HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sageer kuwa zubewa yayi a gaban sweetynsa kansa a sunkuye yace “kukan ki inajinsa tamkar ana yankar naman jikina ,ki tausayamin kiyimin afuwa idan har na b’ata ranki…..” D’ago kanta tayi ,sannan ta goge hawayenta amma wasu na zirarowa ta d’aga hannayenta sama guda biyun ta had’esu alamar rok’on Allah ,cikin k’yarmar murya take fad’in “ubangijina mai sammai da k’assai na rok’eka kacire wannan k’iyayya daga zuciyar mutanen da nake matuk’ar k’auna …Allah na rok’eka ka wanke zuciyarsu daga ganin laifin juna ….burina a duniya a yanzu baiwuce naga alak’arsu tazama kyakkyawa ba …Allah nayi tawassali da annabin Rahama ka sanya salama a zuciyar wad’annan halitta sudena ganin bak’in juna ” sai takuma fashewa da kuka .

     Hamma sageer duk wasu kalamai na lallashi da k'auna da bege saida ya ambatawa Hassana su alokacin ...ya marairaice mata yana bata hak'uri akan abinda yafaru ,da kanta ta katseshi tace "kai zan bawa hak'uri ,kayi hak'uri da abinda sisina tayi maka please " yace "babu komai kidena kawo zancenta yana b'ata ranki kinji " da sauri tace "zancen sisina baya b'atamin rai Hamma sageer ,nafiso ayita min zancenta akan komai ,saboda ina sonta " ya d'an b'ata rai yace "nikuma bakyaso ayi zancena ko ...!?bakya sona ko.....!?tayi far da idanu tace " nagodewa Allah da ya kasance zuciyar bayinsa a lullub'e take ,da bawa na ganin zuciyar d'an uwansa bawa to da Hamma sageer yau yaga zuciyar Hassanar sa ,kuma abinda zai gani zai iya sawa ya sume Dan murna "ya mik'e daga durk'uson yana k'yalk'yala dariya me ban sha'awa yace " do n Allah sweety ki bud'emin zuciyar nagani mana "itama tana dariyar ganin ta wanke masa zuciya tace " karka damu Hamma sageer ,kai da zuciyar tazama taka kai kad'ai ma ,ba ganinta ba har kwanciya zakayi a cikinta kayi birgimarka son ranka "ya runtse idanu yana wata irin dariya yake furta " wayyo soyayya dad'i ,Allah ka nunamin randa sweety na zata zama mata agareni ".

Da daddare suna zaune gaba d’ayansu duka gidan ,ga Adda Nabeela da tayi zuwan magariba tana jiran mijinta zaizo ya d’auketa ,gidan yayi musu dad’i su Hamma sulaiman ko niyyar tafiya gida basayi ,so wajen uku Aunty Sadiya na kiran Hamma Aminu awaya wai yadawo gida tana jiransa ,tun yana amsawa da gashinan har ak’arshe ya kashe wayarma gabad’aya ,Baba ya dubeshi yace ” Aminullahi katashi kajemana ,kasani ko wani uzurin ne shiyasa taketa kiranka …”ya d’anyi dariya yana janyo jakar Adda Nabeela yace “wallahi Baba ta dameni wai kaza takeson ci yau …nikuma banida y’an canji bari naduba jakar babbar Yaya ko za’a samu ” ya fad’a yana k’ok’arin duba jakar ,Adda Nabeela tace “gaskiya k’anina dole Sadiya taci kaza yau ,bari nabaka canji idan yayi saura ka had’amata harda sassanyen lemo ” ta karb’i jakar ta k’irgo kud’i masu yawa ta mik’a masa “yasa hannu ya karb’a yana ” Allah yabar min ke Addan mu ,yau Amsad zataci kaza ta more “ya d’an juya yana kallon Hamma sulaiman da yake damawa Baba fura da hannunsa yace” Hamma sulaiman kaima d’an kawo wani Abu ahad’a kazar zatafi Auki “yayi masa wani kallon k’asan ido yace ” sai dai tamutu bataci kaza ba kuwa “Umma tace” kai yayansu d’iyar tawa …!?ya mik’awa Baba furar yana cewa “toh Umma nima banci kazar ba bare ita ay” Hussaina ta matsa jikin Adda Nabeela tana d’an marairaicewa tace “Addan mu ” Nabeela ta waiwayo tace “ya akayi y’an biyuna …!?ta d’an lashi baki tace” muma zamuci kazar “safwan ya kwashe da dariya yace ” wallahi tunda taji anfara zancen kaza take lasar baki kamar wata mayya “Adda Nabeela tayi dariya tace” safwan banda sharri dai ….Amare ai saida kaza ….Babangida zokaje bakin titi kasiyo muku gasasshiya mana “da hanzari Babangida yazo kusada Adda Nabeela ya durk’usa ,ta zaro kud’i masu yawa ta k’irga tabashi yasa hannu ya karb’a ya cusa a aljihu yaja hannun Usman yana cewa ” Autan Umma zo ka rakani bakin titi “Usman yatashi yabishi suka fice”.

