NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

Mr president ne yayi wannan furucin a yayinda yake shigowa nan kuwa yayi sallama ya koma kusa da shuairat ya xauna umaima ta xare jikinta tana murmushi tace

“Congrats dad”
“Tank u ya exam”
“Alhamdulillh”
“Allah ya taimaka ya bada sa’a kuma Allah yasa a gama lafiya”
“Ameen dad nagode”

“Ina fatan de baki da examz gobe “
“Ehh..har jibi ma bani dashi”
Dariya sukayi shuairat tace

“Ina ruwan umaima sarkin son yawo”
Umaima tana dariya tace
“Allah ina matukar son kano ne”
Dad ya juya yana murmushi yace
“Kodai a can surukin nawa yake”
Shuairat tayi saurin cewa

“Who knows ..nifa ban taba ganin wani yazo wajenta fah”
“Kyaleta..na bata nan da 1month ta fito da miji don tana gama final examz nata na next semester da 1week zan aurar da ita”

Umaima ta shagwabe fuska tace
“Haba dad..kamar ka gaji dani”
“Toh umaima zaman me zakimin? So kike na ajiyeki nayi ta kallo?..ynxu idan wani ya shigo ya ganki tare da Aysha ma ai se a rasa wacece matata a tsakaninku”

Shuairat me xatayi inba dariya bah..umaima kuwa tamkar xatayi kuka nan ta tashi tana tafiya dad yace mata
“Mark my words girl..am not joking”
Shuairat ta juya tana kallonsa tace

“Da gaske kake?
“Yeah…am serious wllhi, matukar lokacin da na bata ya wuce bata gabatar da kowa bah ni zan zaba mata duk wanda naga dama”

“Haba swt hrt ya xakayi haka”
“Don’t worry..u will c Allah ya nuna mana lokacin”
“Ameen…
Nan ya jawota a jikinsa yana cewa

“Com here!..kin ajiyeni ko wlcm kiss baki min ba kun cikani da surutu”
Wani passionate kiss ya fara mata dakyar ta kwace kanta tana cewa
“Haba falo muke fah..baka tunanin wani ya shigo”
Murmushi yayi yace
“Babu mai shigowa don kuwa na basu rules na gidan babu wanda zai shiga last floor matukar ba ke kika nemesu bah”
Bai jira amsarta ba ya cigaba da kissing nata salman ne ya farka yana Neman abincinsa ba shiri Suka sake juna mr president ya shafa kai tare da cewa

“Gaskiya daddy na kana yawan shiga hakki na fah”
Dariya shuairat take masa sannan ta dauki salman tana basa nono mr president kuwa ya xauna a gefe yana masa wasa yaron se dariya yake
Shuairat tace

“Kana sa shi dariya idan ya kware ba ruwana”
“Da ruwanki”
Suna hira suna dariya.

A can ckn daki kuwa umaima ta kwanta tayi shiru tunanin kalaman mahaifin nata take ..tasan halinsa idan ya fadi magana baya canzawa , hankalinta ya tashi tabbas akwai matsala ita tasan duk duniya babu wanda take so sama da bash amma har yau bai furta yana sonta bah shin ya xatayi?
Zuwa xatayi ta zayyana masa halin da take ciki ko kuwa mahaifin nata xata fadawa? Haka ta kasance ckn rudani dakyar ta tashi ta shirya kayanta misalin 4pm jirginsu ya daga xuwa kano tana faman Neman bash a airport Amma Sam bata ganshi bah.
Bayan sallar isha suna zaune a falonsu dama mr president yana da gida a garin kano don haka can Suka sauka falo 2 ne a gidan da dakuna 6 se kitchen da dinning area daga waje kuma bangaren baki ne. Xaune suke a dayan falon shuairat tana kallon news umaima ta xauna shiru ta buga uban tagumi sultan kuwa yana wasa da salman , kamar daga sama Suka jiyo sallamar bash ya shigo tare da waleed nan kuwa sultan ya ruga a guje yayi hugging dinsa
“Oyoyo uncle Nah..
“My boy ya kke “
“Lfy uncle nayi kewarka sosai kuma nagode da ka kawomin kani Nah”
Nan sultan ya rike hannun waleed Suka koma gun salman Suka cigaba da masa wasa. Bash ya xauna Suka gaisa da shuairat tna kallonsa tace

“Ina maman waleed na dauka tare xaku zo”
“Nop…na barta a gida”
“Y?…haba my yaya “
“Bazaki gane bane baby..dama ina son muyi wata magana amma se mun koma ABJ”

“Hop de lafiya”
“Umm..kedai ki bari mu koma”
“Toh..Allah ya kaimu”
“Ameen “ya amsa a gajarce yana satan kallon umaima wacce tayi nisa ckn tunani yayi Dan kasa da Murya yace

“Ita waccan meyake damunta”
Murmushi shuairat tayi sannan tace
“Ita da dad ne as usual”
Daga nan bash ya tashi ba tare da ya kalli bangaren umaima ba ya sallami shuairat yayi ficewarsa.

