NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

“????ur dad? Haba y?

Nan ta gaya mata abunda ya hadasu shuairat tace

“Haba kawa ba kyau fushi da iyaye”

“Ok tanx xan kiyaye next tym”
murmushi princess tayi a dayan bangaren a xuciya tace she is just like her bro.haka Suka cigaba da chat nasu har na tsawon lokaci sannan sukayi sallama.

Ku biyoni….????????????????????
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
39
By Reefat yahya

A airport mr President yayi sallama da mahaifinsa yana rike da hannun sultan suna dagawa daddy hannu har sun juya xasu tafi daddy ya sake dawowa gun mr President yace

“Boy is gud kaje ka gaida surukinka”

“Ok daddy xan samu lokaci”

“No! Son xanso ace yau xaka je”

“Ok insha Allah zanje”
“Ok gud na tafi sai munyi waya”

“Safe trip a gaisheda momsi”

“Ok zata ji” daga nan mr President ya ja hannun sultan Suka shiga mota Suka kama hanyar gida.
Da yamma misalin karfe 4:30 mr President yasha manyan kaya se qamshin turare ke tashi an jera motoci bash na gidan gaba tare da driver a yayinda mr President ke xaune a gidan baya hannunsa rike da magazine yana karantawa , a kofar gidansu shuairat akayi parking na motocin dama can baba ya San da xuwan surukin nasa batare da bata lokaciba Suka shiga ckn gidan bodyguards Suka tsaya a waje bash na gaba mr President na biye dashi.baba na xaune a falo Suka shigo tare da sallama bayan sun gaisa an jerawa mr President kayan marmari iri2 Amma ko ruwa bai iya ya sha bah saboda kunyan baba yake ji, basuyi wani dogon hira bah shiru Suka yi tamkar babu kowa a falon chan baba ya daure yace

“Duk da naji cewa kana kaunar ya’ta amma don Allah ina rokonka ka riketa bisa gaskiya da amana bana son wani Abu ya sameta”

“Insha Allah baba na dau alkawarin kula da ita babu abunda zai taba ta “

“Nagode! Allah ya Baku zaman lafiya da zuria mai albarka”

“Ameen” mr President ya amsa ckn jin kunya daga nan mama ta fito Suka gaisa ta koma ciki ta barsu, haka nan sukayi sallama mr President ya tafi sannan bash ya shigo da bandir din kudade ya ajiyewa baba shi kuma se fada yakeyi wai akan me bash xe karbi kudin bai sauraresa ba yayi ficewarsa saboda ana jiransa a waje xasu koma gidan mr President.


Shuairat CE zaune a dakin da aka sauketa a can Kano ta ajiye kazar da ta sha hadin magunguna a gaba ta rasa ya xata fara cinsa gashi ta taba ta jishi ba dadi anti mairo CE ta shigo tare da sallama

“Lalala..baby har yanxu baki cinye bah? Gaskiya xamu bata dake”
ta tura baki tare da yatsina fuska tace

“Allah anti ba dadi bazan iya ci bah”

“Baby ki daure haka ki ci if not xamu bata oya ..now “
Haka tasa shuairat a gaba dole ta cinyeshi tass tana maida numfashi dakyar.bayan ta huta kadan mai gyaran jiki ta fara tata aikin haka Suka yini ranar gaba daya se gyarata ake yi har dare bata huta bah wani hadin tsimi aka bata dole ta shanye.
Misalin 9:00pm ta watsa ruwa tayi shirin bacci kenan ta kwanta a gado dama dakin ita kadai CE a ciki ta bude data mssgs na watsapp dinta Suka fara shigowa se kuma wayar ta fara ringing sabuwar num ne kuma special har ya kusan tsinkewa sannan ya daga ta kara a kunne tare da sallama

“Hey reporter ina kika je ? Wato baki xaman gida koh?

“Pls who is on d line?
“Baki ban amsa bah”

“Mr president?
“Baki xaman gida ina kike xuwa?

“Mr president ko kamanta cewa am a reporter so I have….

“Luk Ayshah daga yau nayi banning duk fitanki har xuwa ranar daurin auren”

“Aww..da gaske?
“Tambaya kike? Dont u have som respect?

“Umm..am sorry”
Shiru sukayi dukkansu biyu kowannensu ya rasa abun fada daga karshe ya kashe wayar.daga can bangarensa tunani yake meyasa ma ya kirata? Kuma idan tana fita ma meyasa zai damu? Daya bangaren xuciyarsa yace of coz matata tace dole na damu, no! I don’t have too” shiii…ya sunkuyar da kai yana tunani ya kasa samun amsa ko daya.shuairat ma haka abun ya kasance mata ta kurawa wayar ido tana tunani daga karshe ta share maganar kawai ta shiga watsapp dinta Suka fara chatting da princess maimah da kuma shukrah.

