NI DA SHUGABANKASA

“Oh..ni Fatima wato kedai kin nuna kinfi son mahaifin naki a kaina ..ah yayi kyau”
“Fateema wai kishi kike dani”
Baba ya fada yana dariya shuairat ta tashi ta fada jikin mama
“Mamana I miss u”
“Ba wani nan kin nuna kinfi damuwa akan mahaifinki”
“A’a mama kema kinsan ina sonku gaba daya”
Suna dariya mama ta dauki salman tana cewa
“Maigida nasan kai kam kafi sona koh”
Salman se wage baki yake kamar yana jin abunda take cewa baba ya karbe maganar yana cewa
“Wannan Dan lukutin maigidan naki yana ramar min da ya’ “
“Alhaji kodai kishine”
“Haba..kishi da wannan maigidan ba chefene”
Suna ta raha daga karshe Suka gaisa mama ta kawo mata ruwa tasha Suka baje suna hira shuairat tace
“Ina majnoon neh kwana 2 bana ganinsa “
“Waye kuma majnoon”
Mama ta tambaya tana mai kallon shuairat
“Hhhhh.. Yaya bash mana”
Duka mama ta kai mata nan ta goce tana dariya tace
“Ehh..mana ai sunan ya dace dashi majnoon baban soyayya ko romeo ne”
“Bayan kun hanashi Ya’r taku me kuma xaki fada”
“Eyya mama rabone babu”
“Kiji dashi…Allah xai bashi wata”
Baba de se dariya yake musu haka shuairat ta yini har bayan sallan laasar ta tashi da cewa xataje gun shukrah kafin ta koma gida daga nan sukayi sallama tana rokon mama akan cewa don Allah taxo bikin , har mota Suka rabu nan driver ya ja Suka wuce gidan bash.
Shukrah tana xaune ta buga uban tagumi tunani fal a ckn xuciyar ta kamar a mafarki taji sallamar shuairat bata amsa bah shuairat tasa kai ta shigo falon tana faman sauke salman tare da cewa
“Kai mata kina nan shine baki amsa sallama ta bah, tunanin me kike haka”
Wata muguwar harara shukrah ta jefa mata tare da Jan dogon tsaki tace
“Allah wadaran naka ya lalace..mutum yayi asara tunda munafurci da hassada yasa a gaba”
Ckn rashin fahimta shuairat tace
“Ke kuwa waya tabo ki da yamma haka”
Dama jira take nan shukrah ta tashi tsaye tace
“Ke shuairat kada ki mayardani shashasha..kina jina, bayan kin gama hada munafurcin ki xaki xo kina raina min wayo..
“Haba shukrah meyayi xafi haka?
“Ehh..lallai kin nunamin halin yan duniya.ni kike tambaya? Hmm..shuairat kenan tsabar rashin kunya da bushewar ido har xaki iya fuskantata ki…
“Dakata madam! Bana son kwana2* ki fito fili ki gayamin meke faruwa”
“Danakari! Lallai yarinya kina da mugun rainin hnkli..bayan kin gama munafurcinki xaki dawo ki fake ki nuna Ke baki San komai bah??
Shuairat tayi jugum..wai meke faruwa ne?
Me shukrah take nufi??
Ni Reefat nace???????? kodai xancen auren ya tabbata ne??
Toh…muje xuwa dai
Dr Reefat????????????
[2/21, 2:42 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
93
By Reefat yahya
Shuairat taja wani gauron numfashi tace
“Look bestie..let’s sit down n..
“Bestie! ..hmmm tsohon suna “
Shukrah ta tare numfashnta sannan ta cigaba da cewa
“Shuairat a da can baya idan wani ya gayamin cewa xaki iya aikata abunda kika min a ynxu wllhi baxan taba yarda bah amma ba abun mmki bane dama haka amintaka ta gada…cin amana da yaudara da munafurci”
“Haba shukrah wat r u talking about.. Nifa kin sani ckn duhu”
“Kinga malama ki tattara ki barmin gida Nah ..ko sai nan ma xaki nunamin gidan Dan uwanki ne?
“Pls shukrah let’s talk abit “
“I don’t want to…just get out now”
Shukrah ta fada tana nuna hanyar fita nan shuairat ta sabi salman tasa shi a kafada ta kama hanyar fita idanunta sun cika da kwalla tana mamakin sauyin halin shukrah kuma ta rasa gane dalilin.driver yana ganinta yayi saurin bude mata gidan baya ta xauna ya tada mota Suka koma gida.