Hmmm…wace irin magana bash xeyi da shuairat kodai batun umaima ne????????????????????

Muje xuwa…..
[2/21, 2:41 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
79
BY Reefat yahya

10pm mr president ya shigo ya sanarda umaima ta hadawa bash tea ta kai masa yana dayan falon xuciyarta na harbawa dole ta tashi ta hada sai kuma ta xumbula dogon hijab ta nufi falon ta shigo tare da sallama firgigit ya amsa dama yayi nisa ckn tunani suna hada ido tayi saurin dauke kanta nan ta ajiye masa cup din ta juya xata tafi ya kira sunanta a hnkli
“Umaima!
Cak…ta tsaya ba tare da ta juya bah ya sake cewa

“Dawo ki xauna”
Ba musu ta dawo ta xauna a kujerar da yake kallon nasa
“Umaima meyake damunki”
“Kaima meyake damun ka?
Murmushi yayi wanda ya Kara fito da kyawunsa yace
“Ni nace miki wani Abu yana damuna ne?
“Toh.. Ni na gaya maka nawa ne?

“Umaima fuskarki ta nuna kina ckn matsala tell me”
“Kaima ai fuskar taka ce ta nuna hakan”
Shiru yayi daga bisani yace
“Bansan yaushe kika fara boyemin matsalolinki bah..da can baya har nemana kike idan kina ckn matsala Amma ynxu ki canzamin I donno y”

“Hmmm…naga babu amfanin hakan ne shiyasa”
“Haba umaima…don na kasa furta miki Kalmar so?
???????????????? ta daga kanta Suka hada ido tayi saurin sauke nata daga ta mike zumbur ta bar masa falon.tagumi bash yayi..shidai yasan yana matukar kaunar umaima tun ba yau bah Amma Sam …ya kasa gaya mata hakan don gani yake tamkar tafi karfinsa bata dace dashi bah, mahaifinta babban mutum ne mai arziki shiyasa yake ganin kamar soyayyan nasu baxata yiwu bah..duk da cewa ya gane irin tsananin son da take masa Amma shi bazai iya tunkarar mr president da wannan zancen bah.

Umaima tana kwance bacci ya kaurace mata sai tunanin kyakkyawar fuskar bash take gani ..tana sonsa kamar ta hadiyeshi Amma tayi alkawarin danne wannan son matukar bai fito ya furta cewa yana sonta bah ta gwammace sonsa ya zamo ajalinta akan ta bude baki ta gaya masa duk da yagane halin da take ciki.
A bangaren bash ma hakan ta kasance sai faman sake2* yake ga uwa uba canjin da ya fuskanta a gun shukrah. ..kwata2* ta daina kulasa abinci ma sau1 take a rana ga kuma bukatarsa Sam ta daina amincewa dashi..abun duniya ya masa yawa dakyar bacci barawo ya saci wadannan masoyan biyu.

Taro yai taro jamaa ne makil duk inda ka duba ga kuma yan Chinese yawanci sune ma’aikatan katafaren kamfanin mai suna
AS4 textile industry bayan an kaddamar da bude sabon kamfanin aka raba abinci da sauran abubuwa daga karshe aka rufe taro da adua ga yan jarida nan birjik sai daukan rahoto suke..ckn kamfanin Suka shiga tare da iyalansa da sauran abokan arxiki daddy ma ya halarci taron yana rike da salman duk yawon da suke story building ne mai kyawun gaske ga ofishin maaikata nan birjik abun de ya hadu.
Har bayan azahar Suka dugunxuma xuwa gida dama da masu aiki Suka zo don haka bayan sunyi sallah Suka baje a dinning, daddy shuairat mr president umaima sultan bash waleed se kuma salman take hannun kakansa suna cin abinci suna barkwanci gwanin sha’awa daddy yayi gyaran murya ya fara magana

“Dama zancen umaima ne boy, akwai wani abokina yace yana nemawa dansa aurenta shine nace sai nazo zamuyi maganar”
???????????????? umaima ta zare ido tace
“Haba daddy…

“Ke rufemin baki shashasha kawai..kina ajin karshe a jami’a me ya rage miki?
Mr president ne yace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button