Baba ya ajiye furar da yakesha ya dubi Adda Nabeela yace" bakya gajiya Nabeela ,kawai sun saki kashe kud'i da daddaren nan ko..!?tayi d'an murmushi tajawo ragowar furar Baba ta kurb'a tace "Baba idan banwa k'annena ba wa zanwa ...!?komai nawa ai mallakin sune " ya jijjiga kai da fad'in "hakane,hakane ,madallah Allah ya k'ara zumunci.

Dukansu suka amsa da Ameen ,sai Alokacin Adda Nabeela ta lura da Hassana da tunda aka zauna tunani takeyi ko magana batayi ba ,sai da takirawo sunanta sau uku sannan tayi firgigit ta amsa ,mamaki ya ishi Adda Nabeela tadubi Hamma sulaiman tace” Abban sadauki dubamin yarinyar nan kaga wani tunani me zurfi da takeyi ,anya lafiyarta k’alau kuwa …!?Umma ce tace “tun d’azu nake lura da ita kamar akwai damuwa acikin zuciyarta ,amma k’ila tafad’awa Y’ar uwarta Ku tambayi Hussaina kuji ” kafinma a tambayetan Hussainar tayi magana tace “bata gayamin komai ba Umma ,tund’azu nima nake tambayarta damuwarta ,amma tacemin ba komai ” Hamma Aminu yace “No,duk Wanda ya ganta yasan tana cikin damuwa ,ya kamata tabud’e baki tayi magana ,tafad’i abinda yake damunta …..” Ya juya ya kalli Baba da yayi shiru yana k’arewa Hassana kallo yace “Baba a tambayi yarinyar nan tafad’i damuwarta ” Baba ya gyara zamansa ya dubi sulaiman yace “sulaiman tambayeta menene yake damunta ….!?Hamma sulaiman da baice komaiba ya dubeta lokacin har tafara zubda hawaye yace” matso nan “ta taso a sanyaye safwan ya matsa ta wuce kusa da Hamma sulaiman ta zauna ,ya kalleta yace ” kina mantawa da cewa dukanmu nan makusantanki ne ,ga mahaifinki ,ga mahaifiyarki ,ga yayyenki da k’annenki ,babu Wanda yadace yasan damuwarki irinmu ,menene yake damunki …!?ta d’ago kanta taga kowa ita yake kallo ana jiran jin tabakinta,zuciyarta takuma karyewa sai ta kife kanta kan cinyar Hamma sulaiman ta fashe da kuka.

Gurin yayi tsit sai shesshek'ar kukanta ke tashi ,kowa agun zuciyarsa ba dad'i saboda yadda kukanta yake tab'a zuciyarsu ,Hussaina kuwa harta fara tayata kukan,yayinda zuciyar Umma ke fargabar menene yasaka d'iyarta damuwa haka....!?

Kusan Minti biyu babu Wanda Yakuma magana ,illah sauraron kukanta da sukeyi,sai Hamma sulaiman ne yasa hannu ya d’ago fuskarta da tai kaca kaca da hawaye ,yace “ke dubeni nan” ta kalleshi hawaye na ambaliya ,ya d’aure fuska sosai yace “na tab’a marinki kuwa …!?ta gigiza kai tanata kallonsa ,ya D’AN lumshe idanu yabud’e yace”wallahi zan mareki yanzu ,idan har baki bud’e baki kinfad’i menene yake damunki ba ….bakiga yadda duk kika sakamu cikin damuwa bane….!?

