HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL
Hassana ta nisa bayan Abdurrahman yagama bayaninsa ,tace" ya Abdurrahman kanason kasan dalilin fad'awar Hamma sageer cikin wannan halin ko ....?ya d'aga kai yana cewa "tabbas inason sani" sai Hussaina ta katsesu da cewa "ya Abdurrahman please kaci abincinka kar ya huce ...kubar maganar mutumin nan haka " ya juyo yana kallonta da murmushi a fuskarsa yace"ki d'an yimin uzuri tawan, inason jin labarin sageer ne ,indai abinci ne zanci har ...."kafin ya kamala maganarsa ta tashi fuuu tayi waje tana kumbura fuska .
Yayi dariya yabita da kallon so a ransa yana fad'in "Y'ar rigimata kenan" sannan ya waiwayo gurin Hassana da fushin sisinta yake damunta a zuciyarta yace "barni da ita ,nasan yadda zan shawo kan Y'ar rigimata ,kedai kawai ina saurarenki "
Nan Hassana ta kwashe labarin komai ta fad'awa Abdurrahman ,ta kuma gangarowa kan farkon ganinsu dashi da abinda yayi musu har Hussaina ta tsaneshi ,da had'uwarsu da mamma da rok'on da tayimata akan ta taimaketa akan sageer ,har zuwa sanda sukayi magana itada sageer d'in da kuma nasihar da tayi masa har ya karb'i nasihar da cewar ya dena ,abinda ta b'oye masa kawai soyayyar da sageer ya bayyana mata "
Abdurrahman yaji shigar wannan labarin a jikinsa sosai ,ya tausayawa Abokinsa kuma Amininsa ,yaji kunya sosai akan abinda yayi masa na gudunsa a lokacin da yakamata yajashi jikinsa kodan yaji damuwarsa ...gashi yanzu abinda yakasayi a matsayinsa na namiji mace tayi ...macen ma Y'ar uwa a gareshi ...wani bala'in shauk'in sageer yaji a zuciyar sa ,yaji yana d'okin ganinsa a idanuwansa ,shiyasa da hanzarinsa ya mik'e yana d'aukar mukullin motarsa yadubi Hassana idanunsa jajir yace "shiga ki kirawota Ku kaini gun sageer ,na rantse bazan iya d'aukar lokaci ba tare da na ganshi ba " Hassana ta kalli abincin gabansa tace "kaci abincin tukun sai mutafi " ya girgiza kai yana nufar k'ofa yace "bazan iyaba ,bazan iya ciba, kawai kirawota mu tafi.
Hassana ta sauke ajiyar zuciya ,ta na jin zuciyarta na k'issima abubuwa da dama, sannan tamik'e tabi bayansa suka fito .
……….Har sukazo gida Hussaina cikin b’acin rai take ,sai kumburi takeyi tak’iyiwa kowa magana acikinsu ,musamman ganin akan wani sageer ko abinci Abdurrahman yak’ici,saboda fushi ma k’in Shiga gaba tayi takoma baya ta zauna ,sai Hassana ce ta zauna a gaba …Abdurrahman da yasan halin kayarsa shiyasa shima ya d’auke mata wuta ya shareta ,hakan yakuma asassa tsanar sageer a zuciyarta ganin yadda Abdurrahman yanuna yafi damuwa da lamarinsa a kanta …kawai sai takife kanta a cinyarta tafara hawaye .
