NI DA SHUGABANKASA

“Ok na kashe wayar ne tym da zamu tashi”
” mr President fah yana ji dake yarinya ! Kinga kalan zirga -zirgan da yan gidansa suke?
“Allah ko”
“Ehh ..mana wllhi ki rike tsohon nan da kyau don na lura yana sonki sosai”
Gaba daya Suka kwace da dariya Ummi tace
“Wa ya gaya muku shi tsoho ne? He is just 40 somtin ne fah “
Sadiya tace
“Gaskiya kam! Kimanta da zancen wani tsoho ki fito ki nuna masa so zalla Ku zauna lfy ya fiye miki wllhi, kuma kinga yana da wata shu’umar ya’ mai shgen girman kai kada ki kuskura ki bari ta rainaki wllhi”
Shuairat tayi murmushi tace
“_ina nake da lokacin ta”
Mama CE tayi sallama a bakin kofar dakin shuairat ta ruga a guje ta bude ta fada a jikinta tana dariya
“Mama na I miss u”
“Ba wani u miss me bayan kinzo kinyi zamanki a nan baki nemi gani na bah”
“Wllhi Bahaka bane! Naga mutane sunyi yawa ne”
Daga nan tabi bayan Maman nata sukayi ckn gida.
Love u my fans????????
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
43
By Reefat yahya
Karfe 4pm harabar city garden ya cika makil da manyan motoci kala2 idan ka duba can ciki bangaren da akayi decoration kuwa xaka bude baki ne galala tsantsan haduwar filin nikam xan iya cewa tunda nake ban taba ganin hadadden decoration irin haka ba???????????? dama ansan city garden waje ne mai kyau kuma babu hayaniya se kukan tsuntsaye ga kuma flowers masu kyaun gaske anyi arranging kujeru kowane table kujeru hudu na zagaye dashi an rufesu da kyalle masu kyau colors daban2 wato multi color kenan haka nan bangaren da amarya zata zauna tare da kawayenta ma multi color ne abun de sai Wanda ya gani.
Idan ka duba kujerun sun cika da jamaa dangin mr President yan uwan marigayiya matarsa zainab dangin Maman shuairat da kuma dangin babanta ko ina dai manyan mata ne ansha ado na kece raini ga yan Adamawa kyawawa sun kara haska wajen both dangin ango da na amarya duka fulanin Adamawa ne idan kaga mummuna dai yan ganyan sodi ne???????? a dayan bangaren kuwa invited guest ne ga matan ~gidan gyara~ ~Nisaul jannah~ ~professional writters~ ~Hausa novel grp~ ~dangin juna~ ~qasaitattun mata~ da dai sauransu.idan ka duba wani bangaren kuwa adda benaCE da m jabo pherty Maman shakur khaleesat haidar miemie bee Ummi Aysha da sauran online writers nima a can na xauna ina watsa rubutu na. Yan gidan TV radio da news papers duk sun hallara ana daukan live a kowane tashar TV idan ka kunna xaa hasko maka walimar Aysha (shuairat) bello matar mr President????, nayi rubutu har na gaji sai na taba miemie nace “amarya baxata zo bane” ta watsa min harara tace “tsiyata dake kenan rashin hakuri”???? daga nan naja bakina nayi shuru wani dadaddan qamshi ne ya buga hanci na ina daga kai na hango shuairat tare da tawagarta????????????
Mutuwar xaune nayi halamcy CE ta saka hannu ta tare min baki na Wanda saura kiris ya fada kasa…hmmm kawai na ajiye Biro na nace baxan iya siffanta irin wannan kyawun bah sai Ku jira afrah idan ta gama da jumaiya se ta siffanta muku kyaun da shuairat tayi.????????????Amarya da kawayenta Suka sauna a filin da aka tanada musu nan kuwa yan jarida Suka fara daukansu hoto wal…wal hasken kamera kawai nake gani sai kuma aka bude taro da adua nan malama Maryam ta fara gabatar da waazi akan hakkin aure da rayuwar aure a musulunci.haka aka cigaba da taron masu video recording nayi masu daukan hoto nayi ga yan jarida iri2 ga reportrs din tambari magazine ga JF ma sun tura Mahmud Wanda kansa me kallon kasa yana jin wani radadi har ckn ransa .Karfe 6pm aka raba souvenirs iri2 har da kayan makeups a ciki abinci kuwa dama table by table aka raba daga nan akayi adua sannan kowa ya fara shirin komawa gida a yayinda wasu sukaje daukan pix tare da amarya dakyar ta samu hanya wannan ma don bodyguards ne.
????????????
