HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

* * * Tsananin mamaki ne Yakama Hassana ganin barci yak'i zuwa idanunta ,da ta rufe idon fuskar matashin saurayin ke haska ganinta ,me yake faruwa da ita hakane ......!? menene tsakaninta dashi da har hoton fuskarsa da tunaninsa zai dameta ........!? Ita dai tasan batada wata alak'a dashi tun lokacin da suka fara ganinsa kullum zaune a wannan dakalin, har kawo yau da ya aikata abinda ya aikata har Hussaina ta wanke shi tas .......
A rayuwar ta babu abinda ta tsana irin maza masu shaye shaye ,amma yau ga d’an shaye shaye ya tsaya a zuciyarta ,maimakon taji zafin abinda yayi mata ah ah saima wani mugun girma da tausayin sa da taji ,ta tabbatar da cewa duk yadda akayi halin rayuwa ne yasashi a wannan halin ,domin da ganinsa baiyi kama da mutumin banza ba .
Nan ta hangi yadda fuskarsa ta nuna muzanta a sanda Hussaina ke surfa masa masifa ,ga yadda jikinsa yayi sanyi idanunsa sun sauya kala a sanda ya juyo yana dubansu saida taji fad'uwar gaban da bata tab'a jiba.
kimanin sati uku kenan da suka fara ganinsa a layin nasu ,kullum suka taso daga islamiyya anan suke ganinsa yana y’an zuk’e zuk’en sa ,basu tab’a kulawa da lamarinsa ba ,sai dai muddin zasu wuce idan har sukaji warin sigarin sa sai Hussaina tayi tsaki ,haka wataran zasu isa gida tana mita da fad’in “wannan gayen yayi asara ,baida aiki sai bankar hayak’i ko ta lafiyarsa ma bayayi ……..”
Sauda yawa Hassana kanyi murmushin rigimar Hussaina ,ko ina ruwanta dashi oho ,sai dai kuma asaninta Hussaina bata ta'ammali da mutumin da yake sab'awa Allah ,wanda bayajin kunyar Allah da ta mutane, Wanda zai iya fitowa fili bainan nasi yana zuk'e zuk'e ba tare da jin kunya ba .
Hussaina tanada nagartattun halaye irinna Hassanarta ,guri d'aya sukasha bam bam , Hassana Nada matuk'ar hak'uri ,da kauda kai a yawancin al'amura,koda kuwa ita aka cuta ,yayinda Hussaina tazama me yawan fad'a da rashin d'aukar raini bata yadda wani ya takata ba ko kad'an ,haka daka tab'a Hassanar ta Rabin jikinta acewarta ,gara ka tab'ata ,domin ansha fad'a da Hussaina akan Hassana ,A kullum Hussaina na fad'in a duniya in kacire uwa da Uba babu kamar Hassanarta a zuciyar ta .
Mirginawa Hassana tayi daga kwancen tadubi Hussaina dake faman bacci tana sauke numfashi a hankali ,taji k'aunar sisin ta ta kuma kamata ,tanason Hussaina so mai tsanani ,bata k'aunar abinda zai rabasu ko na second guda ,komai nasu tare sukeyi babu bambamci ,sannan sosai suke kama ta yadda mutane da yawa basa iya bambance su sai ta guri d'aya ,ita Hassana tanada wani k'urji me kama da tusar jaki a k'asan bakinta dai dai hab'arta ,bak'i ne Wanda ya k'ara mata kyau a fuskar ta ,sau da yawa Hussaina takan tab'ashi tana shafawa ta dinga fad'in "Rabin raina inama Nike da wannan abin ,yana k'ara miki kyau fa .........,ita kuma Hassana takan ce " nikuma inama ni nake da dimple d'inki ,bakiga kyawun da kike ba in kinyi murmushi ,haka kobakiyi murmushi ba indai kina magana yakan fito ya k'ara bayyana kyawunki sisina .........,sai dukansu sukama dariya Hassana na tab'a dimple d'in Hussaina ,itama Hussaina na tab'a tusar jakin Hassana .