Har sukazo k'ofar gida Hassana ta bud'e k'ofar motar tafita tashige gida,ga motar Hamma sulaiman a gefe da alamun yana cikin gidan ,Hassana tanada dalilinta nak'in yiwa Hussaina magana itama ,haka Abdurrahman shima yafito daga motar,amma Hussaina tana zaune tak'i fitowa kanta bisa cinyarta tana shesshek'ar kuka ....Abdurrahman yaji bazai iya daurewa ba kawai saiya bud'e murfin bayan motar yashiga ya zauna kusa da ita ,a hankali cikin damuwa ya kirawo sunanta ,amma tayi shiru tak'i amsawa sai ajiyar zuciyar kuka take,tilas yasa hannunsa yad'ago kanta yana kallon idanunta da sukayi ja hawaye na kwarara ,ya d'an girgiza kai yace "menene damuwar kine.... !?meyasa kike kuka ...!?tad'an k'wace fuskarta daga hannunsa tana kawar da kai ,ya kuma juyo da fuskar yana karya wuya yace" yaseen nima zanyi kukan idan bakiyi magana ba "saita d'an kwantar da kanta a tafin hannayensa cikin damuwa tace" ya Abdurrahman kai da rabin raina kun dena sona, wannan mutumin yanason Shiga tsakani na da masoyana wad'anda nafiso ...inata gayawa rabin raina bana son alak'arta dashi tak'i ganewa ,ya Abdurrahman kamarfa soyayya sukeyi ,kuma kaga basu dace ba ,gara ta auri Malam Huzaifa yafi dacewa da ita, kuma kaima nakawo maka abinci amma kak'ici saboda d'okin kazo ka ganshi ...shiyasa nake kuka ganin yanaso ya k'wacemin masoyan na "
Har ta kammala yana saurarenta yana murmushi ,gabad’aya bayaninta babu wata hujja gamsasshiya sai tsabar rigima da kishin sageer da takeyi ,ta lura sageer na da fada sosai a gun Hassana da Abdurrahman shiyasa take kishi ,kawai sai Abdurrahman ya kwantar da murya cikin rarrashi yace “tawan” ta d’an d’ago tana kallonsa shikuma yasa yatsa yana wasa da hawayen fuskarta yana zanawa yana tab’a dimple d’inta ,yanai mata murmushi yace “kin san me yake damunki kuwa ….!?shagwab’a da rigima da kishi ne kawai ba wani abuba ,idan ma harda gaske soyayya ce tsakanin sageer da Hassana zanfi kowa jin dad’i da murna ….domin bakisan wanene sageer da qualities d’in saba ne …ita da tasani gashinan tana shirin fad’awa tarkonsa ,bakiyi wa Hassana adalci ba idan har baki tayata son abinda takeso ba ,duk abinda kikeso tana k’ok’arin ganin ta tayaki son abun koma tafiki sonsa, idan har kikayi k’ok’arin ganin kin tirsasa ta tak’i amincewa da sageer to kin zalunce ta,domin ta farat d’aya na hangi soyayyar sageer a idanunta…abinda kike tuhumar sageer da shi kuma da yardar Allah inada tabbaci yadena ,daman ba halinsa bane ,k’addarace tasashi ciki ,ba Hassana ba ni kaina ina son sageer ,kuma ina k’aunarsa tawan”
Hawaye yak'ara ziraro mata ganin bata samu goyan bayan ya Abdurrahman ba da rawar murya tace "nikuma bana sonsa ya Abdurrahman" yakuma murmusawa yana share mata hawayen fuskarta ,yasan cewar ita mutumce Mara b'oye abu acikin zuciyarta ,kai tsaye take fad'ar Abu ,wannan halayyarta CE shiyasa baya ganin laifin ta ,saida ya goge mata hawayen tsaf sannan yace "idan bakyason sageer yanzu ,k'ila watarana zaki soshi ,kidena yawan tsananta tsanar Abu a ranki, duk wani Abu da kike k'i to ki k'ishi saffa saffa kinji masoyiya ta ,abinda nakeso dake yanzu ke zamu k'arasa ki nunamin gidan Aunty Nafeesa naga sageer d'ina ,tunda kin kori rabin ranmu da kukanki ,nasan bazata iya jure ganin hawayenki ba shiyasa ta tafi ta barmu .
"Wani b'acin rai taji sosai akan yace ta rakashi ,amma bazata iya musu ba kar yaga kamar batad'auki maganar saba,ita dai tasan batason sageer,kuma bazata tab'a sonsa ba " basu fito daga motar ba saida Abdurrahman ya tabbatar ya wanke zuciyar masoyiyarsa da kalaman k'auna ,sannan suka fito suna takawa a hankali suka nufi gidan Aunty Nafeesa .
