NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

“Sorry ur exceelency na barka kai kadai “

Murmushi ya sakar mata daga nan ta juya ta dauko hulan da ta gani a kan gado ta saka masa a kai sai kuma tace

“Muje kaci abinci koh”
Falo Suka fito a Jere har dinning area ga abinci nan kala2 a Jere ba abinda babu ta tambayeshi abunda yake bukata yam freets ne da sausage rolls yaci sannan ya dora da coffee .ita kam bata wani sake sosai ba kunyarsa take ji chips da sauce din kwai take ci a hnkli tmkar bata so yana kurba coffee yana kallonta tana da natsuwa sosai tana yin komai ckn tsari babu rawar kai, samm…bai taba tunanin cewa haka halinta yake bah yana ganintane a matsayin futsararriya wacce zata…

“Mr president yaushe umaima xata dawo”
Muryar shuairat CE ya katse masa tunani har ga Allah shi ya manta da xancen wata umaima

“Ohh..umaima! I rily don’t knw gskiya cos mun kwana2 bamuyi communicating bah”

“Haba dadyn sultan.. Me yasa?

“Mom sultan ni na haifi umaima at least I deserved som respect amma ta raina ni batajin magana ta ko kadan”

“C’mon dad sultan she is a kid lallabata zakayi ka…

“Aysha! Let’s not talk abt dis ok!

“Ok sir! Am sorry kayi hakuri na shiga affairs din familynka koh…sorry”
Nan ta ajiye fork din hannunta ta tashi idanunta sun cika da kwallah tayi hanyar kofa ba shiri mr president yabi bayanta baiyi wata2 bah ya jawota ta fada jikinsa nan ta fara kuka a hnkli ya rungumeta yana shafa bayanta alamar rarrashi sai ajiyar xuciya take a hnkli ya furta

“Am sorry mom sultan I din min 2hurt u..
Ta cigaba da kukanta bata saurareshi bah haka Suka kasance ya sake cewa

“Pls mana Aysha wadu munyal( yi hakuri ..da yarensu????) am sorry ok..
Ta dan sagaita kukan yana murmushi yNa shafa kanta dankwalinta ne ya zame zai fadi Mr president yayi saurin rikewa ..wow…kitsonta ne ya bayyana kanana masu kyau ga gashin ya bazu a baya da kafadanta ya kurawa gashin ido nan ta daga kanta da yake kwance a kirjinsa Suka kurawa juna ido , ita ta fara dauke nata shi kuwa murmushi yayi

“Ya’r shagwabar baba da mama ..am sorry koh”
Kai ta sunkuya ckn jin kunya sannan ta xumbura baki tana magana ckn shagwaba tayi rau-rau da ido tace

“Ba Kaine kamin tsawa bah”
Ya rike mata hannu yana murmushi yace

“Am sorry my first lady nayi laifi a yafe min ok!
Bash ne ya tura kofar tare da sallama carab Suka hada ido da shuairat yayi saurin sunkuyar da kai ya gabatar da gaisuwarsa sannan ya shaidawa Mr president cewa daddy na bukatar ganinsu da shuairat nan Suka amsa da cewa suna nan tafe , daga nan bash ya juya ya bar falon.
Shuairat ta sunkuyar da kai ckn jin kunya tace

“Nikam bazan kara xuwa side dinka bah kullum securities suyi ta kallona zasu ce bani da kunya”
Yana murza yatsunta a hnkli yana murmushi yace

“Toh me ne? Ba matata bace?
Ta gyara dankwalinta Suka fito ajere bodyguards Suka diban gaisuwa gun Mr president yana amsawa ckn sakin fuska da faraar da basu taba ganinsa dashi bah…

Ku biyoni????????????
[2/21, 2:39 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
50
By Reefat yahya

An kawo mota a gaban Mr president ya daga musu hannu alamar cewa da kafa zasu taka haka ko akayi suna tfya suna hira sama sama da shuairat ita kanta tana mamakin halayen Mr president da tana ganin tmkar idan sunyi aure zai wulakanta ta Amma sai taga sabanin hakan.
John ya bude baki yana kallonsu bash ya juya ya dafe kafadarsa yace
“Me haka john”
“Bash am rily happy 4mr president, ban taba ganin irin wannan murmushn a fuskarsa ba tun bayan rasuwar matarsa sai yau.lallai yana bala’in son wannan yarinyar”

Murmushn jin dadine ya bayyana a fuskar bash duk da cewa har yau in banda Mr president da daddynsa babu Wanda yasan cewa shuairat kanwarsa ce , ya juya yace
“Gaskiya naga alama suna son juna sosai , ni har kunyar shiga side din Mr president nake ji cos dazu ma na samesu suna soyewa”

“Hmmm..ai ni naga love jiya da dare, ina ganin Mr president ya tsufa Ashe de ya kware .kaga wani warm hug da ya bawa matarsa jiya? Na shiga basu ganni ba sai na fito ai @ 380…
Me bash zaiyi in ba dariya bah haka Suka cigaba da yaba irin kulawan da Mr president ke bawa amaryar tasa.

