NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

“Uban wa ya turaki ki fito gaban jamaa kice mr President yana nemanki ?

“Yaya me….
“Talk me bana son bata lokaci” ya daka mata tsawa bata taba ganin yayan nata ckn bacin rai haka bah
Ai kuwa ta fashe da kuka

“C ba kuka zakiyi ba koma menene I don’t kia just answer me”

“Yaya nifa ba soyayya muke yi bah

“Meyasa zakije ki gayawa duniya hakan?

“Yaya….
“Answer me! Kina da hnkli kuwa? Kinsan kuskurenda kika aikata?

Kuka sosai shuairat take nan ya juya ya bar dakin baya son ganin wani ya sata kuka bare shi da kansa amma ya xama dole ya nuna mata kuskurenta.ya fita ya barta ta cigaba da kukanta babu me bata hakuri .

Ku biyoni ~reefat~
Lov yah…????????????????
[2/21, 2:38 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
23
By Reefat yahya

D next day shuairat ta gaishe da yaynta yayi bnxa da ita haka ta tashi ta koma dakinta ta kwanta tayi kuka mai isarta sannan ta fara shirin xuwa wajen aiki.
A can office nasu ma hakan akayi Mahmud yana ganinta ya fara wayar karya ita kuwa ta gane sarai Amma ta share ta xauna ta cigaba da harkokinta.

A can office din mr President kuwa ya kasa tabuka komai kawai so yake ya xauna da shuairat ta amsa masa tambayoyin da yake bukatan ji.bash ya kira ya umarcesa da ya nemo masa shuairat , ya sunkuyar da kai yana tunani kodai da gaske soyayya suke yi? Nan ya tashi ya tafi JF Reporters gun mr Muawiya ya nufa ya sanar dashi sakon mr President nan aka bashi ixinin tafiya da ita, tana xaune tana danne-danne a gaban computer sarai taga wucewarsa Amma bata damu bah yaxo ya tsaya a kanta ya wani bata rai yace

“D president wants to c u”
Ko motsi batayi ba bare ya sa ran xata kulashi daman yasan xaayi haka yasanta idan tayi fushi.

“Miss bello mr President wants an audience”
Ya sake maimaitawa a yayinda yan office din sun juna suna mamakin yan uwan junan da suke Abu tamkar basu taba haduwa bah ganin kallon yayi yawa ne yasa shuairat ta tashi ta rataya Jakarta tare da yiwa su Sarah sallama suna hada ido da Mahmud ya kawar da kansa gefe daga nan ta fice tayi hanyar mota.

A hanya ma babu Wanda yayiwa wani magana a gidan baya ta xauna shi kuwa yana tuki.
A kofar building din yayi parking bayan ta fito da turare ta kara fesawa tayi hakan ne don batawa yayanta rai ta dau farar hoda ta shafa da kuma lipstick daga nan ta bude kofar ta fito bata jira yayn nata ba tayi aikuwa securities Suka fara gulma ana nunata ana cewa ga budurwar mr President ta xoh.ko a jikinta haka ta karasa duk inda ta wuce ana bata girma direct office da yake ganawa da baki ta wuce.ta tura kofar a bude ta shigo tare da sallama yana xaune yau suit ya saka yayi kyau sosai bazaka CE ya kai shekaru 40 da doriya a duniya bah.ya daga kansa yana kallonta sosai tayi kyau ga kuma qamshin turarenta mai sanyaya xuciya ta nemi kujera ta xauna nan ya tashi daga inda yake ya dawo kusa da ita suna fuskantar juna

“D first lady” ya fada ckn xolaya dum…shuairat taji wani Abu ya tokare mata kirji me hakan yake nufi?ta daga kai Suka hada ido ya sakar mata wani murmushin da ya kashe mata jiki

“My first lady ba gaisuwa ne?
Nan ma shiru kake ji.
“Ok nasan kunya na kike ji pls ki gayamin a ina kika samu tarihin rayuwata?

“Namanta”
Ya mata wani irin kallo ta sunkuyar da kanta saboda baxata jure kallon ba.

“Ok naji! Now ki gaya min meyasa kika CeCe ni ta hnyar cewa mun Dade muna soyayya”

“Nayi hakan ne don bana son ka rasa kujerar ka”
“Idan na rasa mulki na ta ina hakan xai shafeki”

“Ko kadan bazai shafeni bah nayi hakan nan don bana son ka rasa aikinka saboda nice sila”

Yayi shiru yana nazarin maganganunta
“Kai kuma meyasa ka sharemin hawaye wancan lokacin?
Da Sauri ya daga kai yana mamakin tambayar tata

“Kada kiyi tunanin share miki hawayen da nayi yana nufin wai ina sonki ne no! Tausayinki naji shiyasa na share miki”
Wani shuumin murmushi tayi tace

