NI DA SHUGABANKASA

“Yi hakuri daddy daman nima na gaya mata idan ta gama da 1week zan aurar da ita kuma…
“Gafara can…dama ba kai kake biye mata bah, idan ba kam dage bama da zan bari tayi karatun jami’an ne?…toh nidai na gama magana aure de dole tayi ko taki ko taso”
“Sorry daddy Nah..ba ina goyon bayanta bane but na bata damane ta fito da wanda take so sai ayi auren”
“Bana son shiririta ita wannan ka taba ganin wani yazo wajenta ne? Ba ta dauki girman kan tsiya ta dorawa kanta bah..gani take tmkar tafi karfin kowa “
Sai ynxu shuairat tasa baki tace
“Allah ya huci xuciyarka daddy insha Allah xaayi auren nan ba da dadewa bah”
Sai ynxu yayi murmushi ckn jin dadi yace
“Yawwa Ya’r albarka ynxu naji magana..kinga mijin naki da ya’rtaki duk mashirmata ne rabu dasu “
Murmushi shuairat tayi ta kashewa mr president ido sannan tace
“Don’t worry daddy kam kwantar da hankalinka “
“Tank u my Dota…am now counting on u”
“Trust me daddy”
Daga nan Suka fara hirarsu mr president kam yasha jinin jikinsa bash kuwa sai Satan kallon umaima take ita kuwa ta cika tayi famm..murmushi yayi ya mata gwalo batare da kowa ya gani bah yace
“Gaskiya gara a aurar da ita da wuri daddy..don kuwa ta fara tsufa”
“Yawwa ganemin hanya dai basheeru..mu a zamaninmu mace tana 13-14 zaa aurar da ita Amma ynxu yahudu ya bata muku rayuwa kuna nan kuna biyewa bokon banza”
Umaima dama kiris take jira nan ta fara kuka ta tashi tabar dinning daki ta wuce shuairat ta harari yayan nata tace
“Se kaje ka lallabata ai..kasan halinta sarai Amma kake tsokanarta”
Daddy yace
“Rabu da wannan shagwababbiyar “
Dama abunda bash yake so kenan..don haka ya tashi yabi bayanta mr president kuwa ya cigaba da cin abincinsa sultan kuwa sun koma falo da waleed. daddy ya juya yana kallon Dan nasa yace
“Boy wai fushi kayi “
Shiru bai amsa bah daddy ya shafa kansa yace
“C’mon..smile my boy, kam tsufa ai fushi ba naka bane “
Ya hada rai yace
“Toh..daddy ba Kaine kake min fada akan laifin da ba nawa ba”
????????????????????shuairat bata San lokacin da dariya ya kubce mata bah tace
“Oh…dad sultan yaranka suyi shagwaba kaima kayi?
“Daddy ka jita koh..
“Yi hakuri boy din daddy duk laifina ne OK”
Haka daddy ya cigaba da lallaba mr president tamkar wani karamin yaro shuairat kuwa sai tsokanarsa take tana mamakin irin son da daddy yakewa dannasa Sam baya so yaga bacin ransa ko kadan.
Umaima kuwa ta fada gado tana rusa kuka ..ita ba kalaman bash ne damuwarta ba aa xancen hadata da wani da daddy yayi ne ya daga mata hankali ..shikenan ta rasa bash har abada! Ya shigo ya tsaya yana kallonta bata ji shigowarsa bah ya nemi kujera ya xauna a hnkli ya furta
“Tashi ki xauna magana xamuyi”
Ta juya jajayen idanunta tace
“Baka da abunda zaka gaya min kawai ka fita ka barmin daki “
“Look umaima am sorry bansan kalamai na zasu bata miki rai haka bah…am sorry pls”
..hmmm lallai ma wato ba zuwa yayi yace yana sonta ba kawai yaxo bata hakuri akan silly maganar da yayi dazu? Bash y? Meyasa yake wahalar da xuciyRta?…umaima CE ke wannan tunanin hawaye wani na bin wani ta nuna masa kofa ckn tsawa tace
“Out of my sight ..now!
“Sorry…
“I said…out…nowww!
Ta karasa ckn daga murya nan ya juya ya fita ckn bacin rai ita kuwa ta kara fashewa da wani sabon kuka
“Shikenan na rasashi har abada”
“Baki rasashi bah matukar ina Raye…babu abunda zaki nema a duniya ki rasashi umaima”
???????????? ta juya don tabbatar da abunda kunnuwanta Suka jiye mata …carab! Suka hada ido….
