NI DA SHUGABANKASA

“Allah ya miki albarka nagode sosai ki fitar dani kunya tnx much Allah ya biyaki”
“Amee..men” dakyar ta amsa daga nan ya sake ta yace
“
“Muje ki kwanta dare yayi”
Nan ya rike hannunta Suka fita gidan shiru sai securities ke kaiwa da komowa sunata kallon Mr president hannunsa tsarke ckn na matarsa suna taku a hnkli farinwata da hasken fitillun gidan sun haska koina , haka Suka cigaba da tafiya har xuwa bangaren shuairat aka bude musu kofa a tuaninta nan zai dakata da rakiyar se kuma taga ya biyota har dakin bacci ya bude kofar ga mamakinsa sultan ya gani kwance yana sharar baccinsa ya juya Suka hada ido tayi murmushi nan ya sake mata hannu ya koma kusa da sultan ya shafa kansa tare da tofa masa aduoi daga nan ya tashi yace
“Nagode sosai gud nite”
“Nite” ta fada a hnkli daga nan ya sa kai ya tafi tare da rufe musu kofar yana tafiya yana murmushi shi kadai yasan abunda yake ji.
????????????????ku biyoni kusha labari
Reefat ce
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
48
By Reefat yahya
Shuairat ta gama shirin kwanciya tsaf tayi aduoin bacci ta kwanta sai kuma abubuwan da Suka faru tsakaninta da Mr president ne yake yawo a kwakwalwarta haka nan ta tsinci kanta ckn wani farin ciki he is so calm bashi da matsala tabbas idan haka yake toh lallai zasu zauna lfy.haka dai ta cigaba da sake sakenta har bacci yayi awon gaba da ita.
A bangaren Mr president ma hakan ta kasance Sam ..ya kasa yin bacci fuskar shuairat yake gani idan ya rufe idanunsa dama matarsa wayayyiya ce? Daman haka take da kyau? She is so cute n presentable.tabbas yayi dace kuma yaji dadin ganin sultan a dakinta da alama tana son yara kuma xata rike masa sultan da amana , haka nan ta faranta masa rai haka ya cigaba da sake sake har bacci ya daukesa ba tare da ya sani bah.
Asuban fari shuairat ta tashi tayi wanka tare da daura alwala tayi nafilfilun ta sannan tayi sallar asuba tayi lazimi bayan ta gama tayi adua ta shafa sannan ta koma bakin gado ta zauna a hnkli ta fara shafa kan sultan bayan wani Dan lookaci ya bude ido a hnkli tace
“Boy tashi kayi sallah koh”
Ckn muryan bacci yace
“Um um anty nikam ki bari ba ynxu bah”
“Haba my boy jiya fa cemin kayi kana son ka shiga aljannah ka tuna?
Kai ya gyada mata tayi murmushi tace
“Good! Duk Wanda baya sallah akan lokaci bazai shiga aljannah bah, oya get up”
Nan kuwa sultan ya tashi ya shige toilet yayi alwala ya fito ta shinfida masa sallaya ya tada sallah tana zaune tana kula da yanda yake sallar a natse lallai ko ya iya batayi mmki bah sabida a hiran da sukayi ya gaya mata akwai malamin da yake xuwa har gida yana karantar dashi.bayan ya idar da sallah nan ya koma gado ya kwanta shuairat tace
“Boy ba gaisuwa ne?
Murmushi yayi yace
“Morning anty!
Ta shafa kansa tace
“Morning my boy! Ynxu se mu dau Qur’an mu karanta koh”
“Anty bacci nake ji kuma kinsan anjima zanje skul “
“I knw my boy! But pls mu karanta koda 5pages ne se mu koma bacci koh
“No! 5pages yayi yawa”
“Ok 3pages koh”
Dakyar ta lallabashi ya karanta pages 2 na suratul baqarah sannan ya kwanta , ita kuma ta cigaba da karatu har 6:30 sannan ta wuce falo nan ta hadu da masu aiki suna xuba gaisuwa ta bukaci su kawo mata kayan makarantar sultan babu bata lkci kuwa aka kawo duk abunda zai bukata ta bada umarnin a shirya masa kayan kari sannan ta koma daki.
Karfe 7am masu aikin sultan Suka nemi izinin ganin sultan saboda xaa mishi wanka ya tafi skul, shuairat ta hana.ita kanta ta masa wanka ta shirya sa ckn kayan makaranta ya fito fes dashi ta fesa masa turare itama ta sha wanka tayi ado ckn atamfar super masu kyau ta ajiye dankwali ga gashin kanta ya kwanta a kafada tayi kyau sosai tana rike da hannun sultan Suka fito falo masu aikin Suka kura musu ido tabbas sunyi kyau sosai.