A falo Suka tarar da daddy da momsi Mr president ya wuce gun momsi tana zaune a 3seater nan yayi kwanciyarsa ya kwantar da kansa akan cinyarta tana dariya tace

“Hoo…boy baka San ka girma bane”
Shuairat kuwa mamkine ya bayyana a fuskarta wai dama haka Mr president yake xuba shagwaba a gun iyayensa? Muryan daddy ne ya katse ta

“Com hre boy! Rabu da momsi ai dama nagaya mata ni nafi sonka dawo nan ka kwanta”
Gaba daya Suka yi dariya shuairat kuwa kunyansu take ji ba gardama Mr president ya tashi ya koma kusa da mahaifinsa ya jingina kansa a jikin daddy .momsi tace

“Taho nan ya’ta wannan mijin naki bashi da kunya haka daddynsa ke biye masa suyi ta xuba shirme”
Kan shuairat na kallon kasa kawai jin momsi tayi kusa da ita tana daga kanta Suka hada ido momsi ta cigaba da cewa

“Ba kunya tsakanin mu ki daukeni tamkar mamanki kinji koh”
Kai ta gyada Mr president yace
“Momsi ita wannan ta fini shagwaba fah”
“Ba dole tayi bah! Ita karamar yarinya ce kai kuma fah?
Daddy yayi carab yace

“Shima karamin yaro ne a guna har yau ganin yaro nake masa”
Haka dai Suka cigaba da hirarsu ckn nishadi gwanin birgewa daga nan aka Dora da nasiha akan su xauna lfy haka nan momsi ma tayi tata nasihar mai ratsa jiki gaba daya jikinsu yayi sanyi kowannensu da tunanin da yakeyi a ckn xuci Mr president yana tunanin anya zai iya tunkarar shuairat a matsayin su raya sunnah har ya samowa iyayensa farin ckn da suke nema? Hmmm …akwai aiki kenan.daga nan daddy ya sanar dasu cewa jirgin yamma zasu bi su koma Lagos yau.shuairat bata ji dadin hakan bah cos momsi na debe mata kewa, haka Suka kasance sannan Mr president yayi sallama da cewa zashi office. Daga nan itama ta koma bangarenta tayi lfyar gado nan bacci yayi gaba da ita.


Bayan kwana2 da komawar su momsi da daddy zaman kadaici ya isheta sabida Mr president yana nan busy ckn kwana biyun basu hadu bah , sultan ne ke Dan rage mata kadaicin idan ya tafi skul kuwa shikenan zatayi bacci idan ta gaji tayi kallo tayi karatun Qur’an shikenan.
Yauma tana zaune misalin 2:30pm sultan se 5yake dawowa don yana xuwan islamiyya , ta rasa me zatayi sai ta bude watsap dinta rabon da ta shiga tun kafin aurenta yakai 1week kenan.aikuwa shukrah da princess meemah suna online nan Suka fara chatting shukrah na zolayarta wai amarci ya boyeta kurum ta daina hawa online, haka nan princess meemah tace tayi missing nata har laasar sannan ta ajiye wayar ta tashi don gabatar da sallah.

Haka rayuwa ta kasance har shuairat ta fara sabawa da al-amuran gidan shugabankasa , yau ta share 2weeks kenan a gidan kuma basa haduwa da Mr president idan taje sai ace yana meeting har 11 na dare zatayi ta jiransa bazata samu ganinsa bah sai dai ya tura text yana tambayar lfyarsu itada Sultan.
Da yamma tana xaune a falo ana sefe mata kai tana chatting da shukrah bodyguards ne Suka fara shigo da kaya bata damu bah, wata kofa aka bude Wanda tun xuwarta gidan bata taba ganin an bude part din ba sai yau…umaima CE ta shigo tare da sallama masu aiki suna mata maraba ko kallo basu isheta bah shuairat kuwa ko daga kanta batayi bah hakan ba karamin batawa umaima rai yayi bah.ckn gadara ta karasa kusa da shuairat tace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button