HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Comments
Share
Vote
Pls
HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍
TYPING????
???????? HASSANA ????????
*DA*
❣???? HUSSAINA ????❣
TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍
page3⃣1⃣to3⃣2⃣
WATTPAD:hassana3329
® PEN : WRITERS ASSOCIATION
~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~
AIKI ME FALALA????
MANZON ALLAH (S A W) YACE “DUK WANDA YA TASHI DA DADDARE KUMA YA TASHI MATARSA ,SUKAYI SALLAH RAKA’A BIYU A TARE ,ZA’A RUBUTA SU DAGA CIKIN MASU AMBATON ALLAH DA YAWA MAZA DA MASU AMBATON ALLAH DA YAWA MATA
TUNASARWA????
MANZON ALLAH (S A W)YACE “ALK’AWARIN DA KE TSAKANIN MU DASU (KAFIRAI) SHINE SALLAH ,DUK WANDA YA BARTA TO YA KAFIRTA ,KUMA YACE ” TSAKANIN MUTUM DA SHIRKA ,BARIN SALLAH
INA YAWAN SAMUN TAMBAYA DAGA FANS WAI SHIN LABARIN HASSANA DA HUSSAINA LABARINA NE NIDA TAWA HUSSAINAR??
AMSAR ITACE????
BA LABARINMU BANE BA KUMA TARIHIN MU BANE ,BABU MA ABINDA YAYI KAMA DA LABARINMU A LABARIN ,WANNAN K’IRK’IRARREN LABARI NE DABAN DA NUFIN FAD’AKAR DAKU DA NISHAD’ANTAR DAKU ,TARE DA SANIN DAD’IN ZUMUMCI A RAYUWA,DAFATAN KUN FAHIMTA MASOYANA ,ANA KYAWUN TARE TSAKANINA DAKU????????????
****Hussaina tanasa kanta cikin soro Hamma sulaiman na shirin fitowa ,ta kauce tana gaisheshi ,ya amsa yana cewa “ke d’an biyoni cikin mota inbaki sak’o ” yayi gaba abinsa .
Tad'an bishi da ido tana tunanin wane sak'o kuma.....!? Har yashiga motar sannan tabishi itama ,ta bud'e wajen me zaman banza ta shiga ta zauna tace "gani Hamma " bai dubeta ba wayarsa a hannunsa yana daddannawa sai da ya d'auki lokaci sannan yace "ni waye a gareki...!? Taji tambayar a bazata shiyasa ta d'ago kai tana kallonsa kawai batace komai ba ,idanunsa akan wayar yakuma cewa " kamar fa tambayarki nayi amma kikayi shiru kina kallona ,meyasa idan an tambayeku Abu bakwa bada amsa kai tsaye sai ku tsaya kallon mutum ...!?me kuke kallo a fuskata da Baku sanshi ba ne...!?Hussaina ta kawar da kanta daga kallonsa tana k'unshe dariya tace "sorry Hamma, kai d'in ai babban yaya nane, kuma magajin Uba agareni " yana jin tafad'i haka ya ajiye wayar kan cinyarsa yajuyo yana dubanta face to face yace "Ashe idan nanemi alfarma a wajenki zan iya samu kenan ...!?ta d'an sunkuyar da kai saboda yadda Hamman ya tsareta da idanu tace" kadai bani umarni kawai Hamma ,ai kafi k'arfin Neman alfarma a gurina ,ya d'an lumshe idanu yayi wani murmushi da baicika yin irinsa ba ganin tabashi babbar dama ,yace "so nake ki hak'ura da Abdurrahman ...kicireshi a zuciyarki ...kuma ki hak'ura da aurensa ..."
A gigice ta d'ago kanta tana matsowa jikinsa kamar zata haye cinyarsa ,ta dafe k'irjinta wajen zuciyarta idanu a warwaje take kallonsa ,bakinta yana mugun rawa takasa magana sai girgiza kai takeyi hawaye yaciko idanunta ....ganin yadda tayi mugun razana hannunta ak'irjinta yasa Hamma sulaiman ya kalli hannun da ta dafe k'irjin yace "ya dai ...!?zuciyarki tayi ciwo ne saboda nace ki rabu da Abdurrahman ...!?hawaye ya kwararo idanunta da k'yar tayi magana tace" eh Hamma, bakaji yadda zuciya ta take bugawa ba wallahi ...."ya k'ara murmushi yace "kefa kikace nafi k'arfin alfarma agunki ...sai dai nabaki umarni ...Ashe bazaki iya bin umarnin ba kenan ....!?sai takuma matsowa ta d'ora kanta a kafad'arsa tana hawaye tace" kayi hak'uri Hamman mu ....ka sauya wani umarnin ,wallahi inason ya Abdurrahman ,bazan iya rabuwa dashi ba Hamma, ya d'an ture kanta yana fad'in "d'agani malama " ta d'aga masa kafad'ar amma kuma sai takama hannunsa ta rik'e ,hawaye nata ambaliya a fuskarta .
