HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tana rufe baki k'ofar d'akin ta bud'e ,saiga Hamma sageer ya shigo yana takawa a hankali ,hannunsa da ya karye a d'aure ,yayi wata irin zurmawa kamar bashi ba ,bayansa Mamma da Aunty Nafeesa ne da Hamma Aminu da Baba ,daman suna can d'akin da yake, kuma tun bayan farkawarsa shima yake nacin akawoshi yaga sweetynsa ,har kuka yayi ,shine doctor yabada damar akawoshi ya ganta d'in .
Shigowarsa yayi dai dai da d’agowar Hussaina ,zumbur ta mik’e ta nufeshi yana takowa tana nufarsa ,tana zuwa dab dashi kawai tasa hannu ta damk’i kwalar rigarsa ta cukume ,cikin masifa take zazzaro masa idanu tana jijjiga k’irjinsa tace “nanma kabiyo mune ka k’arasa mu …!?toh ta Allah ba takaba azzalumi ,kaje kayi shaye shayenka yagaya maka k’arya shine ka kwashemu a mota zaka kashe muko …!?gurin yayi tsit anrasa me magana kowa ya zuba musu ido yana kallonsu ,Baba yanaso yayi magana amma kamar and’aure masa baki ,sai shi Hamma sageer d’inne yakemata wani irin kallo idanunsa a juye da tsantsar b’acin rai ,cikin wata shak’ak’k’iyar murya yace” sakeni ,sakar min wuya …”yana kallon hannayenta da taci kwalarsa dasu,itama cikin b’acin ran da hargowar fita daga hayyaci tace “bazan sake kaba …dole kafita daga d’akin nan bazaka k’arasa gareta ba “
Da k’arfi sukaji Hamma sulaiman ya ambaci “innalillahi wa inna ilaihir raji’un ” hakan tasa suka waiwaya dukansu ,ganinsa sukayi rik’eda Hassana idanunta na k’ok’arin k’ak’k’afewa sai mik’owa Hamma sageer da Hussaina hannu takeyi .
Wata irin bangaza sageer yayiwa Hussaina ya fincike wuyansa a hannunta ,yanufi Hassana a gigice ,yayinda Hussaina tarufa masa baya da gudu itama ,suka fara turereniya itada sageer kowa na yunk’urin fara isa ga Hassana ……….
Comments
Share
Vote
Pls
HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍
TYPING????
???????? HASSANA ????????
*DA*
❣???? HUSSAINA ????❣
TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍
page4⃣3⃣to4⃣4⃣
WATTPAD:hassana3329
® PEN : WRITERS ASSOCIATION
~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~
TUNASARWA????
TAFIYA TA DIN DIN DIN
K’ABARI SHINE MATAKIN FARKO DAGA CIKIN MATAKAN LAHIRA,RAMI NE DAGA CIKIN RAMUKAN WUTA DANGANE DA KAFIRI DA MUNAFUKI ,AMMA DANGANE DA MUMINI,DAUSAYI NE NA ALJANNA,KUMA AN RAWAITO CEWA ,ANAYIN AZABA ACIKINSA SAKAMAKON WASU LAIFUKA ,DAGA CIKINSU AKWAI:
RASHIN TSARKAKA YAYIN FITSARI
YAD’A ANNAMIMANCI
BARIN SALLAH SABODA BARCI DA GANGAN
K’AURACEWA ALK’UR’ANI
ZINA DA LUWAD’I
DA SAURANSU .
KUMA DAGA CIKIN ABUBUWAN DA SUKE TSERARWA DAGA AZABAR K’ABARI AKWAI:
KYAWAWAN AYYUKA DA AKAYISU SABODA ALLAH
NEMAN TSARI DAGA AZABAR K’ABARI
KARANTA SURATUL MULK
DA SAURANSU.
DAGA CIKIN WAD’ANDA AKE KARESU DAGA AZABAR K’ABARI AKWAI:
SHAHIDI
WANDA YA MUTU WAJEN D’AUKAKA KALMAR ALLAH
MUMININ DA YARASU RANAR JUMA’A
WANDA CIWON CIKI YAYI SANADIN MUTUWARSA
DA SAURANSU.
AIKI ME FALALA????
MANZON ALLAH (S A W )YACE “DUK WANDA YA HALARCI JANA’IZA HAR AKAYI MATA SALLAH ,TO YANADA LADA KAMAR (KIRADI)D’AYA ,KUMA DUK WANDA YA HALARCETA HAR AKA BINNETA YANADA LADA KAMAR (KIRADI )BIYU,SAI AKACE :KAMAR YAYA KIRADI BIYU YAKE?SAI MANZON ALLAH (S A W)YACE” MISALIN DUWATSU GUDA BIYU MANYA MANYA.(ABDULLAHI D’AN UMAR )YACE”LALLAI MUNYI SAKACI DA (KIRADODI )DA YAWA
????????????????????????????
***Suka isa gareta a tare kowa na k’ok’arin rik’eta ,wani mugun kallo Hamma sulaiman yabita dashi ya daka mata wata muguwar tsawa yace “matsa daga nan kafin na tattaka ki wallahi ” nan da nan tafashe da wani irin kuka takasa matsawa daga gurin illah rik’e hannun Hassana da tayi tsam ,Hamma sageer kuwa yana isa ya zube a gaban gadon ya d’ora kansa gefen cinyar Hassana yana wata irin ajiyar zuciya hawaye na malala akan fuskarsa ,yanajin zuciyarsa tamkar tafaso k’irjinsa tafito .
