NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

***washe garin…mr president ya raka shuairat da umaima airport jirginsu ya daga xuwa Dubai ya rage dashi da sultan kadai a gida. Umaima se kuka take shuairat tana rarrashinta a haka Suka kasance a ckn jirgin ma babu abunda take sai kuka.
Bash yana xaune a ofishinsa yayi jugum..tunanin duniya ya addabesa ynxu shikenan an rabashi da umaima ?? Yau saura 3weeks auren ta da wani bashi bah ..kwankwasa kofa akayi sectry dinsa ne ya shigo ya shaida masa yayi bakuwa ba tare da wani dogon tunani bah yace a shigo da ita.yana xaune ta shigo qamshin turarenta ya gauraye ofishin gaba daya ba shiri basheer ya daga kansa fara ce Sol daga ganin hasken nata na mai ne tana tauna cingam ji kake kas! Kas!! Wata shaidaniyar doguwar Riga ce a jikinta Wanda ya matseta gam Rabin kirjinta duka a bayyane fatee kenan…hannu ta daga masa ckn salon Jan hankali tare da cewa

“Hi basheer am fateemah “
“Aw daz gud..fateema me Ke tafe dake ?
“Well..actually ba wani Abu bah illa so da kauna”
Ckn Sauri ya daga idonsa ya jefa mata wani mugun kallo bata ji ko darr ba ta cigaba da cewa

“Na Dade ina kaunar ka baaheer, a rayuwata ban taba son wani namiji bah sai kai..pls ka amince muyi aure”
Wani murmushi yayi sannan yace

“Wai ba kece Ya’r uwar shukrah da ta kawo mata ziyara kwanakin baya bah”
“Yeah…u r right anyi haka Ashe dai baka manta dani bah”
Ya juya idanunsa tamkar mai shirin yin bacci ya nuna kofa tare da cewa
“U can leave pls..
“C’mon basheer kasan nafi matar ka da komai kuma ynxu ita bata da wani amfani tunda ba haihuwa xatayi bah”
Ya bude ido sosai yana mamakin kalamanta ya akayi tasan shukrah baxata kara haihuwa bah??…wato shi ya rike maganar as sirri bai sanarwa kowa bah amma ita tana can tana yada kanta tana tona masa asiri..tirr da halaye irin nata.
“Kayi shiru my love, ko kana bukatan lokacin tunani?
Ya watsa mata wani mugun kallo tare da cewa

“Tunani? Koda a ce matan duniya sun kare kece autar mata , wllhi na hakura gara na mutu banyi aure bah akan na aure ki fateema”
Daga nan ya tashi ya bude kofa yace
“Out..now”
Ta gyara xama tana wani juya idanu taji saukan mari tass! Sai da taga taurari..ya nuna ta da dan yatsa yace

“Ki lura da inda zakiyi iskancinki ni ba sa’ar yin ki bane , ki kula..kada na kara ganinki fita ki ban waje “
Ya karasa maganar ckn tsawa nan take ta fisge Jakarta tayi waje hawaye na bin kuncinta Marin ya shiga sosai???????????? tunda take a rayuwar ta babu Wanda ya taba cin xarafinta irin na yau, taxi ta tare ta gaya masa inda xata je ta biya kudin Suka dau hanya.
Shukrah tana xaune tayi nisa ckn tunani hawayene Ke sauka daga idanunta taji kamar motsi nan ta tashi Suka yi ido 4 da fatee ta rike kugu tana murmusawa ckn xafin nama shukrah ta cafke wuyar rigar ta

“Azzaluma me kike nema a gidana”
Wani irin dariya fatee take sannan tace
“Haba sahibar ki ce fah”
“Zan kasheki fatee kowa ya huta”
“Allah sarki yarinya har kisa kika koya..abun yayi sosai idan kin kasheni se ki karasa rayuwarki a gidan kurkuku umaima kuwa ta aure mijinki suyi rayuwarsu ckn so da kauna”
Shukrah ta sassauta rikon tana kallonta murmushi fatee tayi a karo na 2 daga bisani ta cigaba da cewa

“Oh…Ashe dai kinyi tunani mai kyau, ina son kisan cewa ba wai naxo Neman gafara kan abubuwan da na saki aikatawa bah ah ‘ah..nazo ne don sanar dake cewa burina na son auren mijinki bai cika bah, kuma mijinki yana yan yana shirin kara aure nan da sati 3 xai auri umaima Ya’r gidan shugabankasa na da.ynxu haka suna kasar waje tare da aminiyarki suna siyayyan aure kuma…..

