HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ba shiri Hamma sulaiman ya sunkuceta yayi mota da ita ,haka Babangida da Aminu suka saka Hussaina a mota ,mutum biyu suka d’auko Hamma sageer shima aka sashi ,Allah ne kad’ai ya kaisu asibitin nan lafiya saboda mugun gudun da suka yi .

Federal teaching hospital Gombe (F T H )babban asibitin garin nan Hamma ya nufa ya kaisu ,nan da nan aka karb’esu a emergency likitoci suka fara aiki a kansu da hanzari .

Hamma Aminu da Babangida idanuwansu har sun kumbura saboda kuka ,shikuwa Hamma sulaiman yakasa kukan ,hawayen yak’i zubowa saidai kukan zuci Wanda yafi na fili ciwo yakeyi ,banda sintiri babu abinda yakeyi yakasa zama ,Babangida ne yataso ya rik’eshi ,fuska duk hawaye yace “Hamma sulaiman akirawo Baba da Umma a fad’a musu abinda yake faruwa ” sai Hamma sulaiman da idanunsa sukayi jajir ya d’ago kansa yadubi Babangida yace “banason hankalinsu yatashi ne …mud’an bari muga abinda hali zaiyi ko ….!?Hamma Aminu yataso ya dafa kafad’ar sulaiman ,yad’an share hawayen fuskarsa yace ” yakamata a sanar dasu Hamma ,b’oye musun bashida wani amfani …”Hamma yabi Aminu da ido kamar zautacce ,saboda gabad’aya kansa ya d’auki zafi yace “bazan iya kiran Baba ko Umma a wannan yanayin ba ….Aminu ina tsoran kar wani Abu yafaru ga iyayen mu ” Hawaye ya kuma b’allewa Aminu da Babangida ,cikin hawaye Aminun yace “babu abinda zai faru da yardar Allah ,fatanmu Allah yatashi kafad’unsu ,bari naje gidan na d’auko Umma da Baban kawai “

Aminu ya juya ya tafi, shikuma Babangida yaja hannun Hamma suka zauna kan kujerun dake reception d’in gurin ,Babangida yad’ora kansa kan kafad’ar Hamma sulaiman yanata zubda hawaye ,yayinda Hamma sulaiman ya runtse idanu yana ambaton Allah a zuciyarsa ,zuciyar tasa cikeda matsanancin tsoro.

Awa d’aya bayan haka saiga asibitin ya cika sosai ,y’an uwa da abokan arzik’i kowa ya zazzo tsakanin dangin su Hassana da na Hamma sageer ,cikin k’alilan d’in lokaci labarin had’arin ya baza ko ina ,Hamma Aminu da kansa ya d’auko Baba da Umma zuwa asibitin ,kowa cikin tashin hankali wasu na kuka wasu na tagumi .

   Ya Abdurrahman kuwa daman tun a safiyar ranar yake fama da yawan fad'uwar gaba da zazzab'i shima ,jikinsa ne yake bashi wani mummunan Abu zai faru ,shiyasa yake kwance a d'akinsa yakasa fita ko ina, Y'ar wayar ma da yakewa Hussaina ranar kwata kwata ya kasayi mata ,hannunsa yayi masa nauyi wajen danna wayar kanta ,birgima kawai yakeyi daga hagu zuwa dama akan bed d'in sa.wayar da ya safwan yayiwa mummy Aisha itace tasa mummyn cikin tashin hankali da dabarbarcewa ,da gudu ta nufi d'akin Abdurrahman ta banka k'ofar tashiga a gigice ,ganin tashigo a wannan yanayin yasa Abdurrahman ya mik'e zaune yana zare ido ,k'irjinsa na tsananin bugawa yace "lafiya mummy ....!?me yafaru ..!?hannunsa ta fincika da fad'in " taso Abdul ba lokacin magana bane yanzu ....subhanallahi ...Abdul maza ka kaimu  Babban asibiti akwai matsala "duk yadda yaso tayi masa bayani kasawa tayi sai hawaye take zubarwa masu tsananin zafi ,tunani iri iri ya dingayi har sukaje asibitin mummy na kuka ,shima jikinsa banda rawa babu abinda yakeyi ,tuk'inma da k'yar yakeyi .