Tana isowa ta share hawayen da ya bata mata fuska sannan ta karasa ckn gida baki ne a cike da falon suna ganinta Suka fara mata sannu da dawowa itama tana musu barka da xuwa se rawar jiki sukeyi a kanta wata ta karbe salman tana cewa
“Fine boy ya kke”
Dangin mahaifiyar umaima ne da kuwa wasu daga ckn yan uwan mr president sauran kuma washe garin xasu taho , shuairat ta shiga musu hidima se yabonta ake bayan ta tanada musu komai duk cewa masu aiki sun Riga sun kawo musu abinci har magrib ta samu ta koma dakinta tayi sallah bayan ta idar ta samu ta watsa ruwa har ynxu salman yana gun yan uwansa don haka ta shirya a nitse ta saka wata simple doguwar riga Mara nauyi ta fesa jikinta da turare nan ta kwanta a gado kalaman shukrah ne Ke yawo a kwa2lwarta ta rasa gane inda maganganun Suka dosa, mr president ya shigo har ya karasa kusa da ita ba tare da ta sani bah hannu taji ana shafa fuskarta yasa tayi saurin dagowa ya jawota a jiknsa ya rungumeta tamkar jira take nan ta fashe masa da kuka dakyar ya rarrasheta ta daina kukan wani light kiss ya mata na 2 mins sannan ya kwantar da kanta a saman kirjinsa tayi luff ta kwanta sosai ckn Muryar rada yace
“Tell me…
Babu gardama ta xayyana masa komai bata hakuri yake bata yana nuna mata cewa ta kwantar da hankalinta wataran xasu shirya daga nan ya fara mata wasu abubuwan da yasa ta manta da damuwar da take cki.
Washegari …daddy da momsi Suka zo ga gida de a cike makil babu masaka tsinke a ckn dangin nata ne shuairat ta xabi kawaye 4 ta basu anko din ta shirya dinner hadadde bayan an daura aurene xaa yi , umaima kam tace ba ruwanta a cki ko walimah baxata yi bah..dakin umaima ta shiga ta xauna a gefen gado umaima ta tashi xaune tace
“Don Allah mom sultan ki taimaka ki barni naga uncle bash..wllhi ba dadewa zanyi bah kawai sallama zamuyi”
“Bbu inda zaki..so kike ki jawo min magana gun daddy koh, toh wllhi babu ruwana a cki”
” haba mana…eyya mom plsss”
ta marairaice shuairat tace
“xan kirashi yaxo nan gidan ya sameki”
” ehh..na amince don Allah ki taimaka”
Ta bata tausayi ba kadan bah..nan ta cire wayarta yayi ringing har ya katse baa daga bah, ta sake kira har sau3 daga bisani ya daga a wahalce yake magana
“Salamu alaikum”
Gaban shuairat ya fadi badai rashin umaima ne ya kwantar dashi haka bah ya salam! Muryarsa ne ya katse tunanin da take
“Baki jina ne”
“Yaya ina ji meyake damunka naji voice naka somhw”
tsaki yaja yace
“Wani Dan xaxxabine yake damuna amma naji sauki”
“Ahm..dama umaima ce take son ganin ka “
“Da gaske? tana ina?
“Yaya..tek it easy pls, kaxo gida ynxu amma kada ka bari mr president yasan da xuwan naka ok”
“Ok gani nan xuwa”
Nan ya kashe wayar tausayinsu ne ya kama shuairat jikinta ya mutu ta juya ga mmkinta hawayene a idon umaima tace
“Mom sultan kin gani koh…wllhi yana sona nasan yana ckn tashin hnkli ynxu”
“Umaima kiyi hakuri babu ynda muka iya umarnin iyaye ne Allah yasa hakan shine mafi alheri “
“No…ba alheri bane ni nasan aurena da uncle bash shine mafi alkairi “
Nan ta fashe da kuka shuairat tana bata hakuri dakyar ta sagaita kukan daga nan ta tashi tayi wanka ta xauna xaman jiran masoyin nata.
Har yamma babu labarin bash ga layinsa bayya shiga umaima ta birkita shuairat gaba daya ta xama tamkar wata mahaukaciya tun suna boyewa har jamaa Suka gane sun fara tambayar shuairat ko lfy shuairat de ce musu take kan umaima ta tuna da mahifiyarta shiyake sanyata yawan kuka.
Da dare suna xaune sunyi jugum shuairat ma ta shiga damuwa don rashin samun layin Dan uwan nata gashi tana kiran layin iyayen nata basa dagawa babu halin ta fita kuma don mr president baya gida.haka ta hakura momsi ta shigo dakin suna Dan taba hira sama2* dakyar Suka lallaba umaima ta yarda taci abinci, kadan ta ci ta kwanta.
11pm mr president ya shigo a wannan lokacin shuairat ta gama shirin bacci ta kwanta amma baccin yaki xuwa , ya shigo tare da sallama ta tarbesa tare da kawo masa abinci bayan ya gama wanka ya fito ya ci abincin sarai ya lura da halin da take cki amma ya share nan ya hau gado ya kwanta ckn sanyin murya ta kirasa
“Swt hrt!
“My lady yaya?
“Uhm..dama numban yaya bash ne baya shiga”
“Meya faru kuma meyasa kike nemansa”
“Uhm..dama ..daman “
Sai kuma tayi shiru ta rasa karyar da xata shirya ya kura mata ido yace
“Ina sauraronki”
“Uhm..numban mama ne idan na kira bata dagawa shine nake son ji ko lfy”
Murmushi yayi ya jawota yace