Tarin ya tsagaitawa Hassana ,idanuwanta har sun birkice saboda tsananin wahala amma haka tasa hannu ta kamo Hussaina ta kwantar da kan Hussainan akan k’irjinta daga gefe ,abinda bata tab’ayi ba shi tayi ,wato tasaka hannunta akan kan Hamma sageer tana k’ok’arin d’agoshi ,yana d’agowa taga yadda yake kuka saita girgiza masa kai tayi murmushi me ciwo tana kallon karyayyen hannunsa ,muryarta da rauni tace “nasan da kaida sisina zakufi kowa kokawa a y’an kwanakin nan ,gashi nikuma babu abinda banason gani irin hawayenku ,akwai babban al’amari da zai riskeku Wanda Allah ya kimsamin shi a zuciya ta ,Allah yasani bana ganin laifinku abisa k’in da kukewa juna ,sai dai kuma banida burin da yawuce a duniya yau naganku kundena k’in juna ,tun randa mukafara ganinka da sisina bantab’a d’ora goshina ak’asa ba face sainayi addu’ar Allah ya daidata tsakaninku cikin aminci ” ta D’an numfasa yayinda duk mutanen d’akin suke zubda hawaye kowa jikinsa yayi sanyi ,takuma yunk’urawa tana son tashi, Hussaina ta d’agamata k’irji tanata kuka ,Hamma sulaiman da kansa ke masifar juyawa ya gyara mata zama ajikinsa ,saita kalli Hamma sulaiman tayi murmushi tanajin cikinta na azabar ciwo tace “D’an uwana in baka wata Amana…!? Yabita da idanuwa ya kasa magana ,gabad’aya Hamma sulaiman baya cikin hayyacinsa har wata rama yayi a ranar ,sai ta kamo hannun Hussaina da Hamma sageer ta had’a ta dank’asu a hannun Hamma sulaiman tace ” Na amince dakai Hamma sulaiman ,shiyasa zan baka wannan amanar ,wad’annan mutanen ina sonsu fiyeda rayuwata ,don Allah Hamma sulaiman ka kula min dasu aduk lokacin da bana tare da su ,ko idan nayi wata tafiya me nisa ,kar ka barsu suyi kuka ,kar ka barsu susha wahala ,karka kuma dukan sisina ,idan tayi laifi kayi mata Nasiha ,sannan ka kula min da tarbiyyar Hamma sageer ,aduk lokacin da akaga zai kauce hanya adawo dashi dai dai… kar a hantareshi… kar a k’yamaceshi ,akula dashi kamar yadda za’a kula da k’aramin yaro ,inason Hamma sageer sosai ,amma Allah shi yabarwa kansa sanin ya zaiyi da Hamma sageer da sisina,na rok’eka Hamma sulaiman ka rik’emin amanata ,wad’annan mutanen sune amanata agareka .
Kasa jure maganganunta Hamma sulaiman yayi, shiyasa ya saketa yatashi da hanzari yabar d’akin yana had’a hanya kamar zai fad’i.
Kukan da Hussaina da sageer keyi yafara yawa ,don Hussaina har shid’ewa takeyi kamar zata suma ,yayinda Hamma sageer ya mik’e ya zauna gefen Hassana yana zubda hawaye ya d’ago hannunsa da niyyar tab’ata tayi saurin kama hannun tace “karka fama hannunka Hamma sageer ,ina fatan Allah yabaka lafiya ” kawai sai yajata jikinsa ya rungumeta k’ak’am ko zafin hannunsa bayaji ,yayinda hawayensa ke tsananin zuba yana sauka a dokin wuyan Hassana zuwa bayanta .
Wannan rana dai ilahirin wannan dangin da ahalin sunga tashin hankali ,har wajen sha biyu nadare mutane dank’am a asibitin nan kamar me ,saida Baba ya tsawatar yace kowa yatafi gida babu abinda zaifaru sai abinda Allah ya k’addara ,sannan kowa yatafi ba da son rai ba ,Hamma sulaiman ya d’auki sakeena wadda sukazo daga baya itada sadiyar Aminu da Zahra ,irin kukan da Zahra tayi kuwa yanada yawa itada Asma’u da itama tazo ,Hamma Aminu ma ya d’auki Umma dasu Babangida da safwan da Usman ya maidasu gida bisa umarnin Baba ,za’a bar Adda Nabeela da mummy Aisha su kwana anan ,yaran Nabeela ma sai gidan Umma aka wuce dasu.
Hamma sageer da Hussaina na nanuk’e da Hassana ,ko Yaya ta motsa zasu fara tambayar ta me takeso ,ko ta Kansu da ciwon jikinsu basayi kwata kwata ,kusan a d’akin Hamma sageer ya kwana Dan yak’i komawa d’akinsa ,ko doctor da zai dubashi sai gadon Hussaina ya hau ,ana gama dubashi ya sauko yadawo gurin Hassana ,doctor dukansu yayi musu allurar barci Dan su samu hutun jikinsu.
Hamma sageer zaune kan gadon ya d’ora kan Hassana a cinyarsa yana Shafa kanta ,yayinda kan Hussaina ke k’irjin Hassana a kwance itama ,idan ka gansu a wannan yanayin dole subaka tausayi sosai ka zubar da hawaye .