ki tashi don Allah”
“Ni ka rabu dani don Allah” ta sake gyara kwanciya ya rike kai haka yake fama da wannan ckin se masifa da shagwaba haka laulayin yaxo mata Abu kadan ta fara fada ko kuma ta fashe da kuka ..ya ja dogon numfashi ya marairaice “haba mom sultan kinsan ba kyau mace ta dinga kwanciya sanyi na shigarta is not gud pls”
“Ni a nan xan kwanta” yasa hannu ya dagata duk da nauyin da ta kara haka ya dagata xuwa daki ya shimfidata a gado nan kuwa ta fara kuka ya xauna a gefe yana lallabata dakyar bacci yayi gaba da ita. Bayan magrib ta farka ta gabatar da sallah sannan tayi wanka , wata doguwar farar Riga ta sa mai dogon hannu a hnkli take tafiya ta fito falo suna xaune sultan yana koya wa salman ABCD mr president yana kallon news ta shigo babu ko sallama fuska a hade salman ya daga kai Suka hada ido yayi dariya yace “lah…mother conpesho(confessor) bhai!( sunan da yake kiran sultan dashi wato yaya da harshen Hindu) bhai ka tuna film da muka kalla na mother conpesho..irin rigarta ne mummy ta shaka” yana magana da harshen yara masu koyan magana wata uwar cafka shuairat ta kai masa ta matse bakin tana huci tace “nice mother confessor? Uban wa yace ka kalli film har xaka rike sunayensu..ban hanaku kallon film bah” ta juya gun sultan cikinsa ya duri ruwa ya sunkuyar da kai yace
“Mom kiyi hkri wllhi…
“Rufemin baki daga yau nayi seizing laptop dinka ” salman yana kuka ta turashi gefe nan mr president ya jawosa yana lallabashi yaron se kuka yake ita kuma ta xauna tana karkada kafa ta cika tayi fam ..sultan kuma jin an ambaci xaa rabashi da laptop nan ya fara kuka ya tashi xai koma dakinsa shuairat ta daka masa tsawa tare da cewa “dallah dawo nan ka xauna ina kake tunanin xaka je , ni Saar ka ce don na maka fada xaka tashi ka tafi..ynxu Ku rufemin baki Ku tashi Ku cigaba da karatu ko na tattaka yaro a nan wajen” sum-sum ya dawo ya xauna salman ma ya hadiye kukan da yake don yana tsoron maman nasu bata daukan wargi , mr president de sai kallo kawai yake musu bai tanka bah bayan ta gama yace “my lady can we talk” bata ce komai ba ta tashi ta koma daki yabi bayanta da ido daga bisani ya tashi ya wuce dakin tana kwance a bisa gado tayi matashi da filo se karkada kafa take ya xauna dab da ita tare da rike mata hannu “my lady pls ki rage yawan fadan da kike wa yaran nan xasu fara jin tsoron xama inda kike” “naji xan rage amma kasan yara idan an sake musu kadan shikenan se kaga tarbiyarsu na Neman lalacewa kuma gskiya kana sake musu too much” murmushi yayi yace “oh wannan babyn rigimammiya ce gata da yawan fada ga kuma shagwaba” ta gyara kwanciyarta ya jawota a jikinsa yace “baki ci abinci bah Ayshata y? “Ni bana jin yunwa” “pls ki daure ki ci koda dan kadan ne nikuma I promise u xan kawo miki icecrm” bitt ta tashi xaune ckn jin dadi tace “da gaske ..wllhi kuwa xan ci muje mu fara siyan icecrm b4..
“Haba my lady bani nace xan siya miki bah..trust me” ta tura baki tace “toh ba Kaine ka daina siyamin bah kana biyewa munafukar jankim wai ka hanani yawan shan sanyi da zaki” “yau kuma gum Jan takin ce ta xama munafuka..lallai babyn nan se a hnkli” ta tura baki wai fushi take bata Ankara ba taji bakinsa ckn nata nan ya rikita mata kwakwalwa tuni ya mantar da ita xancen wani icecrm????????.
Da safe tana xauna a falo da kofin tea a hannunta salman da sultan Suka shigo bayan sun gaisheta ta amsa ba laifi mr president ya shigo ya xauna tare da manna mata peck a kumatu murmushi tayi ta cigaba da kurban tea nata salman yana xaune yayi shiru mr president yace “fine boy meke damunka” ya bata fuska yace “ba mom ce ta daina kirana da sweetie bah” me zasuyi idan ba dariya bah mr president yace “ah toh..lyk mother lyk son shagwabar de gado ce” murmushi shuairat tayi tace “com here ” ba gardama ya karasa kusa da ita ta ajiye cup din hannunta ta daga shi tana nishi “uhm..my sweetie ina sonka kaji..but ka daina kallon film kayi karatu ka xama likita kamar anti jankim.. Ba kacemin kana son saka fararen kaya irin nata bah” “ehh..Jan yiwa bhai allula koh” “ehh..har dad ma zaka masa” murmushn jin dadi yayi shuairat ta kalli sultan tace “zo nan engineer sultan Suleiman.. Ko injiniya ss ne” sultan yana dariya ya dawo kusa da ita ta hadasu ta rungumesu tare da cewa “I Lov u koh..mom tana sonku Allah ya rayamin Ku ya muku albarka” “ameen”Suka amsa har da mr president daga nan tace su koma daki suyi karatu tunda weekend ne babu makaranta da yamma kuma kullum ita take koya musu karatun Qur’an. Mr president ya rungumeta yace “I Lov u Ayshata kina burgeni kin bani komai na rayuwa Allah ya sakar miki da gidan aljannah” “ameen my man Lov u more” wow…Lov birds????????????..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button