HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da k’arfi Allah ya bud’i bakinta ta ambaci sunan da ba ta tab’a ambata ba sai a ranar,da iyakacin k’arfinta ta bud’e murya tace “Hamma Sageeerrrrr ” gaba d’aya jama’ar wajen hankalinsu yayo kanta …bata kula da yadda ake kallonta ba inda taruga da mugun gudu tayi kansa, shima d’agowa yayi daga jikin Abdurrahman yana kallon yadda take gudu zuwa gareshi ,tana isa takama shi tana jijjigashi idanunta a warwaje ,Nuna masa makarar take tana cewa “Hamma sageer kaga zasu d’aukemaka sweetyn ka ,Hamma sageer kaga zasu tafi da rabin raina ,kar ka barsu su d’auke mana Hassanar mu , kaje ka karb’o mana ita, dansu mak’aryata ne sukace wai Hassanarmu ta mutu ,Hamma sageer nasan sweetyn ka bazata tafi ta barmu ba ko ….tana k’aunar mu nida kai …kullum fa sai tagayamin cewa tana sonka….har kuka takefa idan tana tunaninka tsabar son da takemaka…Dan Allah ka karb’i sweetyn ka karsu rabamu da ita” surutai kala kala ta dingayi tana girgiza sageer da hannayenta ,hannunta akan karayarsa tana jijjigawa amma sageer bayajin zafin gurin tsabar masifa da tashin hankali ,Hussaina takuma tayarda hankalinsa saura kad’an yafita a hankalinsa ,idanunsa na kanta yana kallonta yana had’iyar wani Abu me tsananin d’aci a mak’ogoronsa.
Hamma sulaiman ne yazagayo ta bayanta ya rik’e hannayenta yace “sakeshi ,kinga hannunsa akwai ciwo
Kiyi hak’uri ” jin muryar Hamma sulaiman yasa tasaki sageer ta waiwayo ,sai tarik’eshi tace “yawwa Hamma sulaiman kazo !?kaga wad’ancan mutanen sun d’auke mana Hassanar mu zasu tafi da ita ….karb’o mana ita kaji Hamma” hawaye masu zafi suka zubo masa ya girgiza hannunta yace “kiyi hak’uri ta rasu ne,za ‘a kaita gidanta na gaskiya ne ” tace “Ku had’amu Ku kaimu tare Hamma,bazan iya zama ba tare da ita ba ” ya kuma girgiza kansa ya rungumeta ,cikin hawaye yace “ba’ayin haka ,kiyi hak’uri ” wata irin shak’uwar tashin hankali tafara tana wani k’andarewa a jikin Hamma sulaiman kafin daga k’arshe ta sume a jikinsa ……
Kowa kukan tausayin Hussaina da sageer yakeyi a gurin,haka Hamma sulaiman ya kirawo Aminu yabashi Hussaina ya shigar da ita gida ,tamkar jaririya haka Aminu ya d’auki Hussaina yashige da ita yana kuka .
Abdurrahman kuwa kukan da yayi ba zai misaltu ba ,idanunsa sunyi jajor sun koma ciki.
Haka zugar mutane suka sallaci gawar Hassana bayan an idar da sallar juma’a ,daga nan aka rakata gidanta na gaskiya aka hak’a k’abari aka binneta ,Akayi addu’o’i mutane suka fara watsewa ,sai ahalinta da Hamma sageer dake tsugune akan kabarin sunata zabga addu’a kamar bazasu tashi ba ,kallon k’abarin kawai sageer keyi ,ya tuna Cewar shikenan sweetynsa tatafi ,bazai k’ara ganinta ko jin daddad’ar muryarta ba,wani gagarumin tashin hankali yadaki zuciyarsa ,take yakuma fad’uwa sumamme acikin mak’abartar ………????.
wani mawak’i yana cewa????
Dubi ayar k’ur’ani
Kullu nafsin tai bayani
Za’ik’atul mautu aini
Babu Wanda bazai mace ba.
Aina ma kuntum kugane
Yudri kumul mautu kune
Ai walau kuntum mutane
Fi burujin can gabanne
Y’an uwa ban k’arasa ba
Ma’ana Allahu yace
Zatazo muku karku mance
Mutuwa Allah sa mudace
Kan tazo mana duk mutuba.
kad’an daga baitocin kenan????Allah yasa mucika da imani ,Allah ya kyautata k’arshenmu????
Comments
Share
Vote
Pls
HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍
TYPING????
???????? HASSANA ????????
*DA*
❣???? HUSSAINA ????❣
TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍
page4⃣7⃣to4⃣8⃣
WATTPAD:hassana3329
® PEN : WRITERS ASSOCIATION
~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~
TUNASARWA????
AUNA AYYUKA
ZA’A AUNA AYYUKAN HALITTU DOMIN AYIMUSU SAKAMAKO A KAI ,DA MA’AUNI NA HAK’IK’A SIRIRI MAI TAFUKA GUDA BIYU ,KYAWAWAN AYYUKA DA AKAYISU DA IKLASI SUNE SUKE CIKA,,DAGA CIKINSU AKWAI :FAD’IN LA’ILAHA ILALLAH ,DA KYAWAWAN HALAYE ,DA ZIKIRI KAMAR FAD’IN ALHAMDULILLAH ,DA FAD’IN SUBHANALLAHIL AZEEM ,KUMA ZA’A BIYA BASHIN MUTANE DA AYYUKA KYAWAWA DA MUNANA
AIKI ME FALALA????