Suna shiga reception d’in yaga danginsa dank’am duk agurin ,wasu na kuka wasu na addu’o’i cikin gigicewa ,da sauri mummy ta nufi Umma dake zaune da carbi a hannunta ta rungumeta tana hawaye tace” Umma yau kuma da abunda muka tashi a zuri’ar mu kenan …hasbunallahu wani’imal wakeel ….inna lillahi wa inna ilaihir raji’un”ta kuma fashewa da matsanancin kuka ,Umma ta share hawayen fuskarta tace “toh yazamuyi Aisha ?k’addara tariga fata…..sai dai kawai muyi addu’a Allah ya tak’aita wahala “

Muryar ya Abdurrahman ta karad’e gurin ,cikin gigita yake tambayar abinda yake faruwa ,ganin hawaye a idanuwan mutane ,ga mamma da Aunty Nafeesa suma sai kuka sukeyi ,Babangida yataso da gudu yafad’a k’irjin Abdurrahman yana gurshek’en kuka ,ya rik’eshi a jikinsa yana tambayarsa menene ya faru …!?cikin kukan Babangida ke cewa “Ya Abdurrahman Hamma sageer da sisters twins sunyi had’ari ….” Maganar tadaki kunnen Abdurrahman, da k’arfi ya hau girgiza Babangida yana fad’in “me kake fad’ane Babangida ….!?wace irin magana kakeyi ….!?sai kuma yasaki Babangidan ya nufi Baba da ke zaune ya rafka tagumi ,ya tsuguna gabansa Yakama hannayen Baban ya rik’e jiki na rawa idanu na jujjuyewa yace ” Baba kaji abinda Babangida ke cewa kuwa ….!?Baba k’arya yakeyi ko ….!?Baba ya maida hawayen sa dake k’ok’arin b’ullowa yace “kayi hak’uri Abdurrahmanu ,babu yadda zamuyi da k’addara ,y’an uwanka da abokinka suna cikin wani hali kayi musu addu’a ” kawai sai ganin Abdurrahman sukayi ya fad’i daga tsugunen ya sume.

Guri ya k’ara rincab’ewa da koke koke, da k’yar akasamu ya farfad’o ,yana dawowa hayyacinsa shima ya dira nasa kukan ,ya dage yanason ganinsu atemakeshi a nuna masa su ,likitoci sukace aikinsu sukeyi a jirasu ,kasancewar Hamma sageer da Hussaina sun zubda jini da yawa sai akace za’ayi musu k’arin jini, akaje aka gwada aka samu na Hamma sulaiman da ya Abdurrahman da ya safwan yayi dai dai ,sai aka d’ibi nasu aka jona musu ,sannan aka yimusu treatment d’in raunukan jikinsu ,Hamma sageer harda karaya a hannunsa na hagu ,shiyasa aka d’aure hannun.

Har dare Hussaina da Hamma sageer basu dawo hayyacin su ba ,sai Hassana ce kawai tadawo hayyacinta ,ta farka da ambaton Allah a bakinta sannan tafara kiran sisinta da Hamma sageer d’inta .

D’akin da aka saka Hassana aciki aka saka Hussaina ,kowa gadonsa daban ,yayinda d’akin Hamma sulaiman ya kasance daban da nasu tunda shi namiji ne ,d’akin Umma da Baba ne kawai aciki ,suma d’in da k’yar doctor yabarsu suka shiga ,ragowar jama’ar duk suna waje.