 Hassana cikin shesshek'ar kuka tafara magana" Hamma daman ....Hamma sageer ne ...yacemin ...wai ..Mamma tace... Abuja zasu tafi dani bayan bikinmu ...a can zamucigaba da zama...nikuma banason rabuwa daku ....gashi na amsa masa kodan yayiwa mahaifiyarsa biyayya .....banason rabuwata daku...banason natafi na barku..."ta kuma fashewa da matsanancin kuka .

Kafin kowa yayi magana,Hussaina ta mik’e tsaye a firgice,idanunta a warwaje ta dafe k’irjinta ,da k’arfi tace “whatttttt….!?me kika ce……!?

Comments
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍


TYPING????

???????? HASSANA ????????

            *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page3⃣7⃣to3⃣8⃣*

WATTPAD:hassana3329

® PEN : WRITERS ASSOCIATION


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

TUNASARWA????

MANZON ALLAH (S A W ) YACE “KO KUNSAN ME AKE CEMA GIBA ?,SAI SUKACE ” ALLAH DA MANZONSA NE KAD’AI SUKA SANI ,SAI YACE “SHINE KA AMBACI D’AN UWANKA DA ABINDA BAYASO .SAI SUKACE ” SHIN IDAN ABINDA AKA AMBACESHI DASHI GASKIYANE FA ?,SAI YACE “IDAN ABINDA AKA AMBATA D’IN GASKIYANE ,TO KUNCI NAMANSA ,IDAN KUMA ABUN BA GASKIYA BANE TI LALLAI KUNYI MASA K’ARYA

AIKI ME FALALA????

MANZON ALLAH (S A W )YACE ” BABU WANI MUSULMI DA ZAI ZIYARCI MUSULMI MARA LAFIYA DA SAFE ,FACE MALA’IKU DUBU SABA’IN SUNYI MASA ADDU’AR HAR SAI YA KAI YAMMACI,IDAN KUMA DA YAMMACI YAYI ZIYARAR ,MALA’IKU ZASUYI MASA ADDU’A HAR ZUWA SAFIYA ,KUMA ZAI SAMI GONA ACIKIN ALJANNA

DEDICATED TO

ALL MY FAN’S????????????

Kowa yabi Hussaina da kallo ganin yadda jikinta ke wani irin tsuma na tashin hankali ,bata damu da kallon da suke mataba illah Hassana da ta nufa ta zube gabanta ta fizgo kafad’unta ,cikin makyarkyatar murya tace “da bakinki kike fad’in zakibi wani Abuja ki barni ….!?ina alk’awarin da mukayiwa juna nacewa d’ayanmu ba zai nisanci d’an uwansa ba …!?tambayarki nakeyi ina alk’awarinmu ko kin karya ne ….!?tafad’a da k’arfi tana zazzaro idanuwa “

       Kifawar Hussaina kawai suka gani kan Hamma Aminu ,saboda wani gigitaccen mari da Hamma sulaiman ya sakar mata ,k'irjin Hamma Aminu tafad'a tana wani irin kuka me tada hankali da ajiyar zuciya ,tana kukan take fad'in "bazan iya rabuwa da Y'ar uwata ba ....bazan iya jure tafiyarta guri me nisa ba .....Hamma sulaiman na yadda kaita dukana idan har zakace kar tabishi Abuja ....meyasa yakeson rabani da gudan jinina ...!?meyasa yakesan d'aukemin ita bayan ....." Saita kasa k'arasawa saboda kukan da yaci k'arfinta ,hawaye da majinarta na malala a k'irjin Hamma Aminu .



