NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

A kofar gidan ya tura a kirata yaron ya dawo ance ya shiga cki, a wani daki aka saukeshi babu komi a ciki sai tabarma da kuma wata ya’r darmuma.
Kannenta ne Suka shigo da kwanikan abinci bayan sun gaisa Suka bashi waje bayan kankanin lokaci ta shigo tare da sallama wani uban qamshin turare ne ya buga hancinsa habawa ya daga kai Suka hada ido tayi kyau sosai ckn atamfar Sheraton dama tana da Dan jiki dinkin yayi mata kyau sosai.
Bash ya kasa cire idanunsa a kanta ita kuma kunyarsa take ji

” ina yini” ta fada ckn siririyar murya murmushi yayi ya fara kwaikwayon muryarta
gaba daya Suka fashe da dariya
” na sameku lfy
“Lfy alhamdulillh ya hanya
“Lfy lau
” ka sha ruwa se ka ci abinci nasan ka gaji sosai

Bata jira amsar sa ba ta bude kulolin abincin rice n stew ne se kuma danwake yasha hadi har da kwai da cabbage se kuma farfesun kayan ciki..

“Wanne zaa fara xubawa
“Ni danwake kawai xan ci
“Haba ka isa?
“Y not” ya fada yana murmushi

” Allah baka isa ba sai ka cinye duka

” haba shukrah kema dai kinsan baxan Iya cinye wannan ba”

Baya CE komi ba ta diba masa danwaken dama shuairat ta gaya mata yaya bash na balain son danwake, ta ajiye a gabansa sannan ta xuba zobo a ckn Kofi ta tura masa a gefe ya daga kai Suka kalli juna yace

“Sai ki matso muci tare ai”
” a koshe nake”
” no! Ki xo mu ci”
” a’ah naci nawa tun dazu”

Murmushi kawai yYi ya hau ci a hnkli yake kominsa gwanin burgewa shukrah tana satar kallonsa guy din ya hadu????
Carab ya kamata tana satar kallo ya murmusa yace

” ya dai”
” ba komi”
” ki fadi gaskiya”
Ta rufe fuska ckn jin kunya tace

“Zan koma ckn gida idan ka gama ka kirani a waya”

” no! Kiyi xamanki ni bana jin kunya ai kece me jin kunyana”

Tana dariya ta kawar da fuska a gefe.
Bayan ya gama cin danwaken yana santi yace

” wannan girkin inna koh? Nasan naki bare kai wannan dadi bah”

“Naji na yarda”ya shanye zobon ma yaji ya koshi yayi hamdala ya juya suna fusksntar juna sosai nan Suka fara magana ta fahimtar juna ya nemi jin raayinta game da auren nasu ita tace duk yadda sukayi ya mata daidai bata da zabi .

Haka Suka kasance har magrib sannan ya mata sallama ya tashi ya tafi kamar karsu rabu sabida dan xaman da sukayi sun fara sabawa da juna.
[2/21, 2:37 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
20
By Reefat yahya

Dakin ya cika makil da jamaa daga ministoci senators members da dai sauransu mr Joshua yana xaune wato vice president kenan ga bodyguards a gefensa ta kowane bangare.
Idan ka duba wani bangare kuma yan jarida ne birjik ga maaikatan yada labarai dai daban daban ana jiran fitowar mr President , ya fito kuwa ckn manyan kaya yayi kyau sosai fuskarsa ba yabo ba fallasa yana taku ckn kasaita yana wani ji da kai tamkar sarki ????????( lols me banbancin)
Ya nemi kujera ya xauna nan wani mutum ya fara magana yana murmushi daga ganinsa yana jin dadin yanayin da yaga mr President a ciki….

“Mr president yau ne karo na karshe da xamu maka wannan tambayar…me hadinka da wannan yarinyar?
Shiru ba amsa ya maimaita maganar sau3 ko uffan mr President bai tanka masa bah
Nan aka fara hayaniya kowa na fadin albarkacin bakinsa..

” muna ganinka mutumin arxiki shiyasa muka baka wannan matsayin Amma ka kunyatar damu …
Wani dattijo ne ya fadi haka yana rike da speaker.mr president ya runtse ido yana jin wani irin radadi a ckn xuciyarsa dakyar yake furta sunayen Allah.

“Silence” wata siririyar murya ta fada da karfi sanye take ckn wani gown me kyawun gaske black da adon pink tayi rolling da pink veil ta sa lipstick pink Dan kadan tayi kyau sosai.