Shukrah bata bari ta karasa maganar ba shaketa sosai tamkar xata kai fatee lahira ckn daga murya tace

“Karya kike bakar munafuka me bakar aniya..
“Wllhi da gaske nake , idan baki yarda bah ki kira aminiyar taki ki tambayeta suna ina xata gaya miki”
Shukrah ta xame ta xauna a kasa ta tallabo kanta dake faman tsarawa a hnkli ta CE
“Fatee da gaske baban waleed zai auri umaima ? Kuma har ansa rana shine baxai sanar dani bah”
“Ehh..dama ina da masu bani labarin duk wani movement din mijinki su Suka gaya min abunda yake shirin faruwa”
Shukrah ta fashe da kuka mai ban tausayi fatee kam ta warce Jakarta tace

“Toh shukrah sahiba! A rungumi kaddara a kiyaye gaba kinga tafiyata sai wata rana tunda ma Allah yaso ki mijin naki yaki amincewa da aurena da kukan zaifi na ynxu don haka ki godewa Allah umaima xaa kawo miki ba niba”
Daga na tasa kai tayi ficewarta tana faman gyara gaban rigarta tana kunkuni tana cewa
“Boka kuwa xeci uwarsa ba ni xai yiwa karya bah…hmm gashi bukata bata biya bah wllhi xai gwammace kida da kara2”
????????????

Muje xuwa
[2/21, 2:42 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
92
By Reefat yahya

sorry fans bana yawan posting dese days pls bear wit me kunsan duniya up n down ???????? just busy hre n dre ne kawai..Lov u all, godiya gareku masoyana masu turamin mssgs ta private da masu kirana a waya tnx a lot Lov u all

Fatee tana son raba tsakanin shuairat da shukrah shiyasa ta sanar da ita cewa basheer zai auri umaima..tana barin gidan ta xarce filin jirgin kasa don komawa kd.
Shukrah kuwa babu abinda take sai aikin kuka tana jin xuciyarta tamkar xata fito fili wani haushin shuairat take ji tasan tabbas aikinta ne hada auren bash da umaima lallai sai ta dauki mataki akansu duka xata nuna musu kuskuren da Suka tafka..umaima kuwa xatayi regret.

A can UAE wato birnin Dubai shuairat ce take shiga da fita xuwa kasuwanni daban2* umaima dai se kallo don bata xabi ko cokali bah haka nan shuairat ta fita sabgarta kullum a kasuwa suke yini idan sun koma masaukinsu kuma shuairat xata kira masu gyaran jiki a gyarata duk da bata so.
Haka Suka kasance har tsawon sati 2 sannan sukayi haramar dawowa 9ja.
Bayan dawowarsu da 2days aka kawo lefe akwati set3 da tulin kaya masu kyau da sada, daga nan aka soma shirye2*n biki yau saura 1 week ciff.duk yadda bash yaso ganin umaima abun ya faskara saboda shuairat ta gindaya mata sharuda sosai bata xuwan ko ina kullum tana ckn dakin baccinta gashi an kwace wayarta bata aiki se kuka, ga yan uwa sun fara xuwa shuairat se shiga da fita take Sam bata da lokacin xama ita ta kira tela yaxo har gida ya karbi dinkunan da xaa yi, mr president ya bude bakin aljihu ya xuba kudi sosai duk abunda ake bukata sun rigada sun siya ..
Shuairat ce kwance a dakinta salman yana gefe yaron ya girma yayi wayo sosai gashi da girman jiki tamkar ya’yan turawa ga fara’a ga kyau tubarakallah..mr president ya shigo yana waya bayan ya gama ya juya gun matarsa suna fuskantar juna
” sorry my Lady gskiya kina kokari Allah ya miki albarka”
“Ameen my man”
tana murmushi ta koma kusa dashi ta xauna tare da cewa
“Nasan ka gaji kwanta na maka tausa”
Babu gardama ya mike akan gado kwanciya yayi rub da cki nan ta fara masa tausa har wani lumshe ido yake tamkar mai shirin bacci shuairat tace

“Dad umaima”
“Uhmm..
“Pls gida nake son xuwa “
“Yaushe?
“Ko xuwa anjima “
“Ba damuwa ki shirya driver ya kai ki”
“Tnx swt hrt”
Ta manna masa peck a kumatu murmushi yake haka ta cigaba da masa tausa har bacci yayi awon gaba dashi.
Ta gama shirinta tsab ta shirya salman sun yi kyau sosai ta sanar da masu aiki kan cewa su kula da umaima xata je gidansu baxata Dade bah, daga nan ta wuce gun mota driver ya ja Suka dau hanyar xuwan gidan su.
Falon babanta ta fara xuwa yana xaune da carbi a hannu dayake baa dde da yin sallar axahar bah..yana ganinta fuskarsa ya fadada da murmushi yace
“Ya’r baba..Barka da xuwa”
“Yawwa..
Waje ta nema kusa dashi ta xauna yasa hannu ya karbi salman yana cewa
“Waii…haka kike fama da wannan lukutin Alhajin yana wahalar min dake”
Dariya kawai take musu gskiya salman akwai nauyi kamar my boy haneef????????.
Mama ta shigo tare da sallama ta tabe baki da ganin shuairat tace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button