NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

Ckn jin kunya ta gaisa da baba da kuma daddy sai kuma bash , umaima kuwa Sam ta tashi ta koma kusa da shuairat. Haka Suka kasance daga nan Suka xauna akan dinning table lafiyayyen abinci masu aikin gidan Suka shirya musu, daga Chinese dishes da Nigerian duk babu abunda babu suna ci suna hira babu batun kunya abun dai gwanin burgewa.baban shuairat yake Dan jin kunya daddy ya lura da hakan yace
“Alhaji bello gara ma ka cire kunyan nan ka ajiyeta a gefe kaga surukin naka babu alamar kunya a tattare dashi”
Gaba daya Suka fashe da dariya mr president ya Dan Sosa kai..har ga Allah shi yamanta da cewa a gaban baba ya fadi xancen cikin. Bayan sun kammala cin abincin aka nuna musu masauki Chinese president yaxo Suka gaisa da iyayen nasu sannan ya tafi , mr president tare da iyayensa Suka ware suna hira haka nan shuairat ma dakin baban ta Suka xauna ita da bash da kuma sultan suna ta hiran yaushe gamo.

D next day Suka shirya gaba daya daddy momsi baba shuairat bash umaima sultan da gum jankim yawon bude ido Suka fita, sun zaga garin sosai gskiya hong Kong ya hadu har yamma Suka koma gida bayan sun tsaya sunci abinci a wani restaurant.
Washe gari Suka sake fita , haka dai Suka kasance har tsawon 5days kullum suna tare.shuairat sai nan2* ake da ita duk motsin da tayi mr president ko momsi ko daddy zasu tmbayeta wani Abu take ji ne? Itakam har kunya take ji irin yanda Suka dau son duniya Suka doramata ita da ckn nata gashi ynxu ckn ya bayyana cos yana 7mnth ne.bayan kwana 2 Suka fara shirye2* komawa 9ja duk nacin momsi na son tafiya da shuairat firr…mr president yaki yarda yace musu zasu ga likita kafin su koma Nigeria, babu yadda Suka Iya dole ta hakura nan Suka cigaba da shirinsu.
Misalin 8pm umaima tana kwance a dakin shuairat tana chat a waya shuairat ta shigo ta zauna a gefe tana fuskantar ta tace
“Baby ya maganan aure ne kinga ynxu kin girma fa ya kamata ace kin fito da Wanda kike so”
Shiru umaima tayi a yayinda xuciyarta ya fara bugawa can ta kirkiro murmushi tace
“Anti Nah dad ne yace ki min maganan aure?
“Ah’aa wllhi nice dai naga ya dace cos zaki shiga final year naki a uni daz y”
“Ok ki bari idan Allah yasa kin sauka lfy after den sai muyi maganar”
“Toh Allah ubangiji ya nuna mana.. Amma ni ban taba ji ko ganin wani saurayi yazo wajenki bah”
“Oh..antyyy…wllhi har kinsa naji kunya”
Daga nan ta tashi ta gudu tana murmushi ganin shuairat na Neman tona mata asiri. A bakin kofa ta tsaya tana maida numfashi, bash ne ya shigo Sam hnklinta baya ckn jikinta tunanin maganganun shuairat takeyi ynxu ya xata yi? Pamm! Bash ya tafa hannayensa a saitin fuskarta ckn tsoro ta bude baki xatayi ihu yasa hannu ya toshe bakin nata yana dariya sannan yace
“Matsoraciya kawai”
Daga nan ya cire hannun nasa ita kuwa taja dogon numfashi
“Haa..yaya kaban tsoro wllhi na razana ba kadan bah”
“Ajebo kawai..babu abunda kika iya sai shagwaba wllhi mijinki zai sha fama dake”
Umaima ta rage sautin muryarta tayi magana ciki2* tace
“Kaine zaka sha faman ai cos kaine mijina”
“Wat? Me kike cewa”
“UHmm
.ni nayi magana da kai ne?
Ta fada ckn tsigar shagwaba yana dariya yace
“Hmmm a cigaba da boye2* dai wata ran dole a amayar”
“Wat? Hw do u min?
Ta tambaya ckn tsarguwa
“Oho..nima nayi magana dake ne?
Harara ta watsa masa sannan ta wuce falo ta xauna yana dariya yabi bayanta shima xaman yayi kusa da ita.