Tofah ya zata kasance idan aka had’u ?ga dai Abdurrahman da Hussaina sun nufi gun sageer
A soro Hassana taci karo da Hamma sulaiman yana waya, da alamun fitowa yayi daga gidan,yad’an dubeta kad’an yanai mata alamun ta tsaya ta jirashi,saita koma gefe tana kallon yanayinsa ganin yadda yake magana yana b’ata fuska ,taji yana cewa “sakeena kinfiya son yawo wallahi …inajin dai duk duniya danginku yafi nakowa yawa,Ku kenan biki ko suna ” ya d’anyi shiru yana saurarenta har tagama magana shima yad’ora “ni zakiyiwa dad’in baki sakeena ..!?da dai ban sanki bane sakeena ,ai nace miki kidena kirana a waya kina tambayar unguwa ,meyasa Baki tambayeni ba kafin nafito …!?sai naga yana murmushi yad’an lumshe idanu a hankali yace ” soyayya dai ta d’auke miki hankali har kika manta sakeenan sulaiman “ko metace masa oho sai naji yana cewa ” shikenan ki shirya kitafi ,zan biyo na d’aukeki idan nadawo ,kiyimin tanadin tukuici kuma ,dan bazan miki wannan tagomashin a banza ba “sai naga yad’an dafe kai yana lumshe idanu da wani murmushi me k’ara masa kyau bayan yagama saurarenta yace” na rantse kawai sokike ki sukurkuta ni sakeena ,gashi inada abinyi Baba yabani wani aiki ,amma dai kawai kirik’e kalamanki idan nadawo zaki biyaminsu yadda zanfi d’aukarsu “yana fad’in haka ya sauke wayar ya kashe yana sakata a aljihunsa.
Yana dubana ina kwashewa da dariya nace" Hamman mu na Aunty sakeena"ya d'an kalleni yana basarwa yace"keh gurinkifa nazo zamuyi wata magana ...Umma tacemin kuntafi gidan mummy ashema ba dad'ewa zakuyi ba ....!? Nace "eh akwai dalilin da yadawo damu ne da wuri ...kuma nima daman akwai maganar da nakeso nayi da kai Hamma, yanzu waye zai fara ...!?
” kifara kawai babu damuwa “na d’an haye kan mashin d’in Babangida dake soron nagyara zama sosai ,yayinda Hamma sulaiman yake tsaye ya jingina da Bango yana fuskantata .
Nace” Kaine zaka fara Hamma ,a ko’ina ai maza sune gaba da mata…Allah (S W A )Yace “Arrijalu k’awwamuna alan nisa’i” kaga kenan Kaine gaba dani ,fara gayamin maganarka Hamma, idan kagama saikaji tawa maganar”
Ya d’an tsura mata ido yana jinjina kaifin hankali da basirarta ,yasan maganar da zai fad’amata yanzu me girma ce kuma zatazo mata a bazata ,tunda batada masaniya akai ,amma yana fatan tayi wa maganar kallon basira kuma ta fahimceta “
A hankali yakuma d’aga idanunsa yazuba mata su ,itama idanunta na kansa,ya bud’e baki a wani yanayi yace “ina son……… ….!
Comments
Share
Vote
Pls
HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍
TYPING????
???????? HASSANA ????????
*DA*
❣???? HUSSAINA ????❣
TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍
page2⃣9⃣to3⃣0⃣
WATTPAD:hassana3329
® PEN : WRITERS ASSOCIATION
~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~
TUNASARWA????
MANZON ALLAH (S A W)YACE “BAYA HALATTA GA MUSULMI YA TSORATAR DA D’AN UWANSA MUSULMI,KO DA KUWA DA WASA YAKEYI ,DUK WANDA YA NUNA D’AN UWANSA DA WANI K’ARFE ,TO MALA’IKU SUNA TSINE MASA HAR SAI YA SAUKE
AIKI ME FALALA????
MANZON ALLAH (S A W)YACE ” KA YAWAITA YIN SUJJADA GA ALLAH ,DOMIN BABU LOKACIN DA ZAKAYI SUJJADA FACE SAI ALLAH YA D’AUKAKA DARAJARKA ,YA KUMA GOGE MAKA ZUNUBAI
SADAUKARWA GA
Y’AN K’UNGIYA TA TA PEN WRITERS ASSOCIATION, ALLAH YA K’ARA HAD’A KANMU YA K’ARA MANA BASIRAR RUBUTU WANDA ZAI AMFANI AL’UMMA????????????
BARKAN MU DA JUMA’A SISTERS ,ALLAH YABAMU ALBARKACIN WANNAN RANA TA JUMA’A????????????
…………………Inason shaida miki abinda Baba ya kirawoni ya fad’amin ,kuma yabani damar tattaunawa dake akan maganar “
Na d'an kalleshi alamar shi nake saurare ,sai yaci gaba da cewa "kin san Huzaifa malamin Ku ko ....!? Gabana ya d'an fad'i amma ban bari ya ganeba nace " eh na sanshi Hamma shine malamin ajinmu a islamiyya ai "Hamma sulaiman yace" OK ,daman kuna soyayya ne ...!?sai Kalmar tayimin nauyi na rufe baki ina Y'ar dariya nace "Hamma sulaiman wannan tambayar tayi min tsauri da yawa wallahi " ya d'an harareni yana cewa magana ta tayi miki tsauri ko ...!?amma soyayya batayi miki tsauri a Makaranta ba ko ...!?toh zancen dai shine ,Huzaifa ya turo magabatansa gurin Baba da niyyar sunaso ayi masa izni yafara zuwa zance gurinki ,sannan kuma yanaso yakawo kud'in aure dan ayi komai cikin lokaci da wurwuri ,shine Baba ya kirani ya fad'amin akan nasameki muyi magana ,ya kika gani ....!?menene ra'ayinki akan hakan....!?