Dinning area Suka wuce a nan ta zuba masa abinci yaci sosai tana xuba mishi hira ckn raha tana biye wa duk shirmensa har ya gama aka kai jaka da lunchbox nasa a mota.an bude motar ana jiran fitowarsa shuairat ta rike hannunsa tace
“Muje ka gaida dady koh”
Ba musu Suka wuce bangaren Mr president masu aikin Suka xuba musu ido ckn shaawar ganin sabon chanjin rayuwa da sultan ya samu.a hnkli ta tura kofar dakin da take tunanin dakin barcinsa ne sabida basu tarar dashi a falo bah, ta shigo tare da sallama yana zaune da Qur’an a hannunsa bayan ya rufe qur’anin ya amsa sallamar nan Suka hada ido shuairat tayi saurin dauke kanta
“Good morning ur Excellency”
“Morning hw was ur nite dafatan kun tashi lfy mom sultan”
Wani kayataccen murmushn jin dadi tayi saboda sunan da ya kirata dashi
” lfy alhamdulillh dady sultan hop kaima haka”
“Alhamdulillh”
“Dady good morning”
Sultan ya furta bayan ya karasa kusa da mahaifin nasa
“Morning my boy “
“Laa..dady kaga anty ma boy take kirana fah
Murmushin jin dadi yayi yana kallon shuairat wacce kanta ke kallon kasa
“Dady kaga yau na karanta Qur’an har 2pages ni da anty
“Wow…am so happy my boy kip it up koh Allah ya muku albarka da kai da antyn naka “
“Ameen dady”
Shuairat ce ta katse hiran nasu ta hanyar cewa
“My boy kamanta mota na jiranka kar kayi latti let’s go”
Ya tashi tsaye yace
“Bye dad na tafi”
“Ok takkia ayi karatu banda wasa koh”
“Ok dad zanyi cos anty tace idan ina karatu sosai zata siyamin yacht kuma zan shiga aljannah”
Dariya sosai Mr president yayi yana kallon shuairat gwanin birgewa yace
“Ok a dawo lfy”
Daga nan Suka fita Suka bar dakin ya bisu da kallon shaawa shi ganin shuairat yake tmkar ita ta haifi sultan nan da nan wani farin ciki ya ziyarci xuciyarsa ya manta da duk wani bakin ckn da yake cki a da tabbas maganar dadynsa gaskiya ne da yace masa shuairat zata zame musu alkairi a rayuwa zata kawo musu farin ciki , gashi tun baaje ko ina bah ya tsinci kansa ckn farin cki Mara misali.
Ku biyoni love u my fans masu turamin mssg ta private tnx alot I love u all????????????
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
49
By Reefat yahya
Shuairat ta raka sultan a bakin mota suna dagawa juna hannu har ya bace mata da gani sannan ta wuce bangaren momsi a falo ta sameta tana xaune da carbi a hannu ta karasa tare da sallama sun gaisa ckn girmamawa ta amsa tana mai faraa daga nan ta bukaci shuairat ta jira daddy ya fito su gaisa bayan yan mintuna Alh Mohammed ya shigo falon fuskarsa dauke da murmushi Suka gaisa da shuairat daga nan ta musu sallama ta koma bangarenta daki ta shige ta haye gado tayi kwanciyarta wayarta ce ta hau ruri layin anti mairo ta gani nan ta daga
“Ina kwana anty”
“Amarsu ta ango an tashi lfy ya gida ya kadaici”
“Alhamdulillh anty dafatan kuna lfy”
“Lfy me kikeyi haka”
“Wllhi ynxu na dawo daga rakiyar sultan ya tafi skul shine nace bari na samu bacci kadan”
“Kaji min yarinya da shirme..sultan kika aura ko ubansa? Bazaki je ki duba lfyar mijinki bah se dansa?
“Anti naje mun gaisa fah dazu”
“Haba baby..ynxu duk abubuwan da na gaya miki sun tashi a banza kenan? Mijinki ne bazaki je ki kula dashi bah ki tabbatar yaci abinci yayi shirin office sannan ki mike a gado wai bacci zakiyi ? Anya zaki sinana abun kirki kenan..
“Eyya fah anty..
Ta fada ckn shagwaba
“Eyya me? Ki tashi maza ynxun nan kije ki kula da mijinki ki tabbatar ya shirya ya fita office kan ki dawo kiyi baccin..aikin me zakiyi girki ko shara? Eyye..
Haka dai anti mairo ta dinga balbale shuairat da balai ba shiri ta tashi bayan sunyi sallama ta sake fesa turare ta kara makeup kamar yanda Antin ta umarceta ta tsaya a gaban dressing mirror ita kunyan masu aikin gidan take ji , ya zaayi ta dinga shiga tana fita a bangaren Mr president ? Ya ilahi ya zatayi?
Haka ta daure ta fito bayan ta yafa veil nata se uban kamshi ke tashi ta fito tana taku dai2 har ta fito nan bodyguards Suka bude mata mota duk da cewa ba wani nisa bane Amma abunka da manya haka aka ajiyeta a bangaren Mr president ta fito bayan an bude mata kofa ana xuba gaisuwa tana amsawa ckn sakin fuska nan Suka gaisa da yayanta shima se kallonta yake daga nan ta wuce ciki .baya falonsa don haka dakin bacci ta wuce direct ta kwankwasa tare da sallama ta tura kofar carab Suka hada ido yana tsaye ya gama shiryawa yana rike da turare a hnkli ta karasa tare da karban turaren a hNnunsa ba tare da tayi magana ba shi kuma ya bita da ido ta fesa masa koina ckn kasaita da wani irin salo, Mr president de ya xuba mata ido kawai bai CE ko uffan bah bayan ta gama ta ajiye ta sake daukan wani haka ta fesa masa turare har kala5 a hnkli ta daga kanta Suka hada ido ckn jin kunya tace