“Yawwa..yaya bash nifa bazan koma gidanka bah”
“Ina zaki koma ?
“Gidan baba xan koma b4 su dad su koma”
“Matsoraciya shukrah ce ta hanaki koh”
“Hmm..wannan matar taka se a hnkli”
“Ba dole bah..ta gane kina son mijinta ai dole tayi kishi”

????????waat?..mijin wa? Ni din?
Ta jera masa tambayoyin ckn mamaki da firgita wani murmushi ya sakar mata sannan ya tashi Sam ya dawo kusa da ita har suna jin hucin juna ya kura mata ido yace
“C’mon baby sis..stop pretending ya isa haka ki daina wahalar da xuciyar taki kowa yasan cewa ni kike so stp hiding n b strait fowod”
Xuciyar umaima sai dukan 3-3 yake bash ya cigaba da cewa
“Umaima na Dade da sanin cewa kina sona kawai kunyace ya hana ki gayamin.tun bayan dawowata daga Adamawa kika kirani na sameki a gidanku kina kuka kina maijin haushin cewa nayi aure ban gaya miki bah, tun a wannan lokacin na fuskanci sona kike.duk rashin lafiyar da kikayi bayan aurena ina sane da hakan kuma dad ma ya gane lagonki shiyasa yake turani miki magana a duk lokacin da kikayi fushi dashi, n naga chat naki da shuairat a yayinda kike gaya mata cewa kina son wani amma kin kasa tunkararsa har yayi aure. Ranar da kuka samu misunderstanding da shukrah har na lallabata xuwa daki nace ki koma dakinki ki jirani bayan na dade kafin na je dakinki nan ma na hango kishina xalla a kwayar idanunki har na tambayeki hiran samarinki kika cemin saurayinki ya mutu kin tuna? kuma dazu maganan da kikayi cewa nine mijinki duk naji abunda kika fada , so umaima pls ki daina wahalar da xuciyarki ki fito ki bata abunda take nema”

Yana gama fadin haka ya tashi ya kashe mata ido daya sannan ya juya yayi tafiyarsa.mutuwar xaune umaima tayi tana mamakin faruwar al-amarin dakyar ta tashi ta koma dakinta ta hada kayanta don jirgin safe xasu bi.

*da safe mr president da shuairat Suka rakasu xuwa airport har jirginsu ya daga sannan Suka juya don komawa gida.
A ckn jirgi kuwa umaima Sam taki hada ido da bash don wani Sabin kunyarsa take ji haka Suka kasance har lokaci da jirginsu ya sauka a Lagos.umaima tace xata kwana 2 kan ta koma Abj haka bash da sultan da kuma baba Suka wuce Abj gidan baba direct Suka sauka.bayan kwana2 umaima ta koma Abj a gidansu shuairat ta yada Zango ta sanarwa mama cewa tare zasu zauna ita kuwa taji dadi sosai dama zaman kadaici ya isheta don ma sultan yana nan kenan.


Shuairat kuwa jankim CE ke kulawa da ita duk awon ciki da komai ita take mata tana shan magunguna masu inganci don karawa bbyn lfy.honey moon Suka shirya xuwa jankim tana xolayarsu wai honey moon da tsohon ciki, har airport ta rakasu jirginsu ya daga xuwa Akita Japan wani hadadden city ne a can Japan jankim CE ta xaba musu garin akita saboda tsarin yanayin garin akwai dadin xama don kuwa duk arean tsakanin Korea China da Japan babu garin da yakai akita kyawun weather.
Bayan sun sauka taxi ne ya kaisu can gefen gari a akita snow fall wow..kankara ne ke xuba kotaina wani hotel mai kyawun gaske Suka kama daga nan wanka Suka shiga tare ..tafasashen ruwan zafi Suka Tara a jacuzzi shuairat na ganin haka ta xare ido tace
“Haba???? my man ynxu kana nufin ckn ruwan nan xamu shiga?
Ya jawota jikinsa yace
“Don’t worry my lady ..kinga nan snow fall ne bqzaki ji xafin ruwan bah”
“Ah’ah nikam gskiya baxan shiga bah”
“Plsss..haba ke baki jin sanyi ne? Nida nake son ki haihu a nan kiyi wankan jego kinga bazaki ji radadin wanka da ruwan xafi bah”
“Mm..dama wa yace zanyi wanka da ruwan xafi”
Ckn dabara ya tura bakinsa ckn nata ya fara kissing dinta cak ya dagata sai ckn jacuzzi….
Ummmm a hnkli na ja kofar bayin nayi waje.

Ku biyoni????????????????
[2/21, 2:41 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
70
By Reefat yahya

Wata sabuwar rayuwar soyayya da kulawa mr president da shuairat Suka shimfida a akita bata daga komai hatta wanka shi yake mata kullum suna fita trekking saboda yana da kyau mace mai ciki ta dinga motsa jikinta kwanciya ba naki bane..a wannan lokacin ne shuairat ta kara tabbatar da irin son da mr president ke mata shikuwa gani yake tmkar baxe Iya biyanta karamcin da ta nuna masa, kullum suna manne da juna basu rabuwa wata irin shakuwa da so mai karfi ya kullu tsakaninsu.cikin ya shiga wata 9 su momsi Suka damesu da kira kan cewa yaushe zasu dawo mr president yace suna nan tafe momsi ta umarcesa da ya dinga karanta yasin kafa1 ya tofa a ruwa ya bata tana sha kullum saboda Neman haihuwa ckn sauki da iznin Allah.hakan kuwa akayi kullum mr president sai ya tofe suratul yasin 1 ya bata tasha. Doughbunji hospital akita Japan can sukaje aka shaida musu cewa haihuwan na nan bada jimawa, habawa mr president ya fara shopping ne kamar ba gobe babu abunda be siyo bah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button