Muje xuwa…
[2/21, 2:41 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
80
By Reefat yahya
dis page is dedicated to Rabeah majeed???? tnx 4ur kia
N ~2all fanz of nida shugabankasa ina sonku sosai..mr president ma yana sonku. Jameelah feekah n co, tnx to u all~
Umaima tana daga kanta Suka hada ido da shuairat tayi saurin sunkuyar da kai shuairat ta karasa tare da rungumarta tana rarrashinta umaima kuwa sai hawaye ke fita a idonta tana kuka ..wani irin radadi take ji a ckn xuciyarta
“Umaima am sorry..I donno hw u feel abt dis but am very sory”
Ta share hawayen da yake xuba tace
“Mom pls..ki taimakamin ina sonsa bazan iya rayuwa idan babu shi bah”
“Zaki rayu insha Allah..ki kwantar da hankalinki burin ki zai cika ckn kankanin lokaci”
“Kina nufin zaki taimakeni”
“Matukar hakan zai sanyaya ranki umaima I can do dat 4u”
Nan umaima ta kankameta ta cigaba da kuka tana cewa
“Tnx so much…I Lov u mom sultan”
“Shhhh…ya isa haka bana son ki sake cewa komai, kiyi shiru da bakinki ki xuba ido..yaya zaixo ya durkusa a gabanki ya furta miki kalmar so harma ya nemi ixinin aurenki I promise”
Haka shuairat ta cigaba da bawa umaima hakuri dakyar ta daina kuka daga nan Suka tashi don gabatar da sallan la’asar.
D next day Suka koma ABJ daddy ya wuce Lagos umaima bata kara saka bash a ido bah duk tabi ta damu.
Da dare shuairat tana xaune a falo aka sanar da ita xuwan yayan nata nan ta bada ixinin shigowa dama ita kadai CE a falon ya shigo tare da sallama ta amsa Suka gaisa ya fara magana
“Baby magana zamuyi ta fahimtar juna pls..kada ki boyemin komai ok”
“Ok my yaya..go ahead”
“Baby.. Kin xauna da shukrah sama da 10yrs kinfi kowa sanin halayenta shin wai dama kinsan bata da halaye na gari shine kika bada shawara na aureta?
Tambayar yaxo mata a bazata..ita ta dauka zancen umaima zasuyi…muryarsa ne ya dawo da ita daga tunanin
“Answer me…”
“Umm..emmm yaya u knw wat”
“C…baby don’t dare lie to me ki fadamin gaskiya”
“Calm down pls yaya…meya faru tsakaninka shukrah just tellmi”
“Babu abunda bai faru bah..shukrah ta canzamin gaba daya, she is now a monster”
“Subhanallah..yaya y u saying dis…
Idanun bash sun kada sunyi jaa dakyar yace
“Bazan boye miki u r my 6* n she is ur friend.. Baby nayi nadamar auren shukrah”
“Innalillahi…abunda shuairat take nanatawa kenan dakyar ta daure tace
“Yaya am very sory abt dat…but kowa yasan shukrah is a good person maybe zugin kawaye ne “
Tsaki yaja Sam babu mafita don haka xumbur ya mike ya mata sai da safe yayi tafiyarsa , shuairat ta kasa motsawa daga inda take lallai shukrah na ckn matsala dole ta nemi hanyar da zata bi ta daidaita tsakanin su. Dare yayi sosai tana nan xaune a falon gaba daya ta rasa me ke mata dadi, mr president ne ya shigo ya sameta da taimakonsa ta rage yawan tunanin da take sukayi shirin kwanciya.
***bayan 2weeks umaima ta gama jarabawar first semester dinsu saura semester daya ta gama makarantar Hutu na musamman mr president ya shirya musu dama sultan suna Hutu , tafiyar kasar China ya shirya musu xasu kaiwa Chinese president xiyara a hong kong daga can zasu je Singapore da kuma Korea ..murna tamkar suyi yaya nan kuwa ya kira bash ya sanar dashi cewa tare zasuyi tafiyar don haka ya shirya shi da iyalinsa duk zasu tafi.
Ckn tsananin farin cki ya wuce gida yasan dole zasu shirya da shukrah a Daren yau matukar taji wannan kyakkyawan albishir don kuwa zaman nasu har ynxu babu wani sauyi tana gallaza masa son ranta…bash yana da hakuri sosai samun irinsa a wannan xamanin se a tona, bai taba gayawa wani sirrin zaman nasu bah face shuairat itama bai sanar da ita komai bah…ya shigo falonsu babu kowa daki ya wuce kofar a bude take yasa kai xe shiga kenan Amma abunda kunnuwansa sukaji yasa yayi Saurin komawa da baya ya labe a gefe yana sauke numfashi… Shukrah tana magana ne a waya tana kuka tace