NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

” kije dakin ki ina xuwa” daga nan ya ja shukrah Suka bar kitchen wani kishine ya turnuke umaima nan ta koma daki ta cigaba da kukanta tasan lallai ta rasa bash har abada idan ta tuna yanda yake lallaba shukrah sai ta ji wani tsananin kishinsa..hmmm anya burinta ze cika?

Muje xuwa????????
[2/21, 2:41 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
67
By Reefat yahya

A daki bash yake bawa shukrah baki
“Haba my love ki Dan rage kishin nan mana ai zata raina ki..kuma ni ban ce miki ina sonta ba meyasa zaki damu kanki she is just lyk a 6ter to me pls kidaina wannan haukan”
“Ohh..hauka kace koh? Toh shikenan zaka ga haukan wllhi xanyi maganinta..zancen so kuma ai naga kwayar idonta sonka ne zalla a ciki, wllhi bazan barta bah”
Dariya sosai bash yayi sannan yace

“Hohh..shukrah! Dama haka kike da kishin tsiya?
Ta tura baki ckn shagwaba tace
“Dariya kake min koh..wllhi ni nasan tana sonka kuma kaima kana sonta kawai boyewa kake”
“Ok naji tana sona ..amma trust me ba komai tsakanimu kinji? Ki kwantar da hnklinki , aiki kuma idan kina janta a jiki ita da kanta xataji shaawar koya ba sai kin nuna mata karfi bah pls my love kiyi respecting din kanki ok”
Kai ta gyada masa haka nan ya lallaba abarsa sai gashi ta sakko abunka da mata da miji har ya mantar da ita xancen wata umaima ckn salon soyayyarsa nan Suka lula sararin samaniya duniyar masoya????????.
Umaima tun tana sa ran xuwansa har ta fidda rai tayi kuka mai isarta lallai namiji munafuki ne ynxu ya shanyata yana can tare da matarsa yana bata kulawa hmmm ke kuma a suwa? Hakane bata dawani matsayi a gunsa haka ta kwanta a gado ckn rashin kwarin guiwa.
Bayan 1hr ya shigo dakin tare da sallama ckn shigar kananan kaya yayi kyau sosai ga sajenasa kwance luf-luff se qamshin turare ke tashi a jikinsa yayi kyau sosai umaima ta kura mishi ido babu ko keftawa har ya karasa kan kujera ya xauna fuskarsa dauke da murmushi yace
“Em..sorry sis kinji ni shiru koh”
“Ah..ah ba komai “
Ta furta a hnkli se yaji tausayinta ya kamashi tabbas yasan kadaici na addabarta a rayuwa bata da abokin hira se TV ko waya don bai taba ganinta da kawaye bah toh saurayi fah?ya daga kansa Suka hada ido har ynxu kallonsa take ckn tsananin kunya ta dauke kanta

“Yadai ko nayi kama da wani ne?
“Wani? Kamar waye kenan?
“Oho..maybe mr right”
“Hmmm..kai kasan wannan”
” ohh..ke baki sani ba kenan, yawwa gskiya fa umaima baki taba hadani da bro-inlaw na bah ko rowarsa ake mana”
Haushin maganganun take ji wato shi bata taba burgeshi bah koh..Allah sarki baisan tana yi bah , nan kwalla ya cika mata ido

“Umaima lfy..ko tambayan da na miki ne? Am sorry pls”
“No..is ok ba komai”
“Akwai mana..gashi kina Neman xub da hawaye ko kun rabu ne shiyasa kika tunashi kina son yin kuka”
Ckn haushi tace
“Ya mutu”
????????????????bash yaso yin dariya amma ya gimtse don daga ganin yadda tayi maganr yasan karyace don haka yaja bakinsa yayi shiru.haka Suka xauna har tsawon minti10 babu Wanda ya sake cewa komai don haka bash ya tashi yabar mata dakin ta fada gado ta cigaba da kukan rashin masoyin nata.haka rayuwa ta kasance ba laifi ynxu shukrah na amsa gaisuwarta kuma ta daina takura mata , waleed ya fara sabawa da umaima haka nan sultan ma yana xuwa su yini idan babu makaranta.umaima kuwa tana xuwan tasu makarantar amma har yau bata da kawaye ko abokai, mr Joshua kuwa shi yake kula da al’amuran kasar..Rayuwa kenan.


Shuairat ta share wata 2 da xuwa hong Kong ynxu wata3 kenan da kwanciyar mr president rashin lfy amma har yau bai farfado bah..wani lokaci shuairat gani take tmkar ya rasu kawai boye musu akeyi bayan likitoci kuwa sun bata tabbacin cewa zai warke don haka ta dage da adu’a ba dare ba rana tana yawan karanta masa Qur’an a saitin kunne haka nan tana tofa masa wasu ayoyin, nafilar dare kuma ba’a magana .daddy da momsi kafarsu2 suna xuwa haka nan bash ma yaje sau1 umaima kam duk nacinta daddy ya hana sabida cewa yayi idan taje hnklinta zai tashi.
Shuairat tana xaune apple ne a hannunta tana taunawa a hnkli mr president yana kwance a gadon marasa lfy na’urori ne iri2* makale a jikinsa ga kuma ledojin ruwa. Jankim CE ta shigo tana murmushi ta fara magana da turanci