Saida ya numfasa sannan yace "duk wannan hawayen na rabuwa da masoyi ne ....!?toh waima meyasa bazaki iya rabuwa dashi ba .....!?tace" saboda ina sonsa da k'aunar sa Hamma "ya tsura mata ido yad'an d'age gira yace " kamar yadda twins sister d'inki ke son sageer ko ....!?kawai sai Hussaina tasaki baki da ido tana kallon Hamma sulaiman ,mamakinta a ina Hamma yasan abinda ke tsakanin sageer da Hassana .
Yana kallon yanayinta yace "idan baki rufe bakinki ba k'uda yafad'a babu ruwan sulaiman ...tambayarki kawai nayi kiban amsa " duk da haka Hussaina sai takasa magana illah kallon Hamma da takeyi kawai ,sai yad'an juyar da kansa gefe yace "zafin da kikaji a zuciyarki a sanda nace ki rabu da Abdurrahman ,to irinsa Y'ar uwarki takeji aduk sanda kika furta cewar ta rabu da sageer ....yadda kikeson naki masoyin itama kibarta taso nata mana ....menene dalilinki na cewar lallai saita rabu dashi basu dace ba ....!?sai lokacin tasamu bakin magana tace" wallahi Hamma basu daceba ,shaye shaye fa yakeyi "ya kuma juyowa ya kalleta yace " nasan wannan Hussaina, amma shiriya a hannun wa take ...!?tace "shiriya A hannun Allah take Hamma sulaiman ..." Yace "good ,saboda haka Allah ne mai shiryawa ,a duk lokacin da wani bawa ya kasance yana aikata Abu Mara kyau ba kyararsa da gudunsa akeyi ba ,no ,jawoshi akeyi ajiki Dan asan damuwarsa da kuma hanyar warware damuwar ....k'yamatar da al'umma sukeyi musu itace takesawa su kasa dainawa ,abinda Y'ar uwarki tayi jihadi ne,muna fatan Allah ya shiryeshi kuma bazai sake aikatawa ba ...kuma kema d'in banga laifinki ba ,soyayyar da kikewa Y'ar uwarki tajawo hakan ,bakyason fad'awarta cikin wani hali, toh kisani fa idan bata fad'a cikin wani hali akan abinda kike tunani ba ,toh zata fad'a wani hali dalilin k'iyayyar da kike nunawa abinda take so ....Y'ar uwarki tana sonki tanason abinda kikeso ,kema kiyi mata wannan halaccin kiso abinda takeso mana "
Tayi ajiyar zuciya me k'arfi tace "hakane Hamma ,na amince ta aureshi tunda shi take so ,amma Hamma kar a takuramin sai nasoshi dole ,danni har yanzu banji ya kwantamin ba wallahi " sai yayi murmushi yace "akwai mutane da yawa irinki a duniya,wad'anda basa iya b'oye k'iyayyarsu ko soyayyar su ,haka kawai sai kaga mutum kaji baka sonsa... Ko kuma kaga mutum kaji kana sonsa, irinku ina tausaya muku randa Allah zai muku talala " sai tayi dariya kawai batace komai ba "sai shine yace " toh sakarmin hannu duk kinsa hannuna yayi gumi saboda rik'o,sai tasaki hannun tana dariya ,tasa haannun nata ta d'auki wani turare a saman motar ta shinshina ta lumshe ido tace "wow ,Hamma don Allah kabani turaren nan ,k'amshinsa dad'i wallahi " kai tsaye yace "turaren maza ne ba na mata ba " da sauri tace "eh inaso haka Hamma, sai nabawa ya Abdurrahman yadinga fesawa inajin k'amshin kawai " sai yabita da kallo yad'anyi murmushi yace "yaran zamani kenan ...karasa ina suke koyon soyayya ma " yana rufe baki ta d'ora tana dariya tace "Aunty sakeena ce take koyamin fa " yayi mata wani kallon gefen ido yana harararta yace "fita a motar nan malama"
Tana dariyar ganin yadda yayi tafita a motar da turaren a hannunta tace “Adawo lafiya Hamman mu ,Allah ya tsare mana kai ” sannan ta rufe masa k’ofar yaja ya tafi, ita kuma tashige gida tanaji a zuciyarta Hammansu daban yake da Hamman kowa.