Hassana ta kuma juyawa tana runtse idanunta domin tasamu bacci ya sureta ,amma batayi nasara ba ,tunanin mutumin da batasan ko sunansa ba ya gallabeta ,bata sanshiba ,batasan waye shiba ,batasan daga ina yafito ba, domin ba d'an unguwar bane ayadda alamu suka nuna ,daga ganinsa daga wata babbar unguwa ta masu kud'i yafito ba irin unguwar su ta talakawa ba ,babban abin tambayar menene dalilin zuwansa unguwar su ya zauna yana shaye shaye .....?menene tarihin rayuwar sa da kuma shigowa unguwar su cikin layinsu ,duk da kasancewar unguwar tasuma akwai gidajen masu kud'i jefi jefi amma baya d'aya daga cikin yaran gidajen ,asali ma fuskarsa bak'uwa ce a unguwar .
A zuciyar ta taji cewar insha Allahu sai tayi k'ok'arin sanin wanene shi ,kuma tanaji a zuciyarta zatayi iya yinta domin ganin tacireshi daga yanayin da ta ganshi ciki ,haka kawai taji ya kwanta mata a zuciyarta farat d'aya ,jinsa tayi tamkar Hamma sulaiman d'an uwanta ,a zuciyarta tace ko ya sunansa ma oho ...............!?
Dataga babu alamun barcin zai d'auketa sai ta tashi tashiga toilet d'in d'akinsu ta d'auro alawala tazo ta sallaci Daren ,bayan ta idar da sallar tayi adduo'in ta ,sannan tasamu kanta da yiwa wannan kyakkyawan saurayi addu'a batasan menene dalilinta ba .
Cikin ikon Allah tana kammalawa ta kwanta sai barci ya d'auketa ,ammafa cikeda mafarkin kyakkyawan saurayi me shan sigari .
Washe gari safiyar alhamis sukayi shirin tafiya Makarantar boko ,(senior secondary school herwagana ) itace makarantar su inda suka kusan kammalawa tunda suna SS 3 ne ,Makaranta ce ta gwamnati amma kuma akwai karatu da k'wararrun malamai a cikinta ,sai akayi dace y'anbiyun kuma masu fasaha ne da saurin d'aukar karatu ,tun tasowar su fara Makaranta tun daga nursery ,primary ,har zuwa junior secondary d'insu me suna( G S T C Gombe )basu tab'a wuce Na uku ba ,har zuwa yanzu da suke babbar secondary ,kullum result d'insu idan akayi exam position d'insu baya wuce Hassana tayi na d'aya ,Hussaina tayi na biyu ,ko kuma Hussaina tayi na d'aya ,Hassana tayi na biyu ,shiyasa malamansu ke matuk'ar sonsu da k'aunar su saboda k'wazonsu .
Bayan sun karya da kunu da k'osai Wanda suka sarrafa da hannunsu suka taya ummansu ,sai sukasa kayan Makaranta domin tafiya ,d'akin baba suka shiga domin yimasa sallama don tafiya ,suna shiga suka durk'usa yana kashingid'e kan dadduma yanajin labarai a redio na safe, ga carbi a hannunsa yana ja yana hailala ,shigowarsu tasashi tashi ya zauna dai dai ,bayan ya amsa sallamarsu sun tsuguna Hassana tace "Baba mun shirya zamu wuce Makaranta "
Baba yace "madalla kyautar Allah sannunku da k'ok'ari ,Allah ya tsare yabada ilimi me amfani ,sannan ya zura hannu a aljihun rigarsa yazaro d'ari biyu ya mik'o musu yana cewa " toh ga wannan kusayi wani d'an abun Ku tab'a kafin kudawo gida ko ,tunda dai bawai mota zaku hau ba ..........!?
Girgiza kai Hassana tayi tana cewa "ka barshi Baba munada ragowar kud'i a hannunmu da Hamma sulaiman yabamu wancan satin zasu ishemu muyi amfani dasu kum ............kafin Hassana ta k'arasa maganarta Hussaina tayi wuf ta karb'i kud'in a hannun Baba tana dariya tace " wallahi Baba inbataso ni inaso, daman inason sayen littafi da Biro yau sainayi amfani dasu kawai ko Baban mu ........!?
Hassana sakato tayi tana kallon Hussaina da murmushi a fuskarta ,a zuciyarta tace sisina kenan ,shikuwa Baba dariya yayi yana cewa "Hussaina ko danke na tashi Na nemi kud'i ,buk'atarki tafi takowa yawa a gidannan fa ,yau acikinku waye zai kawomin abinci da rana ???ya tambayesu .