Tunda yafara magana k'irjina ke bugawa ,tabbas Malam Huzaifa bai rasa komai ba ,sai dai banji ina sonsa a matsayin miji ba ...zuciya ta cike take taf da soyayyar sageer babu masaka tsinke ,duk da har zuwa yau ban furtawa sageer kalmar so ba ,ban ma k'ara bari mun had'u ba saboda banyi shirin bashi amsa ba ,inaso ne insamu kulawar sisina akan maganar ,inason sisina ta furtamin ta amince da alak'ata da sageer kafin na tunkareshi ,amma gaskiyar magana inason sageer ,so me d'umbun yawa Wanda nake kasa bacci saboda tunaninsa da kewar sa,,idanuna suka ciko da hawaye saboda ban San amsar da zanbawa Hamma sulaiman ba .
Ganin nayi shiru yasa shi kiran sunana ,na d'ago kai ina amsawa sai yaga hawaye a idanuna ,ya d'an d'age gira yana kallona yace "zo ,taso nan " a hankali na sauko daga kan mashin d'in naje gareshi ,ya kama hannuna yajani cikin gida har d'akin Umma ,tana zaune da redio a hannunta tana murd'awa muka shiga Hamma sulaiman na sallama ,ta amsa ta na d'aga kai tace "au wai baka tafi ba daman ...!?sai kawai ta ganmu tare ni dashi ,yace " eh Umma ban tafiba ,na tsaya Isar da sak'on Baba ne "sai kuma yad'anyi baya da hular kansa yana d'an Shafa goshinsa da d'aya hannunsa ,d'aya hannun kuma yana rik'e da hannuna ,yana d'an murmushi yace" Umman mu zan d'an tattauna wata magana da yarinyar nan shine nace ko ...."sai yayi shiru bai k'arasa ba .
Kawai sai naga Umma ta mik'e da redion ta a hannu ta na niyyar fita tace "nasan abinda kake nufi ai ,sokake nabaku guri Dan kar naji komai ....toh nabarku lafiya intayi tsami maji nan gaba " tayi ficewarta .
Yana dariya yajani kujera ya zauna, nima na zauna gefensa ,hannaye na na cikin nasa yace min "ke kalleni nan " na kalleshi ina hawaye ,yace "kafin muci gaba share hawayen nan tsaf " nazame hannuna daga nasa na goge fuskata da hawayena ,saida yaga nagoge tsaf sannan ya gyad'a kai yace "Weldon ,idan na canka dai dai daga maganar da nayi zuwa yanzu na fuskanci ba kyason Huzaifa ,hakane ...!?nakasa magana sai kallonsa da nakeyi ,ya d'an tsuke fuska yace " kallon na menene haka ne ...!?naci bashinki ban biya bane kika tsareni da idanu ,bar kallona malama kibani amsata inada abinyi " ban San sanda nayi murmushi na sunkuyar da kai na ba nace "hakane Hamma " ya sake tambayata "wa kike so toh ...!?kamar bazanyi magana ba sai kuma na daure a hankali nace" daman maganar da nakeso kenan nayi da kai Hamma, zan nemi shawararka akan hakan "yayi wani murmushi yace " ina abokiyar shawarar taki yau kike nemana ...!?idona yakuma k'wal k'wal nace "fushi take dani Hamma ,tak'i saurarona " da hanzari yace "kar kimin kuka anan banaso ,kuyita mayar da kanku ragwaye ,magana kad'an ta dinga saku kuka ,,mtsww ya d'an ja tsaki .
Na maida hawayena sannan na sunkuyar da kai na nace" akwai Wanda yake sona da aure Hamma, nima kuma zuciya ta naji ta amince dashi ,sai dai sisina bata sonsa ,batason alak'ata dashi ko kad'an ,hakan yasa har zuwa wannan lokacin nakasa amsa masa, duk da cewar ina sonsa Hamma "
Ya d'an zaro wayarsa yana duba text massage da aka turo masa ,idanunsa akan wayarsa yake tambayata "menene dalilin ta na k'insa ita ...!?kuma wanene shi ....!?A ina yake ....!?ya jeromin tambayoyi .