     Ita kuwa Hassana tamkar a fuskarta Hamma sulaiman yayi marin, saboda zafinsa da taji ,ganin yana k'ok'arin fizgo Hussaina daga jikin Hamma Aminu yasa tayi saurin shiga tsakiya tana duban Hamma sulaiman hawaye na tsananin zuba a idanunta tace "Ashe aduk lokacin da natashi tafiya bazaka iya rik'emin amanar da zan baka ba ,Hamma sulaiman kaifa zuciya ta taketa rayawa cewa zaka rik'emin sisina aduk lokacin da bana tare da ita ,na rok'eka saboda girman Allah kadena dukar min ita " sai Hamma sulaiman yakasa magana illa tsurawa Hassana idanu da yayi ,yana had'iyar zuciyar b'acin rai .

Baba ne yace “sulaiman ” Hamma sulaiman yajuyo ga Baba amma yakasa amsa kiran, Baba yakuma cewa “sulaiman zo nan ,taho gareni sulaiman ” a hankali Hamma yataka gaban Baba ya tsuguna yanata numfarfashi ,Baba yasa hannu yana Shafa kansa ,sannan yadubi safwan yace “bud’e firij d’in can safwan kabani ruwa me rangwamin sanyi ” jiki a sanyaye safwan ya mik’e ya d’akko ruwan ya kawowa Baba ya bashi, Baba ya bud’e ruwan ya tsiyaya a cup d’in da safwan ya had’o dashi ,sannan ya nufi bakin Hamma sulaiman da ruwan yace “bud’e bakinka kasha ruwa sulaiman ” Hamma sulaiman ya d’an runtse idanu yasa bakinsa kan kofin yafara zuk’ar ruwan ,saida ya shanye tas yayi ajiyar zuciya sannan Baba ya janye kofin ya ajiye gefe ,ya kalli Hamma sulaiman yakuma dafa kansa cikin muryar tausasawar Uba zuwa ga d’ansa yace “kanajina ko sulaiman ….!?duk abin bana zafi bane ,idan har tayi wani Abu na ba dai dai ba ,kajata jikinka kayi mata nasiha kabata shawara ,bawai duka ba ,ai shi duka baya shiryar da mutum ,kadena saurin hannu kaji sulaiman ” Hamma sulaiman da b’acin ransa ya ragu ya jijjiga kai ,cikin shak’ak’k’iyar murya yace “nadena Baba ,insha Allahu nadena ” Baba yace “yawwa nagode maka sulaiman ,ai kaga Kaine Babba dole sai kana hak’uri da k’annenka ,musamman matan, saboda rauninsu ” sannan ya juya ya kalli Hamma Aminu yace “Aminu mik’omin kyautar Allah nan itama ” Hamma Aminu yad’agota daga k’irjinsa tanata kuka, ya sharemata hawayenta da hannuwansa ,sannan ya mik’e ya rik’e hannunta ya kaita har gaban Baba ,Baban ya jawota kusa dashi sosai ya rik’e hannunta yace “dai na kuka kyautar Allah” ta had’iye kukanta tana kallon Hamma sulaiman da kansa ke sunkuye ,Baba ya kalleta yace “shi Aure babu inda baya kai mutum koda kuwa birnin sin ne ,muma iyayenta bazamu ji dad’in rabuwa da itaba ,amma idan ubangiji ya k’addara rabuwar dole zamu hak’ura ne ,Abuja ba wani nisa bane ,aduk sands kikaso ganinta Abdurrahman me iya kaiki ki ganta ne ,tunda Abokin sageer d’inne ,itama idan taso ganinki sageer me kawotane ta ganki,kuma karki manta da cewar duk inda had’uwa take akwai ranar rabuwa ,ko babu aure akwai mutuwa ,kidena sawa ranki damuwa ,sageer bai isa yarabaku ba tunda tare ya ganku kinji ” ta girgiza kai tana k’ara share hawaye “Baba yakuma cewa ” kinga kin b’atawa Hammanku rai har ya dokeki ,kibashi hak’uri yan zunnan “ta matsa jikin Hamman ta kwantar da kanta a kafad’arsa hawaye na zuba tace” kayi hak’uri Hamma sulaiman bazan kuma ba !”ya d’an rungumeta da hannunsa cikin sanyin murya yace “babu komai ya wuce ,amma kidinga yiwa Y’ar uwarki adalci ,kidena sakata kuka ” ta goge fuskarta a kafad’arsa takuma cewa “toh Hamma ,nadena insha Allah “.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button