HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

         Cikin tafiyar slow ya dawo gareta tana tsaye kanta a k'asa ....bazata iya k'idaya yawan mamakin sageer da abubuwan da yake aikatawa ba yau ...daman sageer d'in haka yake....!? Ko dai ita ta canja shi yau ....!?

Da yazo kawai durk’usawa yayi a gabanta …gwiwoyinsa a k’asa …kansa ma a k’asa ga kwantacciyar sumar sa dake ta sheki da walwali ,cikin muryar Wanda yafad’a fagen soyayya yace “I need your help sweety ,don Allah ki amince da soyayya ta ….da ke kad’ai zan iya rayuwata …ki taimaki sageer da maraicinsa ki amince da shi “

  "Sorry Hamma sageer " ta fad'a cikin rawar murya ...."ya d'ago kansa yana nacin kallonta yace "sorry....!?but what ...!?ba dai akan soyayyarki ba ko ...!?tad'an dafe kanta tace" wait Hamma sageer ,understand what I mean ...ka bani time akan wannan maganar zanyi tunani a kai please "

Ya mik’e tsaye yana ajiyar zuciya har tana jiyo hucin numfashinsa ,sannan ya karya wuya yace “wani malamin mu a islamiyya yatab’a fad’amana cewar” gaggawa aikin shed’an ne”Dan haka nabaki lokaci kiyi tunanin sweety …sai dai inason idan zakiyi tunanin kidinga tuna cewar, ni d’in tamkar maraya nake me buk’atar taimako …kisa a ranki ni d’in acikin rana nake ,amincewar ki gareni tamkar samuwar inuwa ne a gareni ….a k’arshe inason kiyimin adalci saboda ina sonki adadin yadda harshe bazai iya furtawa ba”

Samun kanta tayi da kautar da maganarsa tashigo da wata”Hamma sageer ka yafewa mamma kuskuren da ta aikata”

Shima d’in bai nuna yadamu da abinda tayiba yana murmushi ya had’e hannayensa waje guda yace”Na dad’e da aikata hakan sweety “

Sai tayi murmushi tace “Nagode Hamma sageer ,bari na wuce gida kar Umma da sisina suga Na dad’e “

Shima yana murmushi yace “Aunty Nafeesa na jiran kifa …”

” Zamuyi waya Hamma sageer ,yanzun bazan iya had’a ido da itaba …kagama bani kunya “sai tafara takawa a hankali da nufin tafiya tana cewa” karka manta alk’awarin da kayi min …karka kuma shan wani Abu da ya sab’awa Allah ,duk lokacin da zuciyar ka ta raya maka cewar kasha …toh kayi hanzarin tuna cewar Allah yana kallonka Hamma sageer “tana kaiwa nan tafice daga gidan ta barshi tsaye cikin shauk’in k’auna da bege da kewa ….sannan a hankali ya furta ” nadena …wallahi nadena …insha Allahu nadena har abada sweety.


Kamar a mafarki yaji ana kiran sunansa “ya Abdurrahman” shiyasa yafara bud’e idanunsa a hankali har ya kamamala bud’esu akan fuskarta ,wani murmushi yasakar mata yana mik’ewa zaune akan bed d’insa ,ita kuma tana tsaye a gefen bed d’in ta hard’e hannuwanta a k’irjinta tana kallonsa ,ya bud’e hannayensa kamar yadda yasabayi mata aduk lokacin da ya ganta yace “oyoyo tawan” yaushe kikazo …!?ta d’an zauna a gefen bed d’in tana cewa “nida rabin raina muka zo fa …munzo gaida mummy ne …ya Abdurrahman kana hutawarka ,wai bacci ma kake a irin wannan lokacin ….!?sai yayi k’aramar dariya yana fad’in” Na rantse baccin ma babu dad’i fa ,tunda babu ke a kusa dani kawai yinsa nakeyi …nifa saura kad’an Na tsinewa candy tunda yak’i saurin zuwa kiyi, kodan ayi bikinmu nadinga ganina kusa dake”

