NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

Muje xuwa….
Reefat
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
41
By Reefat yahya

wacece shuairat???

Alh Bello mamman hafaffen garin maiha ne na jahar Adamawa su hudu ne a gun iyayensu Ahmadu Salihu bello da kuma zainabu a can garin maiha aka haifesu duka amma shi bello ya koma garin mubi da xama gun wan mahaifinsa a can yayi primary da secondary sannan ya wuce jamia ta bayero Kano a can ya karanta bangaren education, bayan ya gama ya dawo gida a Yola yayi bautar kasa a wannan lokacin ne ya hadu da Fatima ya’r layinsu mahaifinta ne limamin unguwarsu a can karamar hukumar maiha ta jihar Adamawa.
Bayan ya gama bautar kasa akayi aurensu da Fatima shi kuma ya samu aikin koyarwa a makarantar secondary na technical school a can mubi.Bello da Fatima suna son juna sosai kullum suna cike da begen juma haka Suka xauna ckn rufin asiri , sun share sama da shekara 6 Allah bai basu haihuwa bah amma duk da haka bello bai taba nuna damuwarsa bah, Fatima tayi2 ya kara aure yaki sauraranta har ta gaji don kanta ta daina kawo masa xancen.kwatsam Allah ya bata ciki sunyi murna sosai hKa Suka kasance ckn farin ciki har Allah yasa ckn ya cika wata9 da yan kwanaki Fatima ta haifi kyakkyawan danta fari tas babu inda ya bar fuskarta cki kuwa har hasken fata saboda Fatima fara CE sosai, ranar suna yaro yaci suna Basheer.

Haka Suka cigaba da rainonsa har ya girma yayi wayo aka sashi makarantar firamari har ya gama Allah be kara basu wani rabon bah , basheer ya gama primary ya shiga secondary har ya kai ss1 sannan Allah ya bawa Fatima wani ckn batun murna kam baa magana basheer duk yafi xumudi akan cikin kullum hirarsa be wuce xancen a haifa masa kanwa ya’r kyakkyawa.
Bayan wata9 ciff Fatima ta haifi kyakkyawar ya’rta wacce tayi kama da bello tamkar anyi kaki an tofar yarinyar baka CE Amma ba sosai bah tana da Dan hasken fatA , haka aka saka mata suna Aisha ana kiranta shuairat.
Shuairat ta tashi ckn gata gaba da baya koina sonta ake musamman yayanta basheer baya barin kowa ya taba ta, a wannan lokacin Alh bello yana koyarwa a jamiar federal university of technology Yola. Daga kan shuairat haihuwa ta tsaya musu cak da wannan lokacin ko bari Fatima bata sake yi bah, haka Suka rungumi yara biyun da da Allah ya basu.bash ya gama secondary dakyar ya yarda ya tafi jamia wai shi baya son ya tafi ya bar kanwarsa dakyar aka lallabashi ya tafi jamiar Ahmadu bello zaria bayan ya kammala ya dawo yayi bautar kasa sai kuma aka daukesa aiki da state security service , shekaru sun gabata Alh bello yayi retire ya koma gida yana hutawa se kuma dansa ya samu canjin aiki xuwa fadar shugabankasa a wannan lokacin ne shuairat take Jin karshe a federal polytechnic dake can mubi har ta samu ta kammala inda ta karanta bangaren mass communication…
Wannan kenan shine takaitaccen tarihin rayuwarta.

A hnkli ta ja wani gauron numfashi kamar a mafarki take ganin duk abubuwan da suke faruwa a rayuwarta “ikon Allah kenan”
ta furta a hankali ynxu matsalarta shine ya xata fara nunawa mr President so? Anya zai kulata kuwa? Wane irin zama zatayi da umaima? Tabbas tana da aiki a gaba idan batayi da gaske ba xata fuskanci matsala a gidan wayarta ta hau ruri sunan shukrah ta gani nan ta daga
“Matar Yayan”
“Amarya bakya laifi ko kin kashe Dan masu gida”

“Lallai sai dai idan baa kashe din bah , ya kike ya gidan”
“Lfy lau yaushe zaki dawo”

“Umm..kinyi missing dina ne “
“Bani kadai ba harda angon mah”

“Bangane bah”
“Ehh..mana wai dama baki gaya mishi zakiyi tafiya bane?