Ban wani tsaya kwane kwane ba na fara bashi labarin sageer tun daga farko ,tun Hamma na danna waya sai naga ya ajiye ya fuskanceni alamar labarin yafara shigarsa ,idanunsa a kaina har na kammala bashi labarin tsaf yanata min kallon mamaki ,ya kuma rik'o hannuna yasa idanunsa acikin nawa yace " kinason sageer ko ...!?na kasa amsa masa da baki sai dai na gyad'a masa kai ,kawai sai naga ya mik'e tsaye yacemin "sai abawa Huzaifa hak'uri kawai ,karki damu sageer ne mijinki insha Allah ,auransa jihadi ne agareki " nayi zumbur na mik'e ina rik'o hannunsa nace "Hamma sulaiman sisina bataso ,ya zanyi da ita " kawai sai ya dubeni yayi murmushi ya girgiza hannuna yace "bakida matsala da wannan yarinyar ,ki barni da ita kawai " yasa kai yafice daga d'akin ,ya barni cikin tunani iri iri .
Har sukaje k’ofar gidan Aunty Nafeesa Hussaina bata saki fuskarta ba sai kumbure kumbure takeyi ,da hannunta ta nuna masa gidan tana fad’in “ga gidan ya Abdurrahman ” ya d’an karkace kai yana duban gidan yace “Ayyah ashema babu nisa ….!!?kinga gidan matan aure ne ko zaki taimakamin ki kirawomin shi …!?tayi wani wal da idanu taci laya tana girgiza kai ,” wallahi bazani ba ya Abdurrahman”tabashi dariya sosai ganin yadda tayi fik’i fik’i da ido ,yana dariyar yake cewa “tawan harda saurin rantsuwa haka …!?tace” eh ai dan karka dameni nema ,nifa ganinsa ma bana sonyi balle magana ta had’ani dashi “dariyar Abdurrahman takoma murmushi ya gyad’a kai yana cewa ” bakyajin magana yarinyar nan “ta d’an shagwab’e fuska tace” nifa babba ce wallahi ….kadena cemin yarinya ….kas….!bud’e k’ofar jikin get d’in yasa suka maida hankalinsu wajen gabad’aya ,saiga Hamma sageer ya bayyana cikin shigar Pakistan na maza me tsananin kyau lemon green colour ,kansa babu hula sai kwantacciyar sumarsa da taketa k’yalli saboda gyaran da tasha ,takalmin k’afarsa silifas ne me taushi irinna maza kyakkyawar k’afarsa fara tas tayi kyau acikin takalmin ,banda k’amshin turare babu abinda yake tashi a jikinsa ….juyawar da yayi zai rufe k’ofar ita tabawa Abdurrahman damar salallab’awa bayansa ya zagaya hannunsa ya rufe masa idanu ruf yana faman murmushi da jin wata k’aunar sageer na ratsa ruhinsa .
Jikin sageer a sanyaye jin anrufe masa idanunsa ,a hankali yabud'e baki yace "ko wanene ma nabada gari" kawai sai Abdurrahman yacire hannunsa da hanzari kuma yadawo gaban sageer yafad'a jikinsa ya rungumeshi k'am yana cewa "sageer d'ina ....Abdurrahman d'inka ne yadawo gareka " Jikin Hamma sageer ya d'auki rawa, a hankali kuma yasa hannayensa yad'ago Abdurrahman ya rik'e kafad'unsa ,fuskarsa na bayyana mamaki yace "Abdul Kaine !?Abdurrahman d'ina yadena fushi dani ya yafemin ne ....!?Abdurrahman ya gyad'a kai yana kallon sageer cikin k'auna yace " Abdul d'inka ne ...Abdurrahman d'inka ne yadawo gareka domin Neman afuwar ka .....ka yafemin abinda nayimaka Abokina ....!sai kawai sageer ya matsa jikin Abdurrahman ya d'an kwantar da kansa akan kafad'arsa ,idanunsa a lumshe yake fad'in "tunda tashigo rayuwata al'amuran rayuwata suke dai daita....zuciya ta da gangan jikina kullum fad'amin suke itad'in alkairi ce agareni ..." Yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya ,Abdurrahman yasa hannu akan sageer yana birkita sumar kansa, cikin k'aramar dariya yake cewa "wacece ...!?wacece tasaka sageer d'ina cikin soyayya haka . .!?sai sageer ya d'an goga kansa a kafad'ar Abdul yana wani irin murmushi da runtse idanu ,a hankali kuma yace " baka santaba Abdul sweety nace ... Na rantse idan ka ganta zaka tayani murnar samumta ...tafita daban acikin mata ..."mamakin yadda sageer yake jero zance Abdul yakeyi ,a saninsa sageer miskili ne Wanda magana ma wahala take mishi ,lallai Hassana taciri tuta da ta bud'e bakin sageer .