Ta k’yalk’yale da dariya jin maganarsa …tace “hmmm ya Abdurrahman baka gajiya da bawa mutum dariya …mummy ce tacefa nazo Na tasheka ko breakfast bakayi ba har rana tayi ….katashi kayi wanka ka shirya ..sai naje na kawomaka abincin”

Ya d'an kashe mata idanu yana kallonta yace "yadda jikina yayi tsamin nan saboda kwanciya ai da munyi aure wankan ma ke zakiyi min wallahi " da sauri ta mik'e tana cewa "ya Abdurrahman Na rantse zancan ka ya girmi kakata ...bari Na kirawo rabin raina ta tayani mu gyara maka d'akin kan kagama shiryawa " murmushi kawai yayi yabita da kallo yanajin k'aunarta Na zagaya ruhinsa.

Har suka kammala gyaran d’akin bai fito ba …sai Hussaina ta tafi daukomasa breakfast d’insa ,itakuma Hassana ta zauna ta d’auki wani album nasa tana kallo .

Tana cikin duba hotunan yafito daga bedroom d'in yashirya sai k'amshin turare yakeyi ...yana ganinta yafara murmushi yana cewa "kaga rabin ranmu ta sheik Huzaifa kenan " tayi dariya tace "kai ya Abdurrahman " ya zauna kan kujerar falonsa yace "ai Tawan takawomin k'ararki ..bawan Allah sai binki yake kina ja masa Aji ...gashi Hamma sulaiman yace ke ake jira ki fidda miji ayi bikinmu tare ,don Allah ki temakemu ki tak'aita mana lokaci kar kisa nakamu da hawan jini"

Dariyar ta ta d’auke a lokacin da taci karo da wani hoto da yad’auki hankalinta sosai ….ta k’urawa hoton me d’auke da maza guda hud’u idanu,dai dai lokacin da Hussaina tashigo da babban tire an shirya breakfast a kai ,tazo ta tsuguna gaban Abdurrahman tana cewa”come and eat ya Abdurrahman “a hankali yazamo k’asa yana kallonta tana had’amasa abin karyawa zuciyar sa fes.

“Wanene wannan ya Abdurrahman….!?abinda sukaji Hassana tace kenan …!?tare suka d’ago Kansu suna dubanta ,sai sukaga tana nuna mutum d’aya daga cikin mutanen cikin hoton hannunta ,wani murmushi yayi ya d’an runtse idanunsa yace ” Muhammad sageer kenan ,my best friend,duk duniya banida aboki ko Amini sama dashi ,ina matuk’ar sonsa da k’aunarsa ,sai dai wata k’addara ta rabani dashi …..amma har yanzu ina kewarsa …ina mararin sake ganinsa ko dan Na gyara alak’ar da ke tsakanina dashi….”

Kafin ma Hassana takuma magana Hussaina dake kallon hoton takama hannun Abdurrahman tana girgizawa a gigice tana cewa “da gaske kake ya Abdurrahman….!?wannan d’an daban abokinkane ….!?ya Abdurrahman kaima sonsa kakeyi kamar yadda rabin raina ke sonsa ….!?me wannan mutumin yake nufi ne ….!?ya shigo rayuwar mu yanata k’wacemin masoyana alhali duk duniya shi nafi tsana….!

Wani irin kallo Abdurrahman yabita dashi ,ya bud’e baki da niyyar magana …. !

Comments
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍


TYPING????

???????? HASSANA ????????

            *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page2⃣7⃣to2⃣8⃣

WATTPAD:hassana3329

® PEN : WRITERS ASSOCIATION


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/groups

TUNASARWA????