“Y? Meyasa xan gaya masa?
“Hmm…dazu ya tura bodyguards wai yana son ganinki”

“Uhmm..yayi kyau”
“Munafuka kina so kina nokewa”
“Ehh..sai akayi yaya”

“Nidai ki dawo da wuri kan a buga mana news paper cewa mr President yana Kano”
“Wannan kuma maysalrku “

“Uhmmm..in tayi tsami ma ji”
“Babu abunda zakuji”

“Se anjima toh “
“Ok bye sai na kira “
“Ok takkia”
Tare Suka katse wayar shuairat tayi jugum tana tunani lfy mr President yake Neman ganinta?
Oho!

Nima nace oho! Ku biyoni
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
42
By Reefat yahya

A bangaren mr President kuwa yana xaune a dakinsa yayi shiru yana tunani anya zasu zauna lfy da yarinyar nan? Ta fiye takama da nuna isa, ysushe sukayi waya amma taki ta sanar dashi cewa tayi tafiya?.mtsww meyasa ya nemi ganinta ma? Lols Reefat tace cos u miss her preety face” wayarsa ya cire yana son kiranta sau 2 yana dialing sai kuma ya fasa a karo na ukun ne yayi ta maza ya kira har ya kusan katsewa sannan ta daya ckn sanyin murya tace

“Ur excellency”
Haka kurum yaji dadin sunan da tayi adressin nasa da shi wani murmushi ne ya subuce a fuskarsa
“My stubborn first lady! Ya kike”

Murmushi tayi da jin sunan stubborn ta gane abunda yake nufi

“Am sorry ur excellency nayi tafiya ba tare da na sanar maka ba”

“Is ok! Zaki iya yin duk abinda kike so as of now b4 ki shigo gidana”

“Don’t worry a gidanka ma abunda naga dama zanyi cos am d first lady”
maganar ya sashi dariya sosai yace

“Well..we shall c! Anyway dama ina son ganinki ne saboda ina son sanin programs naki da kuma amount da kike bukata”

“Ur excellency ka kwantar da hankalinka bana bukatar komi iyayena xasu min idan ma akwai bukatar hakan”

“Nasan da haka but is my duty ..anyway zan tura miki 2mil kiyi shopping idan akwai bai isa ba let me know”

“????2wat? No! No! Me zanyi da 2milion? Walima CE zanyi fah n olredy iyayena sun riga sun tanada komi na walimar so no need pls”

“Bana son jayayya sai anjima”
Nan ya katse waya shuairat ta kurawa wayar ido tana nanatawa 2mil ? Hmmm lallai ma ai wannan almubazzaranci ne.mr president kuwa ya tsinci kansa ckn wani farin ciki haka kawai yana murmushi yana lumshe ido daga nan ya kira bash ya shaida masa yana bukatar account number din shuairat.

***\
Jirgin yamma Suka bi sai gasu nan a Abj shuairat ta kara haske fatar jikinta ta murje tayi kyau sosai duk Wanda ya daga ido ya kalleta dole ya kara kallonta a karo na biyu. Bash ne yazo daukansu ita da anti mairo da diyarta Sadiya wacce take saar shuairat daga nan Suka kama hanyar gida .
Gidansu a cike yake makil da jamaa babu masaka tsinke saboda saura 4days daurin auren shuairat , bangaren shukrah ta shiga a yayinda haj mairo ta wuce gun aminiyar tata ga danginsu nan birjik mutanen Adamawa kyawawa dasu falon shukrah a cike makil da jamaa ta sa kai tare da sallama shewa Suka fara yi wata ya’r kawun shuairat me suna Ummi ta tashi Suka rungumi juna da shuairat se ihu suke sai ga shukrah ma ta fito ta Ruga a guje Suka rungumi juna ta kalli shuairat tayi wani guntun dariya tace

“Gaskiya ne mata a gidan Dr Suleiman Muhammad first ladyn Nigeria da kanta, kasar ta kusa ta dawo hannunmu sai yanda muka juya ta”
Aikuwa sauran yan matan Suka fara shewa
“Aiyuriri …mata a gidan shugabankasa Allah ya bar mana ke”
Dakyar shuairat ta samu ta shige dakin yayanta ita da shukrah da Ummi da kuma Sadiya.shukrah ta kawo musu lafiyayyen abinci ita da Sadiya Suka ci sukayi nak sannan aka baje a gado aka fara xuba shukrah tace

“Bestie kawaye nawa kika zaba”

“Ummi da Sadiya da maimuna ya’r anti luba sai kuma Hafsat mubi”

“Ok! Dama mr President ne ya turo yayanki yazo ya tambaya kuma tym din layinki baya shiga””

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button