MANZON ALLAH (S A W ) YACE “LALLAI KAI BAZAKA TAB’A BARIN WANI ABU BA DOMIN TSORON ALLAH ,MAI GIRMA DA D’AUKAKA ,FACE ALLAH TA’ALA YABAKA MAFI ALKAIRI DAGA GARESHI
***Haka aka d’auko Hamma sageer zuwa gida a sume , a wannan ranar Hamma sageer da Hussaina haka suka dinga suma kamar ba zasuyi raiba ,tamkar suma zasu mace …..saida Baba yasa aka d’auko likita yayi musu allurar bacci tukun ….allurar batayi wani tasiri ba sosai ta sakesu aka koma Y’ar gidan jiya .
Tashin hankali dai wannan dangi sun ganshi, mutuwa tayi musu babban dukan da ya kusa zautar dasu, hawaye idan da yana k'arewa da na wannan ahalin yak'are saboda tsananin zuba ,zuciyarsu zafi takeyi ,ruhinsu yana kewar Hassana ,idanuwansu na mararin sake ganinta sai dai babu dama, Hassana ta tafi inda ba 'a dawowa ,ta tafi inda idanuwa bazasu sake ganinta ba ....sai dai zuciya tayi tunaninta .
Malam Huzaifa da y’an Makaranta sunyi kukan rashin Hassana ,har gidan sukazo suka sauke mata karatun alk’ur’ani sunayi suna hawaye ,sukayi adduo’i masu yawa zuciyoyinsu na tuna musu alak’arsu da Hassana ta zaman lafiya da faran faran ga jama’a ,Malam Huzaifa ya tuna randa tazo har office tabashi hak’uri tana kuka ,wannan shine ganinsa na k’arshe da ita, yagodewa Allah abisa rashin d’aukar fushi da baiyi ba a sanda ya rasata ,ashema Hassanar ba mazauniya bace ….Ashe dashi da sageer d’in duk bazasu sameta ba.
Hussaina da Hamma sageer ba sa ci basa Sha ,sunyi wata irin rama Mara misali …..zuciyoyinsu kullum cikin tsananin kewa da ciwo ,Hamma sulaiman ne yake sakasu a gaba akan suci abinci amma suk’ici suyita kuka ,ya kance “kuyi hak’uri kuci …Ku taimakeni in sauke nauyin amanar da marigayiya ta barmin akanku ….tacemin nakula daku ,nakula da rayuwarku ….kunada matsayi mafi girma a zuciyarta “haka zaita fama da k’yar yake samu suci kad’an suna kuka ,wani zubin sai Baba yasa baki sannan ,Hamma sulaiman yana matuk’ar daure zuciyarsa bayayin kuka ,amma shi kad’ai yasan dukan da mutuwar nan tayi masa ,sai dare sannan yake nasa kukan alokacin da zai samu rarrashin sakeenan sa .
Gidan kullum acike da mutane masu zuwa ta’aziyya ,y’an d’aurin aure dai sun zama y’an zaman makoki ,har zuwa ran litinin da ta kasance ranar sadakar ukun Hassana ,wadda shahada da tsananin yabon da tasamu agun mutane ake ganin tagama dacewa da rahamar ubangiji ,Hussaina ba um ba um um sai tsananin kuka ,surutanta basa tashi sai dare intazo kwanciya duk da ba samun baccin takeba ,musamman in ta laluba gunda Hassana take kwanciya kusada ita taji babu ita nan da nan zata fashe da kuka tafara fad’in” mun rayu acikin cikin ummanmu tare ….munfara zumunci da k’aunar juna tun acikin Umman mu ,Umma ta haifemu rana d’aya muna masu tsananin kama da juna,mun tashi tare ,komai namu tare ,in d’aya tayi cuta d’ayan ma sai tayi ,in d’aya tayi kuka d’ayar ma sai tayi ,in d’ayarmu tashiga damuwa ko farinciki d’ayarmu ma sai tayi ,muci abinci tare ,muyi wasa tare ,muyi bacci tare ,muje Makaranta tare ,rana d’aya muka fara koyon zama,rana d’aya muka fara rarrafe ,rana d’aya muka fara tafiya ,rana d’aya akasamu a Makaranta …..komai namu rana d’aya …amma meyasa ranar mutuwarmu ta kasance ba rana d’aya ba …!?nasaba dake Hassana na ….ina sonki ina k’aunarki …kin tafi kin barni cikin duniyar da babuke acikinta …don Allah Hassana ta kidawo gareni ….kidawo naci gaba da ganinki inajin dad’i “Adda Nabeela da ke kusada ita ta janyota hawaye nazuba a idanunta ta rungume Hussaina a k’irjinta tace” Allah baya barin wani Dan wani yaji dad’i ,kiyi hak’uri bazata dawoba tatafi kenan …kiyi mata addu’a shine soyayyarki gareta “hawayen Hussaina da majinarta na sauka a kafad’ar Adda Nabeela tace” idan ita bazata dawoba ni Ku kaini wajenta Adda,na yarda na amince zan zauna tare da ita ko babu numfashi a gareta muddin zan dinga ganinta kusa dani “Nabeela tace” kin tab’a ganin inda aka kai me rai cikin k’abari …!?tana wata irin shesshek’a tace “kufara a kaina Adda Nabeela …wallahi Ku kaini zan zauna da ita “