" Nice Baba ",Hussaina tafad'a ,Hassana tace " eh Baba ita zata kawo maka ,amma ina son tabari nizan kawo maka yau d'in kaji ........sisi kibari na kaimasa yau inyaso gobe sai ki kai masa .
Hussaina tace "toh Rabin raina na barmiki ladan yau d'in ke kisamu ai kamar ni nasamu ne ,amma gobe sai dai autan Umma yakai ,kinga zamu gidan Hamman mu adda sakeena na Neman mu fa ......ko kin manta .... !?
"Hakane ,hakane fa ,cewar Hassana ",Baba dai nata kallonsu yana jin k'aunar y'an biyun nasa a ransa ,gyaran murya yayi sannan yace " kutashi kutafi karku makara ,Allah yabada sa'a .
Ameen Baban mu ,suka amsa a tare ,sannan suka mik’e suka niyyar fitowa daga d’akin Umma tasawo kanta ciki rik’eda kayan karyawar baba a hannunta ,amsar kayan Hussaina tayi ta ajiye sannan sukayiwa Umma sallama suka fice, Hannun Hussaina dafe da kafad’ar Hassanar ta ………
K'arfe biyu suka taso daga Makaranta ,agurguje Hassana tacire unifoam d'inta daman tuni sunyi sallah a Makaranta ,tanata sauri taje ta kaiwa Baba abincinsa can bakin titin layinsu inda yake sana'ar saida kayan gwari (kayan miya ),Umma ce ta k'walawa Hassana kira da fad'in ta hanzarta tafito ,da sauri ta k'arasa zura hijabinta me hannu ajikinta Wanda yayi mata matuk'ar kyawu ,bata tsaya d'aura nik'abinta ba kasancewar tana sauri ,tafito tana cewa Hussaina "sisina kifito da kayan gugar nan kifara kafin nadawo tunda ankawo NEPA kafin su d'auke kinsan dai ba tabbas garesu ba ",bata jira amsar Hussaina ba tayi kitchen gurin Umma ta karb'i flask d'in da ta zubawa Baba abincinsa ,dafadukan shinkafa da wake ne ta manja ,taji Alayyahu da albasa sai tururi da k'amshi ke tashi ,a hak'ik'anin gaskiya Umma badai iya girki ba ,komai ta sarrafa dad'i yakeyi shiyasa su Hassana suke k'ok'arin koyon girkuna agun Umma musamman na gargajiya ,na zamani kuma sukan koya gun Adda Nabeela ko kuma goggonsu k'anwar Umma kenan.
Sallama tayiwa Umma sannan tafito da niyyar tafiya ,a soro sukayi kacib'us da safwan yadawo daga tasa school d'in ,alamunsa sun nuna agajiye yake ,kansa a langab'e yana k'ok'arin gyara jakar dake goye a bayansa ya dubeta yace " sister ina zuwa haka da zafin ranar nan ,kinji kuwa ranar da ake tamfatsawa ....!?ga wata yunwa da na kwaso ,Allah dai yasa Umman mu tagama abinci na ganki da flask, wallahi muguwar yunwa nakeji kamar ansacemin kayan cikina ......
Ya fad'a yana Shafa cikinsa da k'aramar dariya .
Sosai yabawa Hassana dariya ganin yadda gajiya da yunwa tasa yayi laushi ,cikin dariya tace "kai ya safwan bakada juriyar yunwa tamkar Hamma sulaiman kake ,shifa Hamma idan aunty sakeena nason ganin fushinsa to tabari yadawo gida bata kammala abinci ba ,Allah ko dariyarsa bazata ganiba ranar ......sai dai yaita kama ciki da y'an harare harare da tsaki .
Daga cikin gida tajiyo maganar Umma na fad’in ” oh ni fadimatu, yanzu Hassana keda Waye a soron nan kika tsaya baki tafi kaiwa Malam abincin nan ba ,anya kuwa Hassana kema kin koyi shiririta ko ????
