HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL
Hussaina tana ta kallonta har ta kammala ,sannan tace ” ina zakine kiketa faman shiri….!? Hamma sageer ne yazo ,yana waje “inji Hassana tana gyara zaman hijab d’inta ” Hussaina ta d’anyi tsaki ciki ciki ,sannan tace “wannan mutum yacika naci da yawa ….kullum yadamu mutane da zarya ….don Allah rabin raina kicemasa yarage zuwa haka …” Hassana tana daga tsaye tabita da kallo zuciyarta batai mata dad’i ba amma takasa magana “sai Zahra ce tace ” Hussy bakida kirki wallahi ,kasamu ma mutum ya nuna maka so da k’auna kamar sageer ai alfahari ne …wannan k’iyayyar taki tayi yawa ,na rantse kimai da hankalinki kar rabo ya kasheki ….ayi auren babu ke “
Hussaina na dariya tace "ta Allah ba takiba zahra ,mutuwa ba yanzu ba insha Allah " Zahra ta juyo tana kallon Hassana da jikinta yayi sanyi tace "Hassy jeki abinki kibar wannan Y'ar air d'in " sai Hassana tayi murmushi ta kalli Hussaina tace "kiyi hak'uri sisina " sai Hussainar ta kwashe da dariya tace "zan hak'ura ,amma gaskiya sai kince yarage zuwa yana ta ganemin ke ....haba kar ya lashemin ke mana " Zahra tabi Hussaina da kallo tana jijjiga kai ,sannan ta waigo ga Hassana tace "nacefa kiyi tafiyarki wajen masoyinki ,iskanci kawai yarinyar nan takeji kika tsaya biye mata ".
Hassana tasa kai tafita tana murmushi ,a tsakar gida ta tarar da Usman na wanke unifoam d'insa ,tayi kiransa tace " Autan Umma zo mana "ajiye wankin yayi ya d'auraye hannunsa yazo yace " Adda Hassana gani "ta dafashi tace " maza d'auko dadduma babba a d'akin Umma ka shimfid'a a soro ,Hamma sageer ne yazo ,d'azu kuwa kashare soron dai ko ..!?ta tambayeshi .
Yace “eh na share Adda ,dan ma ya safwan ya ajiye mashin d’insa bai fita dashi ba ,kawai sai na zagaye mashin d’in na share ragowar soran “
Ta Shafa kansa da fad’in” yawwa k’anina good bless you ,Ina alfahari da kai,maza kaje ka kai darduman ganinan “
Da gudunsa ya d’auko yanufi soron itakuma tashiga d’akin Umma Dan Neman iznin Fita.
A zauren Usman ya tarar da Hamma sageer ya d’au wanka cikin shigar manyan kaya na yadin kufta ,harda hula a kansa da ta k’ara fiddo asalin kyawunsa ,zaune yake akan mashin d’in safwan yana game da wayar Hannunsa ,Usman ya durk’usa ya gaisheshi yana niyyar shimfid’a dadduma ,sai Hamma sulaiman yace “barta kar ka shimfid’a Usman kawota nan ” Usman yaje ya mik’a masa yana kallonsa ,bai iya b’oye abinda ke ransa ba yace “Hamman Adda Hassana kayi kyau …!wallahi kayan sun maka kyau sosai …” Hamma sageer yayi murmushin da ya k’ara masa kyau yace “Allah ko Usman ?toh nagode ,ammafa ban kai ka kyauba …shiyasa nakeso idan akayi bikinmu Umma tabamu kai mutafi da kai ,kaga sweety na zatai ta ganin kyakkyawar fuskarka taita haifamin yara kyawawa”
Usman yayi k’aramar dariya yace “Allah Hamma Umma bazata Baku niba, bafa tason rabuwa dani”
A dai dai lokacin Hassana tafito zuwa zauren ,k’amshinta ya tabbatarwa da sageer zuwanta ,ya d’ago kai yanai mata wani kallo na soyayya da birgewa ,Usman na ganin tafito yajuya yashige gida ,shikuma Hamma sulaiman ya diro daga kan mashin d’in ,cikin murmushi ya nuna mata kan mashin d’in yace “hau ki zauna sweety na ,nikuma nasaki agaba naita kallon kayata” tayi murmushi tace “Hamma sageer ai …” Yasa hannu a bakinsa yace “shiiiit …kawai ki hau ,ni yau banason zama fa ,a tsaye zan tsaya ” haka tilas ta haye kan mashin d’in tana kallonsa da sunkuyar da kai ,ya matso dab da ita yadafa mashin d’in shima yana kallonta ya rage murya yace “yadai kike kallona kina sunkuyar da kai …!?ki d’ago ki kalli abinki ni nakine gabad’ayana sweety” sai tayi dariya tana langab’ar da kanta tace “Hamma sageer kayi kyau ,haka many an kaya suke maka kyau daman …!?ya D’AN rausayar da kai shima yace ” bancika saka suba, amma tunda kinaso zan dinga samiki kina gani sweety “ta d’an lumshe idanu tana jinjina kai .