***Yana kammala karanta sak’on wayarsa ya cillar da wayar gefe ya fad’a kan Abdurrahman ya rungumeshi da tsananin k’arfi yana cusa kansa a k’irjinsa ,wani irin dad’i da murna na ratsa ruhin jikinsa ,sai da yagama tumurmushe jikin Abdurrahman da murna sannan ya sakeshi yakuma d’auko wayar da ya jefar ,dawowa yayi fuskarsa tamkar auduga dan fara’a ya zauna akusa da Abdurrahman yana nuna masa wayar,cewa yakeyi “Abdul kalla kagani …Abdul karanta sak’on sweety na kagani …tace tana sona.. tace tana k’aunata ….wai tabani dukkan zuciyarta amana …Abdul kaji yadda nakeji a zuciya ta kuwa …!?daman haka soyayyar take …!?haka take da dad’i Abdul …!?saida Abdurrahman yasa hannu ya karb’e wayar hannun sageer sannan yadafa kafad’arsa yace ” ka nutsu farin shigar soyayya ….me ta rubuto maka ne ka zauce haka ….!?ya kuma narkewa yana cewa “karanta kagani Abdul …na rantse yarinyar nan tagama mamayemin zuciya Abdul …” Yafad’a yana dafe k’irjinsa da lumshe idanu .
Abdurrahman na dariya yake duba sak'on inda yaga bashida wani yawa sai tarin ma'ana da sanin makamar so .
Abinda ke jikin sak’on shine.
Amincin Allah ya tabbata agareka Hamma sageer
so d’aya ne tak, kuma kai nake yiwa shi ,k’aunarka a raina batada misali a fad’in duniya ,nabaka amanar zuciya ta da ruhina da komai nawa, Kaine zab’in zuciya ta a farkon fara soyayya ,kuma Kaine k’arshe da yardar Allah,na amince kazama miji nagari a gareni
*sweetyn ka*
Iya sak’on da ya rud’a sageer kenan a fagen soyayya ,shiyasa Abdul nagama karantawa yad’ago yana duban sageer yana murmushi ,sageer yace “ka karanta Abdul….!?ya jinjina kai yace ” na karanta sageer “sai sageer ya runtse ido yana sauke ajiyar zuciya yace” kuma mun dace ko Abdul ….!?mun dace da juna ko ….!?Abdurrahman yakuma murmushi yace “kun dace sosai ,kamar yadda muka dace nida tawan ,shiyasa nake tayaka murna Abokina ” sageer yabud’e idanunsa da suka cika da soyayya da bege ya dire kallonsa akan fuskar Abdul yace “Abdurrahman ” Abdurrahman yace “na’am sageer ” kawai sai sageer yakamo hannun Abdul yad’ora kan k’irjinsa yace “Abdul kaji yanda k’irjina ke bugawa ….wai shima hakan duk acikin soyayya ne …!?wata muguwar dariya Abdul ya kwashe da ita, sannan ya dungure kan sageer yace ” gaskiya Hassana ta saka a kwana ,irin wannan zaucewa haka …!?kar kabada mu mana please ….!?sageer yad’an zame ya kashingid’a yana cewa “a ina zan badaku …!?yana rufe baki Abdul ya amsa da cewar ” agurin mata mana ….!?sai ya lumshe ido yana Shafa sumar kansa yace”ai daman mun zama na matan Abdul …”Abdul yace “yanzu kasan hakan kenan …..
Tana shiga gidan ta tarar da Umma da Babangida a tsakar gida da waya a hannunsa yana lalubowa Umma numbar Adda Nabeela zasuyi magana ,wayar tana fara ringin ya mik’awa Umma yana fad’in” Umma gashi tashiga ,don Allah in kungama magana kice mata zanzo na karb’i sak’ona fa “Umma ta karb’i wayar ta kara a kunnenta jin har Adda Nabeela tad’aga ,sai Umma tayi wucewarta d’aki tana amsa wayar ,Babangida ya d’aga murya yana cewa ” au Umma baza’ayi wayar agabanmu ba saboda zakiyi magana da babbar y’arki …!?Hussaina ta tuntsire da dariya tace “kasani ko sirri za’ayi tsakanin uwa da y’a ba’aso muji ” shima ya kwashe da dariya ,Umma na jinsu suna shakiyancinsu da dariya tayi musu banza tana amsa wayarta, tasan shakiyancin Hussaina da Babangida itama basu barta ba .
