NI DA SHUGABANKASA

NI DA SHUGABANKASA

Ya shigo tare da sallama babu kowa a falon direct dakin baccinsu ya wuce ya kwankwasa kofa
“Waye? Umaima ta fada ckn wani irin muryar da bazaka tantance ba
Yasa kai ya shigo tare da sallama tana xaune a saman gado sultan kuwa yana bacci a kan cinyarta , ya daga kai Suka hada ido idanunta sunyi ja kamar jini xai fita da alama dai itama taci kuka yaji tausayin yaran sosai.
A gefe ya xauna umaima ta kawar da fuskanta gefe ya rasa ta ina zai fara chan yace
” baby am so…
” dad! Muna lafiya kalau as u can c little ma dakyar yayi bacci yanxu sabida yau birthday din sa ya tuna da mom”
Hawayene ya kara diga a fuskar ta bayan tana kirkiro murmushin karfin hali.
Ya ilahi! Har ya manta yau birthdayn dansa? Me yake damunsa ne ? Tabbas ya cutar dasu Amma ta ina xai fara
” umaima kuyi hakuri nasan…

” oh dad kar ka damu nasan aikine ya rikeka u almost fgt dat muna existing a duniya ma”
“Umaima pls…
“Dad is ok! Muna Iya Rayuwa ko babu kai, muna cin abinci ana bamu kudi muna shiga motar da muka ga dama me yafi wannan dadi a Rayuwa?
Sam ta hanashi magana a hnkli ya jawota jikinsa ya rungumeta nan ta fashe da kuka , shi ma kukan yake yi Amma Mara sauti.
[2/21, 2:29 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
13
By Reefat yahya

Haka mr President ya kasance an rasa mai rarrashin wani tsakaninsu dakyar ya daure ya share mata hawaye yana bata hakuri akan rashin kulawar da yake musu nan little ya farka yana ganin uban nasa ya rungumesa gwanin tausayi daga nan yace su shirya zasu fita.ya koma bangarensa bayan ya shaidawa bodyguards nasa ayi arranging na garden xaayi birthday, umaima da sultan sunyi kyau sosai se wani nishadi suke mr President ma ya sha manyan kaya mota daya Suka shiga .shopping Suka je yaran sun xabi duk abunda suke so daga nan Suka koma gida sun sake sabon shiri don xuwa birthday. Mr President yayi inviting na vice nashi da wasu yan kalilan Suka xo akayi program sultan ya yanka cake akayi hotuna ga yan jarida daban daban , umaima tayi inviting frenz nata irinsu Meenat Zuby khady Mj eesha teemah da sauransu su Zuby an turo baki ana selfie????
Anci an sha sannan aka watse sultan ya samu gifts sosai.haka Suka kasance ckn farin ciki, ranar truout mr President yana tare da yaran nasa har abinci ma tare Suka ci se dare Suka rabu.
Mr President ya kwanta a gadonsa yana jin wani nishadi rabon da ya ji haka har ya manta, shuairat CE ta fado masa a rai tabbas ita CE sanadiyar daidaitawar su lallai baxe manta da ita ba haka ya kasance har bacci yayi awon gaba da shi.

Shuairat CE tare da yaya bash suna komawa gida bayan sun ajiye baba a airport ze tafi mubi Neman auren shukrah.
Shuairat CE ta katse shirun da cewa
” hmmm wa ya ga my yaya ya zama ango”

” xan buge bakinki wllhi kinsan baba baya nan

” yaya shukrah fa wayayyi CE nasan kana mata kallon Ya’r kauye”
” mtswww….wayayyi a ina? Yarinya se kunya yaushe zata zauna ta bani lokaci na

” don’t worry zata daina”
” mtsww dallah can karki bata min rai”
Wayarsa CE ta hau ruri ya daga yayi magana na minti 3 sannan yace” gani nan xuwa “
Ya juya yana kallon shuairat yace

” baby kiyi hakuri mr President yana nema na urgent “

” toh yaya ka kaini gida mana first
” no! Kiyi hakuri ki shiga taxi ko kuma mu tafi tare”
Ta xumburaa baki tace

” ni ka ajiyeni xan samu taxi a nan baxan je gidan ba”
Murmushi yayi sannan ya ajiye ta bayan ya samo mata taxi ta wuce gida shi kuma ya kama hanyar villa.