Da sauri narufe baki ina dariya Ashe Umma najiyo mu kenan ,natsaya hira na barmata miji da yunwa ,nayi hanzarin fita daga gidan inda nabar ya safwan na jijjiga kai yana dariya tare da fad'in "au wai daman Baba zaki kaiwa abinci kika tsaya surutu ???lallaima sister ai ...........ban tsaya jin k'arashem maganar saba nayi gaba rungume da flask a k'irji na ..........
pls comment’s and share
HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍
TYPING????
???????? HASSANA ????????
*DA*
❣???? HUSSAINA ????❣
TARE DA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍
page 5⃣to 6⃣
WATTPAD:hassana3329
SADAUKARWA
GAREKU Y’AN BIYU KYAUTAR ALLAH
1- HASSAN TANKO ATK
2- HUSSAINI TANKO 80k
ALLAH YASAKA MUKU DA ALKAIRI ABISA K’OK’ARINKU GAREMU NA POSTING ,SANNAN INA TAYAKU MURNAR KAMMALA LITTAFINKU ME SUNA K’AZAMA SHALELE ,HAK’IK’A KUNYI K’OK’ARI MATUK’A TWINS
BARKAN MU DA JUMA’A Y’AN UWA ,ALLAH YABAMU ALBARKACIN WANNAN RANA ME ALBARKA ????????????????????????
***Nasamu Baba yana sallamar wasu yara da suka zo sayen tumatur ,bayan ya sallame su ya tareni da fara’arsa yana fad’in “kyautar Allah har kundawo daga makarantar kenan ???shigo shigo ga benci ki zauna .
Na shiga rumfar tasa ta langa langa da buhu inda yake zama Dan sana'arsa ,sana'ar da babu yanda Hamma sulaiman da Hamma Aminu da Adda Nabeela basuyi da Baba yadena taba ,tunda yanzu Allah yarufa musu asiri basu rasa komai ba ,amma Baba yak'i ,yace ba zai iya zaman gida ba yasaba da sana'arsa ,sukace ya sauya Sana'a nanma yak'i amincewa tilas suka barshi badon sun soba ,Hamma sulaiman yafi kowa jin haushin sana'ar nan ta Baba ,amma Baba baya kulawa yakance " sulaiman kenan wannan sana'ar da kake k'i yanzu da ita nayi maka komai har ka girma kazama haka kaida y'an uwanka .
Na zauna kan bencin inayiwa Baba sannu ,ya amsa shima yana zama kusa dani ,na ajiye abincin ina fad'in "kayi hak'uri Baban mu bankawo abincin da wuri ba na barka da yunwa ko .....!?
“Baba yace ” ai bana tare da yunwa me yawa ma ,d’azu nasha fura da nasiya a hannun wata Fillo ,ga kindirmo can ma a k’warya inzaki tafi kiwuce muku dashi gida ,akwai ragowar furar da Aminullahi yakawo jiya sai kudama kusha …..
” Hassana tace “toh Baba Allah yak’ara maka bud’i na alkairi “
“Ameen, Ameen Hassanata” ,Baba ya furta yana k’ok’arin janyo butar dake gefensa domin wanke hannunsa ,da sauri na mik’o masa butar ya matsar da hannunsa gefe na zuba masa ya wanke hannun ,sannan yajawo abincin ya bud’e yana fad’in “nafison inci abinci da hannuna yafi albarka ,shiyasa bancika son saka cokali ba ” nayi murmushi nace “hakan Nada kyau Baba “
Bai dad'e da fara ci ba wata yarinya tazo sayen tattasai ,Baba yana k'ok'arin zare hannunsa Dan tashi yabata nace "Ah ah Baba yi zamanka kurum ,bari nazuba mata da kaina saina nuna maka idan yayi ko ???Baba yace " toh bismillah ,zuba nagani.
Na karb'i kud'in yarinyar naira hamsin nazuba mata, nad'agoshi ina nunawa baba yagani ko yayi ?,Baba yace "d'an k'aramata wannan yayi tsada kyautar Allah " nace "toh Baba "na k'aramata nabata tatafi .
“Nadawo na zauna har ya kammala ci yayi hamdala ga sarki Allah ,yakuma wanke hannunsa ,da kaina nad’auki naira goma a cikin cinikinsa na tsallaka wani kanti nasayo masa pure water ,me kantin sai wani kallona yake yanamin murmushi da Sosa k’eya ,nayi maza na d’aure fuskata ina danasanin fitowa ba nik’ab a fuskata saboda yawan kallon da nakesha a gurin maza ma tamfar su cinyeni .