Ina rabin raina take ne ...!?Hussaina ta tambayi Babangida ,yabi turaren hannunta da kallo yana fad'in "nimafa shigowata kenan gidan ....inajin tana d'akinku ,nafa hangeki a motar Hamma sulaiman da zan shigo gida ...wannan turaren fa ...!?kamar Wanda Hamma ke amfani dashi "
Tana niyyar wucewa d'aki tace "eh shine ,turaren akwai dad'in k'amshi ,nace Hamma yabani shine yabani ,da sauri Babangida ya matsa gareta yana cewa " sister zo musa labule mana ...ki bani turaren nan tunda na maza ne ...."ta tab'e baki tace "cafd'ijam ,wai ma ..wallahi ya Abdurrahman zan bawa shi bazan baka ba ..." Ya d'an yamutsa fuska yana mole baki yace "kai sis ai wannan k'arawa me k'arfi k'arfi zakiyi ,ya Abdurrahman da yake da turare kala kala me zaiyi da wannan ...!?tayi gaba tana cewa " ko guda dubu yake dashi na rantse bazan baka ba ,da nace zan hau mashin d'inka ka d'anani ai k'in yarda kayi ...sai yanzu kace nabaka abuna ,to nak'i wayon "ta shige tabarshi anan yana cizon yatsa da fad'in " zan rama ne hajiyata ,bashi kika d'auka .
A kwance ta tarar da sisinta kamar Mara lafiya ,Hassana na ganinta ta mik'e zaune tana kallonta ,Hussainar ta k'arasa gunta ta zauna kusada ita tana fad'in "wash ,wallahi nagaji " ta zame ta kwanta akan cinyar Hassanar .
Shafa fuskarta Hassana tayi tana wasa da dimple d'in fuskarta ,a hankali cikin sanyin murya Hassana tace "sisina " Hussaina ta amsa tana gyara kwanciyarta ,Hassana takuma cewa "sisina nayi miki laifi " sai Hussaina ta yunk'ura tamik'e zaune tana kallon Hassana da k'iris yarage tafara kuka saboda idanunta da suka cika da hawaye ,k'ura mata ido tayi tace"laifi kuma ....!?laifin me kikayi min ....!?hawayen ya zubo akan fuskarta tace "kiyi hak'uri ki yafemin sisina ,bada son raina na aikata abinda bakyaso ba ,zuciya ta takasa jurewa ne "
Hussaina tace "nifa bangane ba ...yaseen kwata kwata ban fahimceki ba ...warwaremin maganar mana " kawai sai Hassana ta hasko mata wayarta tana cewa "kalla kiga sak'on da na turawa Hamma sageer sisina ,na b'ata miki rai ko ...!?don Allah ki yafemin " Hussaina tabi sak'on da kallo tana karantawa cikin fitar hayyaci da tsananin fad'uwar gaba ..........!
Comments
Share
Vote
Pls
HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍
TYPING????
???????? HASSANA ????????
*DA*
❣???? HUSSAINA ????❣
TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍
page3⃣3⃣to3⃣4⃣
WATTPAD:hassana3329
® PEN : WRITERS ASSOCIATION
~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~
TUNASARWA????
MANZON ALLAH (S A W) YACE “ALLAH YA FAD’A ACIKIN HADISIL K’UDSI ” NI NA WADATU DAGA DUKKAN WAD’ANDA SUKE HAD’ANI DA WANI ,DUK WANDA YA AIKATA WANI AIKI KUMA YA HAD’ANI DA WANI A CIKINSA ,TO NA BARSHI DA SHIRKAR SA
AIKI ME FALALA????
MANZON ALLAH (S A W ) YACE “RAKA’O’I BIYU NA ALFIJIR SUNFI DUNIYA DA ABINDA YAKE CIKINTA” (DUK WANDA YAYI SALLAR ASUBA YANA CIKIN ALK’AWARIN ALLAH)
INAJIN DAD’IN YADDA KUKE SON LITTAFIN NAN SISTERS ,NIMA INA SANKU SOSAI WALLAHI,NAGODE DA YABAWA????????????????