Ku biyoni….
Love u all ????????????
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
40
BY Reefat yahya

Bayan sati daya aka kawo lefen shuairat mata biyu ne kacal Suka xo anyi musu kyakkyawar tarba an karbesu ckn mutunci akwati set 2 ne cike makil da kaya masu kyau Wanda bazan iya siffantasu ba sai dai masu karatu su kimanta da kansu???? daga karshe sukayi sallama Suka tafi bayan an cikasu da snacks da drinks kala2.shukrah kam se santin kayan take xubawa aikuwa tayi snapping ta tura a instagram da watsapp cewa ga kayan lefen aminiyarta amma bata bayyana cewa mr President ne xai aureta. Shuairat ma ta yaba da kayan sunyi kyau ba karya , shirye shiryen biki ake Amma mr President ya hana duk wasu programs da zaayi ciki kuwa har fansan amarya yace bayaso sabida yasan yan gulma zasu cika wajen shuairat CE zatayi walima shikenan.


“Umaima lfynki kuwa? Yarinya kin dau karan tsana kika dora akan mahaifinki bayan kinsan Allah ne ya hallata masa auren kin isa ki hana ne?

“Wllhi anti khady wannan cin amana ne yanxu shekaru nawa ne da rasuwar mom amma har ya manta da ita? Se kuma ta cigaba da kukanta anti khady ta sake baki tana kallonta sannan ta cigaba da cewa

“Nidai baxan goyi bayanki ba umaima wannan ai rashin gaskiya CE , Allah ya halasta masa auren mata 4 ke kice baki so yayi auren? So kike ya kare rayuwarsa haka?

“Anti kinga yarinyar karamace fah wllhi tun bata shigo ba ya daina kulamu kuma…

“Ki bude kunnuwanki kiji abunda zan gaya miki, ki tashi ki koma ki bawa mahaifinki hakuri ki rungumi kaddara ki xauna lafiya da matarsa Allah ne ya kaddara baki isa ki hana bah “

“Gaskiya nikam baxan iya bah, ynxu dama duk son da yakewa mom ya…

“Dakata umaima bari kiji labarin da baki taba ji bah, dad da mom dinku auren xumunci aka hadasu dad naku ba shi ya nemi auren mom naku bah biyayyace ta sa ya amince ya aurota har Suka xauna tsawon xaman da sukayi.dad dinku bai taba yin soyayya a rayuwarsa bah kuma….

“Wait..an..anti kina nufin duk xaman da sukayi babu soyayya a tsakaninsu?

“Bansani ba umaima Allah shine masani nidai nasan dad mutumin kirki ne yana da kara sosai har gobe baraa sami yaro mai biyayya irinsa bah a duk fadin danginmu”
Shiru umaima tayi tana tunani kanta ya kulle kwakwalwarta ya to she anti kady CE ta dafata a kafada tace

“Kiyi hakuri ya’ta nasan kina taya mom naki kishi but koda ace tana raye itama bata da ikon hana wannan auren kiyi hakuri ki shirya ki koma gun mahifinki”

“Zan koma amma ba yanxu bah, sai bayan bikin nasu “

“Shikenan xan kira dad na fada masa kada ya tada hankalinsa gun nemanki “

“Ok anti nagode”
Haka ta cigaba da xubda hawaye tana jin wani radadi a ckn xuciyarta.


Shuairat CE a gaban dressing mirror tana kallon kanta tabbas ta canza ba kadan bah fatar jikinta se sheki yake ga gashin kanta da ya sha gyara se kuma dadaddan qamshin da yake tashi a jikinta murmushi tayi a yayinda ta cigaba da kallon fuskarta tana admiring din kanta lallai mr President yayi dace????????tunaninsa ne ya fado mata a rai fuskarsa ta hango , kyakkyawan karshene ita kanta tasan da hakan kuma yana da karamin ruwa idan bakasan shrkarunsa xaka CE Dan shekara 32 ne ta lumshe ido tana tuna farkon haduwarsu yana magana so cool yana da class sosai kuma yana da tausayi musamman idan ta tuna ranar da ya share mata hawaye lokacin da take kuka, shin zata iya soyayya dashi? Anya kuwa? Hmmmm ko kadan bata taba mafarkin cewa taxa auri babban mutum kamarsa bah sai kuma rayuwarta na baya ya fara dawo mata a kwakwalwa…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button