MANZON ALLAH (S A W)YACE “BABU WANI MUTUM DA ZAICE DA D’AN UWANSA YA KAI KAFIRI,FACE D’AYANSU YA CANCANCI KALMAR” IDAN YA KASANCE YADDA YA FAD’A D’IN GASKIYANE TO SHIKENAN,IDAN BA HAKABA NE KUWA ,TO KALMAR ZATA KOMA KANSA

AIKI ME FALALA????

MANZON ALLAH (S A W)YACE “DUK WANDA YA KARANTA AYATUL KURSIYYU BAYAN KOWACE SALLAR FARILLA ,BABU ABINDA ZAI HANASHI SHIGA ALJANNA ,SAI DAI MUTUWA

D’AN DABA KUMA..!?tawan yaushe sageer ya zama d’an daba kike ambatarsa da wannan KALMAR ….!?

Ta cono baki gaba tana hararan hoton hannun Hassana tace” ya Abdurrahman shaye shaye fa yake …kuma yana raina mahaifiyarshi kaga ai yazama d’an daba kenan” ya d’an lumshe idanu ya waiwayo yadubi Hassana yace “rabin ranmu a ina kukasan sageer ….menene alak’arku dashi …!?Hassana da tayi tagumi tad’anyi ajiyar zuciya ta kalli sisinta tayi murmushi ..sai kuma ta kawar da kanta zuwa ga Abdurrahman tafara bashi labarin lokacin da suka San sageer har zuwa ,amma bata fad’amasa dalilin da yasaka sageer shiga mummunan hali ba ” kawai sun tsinci Abdurrahman na hawaye da idanunsa ne alokacin da yake furta cewar “wannan halayyar da sageer ya b’ullo da ita tun bayan rasuwar mahaifinsa itace silar rabuwata dashi ,sageer Amini nane tun muna secondary har zuwa jami’a ,wannan hoton da kika gani mu hud’u a jiki sageer ne da ni ,sai kuma abokanmu guda biyu faruk da muktar ,ko a Makaranta mu hud’u ne group d’inmu mun shak’u da juna sosai …amma nafi shak’uwa da sageer saboda mutuncinsa da karamcinsa ,ga hankali da cikakkiyar nutsuwa da kamala ,bashida yawan magana ko kwaramniya da shashanci irin na mazan zamani wad’anda da sunga Allah yayi musu kyakkyawar sura da kud’i da k’uruciya sukeyi ,wallahi bazan iya fad’amuku yawan y’ammatan da suke kawowa sageer hari a lokacin ba amma baya kulasu karatune kawai a gabansa ,faruk shine yafita zakka a cikinmu saboda shaye shayen da yakeyi ,muna iyakar k’ok’arinmu wajen ganin ya daina ,musamman sageer da kullum cikin yimasa nasiha da fad’a yakeyi ,kwatsam bayan rasuwar mahaifin sageer sai na tsinci sageer yabi layin da faruk yakebi ,ma’ana shima yafara shaye shaye ,randa na tsinci sageer a d’akin faruk a buge cikin maye nayi bak’inciki da takaici mai yawa ….ko da sageer yadawo hayyacinsa a maimakon nayi masa nasiha sai na haushi da bala’i ina kuka, na gayamasa maganganu marasa dad’i da d’aci ,nace masa bani bashi tunda yazama mutumin banza ,nayi tafiya ta na barshi anan ,daga ranar bansake ganin sageer ba …daga baya nayi tunanin abinda nayi bashine dai dai ba ,kamata yayi nazauna dashi naji damuwarsa inyaso nabashi shawarwari da nasiha ,nasan zai d’auka insha Allah,amma nayi sintirin zuwa gidansu sageer bana samunsa hatta mahaifiyarsa bana samunta …haka nan nake zuwa gun faruk Dan naji labarin inda sageer yake, amma yace shima bai saniba ,mahaifiyarsa da yayarsa sunzo sun d’aukeshi “a yanzu babu abinda nakeso irin naga sageer ko domin nasan dalilin fad’awar sa wannan mugun hali da yafi tsana ,amma kuma yafad’a ciki”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button