Wal wal hasken camera kawai kake gani anata daukanta hotuna gaba daya hnklan jamaa ya koma kanta ta karbi speaker ta fara cewa

” ni xan Baku amsar tambayoyinku… ni da shugabankasa mun kasance muna son junanmu tun da dadewa, shi ba mutumin banxa bane kamar yadda kuke zargi shi jarumi ne mai mutunci yana da Amana da rikon gaskiya”

Wancan mutumin ya juya yace
” kina nufin soyayya kuke yi da mr President?

” ehh …soyayya muke”

” toh meyasa yaki ya fada da bakinsa?
” kunyace kasan Fulani ai”

“Kin tabbata”
“Na tabbata hakan ne” ta gyada kai suna kallon juna ita da mutumin shikam beji dadin xuwanta ba yafi so a CE an cire mr President akan mulkinsa.

Yan jarida Suka rubuta duk abubuwan da yake faruwa a yayinda masu gidan talabijin Suka fara haska nasu a wannan lokacin duk duniya ana kallon abunda yake faruwa.
Mr President ya sunkuyar da kai shikam baiso shuairat ta kawo kanta bah toh meyasa ta ceci rayuwarsa daga zargi da ake masa? Duk da cewa yasan abun ya shafe ta tunda tare aka gansu Amma baiyi tunanin cewa xata hada karya haka don…..
” mr President ko xaka bamu Karin bayani kan abunda ta fada?
Shi bai ma San yan jarida sunxo kusa dashi bah

” babu abunda xan fada a kai” ya basu amsa kai tsaye shuairat ta karasa kusa dashi ta xauna tana kirkiro murmushin dole nan kuwa aka fara daukansu hotuna mr President kam mamakin alamarin yake wai yarinya kamar an turo ta.
An gama meeting lfy bayan an wanke mr President daga xargin da ake masa, suna fita yace a nemo masa shuairat a ckn mota Suka xauna su biyu kawai bayan an rufe musu kofar ya juya yana kallonta yace

“Meyasa kike shiga min rayuwa ? Na gaya miki ki fita sabga ta”

” am sorry mr President but idan ban fito na kashe maganar ba xaka Iya rasa kujerar …

” shut upp! N so wat idan na rasa shi? Kinsan kuskuren da kika tafka? Kinsan matsalar da kika jefa kanki a ciki? Kinsan balain da kika jefani ciki? Da kinsani da baki aikata hakan bah…Ayshah kinyi kuskure “

” mr President…..
“Shut up! Ban gama bah”
Ya tare nimfashinta yana huci kamar wani xaki

” Aysha meyasa kike shiga rayuwata? Meyasa xaki jawomin matsala a Rayuwa? Meyasa ? Meyasa?

Shuairat ta fashe da kuka tana hawaye tsakaninta da Allah mr President ya gitgizata yana nuna wajen window da Dan yatsa yace
” kinsan matsalar da xafi fuskanta ? Me xaki gayawa wadancan nan gaba? Shin har yaushe xaki cigaba da musu karyar? Shin me xan gayawa iyayena? Tell me!
Ta cigaba da kukanta me ban tausayi yayi shiru kansa ya daga ya kura mata ido dakyar yace
” is ok stop crying”
Bata sauraresa ba ta cigaba da kukanta ya xuba mata ido kawai se kuma ya sake cewa

“Don Allah ki bar kukan ya isa pls”
Ta sunkuyar da kai kasa
“Let’s talk pls “wayarsa CE ta fara ringing umaimace ba sai angaya masa bah ya daga kara a kunne

” I hate u dad” daga jin muryarta yasan tana kuka ta kashe wayar yayi shiru jikinsa ya mutu gaba daya duniyar ta masa xafi.
Shuairat CE ta lura da halin da yake ciki bayan ta share fuskarta a hnkli tace

“Mr president ar u ok’
“Am fine I just need to go home”

“Umaima koh?
Ckn mamaki yake kallonta ya akayi ta gane cewa umaima CE? n a ina tasan umaima?
Murmushi shuairat tayi don taga yNa mamaki tace

“Ka lallabata kasan karamace “
Daga nan ta bude mota xata fita

“Ayshah!
Ya kira sunan da wani irin salo ta dakata don jin me zai fada

“I’ll c yhu gobe we have alot to talk about”
Daga nan ta fita ba tare tayi magana bah.

ReefatCE…..Lov u all????????
[2/21, 2:37 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
21
By Reefat yahya

Umaima CE zaune a falonta kuka takeyi tmkar ranta xe fita mr President ya shigo ckn hanzari ya karasa kusa da ita ya kai hannu xe taba ta tayi saurin komawa da baya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button