Bayan Baba yagama shan ruwan sai ya d'akko nonon a k'warya yasa na d'akko bak'ar Leda na bud'e aka juye a ciki Dan yayimin sauk'in d'auka, tunda ga flask zan koma dashi gida shima , Baba ya sallameni ganin wasu masu siyan kayan miyar sunzo .
Baba yana ciniki sosai saboda arhar kayan sa shiyasa wani zubin kan la’asar komai ya k’are ,na d’auki flask d’in na rungume sannan na d’auki ledar nonon a hannuna ,nace ” toh Baba natafi gida sai kadawo ,adawo lafiya Babana ” ya kalleni yana murmushi yace “Allah yasa ” kicewa babangida bayan la’asar yazo zai d’aukar mun wasu kaya mukoma gida tare “nace ” toh Baba” sannan nafito daga rumfar tasa nayi hanyar gida ina tafiya cikin nutsuwa da taku mai birgewa ,kaina a k’asa saboda yawan kallon da ake damuna dashi .
Ina yanko layinmu na hangi wannan farin kyakkyawan saurayin tsaye agefen dakalin da yasaba zama ,ga wata mace a gefensa tsaye itama tana masa magana fuskarta da damuwa sosai ,kamar yadda shima fuskarsa take a d'aure kamar gobara ,sai nacin kallonsa takeyi shikuma yana faman basarwa da d'auke kai daga gareta ,kamarsu d'aya shida matar sak ,sai dai yafita kyau ,itakuma tafishi shekaru daga gani ,sanye take da wani boyel lace na mata mai azabar kyau doguwar Riga ,ba d'an kwali a kanta sai ta yane kanta da mayafi kalar adon boyel d'in ,shikuma sanye yake da k'ananan kaya kamar kullum dai ,a tsawon lokacin da na kwashe ina ganinsa ban tab'a ganinsa da manyan kaya ba kullum sai k'ananan kaya .
Kamar ance ya waiwayo inda nake ,ya kallo b'angaren da nake tawowa kuwa sai karaf muka had'a ido ,nasamu kaina da fad'uwar gaba sosai dalilin fad'awar idanuna cikin nasa ,shikuwa k'uramin idanunsa yayi yana wani irin kallona da dukkan zuciyarsa ,a ransa yake fad'in ga wannan Mara kunyar nan da jiya tamin fitsara ,wadda bak'in cikin abinda taimin ya hanani runtsawa da daddare ".
K'afafuna ne suka soma hard'ewa dalilin kallon da naga yanamun ,idanunsa sun min kaifi da yawa ,jikina har tsuma yakeyi ,narasa meyasa nakejin gayen a zuciya ta fiyeda misali ,ganin irin kallon da yakewa waje d'aya babu ko k'iftawa yasa matar juyowa don ganin me yake kallo saboda ganin gabad'aya hankalinsa ya d'auke a kanta ba saurarenta yakeba ........
Juyowarta tasa muka had'a ido ni da ita ,ina taku a hankali dab dasu ,kallon fuskarta yabani damar shaidata ,matar wani babban lawyer ce da suke a layin ,gidanta shine a farkon shigowa layin mu wani tangameme me azabar kyawu da had'uwa ,so d'aya natab'a shiga gidan dalilin kai mata abincin sallah da Umman mu ta aikeni ,hakanan ganina da ita sau biyu ne ,lokacin da tashigo gidanmu sanda suka tare a unguwar da kuma sanda naje d'in tare da rakiyar Usman ,amma ina ganinta na shaidata ,macece me yawan fara'a da ganin k'imar mutane duk da ta kasance tana auren mai k'umbar Susa wato me kud'i kenan .
” Ko a yanzun ma washemin baki tayi da fara’arta harna k’araso gabanta na tsuguna na gaisheta cikin sanyin murya da kyarmar jiki ganin wani irin mugun kallon da saurayin kemin ,da saurinta ta amsa gaisuwata harda tambayata mutan gidanmu ,nace kowa lafiya “sannan najuya nace da saurayin kaina a k’asa ” ina yini …!?yayi min banza yana juyar da kansa tamfar ba dashi nake ba ……mamaki nema ya kamashi ganin na gaishesu ….a ganinsa Mara kunya kamata ai bata iya gaisuwa da girmama mutane ba .