“Maman bby gskiya babyn nan namu mayen apple ne..kusan kullum shine abincin ki fah”
“Jankim sarkin xolaya..wani bby kike nufi”
Ta karasa kusa da mr president ta fara dudduba na’urorin tana gyarawa tace
“Shu..ai..zaki cemin baki San cikine da ke bah”
“Watt??????????da gaske?
“Ehh..tun farkon haduwarmu na lura kina da ciki”
Mamakine ko murna ko bakin ciki wanne xatayi? Jankim ta bude Jakarta ta dauko kayan aikinta tace

“Muje na gwada ki”
Ba musu Suka wuce dakin da aka tanada don likitoci babu abunda babu a ciki nan da nan ta gama test din ya nuna musu result shuairat tana dauke da juna 2 na tsawon wata 3 ciff sai kuma ta kwanta akayi scanning sun duba komi.murna ne fal ckn ranta sai kuma hawayen tunawa da halin da uban yake ciki sai kuma ta tuna cewa rabonta da period tun a najeriya daga nan suka fita sun sayi magunguna da abubuwan kara lfy har nafila shuairat tayi ta godewa Allah sannan ta roki Allah ya bawa mr president lfy .
Haka ta cigaba da rainon ckn, jankim CE ke debe mata kewa first lady ma ta dawo daga tafiyar da tayi ta jajantawa shuairat haka nan manyan mutane na yawan xuwa duba mr president wasu abokanan aiki ne wasu kuma shuwagabannin kasace daban2* ga tarin duniya da suke xuwa dashi kudade kam ba’a magana shuairat tana turawa a account don bata bukatar komai Chinese president yana matukar kulawa dasu.
Ynxu ckn nata ya shiga wata4 ta kara cika tayi kyau sosai gwanin sha’awa tayi haske kamar me…ta shigo dakin tare da sallama kamar yanda ta saba duk tasan cewa babu me amsawa ta nemi kujera kusa dashi ta xauna ta kura masa ido
“Masoyin yaushe zaka tashi ne we rily missed u nida little… Pls get well soon Allah ya baka lfy”
Hawayen idonta take sharewa sai me??? Alamar ya motsa ta gani tayi waje da ido ta kara masawa

“My man…mafarki nake ne ko da gaske????????
Nan ma ya Dan motsa yatsa ckn hnzri ta gudu kiran jankim..tare Suka shigo nan ta kira likitoci ta sanar dasu ckn kankanin lkc Suka taru a dakin tabbas ya farka ynxu yana jin komai kuma memorynsa is ok a kowane lokaci zai tuna da rayuwarsa na baya don haka ake bukatan shuairat ta dinga zama kusa dashi don ya tuna komai, yana jin komai amma ba lallai bane ya fara magana ynxu .ranar shuairat ta kwana da farin ciki nafilfilu ta dinga yi bata samu bacci sai da safe sannan ta koma bacci.
Haka ta kasance ckn kula da mijin nata kullum tana bashi lbri kala2* na najeriya tare da nuna masa hotuna ..har ynxu motsi kawai yakeyi idanunsa ma a kafe suke sai daga baya ya fara ita kefta su.daddy ya xo ya dubashi yaji dadi sosai haka ya xubawa shuairat albarka nan ta nemi alfarma a gina musu gida a can najeriya kan su dawo, daddy ya shaida mata mr president yana da gidaje da dama sai dai a gyara hakan kuwa akayi yana komawa aka turawa bash kudi ya bada kwangilar sake gidan Nas dake garki babu bata lokaci aka fara aiki.


Bayan wata2 Alhamdulillh mr president yaji sauki sosai har ya fara takawa tamkar karamin yaro haka ake koya masa tfy shuairat kuwa cknta ya Dan fito ta zama abunda shaawa duk Wanda ya kalleta dole ya maida ido ita take koya masa tfyar ya tuna komai na rayuwarsa na baya amma har ynxu baya son yin magana shiru kawai sai dai murmushi.
Yau suna xaune a masaukinsu ta ajiye masa magunguna a gaba ya hada fuska da alama baya son sha nan shuairat ta juya masa baya alamar tayi fushi ba shiri taji ya rungumeta ta baya
“Am sorry swt hrt”
Ya mata rada a kunne ckn mamaki ta juya suna fuskantar juna
“Mr..mr president dama kana magana? Na dauka ka samu problem fah”
Murmushi ya mata sannan ya jawota a jiki ya kankameta sosai har bata iya motsi mai kyau hawaye ne ya fara diga yana kuka ya fara magana a hnkli
“Nagode!! Nagode!! Nagode!! Nana Aysha ke ya’r aljannah CE insha Allah..Allah ya miki albarka ya baki duk abunda kike bukata duniya da lahira..ya baki ya’ya masu albarka bazan manta dake ba har karshen Rayuwata ..bazan tozartaki ba..ya Allah ka bani ikon rike wannan baiwa taka..ya Allah ka yafe mata dukkan zunubanta..ya Allah ka bata gida a aljannah ka biya mata bukatunta ameen…I love u Aysha”
Ya kara kankameta shuairat ma kukan farin ciki take ya Dan raba jikinsa da nata yana kallonta yace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button