“Kana nufin kowace mace zaka Iya share mata hawaye kenan?
Ya jefa mata harara dakyar yace

“Ehhh haka ne”
Shiru sukayi ya rasa wace irin yarinya bace Sam bata jin tsoronsa shi da ko manyan mutane suna jin tsoron kallon idonsa su gaya masa magana Amma ita ko bata damu bah.
Ta sake kallonsa Suka hada ido ta kawar da fuska tana murmushi, bash ne ya shigo ya shaidawa mr President yayi baki suna son ganinsa shuairat ta yi karfin hali tace

“Baka gaya musu muna tare ba ne?
Ba bash ba har mr President yayi mamakin kalaman nata yayi irin ta maza yace

“Sorry bash ka gaya musu ina tare da…. Yayi shiru yana kallonta ta sakar masa murmushi wani irin Yarr..yaji daga tsakiyar kansa yace

“Ina tare da first lady su Dan bani lokaci kadan”
“Ok sir!
Bash ya fada yana kallon shuairat tana wani murmushn mugunta bash ya kai bakin kofa shuairat ta CE

“Uhmmm …wait! Ka saukeni a gida, mr President don’t wory next tym xamu karasa maganar”
Cak! Bash ya tsaya wani irin haushinta yake ji lallai yarinyar nan ta na wuce gona da iri Amma xaiyi maganinta nan shuairat ta tashi ta rataya Jakarta tayi ficewarta bash yabi bayanta mr President kam ya tsaya galala yana kallon ikon Allah daga nan ya wuce dakin da bakin suke jiransa.

…..muje xuwa????????????????????akwai drama kenan!
reefat
[2/21, 2:38 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
24
By Reefat yahya

Gidan baya ta sake shiga ta xauna ya shigo ya tada motar suna tafiya yana kallonta ta ckn mirror ta juyar da kai gefe se wani shan qamshi take

“Wai angaya miki ni driver enki ne”
Ko uffan bata CE masa bah

“Ina miki magana hajiya”
Nan ma shiru tayi yaja wani wawan birki ya tsaya a gefen titi

“Se ki fita ki nemi taxi ya kaiki gida don ni ba drivernki bane”

“Eyya …da tun farko ka gayamin ai xan sanar da mr President kaga kuwa akwai mototci da dama sai wacce na xaba , Amma ynxu din ma is not late let mi just call him ya turo min wata motar “
Ta cire waya tana faman danne danne a dole wai tana Neman layin mr President
Yaja motar Suka cigaba da tafiya yana harararta wani guntun murmushi ne ya bayyana a fuskarta.

“Look baby nifa yayanki ne dole kiyi respecting dina “
Bata CE masa komi bah tana danna wayarta da alama chatting take tana faman murmusawa , yana kallonta yana jin haushin abunda take masa wato sunyi nisa da soyayya haka har xata Iya xartar da hukunci ba tare da mr President yayi gardama bah toh a ina Suka hadu? Yaushe Suka fara soyayya? Yana mamakin wannan alamarin har Suka kai gida babu wani kalman da ya fito daga bakin shuairat.

* A can bangaren mr President kuwa baki yayi daga kasar waje suna tattaunawa dangane da harkokin siyasa har sun gama xasu masauki sannan daya daga cknsu ya juya yana tayasa murnar samun santaleliyar budurwa a matsayin matar da xai aura.

“Yaushe ne zamu sha biki mr President”
Mutumin ya fada ckn harshen turanci ga kuma yan news a xagaye dasu

“Nan ba da dadewa bah da yardar Allah”
Ya bada amsa kai tsaye se kuma yana mamakin ya akayi maganar ta fito daga bakinsa.


Haka Rayuwa ta kasance shuairat da yayanta sun share mako 2 basa magana duk abunda yake faruwa iyayensu basu sani bah don basu ga alamar hakan bah, shirye shiryen bikin bash da shukrah akeyi babu kama hannun yaro ynxu ya rage sati2 ayi bikin. Ya gama hada lefe akwati set daya da kaya kala 45 a ciki , lefe kam yayi kyau sai San barka mama da baba sai shirin bikin suke shuairat kam ko a jikinta kawai ta dinka anko nasu na kawayen amarya kuma ita ta zabi kalar kujerun da xaa xuba a falon amarya, suma sun canza nasu kujerun an sake wa gidan sabon fenti yayi kyau sosai ynxu kam se shirin xuwa mubi don gabatar da bikin.
Tana kwance a daki tana karanta novel din “behind our Lov” na miemie bee????
Novel din ya burgeta sosai hnklinta ya tafi ga karatun dama a watsap ne aka tura a grp din gidan gyara????teemah ashaka CE ta tura musu…wayarta ya fara ringing bakuwar lamba CE ta ja tsaki ckn jin haushin katse ta aka yi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button