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
44
By Reefat yahya
Yau aka daura auren Ayshat bello maiha tare da Alh Suleiman Muhammad mayo ( PhD) akan sadaki naira 100k jamaa da dama Suka halarci daurin auren manyan kusocin gwamnati tare da manyan sarakuna ta kasashe daban-daban ga mutane dai talaka da masu arziki , yan jarida suna nan birjik an daura aure lfy aka watse daga nan villa Suka wuce akayi hadadden reception kowa ya ci ya sha sannan aka watse ango de furkarsa na dauke da murmushi .
A can bangaren amarya kuwa ta sha kwalliya ckn wata hadaddiyar shadda masu kyau da tsada ga gwalagwalai carkaf a kunne da wuyarta tayi kyau tmkar a saceta a gudu tana zaune a bangaren shukrah tare da kawayenta.ta buga wani uban tagumi shukrah CE ta shugo tare da sallama
“Amarya bakya laifi ko kin kashe sultan lolz”
“Hmmm…lallai mah rufa min asiri kan a jiki”
“Tashi muje an tura camera man yazo ana ta daukar hotuna”
“Kuje Ku dauka nikam na gaji”
“Haba ranki shi Dade, kinsan gobe war haka fah ganinki sai da ticket ki tashi muje muyi last card pls”
“Mttsww…me wani na cewa last card sai kace mutuwa zanyi”
Su Ummi suna mata dariya haka Suka fita akayi ta daukan hotuna da yan uwa da abokan arziki.
Tun Karfe 5 shuairat ta shiga wanka tare da anti mairo har magrib suna ckn bayi shiru kawai kake ji na so zuwa in gano me ya sukeyi acan Amma ba dama haka na hakura na zuba ido.by 7 Suka fito amarya sai qamshi take tmkar anyi barin turare dakin mama Suka wuce ta saka wasu atamfa ya’r super mai uban kyau da tsada batayi wani makeup bah dakin babanta aka kaita ya mata nasiha sosai tAna kuka Suka koma dakin mama a can aka kawo mata dafaffiyar kaza ta sha hadi sosai dole ta cinyeshi Tass sabida anti mairo ta sata a gaba, mama CE ta shigo haj mairo tace
“Mutuniyar idan akwai abunda zaki gaya mata kiyi sauri cos ance by 8 zamu wuce da ita gidan mijin nata”
Mama ta sunkuyar da kai tace “ba komi duk abunda ya dace ki sanar da ita ” daga nan ta tashi ta tafi haj mairo ta kara fesheta da turare sannan Suka wuce bangaren yayanta baya nan Mr president ya kirashi haka suka zauna ckn shiri by8 Suka ji tsayuwar motoci . duk yanda shuairat taso ganin mamanta don suyi sallama abun ya gagara firr mama taki fitowa haka Suka hakura yan raka amarya Suka shirya Suka fito shuairat kam se kuka take anti mairo na bata hakuri daga nan akayi mota da ita.
Motocine masu kyau se sheki sukeyi gasu nan birjik sai Wanda ka zaba daga nan Suka dau hanyar villa.
Bayan sun iso gidan aka wuce wani dankareren building upstairs ne mai kyau gaskiya bazan bata lokacina ina zayyana muku tsaruwar ginin bah kawai de kunsan gdn shugabankasa kam????????karshen kyawu kenan. Yan rakiyar amarya sun zaga building din ko ina suna ta yabawa , an nuna musu dakunan daga nan anti mairo ta sallami kowa ya rage daga ita sai kawayen amarya da wata yar mama se kuma kanwar baban su shuairat. Dangin ango sun shigo wasu mata kyawawa su 6 Suka shigo musu maraba tare da ajiye musu abinci mai rai da lfy sannan Suka tafi. Kawayenta daki daban aka ware musu ita amaryar kuwa da anti mairo zata kwana, bayan sunyi shirin kwanciya Karfe 11pm anti mairo ta ajiye shuairat ta fara mata nasiha..
“Baby kiyi hkri bansan ko kina son mijinki koma yaya ne ki daure ki fara sonshi ki koyawa kanki yanda zaki so shi , haka nan shima ki koya masa sonki ki dasa sonki a ckn zuciyarsa Ku zauna lfy.yi nayi bari na bari kuyi hkri da juna wannan shine zaman aure, bauta ne ya kawoki ba wani Abu ba aljannarki kika zo nema kiyi kokari ki kasance mai faranta ran mijinki.ki zauna lfy da kowa ki mutunta kowa nashi ki daraja iyayensa ki girmamasu ki kula da dukiyarsa da ya’yansa, fada da umaima ba naki bane ki kame girmanki kada raini ya shiga tsakaninku…haka dai anti mairo ta cigaba da mata nasiha masu ratsa jiki daga karshe Suka kwanta.