Bayan kankanin lokaci ya iso gidan yayi parking yana Sauri ya wuce ofishin mr President yana xaune ya hada girar sama da ta kasa bash ya gabatar da gaisuwansa ko uffan mr President bai CE masa ba se ya jefa masa wani magazine a gabansa.
Bash ya dau magazine yana dubawa tarihin rayuwar mr President ya gani ..dum! Yaji xuciyarsa ya tsinke dakyar ya daga kai yana jiran umarnin mr President
” ina bukatar ganin yarinyar da take aiki a JF Journals din nan “
“Ok sir!

“Now! Bana son bata lokaci”
” angama sir!
Gumi ne ya fara keto masa shuairat y? Sai da ya hanata rubuta labarin nan but bata jin magana.
Motarsa ya ja yana guduwa tmkr xe tashi sama ckn kankanin lokaci yayi parking a kofar gidansu , shuairat tana kwance dama yau bata je aiki bah ya shigo babu ko sallama ya fisgo hannunta ” yaya lfy?
” zaki sani ne ba ruwana ba kince baki jin magana ba”
” me nayi?
” ban hanaki publishing din tarihin rayuwar mr President ba? Na gaya miki ki rubuta Iya abunda ya gaya muku da bakinsa gashi ynxu yazo yaga tarihinsa kaf an baza duniya”
Shuairat tayi shiru ta rasa me zata gaya masa
” sorry yaya”
” bani zani cewa sorry bah muje mr President yana son ganinki saura kice ni na gaya miki”

????????????????????????????????????????????????hmmmm ba ruwana nima saura tace reefat ce ta gaya min.kuttt wa zai je cell ????????
Lolx…..Ku biyoni Lov u all????????????
[2/21, 2:29 PM] Reefat: ????NI DA SHUGABAN KASA????
14
By Reefat yahya

A gaban mr President shuairat CE tare da yayanta se kuma wasu bodyguards su biyu dakin yayi shiru baka jin komi sai bugun xuciyoyin su, mr President ya daga hannu alamar a barsu nan da nan Suka fita ya rage daga shi dai bash da kuma shuairat mr President ya daga hannu ckn rashin fahimta bash yace
” mr President sir! Kana bukatar wani Abu ne?

“Leave us! Ya fada kai tsaye nan bash ya juya ya fita yana mamaki saboda yasan ko ina suna tare da mr President ya akayi yau yafi son ya kadaice da shuairat ? Yana fita sauran bodyguards ma suna kallonsa ckn mamaki don sun San cewa akoda yaushe yana tare da shugabankasa a ko ina.
A hnkli mr President ya karewa shuairat kallo ba tare da ta sani bah don fuskarta na kallon kasa bata San me yake faruwa ba. Ya fara magana da cewa
” who ar u?
Se ynxu ta daga kanta a hnkli dakyar ta fara magana
” sunana Aisha bello”

Sun share minti 10 babu Wanda ya sake cewa komai sannan mr President ya sake cewa
” ina kika samu tarihin rayuwata?

“Ehmm ..ummmm
“Talk to me” ya daka mata tsawa kuka ta fara a hnkli kanta na kallon kasa.ta share minti 5bata CE komai ba, a hnkli ya taka yaxo kusa da ita suna fuskantar juna har ynxu kuka take.hayaniya Suka ji daga waje da karfi aka banko kofa, yan jarida ne suna fada da bodyguards a yayinda yan jarida suke kokarin ganin mr President bodyguards kuwa suna hanasu shiga.
Cak Suka tsaya ganin mr President da shuairat ckn yanayin da suke , bodyguards din kowa ya sunkuyar da kai yan jarida kuwa Suka fara daukan hotuna.ya fito da handkerchief a aljihunsa ya share mata hawaye ba tare da ya furta komai ba sannan ya tashi ya koma kujerarsa ya xauna.
Yaya bash yaje ya umarci shuairat ta tashi ya mayar da ita gida suna tafiya yan jarida sunyi shaa akanta suna tambayar ta me zata fada game da alamarin ko uffan bata CE musu ba dakyar bash ya bude mata hanya Suka fita Suka wuce mota ya ja Suka dau hanyar gida.

Mr President kuwa yana xaune yan jarida Suka sa shi a gaba suna jera masa tambayoyi ko daya bai amsa musu bah, securities Suka zo aka kori yan jaridan dakyar Suka tafi kowa na fadin albarkacin bakinsa.
A mota ma bata daina kukan ba, bash ya juya yana kallonta yace ” sisy me ya saki kuka? Wani Abu ya gaya miki?
Kai ta gyada masa alamar a’ah.
“Toh meyasa kike kuka?
“Ba komi”
“Gashi kina kuka still kina cemin ba komai”
” yaya nace maka ba komi koh”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Leave a Reply

Back to top button