Abdurrahman ya d'ago kan sageer da ke kafad'arsa idanunsa a rufe sai murmushi yake, cikin k'aramar murya ya rad'awa sageer cewa "kalli can kagani ,wannan ce ta hargitsamin sageer d'ina .. !?a hankali sageer yafara bud'e idanunsa a slow yana bin hannun Abdul da kallo zuwa inda yake nuna masa, idanunsa suka sauka akan fuskar Hussaina dake gefe a tsaye ta hard'e hannuwa a k'irji fuskarta babu annuri ko kad'an ,ganin yadda Abdurrahman ya shanyata ya mantata da ita.
Da k'arfin gaske k'irjin sageer ya buga a lokacin da yaci karo da fuskar Hussaina, badan fuskar iri d'aya da ta Hassana bace da saiyace bayason ganinta ,saboda tsanarsa da yake hangowa iri iri a idanunta ,Hussaina ta dalla masa harara tana murgud'a baki har dimple d'inta ya lob'a ,sai kuma ta juyar da kanta tana sakin tsaki ....."
Zuciya tazowa sageer iya wuya ,ya dubi Abdul idanunsa na canja kala yace “ka fad’amata banason tsaki Abdul …..me nayi mata ne da kullum ta ganni saitayi min tsaki ….!?na rantse abune me sauk’i gareni na fasa bakin yarinya…” A tsorace Hussaina takama Shafa bakinta kamar ma ya fasa d’in …zuciyarta na k’issima mata cewar dabancin NASA yafara kaiwa ga duka kenan ….
Dariya sosai Abdurrahman yayi ,sannan yadubi Hussaina yawani kashe mata idanu yace "jeki gida tawan, ganinan zuwa gareki yanzun nan " kamar jira takeyi da sauri ta juya ta tafi ko waiwaye babu ,Abdul ya juyo kan sageer da ya k'ureshi da kallon mamaki yace "kabani gurin zama muyi magana ...kasan bancika jure tsayuwa ba ..." Kawai sai sageer yaja hannun Abdurrahman suka shige gidan Aunty Nafeesa ....
Sashen da aka bawa sageer suka shiga, suna shiga suka samu guri suka zauna ,sageer ya mik'e domin kawowa Abdurrahman d'an drink sai Abdurrahman d'in ya rik'o hannunsa ya zaunar dashi gefensa ,ya kalleshi yace "magana nakeso muyi sageer ...amma naga alamun tambayoyi a idanunka .. Bismillah tambayeni duk abinda kakeso ".
Sageer ya sauke ajiyar zuciya yace " first ya akayi kasan ina nan ...!?Abdurrahman yace "Hassana ce ta sanar dani " ya k'ara ware idanunsa akan Abdul yace "menene alak'ar ka da sweety na da wannan Mara kunyar da kukazo ...!?Abdurrahman yayi murmushi yace " a fahimta ta sweetyn naka itace Hassana ko .....!?toh alak'a ta dasu me girma ce ,domin da mahaifiyata da tasu cikinsu d'aya ,kuma Hussaina da mukazo tare itace wadda zan aura "
Sageer ya d’an zaro idanu yana kad’a harshe yace “amma nafara tausayinka tun yanzu …karasa wadda zaka aura sai wannan masifaffiyar …!?na rantse Abdul nakusa faffallawa yarinyar nan mari ….” Sai Abdul d’in yarik’o hannunsa yana wata irin dariya yace “yaseen kuwa da nayi shari’a da kai ka dakar min matata …gaba d’aya da kai da itan Baku fahimci juna bane ,amma ai tawan lafiyayyiyar yarinya ce wallahi ….
Sageer ya tab’e baki yana shirin magana wayarsa tayi k’ara alamar shigowar sak’o ,yasa hannu yacirota a aljihunsa yana dubawa ,cikin wani irin yanayi yamik’e yana zare idanu k’irjinsa kamar ya fad’o k’asa ganin sak’on daga Hassana yake…..”