***D’agowa Hussaina tayi ta kalli Hassana tana wani irin b’ata rai da tamke fuska ,gaba d’aya fuskarta ta canza zuwa b’acin rai ,Hassana na ganin haka jikinta yafara rawa da karkarwa ,cikin rawar baki tafara magana hawaye na zuba a idanunta “daman nasan na b’ata miki rai …daman nasan nayi miki laifi ….banso zuwan ranar nan da tasa nayiwa sisina laifi ba …don Allah Dan k’aunar da ke tsakaninmu wadda bazata yanke ba kiyi hak’uri ” Hussaina nabud’e baki zatayi magana sai kawai ta tuntsire da dariya tana lakucewa Hassana hanci ….Hassana tabita da kallon mamaki me takewa dariya ,kuma menene yasata dariyar .
Saida tayi dariya ta isheta sannan tace "kema kin San ko fuskata tana nuna fushi take dake ,to zuciya ta farinciki take da ke ,karki damu indai akan wancan mutumin ne na amince da soyayyarku tuni ...Allah yashiga lamarin Ku yasa alkairi a tarayyar ku" Hassana ta yunk'ura ta afka jikin Hussainanta ta rungumeta tana hawayen murna ,so take tayi magana amma dad'i ya hana maganar fitowa ,sun dad'e a haka sannan Hussaina ta d'agota tana murmushi ta kalleta ta tallabe kumatun ta tace "kina sonsa da yawa sosai ...irin wannan runguma haka kamar zaki b'allani " Hassana tasaki murmushi da hawaye a fuskarta ta kwantar da kanta a tafin hannun Hussaina cikin k'aramar murya tace "inason Hamma sageer sisina ...kema ai yanzu kina sonsa ko ....!?Hussaina ta d'an kauda kanta tace " gaskiya kikeso in fad'amiki ko k'arya "a hankali Hassana ta d'aga kanta tana dubanta tace " sisina gara kifad'i gaskiyar tafi dacewa akan kiyi k'arya ,tunda kin San k'arya babu kyau ...kuma ked'in me bayyana gaskiyar kice akoda yaushe bakya rufe gaskiya kiyi k'arya ".
Saida Hussaina ta numfasa tasaka idanunta acikin na Hassana sannan tace " idan har gaskiyar zan fad'amiki banji ina sonsa a zuciya ta ba .....sai dai na amince yazamo mijinki tunda kina k'aunarsa rabin raina ...."Hassana ta runtse idanu wani sashi na zuciyarta na k'una ,ganin haka Hussaina ta dafa ta tace "kiyi hak'uri bana iya b'oye abinda ke zuciya ta ne ....amma komai da kikeso inasonsa ...na rantse shi kad'aine banaso " Hassana tayi murmushi tace "hakane sisina ,Allah shine yasan zuciyoyin bayinsa ,ban San Abinda Allah yake nufi da hakan ba ....amma zanta addu'a Allah yasa kiso Hamma sageer wata rana ...Allah yacire miki k'iyayyarsa a zuciyar ki "
Mik’ewa Hussaina tayi tana murmushi tace “bari naje naga me zan samawa ya Abdurrahman da zaici ,kinga bai samu yaci komai ba …” Da hanzari Hassana ta mik’e tana cewa “muje na tayaki sisina ” sosai Hussaina ta kalleta tace “shiga toilet ki wanke fuskarki ,kar Umma tagane kinyi kuka” Hassana ta d’anyi murmushi tace “OK ,sannan ta juya tashige toilet.
***Hamma sulaiman yasamu Baba yayi masa bayanin yadda suka tattauna da Hassana ,Baba yaji dad’i sai dai yace ” ina tausayin yaron nan Huzaifa ,yana sonta sosai da alamu “murmushi Hamma yayi yace ” ya za’ayi Baba ,daman ai akwai samu akwai rashi, haka zaiyi hak’uri Allah ya musanya masa da mafi alkairi”Baba yace “toh Ameen sulaiman ,amma bazan iya kiransa nagaya masa wannan maganar ba ,wallahi zanji kunyarsa sulaiman ,sai dai kai kasameshi ko Aminullah ,kuma yadace asanar dashi da wuri ” Hamma sulaiman yace “babu damuwa Baba ,ni zanje na d’auko sakeena a unguwa ne ,amma bari nakira wayar Aminu naji ko yana kusa ” Hamma yazaro wayarsa ya nemi numbar Hamma Aminu ya kira ,bata jima da fara ringin ba yaji and’aga da sallama ,muryar Sadiya yaji a kunnensa a maimakon ta Aminu ,ta gaisheshi ya amsa yana tambayar “ina mijin naki”