Ya kuma rage murya yana kallon fuskarta yace ” kin san me Mamma tace kuwa …!?ta d’an ware idanunta tace “ah ah ,me tace…!?ya d’an tsuramata idanu yace ” Mamma ta maida gabad’aya harkokin kasuwancinta Abuja ,kuma ni takeso nazama manager d’inta akan komai ,tace zaman garin nan ya isheta saboda yana tunamata daddy na da rayuwar da sukayi ..tanemi alfarmata akan nabita abuja nidake muyi zamanmu a can bayan bikinmu tunda tanada gidaje a can,nikuma ban amsa mataba ,nace tabari sai nayi shawara dake duk abinda kikace ayi shi za’ayi “
Fuskar Hassana ta Nuna tsananin b’acin rai har hawaye yaciko idanunta ,da hanzari kamar zai shige jikinta yakuma matsowa jiki na rawa yace “banfa amsa mata Cewar zamu bitaba ,na rantse idan har bakyaso anan zamu zauna ,don Allah karkiyi kuka” ta d’an goge idanunta fuska babu walwala tace “Hamma sageer bakajin magana ko ..!?ya zaro idanu yana marairaice fuska yace” mekuma nayi sweety ….!?ta juyar da kanta gefe tana ajiyar zuciya tace”ba wani sweety ,k’imar Mamma tawuce tanemi Abu agunka kacemata sai kayi shawara dani Hamma sageer ,banaso kazama irin mazan nan masu fifita matansu akan mahaifiyarsu ,hakan bashida kyau ko kad’an ,ko banason zuwa dole zan amince kodan kayiwa mahaifiyar ka biyayya Hamma sageer “ya rasa abinda zaice saboda shauk’i ,kawai sai yad’ebo sambatu ” thank you for your advice ,that’s why I like you ,because you are the only one I love,I love you so much my sweety “
Fitowar su Hussaina yasasu juyawa suna kallonsu .Zahra ta matso garesu tana murmushi suka gaisa da Hamma sageer ,Hussaina kuwa gaba tayi fuskarta a d’aure ko kallon Hamma sageer batayi ba ,haka shima ya d’auke Kansa tamkar bai ganta ba yake amsawa Zahra gaisuwarta ,sosai Hassana taji zafin abinda suke aikatawa.
Zahra tayimusu sallama ta wuce ,daman tafiya zatayi shine Hussaina ta rakota ,a waje tasami Hussainar tsaye tana jiranta ,Zahra na zuwa ta hau Hussaina da masifar bata kyauta ba ,kamata yayi ta gaida sageer a matsayinsa na wadda Y’ar uwarta zata aura , Hussaina ta tsaya cak tana duban Zahra ,kana tayi k’aramin tsaki tace “Malama karki dameni ,bazan gaisheshi d’in ba ,ci yake bani ko sha …!?nafasa rakaki bakin titin ma wallahi tunda damuna zaki dingayi ” Zahra tace “karki rakani d’in ,masifaffiya kawai ” Hussaina tayiwa Zahra gwalo tajuya tana dariya ,yayinda Zahra tayi k’wafa da fad’in “kekam duk randa Allah yatashi kamaki ,zanga yadda bakin masifar nan zaiyi”.
Tana shiga soron tayi gaba abinta ko kallonsu bata kumayi ba ,har zata wuce Hassana tasa baki tayi kiranta ” sisina “Hussaina ta waiwaya ta d’an kalleta tana yamutsa fuska ,da murmushi akan fuskarta jikinta a sanyaye ta dubi fuskar Hamma sageer da yad’an kwantar jikin kan mashin d’in idanunsa a rufe ,sannan takuma kallon Hussaina cikin sanyin murya tace ” sisina karki wuce Baku gaisa da Hamma sageer ba ,Dan Allah kidawo Ku gaisa mana “kafin ma Hussaina tayi magana tuni sageer ya bud’e idanunsa ya waresu akan fuskar Hassana ,idanun har sun sauya kala alamar b’acin rai ,cikin k’ank’anuwar murya yace ” sweety kinji nace ina buk’atar gaisuwar tane …!?tarik’e abarta na rantse batada amfani agareni “yana rufe baki Hussaina tayi masa wani banzan kallo ta murgud’a baki tace ” ko baka fad’aba daman banida niyyar gaisheka ,domin baka cikin irin mutanen da yadace na gaisar ,ni ina gaida mutane masu daraja ne ba irinka d’an shaye shaye ba ,Wanda zuciya ta da bakina sukayiwa lak’abi da D’AN DABA”A wani irin fusace Hamma sageer yad’ago kai ya zuba mata ido ,gabad’aya zuciyarsa ta b’aci da tsantsar bak’inciki da takaici ,idanuwansa suka ciko da hawaye ,kallonta kawai yake yanajin ciwo a zuciyarsa da gangan jikinsa ,a gefe guda Hassana wata matsananciyar kunya ce ta kamata ,ga takaicin mutanen da suke taka muhimmiyar rawa a zuciyarta basa shiri da juna ,kowa acikinsu burinsa ya muzgunawa d’an uwansa ,batasan lokacin da kuka ya kufce mataba tasa hannu ta rufe fuskarta tana shesshek’ar kuka me tsuma zuciya “
Da sauri Hussaina tashige gida saboda batason jin kukan Hassana ,itama d’in ba da son ranta take b’ata ran rabin ranta ba ,ta rasa menene take damun zuciyarta da ta tsani sageer haka ,hawaye ne ya zubomata a kan fuskarta da hanzari ta goge gudun kar Umma tagani.