Muryar matar naji wadda in ban manta ba kamar sunanta Nafisa tana cewa "Muhammad kaifa ake gaisarwa amma ka share ......pls karage miskilancin nan naka baya maka kyau ........!yad'an kalleta ya motsa bakinsa alamar magana a hankali yace " no ,bana amsa gaisuwar Mara kunya "duk da a hankali yayi maganar naji abinda yace ,murmushi ne yaso k'wacemin saboda nasan yayi tunanin Hussaina ce ni ,bai San mu twins baneba ,tunda ranar fuskar Hussaina yagani nikuma tawa fuskar na cikin nik'ab .
Sosai tazaro ido tana cewa " Mara kunya kuma .....!?yaushe ka Santa ma da har zakayi mata wannan shaidar ......!?kai dai kawai rigimarka ta motsane Muhammad sageer ,Allah dai ya shiryeka ya gyaramin kai .
“Ta waigo kaina ina shirin mik’ewa ina mai maita sunansa a zuciya ta MUHAMMAD SAGEER ,Gaskiya sunansa akwai dad’i da kyau ,cemin tayi “kiyi hak’uri da rigimar sageer halinsa sai hak’uri ,ki gaida Umman taku da sauran mutan gidan kinji ,cikin kunya nace ” zasuji insha Allah ,nasaci kallon sageer sai naga har lokacin kallona yake ,da sauri na kawarda idanuna nayi gaba, k’afafuna na hard’ewa na barsu a gun.
Sai da nakusan shiga gida sannan na waiwayo na k'ara dubansu ,sainaga ta rik'e hannunsa tanaja alamar tanason yabita ,shikuma ya wani kwab'e fuska yana Binta da k'yar alamar bayaso, har suka shige get d'in gidanta ,na sauke ajiyar zuciya me k'arfi jikina duk ya mutu ,narasa meyake faruwa dani haka ,ganin da na kumayi masa yau ya k'ayatar da ruhina ba kad'an ba ,ko meye tsakanin sa da matar oho ,amma tabbas akwai alak'a me k'arfi tsakaninsu ko Dan kamar da naga fuskarsu nayi ,haka nasamu nashige gida jikina duk babu k'wari .
A tsakar gida na iske Babangida yana gyaran faratansa da reza,ina shigowa ya d'ago kansa ya dubeni da fad'in "wlcm sis " na shiga kitchen ina ajiye flask d'in hannuna da ledan nonon inacewa "yawwa d'an uwa ,Baba fa yace in fad'amaka bayan la'asar kaje akwai kayan da zaka tayashi d'aukowa ,Babangida yace " OK ,wanka ma nakeson nayi toilet d'in d'akinmu kuma ba'a wanke yakeba ,inason shiga na tsakar gida kuma Usman yashiga yayi zamansa saikace me sanja fata, yaja d'an k'aramin tsaki .....mts....
Nace "kamar bakasan autan Umma da jimawa a band'aki ba ,inyashiga ai kamar yashiga d'aki ,niban San dad'ewar ta meye ba wallahi ", ta sauya maganar da cewa ina Umma ne da sisina naji gidan tsit ............!?
Baban gida yace “
Umma bacci yad’an kwasheta a d’akinta ,ita kuma sisinki gatacan tana guga a d’akinku tasaka earpice a kunnenta tanajin wak’ane shiyasa bataji shigowar kiba .
Har zan wuce saiga Usman yafito daga toilet d'in ,jikinsa babu alamar wanka yayi Dan babu d'igon ruwa a jikinsa,muka bishi da kallo yana wani sunk'e kai ,Babangida kecemasa " kai wai duk dad'ewarka daman ba wanka kayi ba .......!?to me kakeyi a cikin bayi kai kuwa ........!?
“AL GA’ID’U nayi” cewar Usman yana shek’a dariya .
“Babangida yazaro ido yana b’ata fuska yace ” subhanallahi…. ka kashe band’akin Usman ,wallahi bazan iya shiga ba sai ya huce ,kai duk gidannan babu Wanda ya kaika cika Masai , ga tutu d’in naka da mugun wari wallahi ,Baba dai ya shirya sokawe d’insa yakusa cika “ya k’arasa zancen da to she hancinsa .