Umma da Baba sukayi kan Hassana da ta farka a sukwane ,da k’yar take iya bud’e idanunta tana duban mahaifanta dake gabanta sai jera mata sannu sukeyi ,ta mik’o hannunta tanaso su kama ,da hanzarinsu duk suka kama hannayenta suka rik’e ,ta bud’e baki a hankali tace “Ummana ,Babana” Umma takasa magana saboda tsananin tausayin y’arta ,sai Baba ne yayi k’arfin halin amsawa yace “sannu Hassana ,Allah yabaku lafiya ” maganar Baba tasa tatuna cewar dasu Hamma sukayi had’arin ,tayi k’ok’arin mik’ewa zaune amma takasa saboda yadda k’afafuwanta da cikinta suke mata azabar zafi da rad’ad’i ,Baba yayi saurin kamata yana cewa “menene Hassana …!?wani Abu kikeso …!?ta runtse idanu hawaye ya samu nasarar fitowa tace” Baba na Y’ar uwata da Hamma sageer ,suna ina…!? Sai Umma tad’an matsa tana nuna mata Hussaina tace “kin ganta can tana barci ,shima sageer d’in yana cikin k’oshin lafiya ki kwantar da hankalinki kinji ” ta d’agawa Umma kai ,sai takuma kamo hannun Baban ta d’ora akan cikinta tace “Babana kayimin addu’a ….cikina ke ciwo sosai kaji ” sai kuma ta kalli Umma tace “Umma sai nakejin kamar bazan kuma takawa ba ,k’afafuwana kamar ba’a jikina suke ba ” Umma ta share hawayen da ya zubo mata tace “da yardar Allah zaki k’ara takawa Hassana ,zafin ciwo ne kawai zaki warke kinji ” tayiwa Umma wani irin murmushi ta rufe idanunta kamar me bacci ,Umma da Baba suna tayi mata addu’a ,sai bayan minti biyu takuma bud’e idanunta ta kalli Umma tace “ummana d’azu jini yanata zuba ajikin sisina da Hamma sageer ,amma nakasa tashi na taimaka musu ” Umma tafashe da kuka tarasa me zatace ,sai Baba ne yadubi Umma yace “Don Allah kidena kukan nan haka kinji …addu’a itace mafita ba kuka ba ” sai Hassana tace “Baba haka Babangida ma yayita kuka fa ,kace musu sudena kuka Dan Allah ” Umma tayi shiru tadena kukan sai Baba ya Shafa kan Hassana yace “zan gaya musu kowa yadena kuka ,rufe idanunki kiyi bacci ki huta ” sai tayi murmushi tace “bazan iya bacci ba Babana ,da k’afata zata iya takawa da natashi nayi alwala nayi sallah ,na rok’awa Hamma sageer da sisina lafiya ,tunda ni tuni nasamu sauk’i ” Baba ya k’ura mata ido jin tace tasamu sauk’i ,yana sak’a abubuwa da yawa a zuciyarsa ,hawaye yaji ya ciko idanunsa amma yayi hanzarin mayar dasu.

Sai dare sosai doctor yabada damar shiga d’akin ,lokacin Hussaina itama ta farka ,sai dai babu wani rad’ad’in ciwo atare da ita sai kanta dake sarawa kamar yacire ,ga bandeji an nannad’e mata kanta zuwa goshinta inda ya fashe ,kuma tunda ta farka Hassana ce a bakinta tana ambatar sunanta har saida aka nuna mata Hassanar, duk da haka k’in zama tayi a gadonta ta d’awo gadon Hassana ta rungumeta tana duba jikin Hassanar da fad’in “Allah yasa dai bakiji ciwo ba rabin raina….” Hassana tayi murmushi tana kallon ahalinta da suka cika d’akin ,ta d’ago hannunta tana Shafa goshin Hussaina tace”sannu sisina ,da inada dama da nacire ciwukan jikinki sun koma jikina ….wal….”tari ya tasomata sosai ta kasa k’arasa maganar ,sai hannu tad’agawa Hamma sulaiman alamar yazo kusa da ita ,da hanzari yamatso gareta ,tarin ya tsagaita da k’yar tace “Hamma sulaiman inason insha ruwa ,amma kuma bazan iya shaba ” yarik’e hannunta yace “saboda me …!?bata bashi amsa ba takuma cewa ” ina Ya Abdurrahman??Abdurrahman dake gefe ya matso kusada Hussaina yana cewa “ganinan rabin ranmu ,sannu ,Allah yabaku lafiya ” tayi murmushi tana kallon Hussaina da Abdurrahman d’in tace “kayi hak’uri ya Abdurrahman ” yace “hak’uri kuma …!?hak’urin me zanyi ….!?sai bata bashi amsa ba ta kuma juyawa ta kalli Hamma sulaiman tace” na rok’eka Hamma sulaiman Ku kaini naga Hamma sageer ,ko kuma Ku kawomin shi naga lafiyarsa “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button