Dariya Usman ya kwashe da ita sannan ya fito da halshensa yanawa Babangida gwalo ,aikuwa Babangida ya shak’a yamik’e a sukwane ya yarda rezar hannunsa yayi kan Usman zai damk’eshi ,kuma nasan Mintsininsa zaiyi ,Dan Babangida kaman jikan barebari yake gun mintsini ,ga mintsininsa da azabar zafi .
K’iftawa autan Umma ido nayi alamar ya gudu ,aikuwa ya falla yayi waje da gudu ,Babangida ya rufa masa baya yana fad’in ” shakiyyi ka tsaya mana …..wallahi wallahi nasamu k’eyarka sai namaka mintsinin da sai Umma ta gasamaka gurin” sukayi waje da gudunsu kamar wasu yara …..
Nidai dariya dramar tasu take bani ,saboda idan Usman da Babangida suka had'u sai Allah ,sun iya yankar junansu ,nashige d'akinmu ina faman dariya .
Na samu sisina taci k’arfin gugar har takusa kammala was,ina shiga nafad’a kan katifarmu ina sauke numfashi ,waiwayowa tayi tana dubana ,sannan tacire earpice d’in kunnenta tare da kashe socket d’in gugar,ta matsar da iron d’in gefe ,a hankali ta taso zuwa gareni ta zauna gefen katifar ,sannan tasaka hannayenta masu tashi ta d’agoni daga kwancen zuwa zama daram .
Sosai tasa idanunta a cikin nawa sannan tace min “menene…..?
” babu komai sisina “nace ina k’ok’arin kawar da idanuna….
Tak'i bani damar hakan takuma k'ank'ame hannuna tace " baki saba k'arya ba ,yanzu da kikayi sai naga batayi miki kyauba Sam.....ajikina naji akwai abinda yafaru dake .....kuma yanayinki ma ya nunamin hakan .....ko kin manta da cewar zuciyarmu d'aya ce....... So nakeyi nasan menene yafaru a fitarki ...…?menene dalilin dad'ewarki haka ........!?ko kin tsaya yin hira da Baba ne .......?
Narasa me zance mata ,bana b'oyewa sisina komai nawa ,kamar yadda muka zamo sirrin junanmu ,Wanda wani abin ma ko iyayenmu basu saniba tsakaninmu ,sai dai Hamma sulaiman shima nakan gayamasa wani Abu daya shafeni ,saboda mutumne me zurfinciki da bada shawara tagari ,inkayi magana dashi badai kajita a bakin waniba.
Idanuna suka ciko da k’walla nasamu kaina da karyewar zuciya ,cikin sanyin murya bakina ya sub’uce da fad’in “sageer ne sisina “
Ta k’ank’ance idanu tana dubana tace “sageer kuma …..?wanene haka …..?
” me shan sigari ….Wanda kikayiwa fad’a jiya da muka dawo daga islamiyya fa ……!nace ina kwantar da kai na a kafad’arta .
Cikin second biyu naji ta tureni daga kafad’arta tamik’e a gigice tana zaro idanu kamar zasu fad’o k’asa ,cikin bala’i take duba jikina tana fad’in “me yayi miki yau d’in……!?kuma tab’amin ke yayi …….!?baiji gargad’in da nayimasa ba wato …..?na rantse da Allah wannan mutumin bai sanni bane saina Nuna masa kalata …….bari naje na sameshi zai San yashigo gonar HUSSAINA …..
Ta sakeni tana k’ok’arin rarumar hijab ta sanya domin ta fita.
A gigice na mik’e na rik’eta GAM ,cikin fitar hayyaci nace mata ” babu abinda yayimin fa sisina….wallahi bai min komai ba …….kawai dai tun jiyan yakasa barin zuciya ta ne …….tausayin sa nakeji sisina …….idan na rufe ido Hoton fuskarsa kurum nake gani sisina ……jin sa nake yana zagaya zuciyana tamkar wani jinina …….bansan meyasa hakan ba …..bansan dalilin hakan ba …..sisina meyake faruwa dani hakane …..!?