HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wannan Daren saida ahalin gidan suka had’u akan Hussaina anai mata addu’a saboda yadda ta firgice ta susuce gabad’aya ,Baba yadinga had’a mata da nasiha akan hak’uri da karb’ar jarrabawa daga Allah ,haka Hussaina tadinga bin cinyoyinsu tana kuka ,ta hau kan cinyar ya safwan tace “ya safwan kayita yimin Addu’a Allah yasa nabi Hassana ta na huta nima” takoma ta rungume Babangida tace “agabanka mota tayi silar mutuwar Hassana ta Babangida ,da kasani kacewa me motar yajira Hassana ta tafita inyaso ni yabigeni …gara ni namutu nabar Hassana ta ” Babangida ya rushe da kuka hawaye na malala cikin tsananin tashin hankali ,tasaki Babangida takoma gun ummansu ta kwanta kan cinyarta ,tasa hannunta tana sharewa Umma hawayen dake zuba tace “Umma kece kika haifemu nasan duk duniya kinfi kowa sanmu da k’aunarmu ,haka nasan duk duniya babu Wanda ya kaiki jin zafin mutuwar nan …amma kiyi hak’uri Umma ..kin kusa k’ara rasa wata d’iyar taki… Domin nasan nima bazan dad’e aduniya ba kewar Y’ar uwata zai halakani .

      Umma takuma fashewa da kuka, haka dukansu sukaita hawaye har Baba da yakasa magana, daga k'arshe Hussainan ce takoma rarrashinsu su dena kuka har tana cewa " kuyi shiru kudena kuka ,kunnuwana sunji Y'ar uwata nacewa batason kowa yayi kuka ????amma dai ko kowa zai daina kuka na tabbatar ni bazan daina kukan rashinta ba ,Baba akaini nayi alwala zanyi sallah intayiwa Hassana ta addu'a da nema mata Rahama"Adda Nabeela ce taraka ta toilet har wanka yayi mata da ruwa me zafi kasancewar tun ranar da Hassana ta rasu bata k'ara wanka ba ,bayan tai mata wankan saboda babu k'wari ajikinta sai ta d'aura alwala ,Adda Nabeela da kanta tayi mata brush sannan ta rik'ota suka fito ,Babangida ya d'auko mata doguwar Riga tasaka da zumbulelen hijabinta ,sallar ma kasayi a tsayetayi sai a zaune saboda yadda kanta ke Sarawa ga hajijiya na d'ibanta ,ta jima tana sallah me tsawo ...sannan ta idar ta d'auki alk'ur'ani tafara karatu tana kuka, bayan ta kammala karatun tafara addu'o'i hannayenta a sama idanunta na zubda hawaye masu tsananin k'una da zafi .....????

Kamar yadda Hussaina ke fama da tsananin kewar Hassanarta hakama Hamma Sageer ya kasance ,kullum bashida aiki sai kuka da yawan tunanin sweetyn sa, yayi wata irin ramewa saboda tashin hankali da rashin cin abinci ,Mamma tana iya yinta amma wataran itama dole take kukan tausayinsa …tasan Muhammad sageer d’inta yana son Hassana matuk’a ,amma batasan soyayyar takai hakaba saida aka rasata ,saboda yadawo tamkar mahaukaci ,ga tsananin surutai ko barci baya iyayi ,danma Ya Abdurrahman kullum yana tare dashi yana tausarsa da yimasa Nasiha ,Hamma sageer yakan kwanta jikin abokin nasa yana kuka yace “bazaka gane ciwon da zuciya ta takeba Abdul ….saboda kai kana tare da taka masoyiyar …nikuwa tawa tatafi ta barni Abdul …duk duniya kuma babu mai mayemin gurbinta a zuciya ta ” hawaye ya zubowa Abdurrahman yanajin rauni a zuciyarsa ….tausayin kansa yakamashi dalilin gingimemiyar sadaukarwar da yakeso yayi .

     Kwana biyar da rasuwar Hassana amma har lokacin mutuwar tak'i barinsu ,kullum sabuwa take agunsu ,Hussaina dai duk Wanda ya kalleta zai tausaya mata ....tazama shiru shiru bata magana sai kuka da addu'a ,musamman idan taga Abdurrahman haka zata shagwargwab'e ajikinsa taita kuka... Gashi yanzu bayason rab'arta ko kad'an saboda cika alk'awarin Hassana da zuciyarsa ,haka yake daurewa yaita rarrashinta ,idan yakoma gun Sageer ma haka zaita rarrashinsa ,sai dare Abdurrahman shima yakasa bacci sai kuka da k'uncin zuciya ,a wannan kwana biyar d'in Abdurrahman ba k'aramar rama yayi ba.


Ran alhamis da ta kasance kwana shida da rasuwar Hassana Abdurrahman yasamu Baba ya shaida masa cewa yanason a had'a taro da daddare kowa ya halarta ,akwai muhimmiyar maganar da yakeso yayi ,tunda Baba yaji haka jikinsa yayi sanyi ya tabbatar babban lamari zai taso kenan,haka Baba yasa aka sanarda kowa ,yanason ganin kowa bayan sallar isha'i a falonsa ...da yake falon Baba babbane sosai .



   Hakance ta kasance kuwa ,misalin k'arfe takwas da Rabi nadare falon Baba cike yakeda mutane kama daga kan shi kansa Baban ,Umma ,Adda Nabeela da Hussaina da take rungume jikin ta ,Hamma Sulaiman ,Hamma Aminu ,Ya safwan ,Babangida da Usman ,mummy Aisha da mijinta daddynsu Abdurrahman ,ga Mamma da Aunty Nafeesa ,Hamma Sageer da Ya Abdurrahman ne kawai basa cikin falon .



 Kimanin mintuna goma suka kwashe a zaune kafin suji sallamar ya Abdurrahman Wanda hannunsa ke rik'eda na Hamma Sageer ,idanunsa sanye da bak'in glass domin b'oye halinda idanunsa suke ciki....yana janye da 

Hannun Sageer har suka samu gurin zama suka zauna, tunda Hussaina tad’ago kanta ta kalli Hamma sageer batakuma marmarin kallonsa ba saboda muguwar lalacewar da taga yayi ,idanuwansa sun zurma ciki sai dogon hancinsa da yak’ara fitowa ,k’asusuwa rakwacam a wuyansa ..duk uwar ramar da tayi yafita ramewa ….”

    Baba ne yace "ayi salati goma ga annabi (S A W)duk suka amsa kowa yayi ,sannan Baba yabud'e taron da addu'a har ya kammala aka shafa,sai Baba yayi gyaran murya yace " abinda yasa muka had'u anan bawani Abu bane face Abdurrahman yasameni akan yanason muhad'u dukanmu akwai wani jawabi da zaiyi mana ,Dan haka Abdurrahmanu muna saurarenka gabad'ayan mu "kowa ya zubawa Abdurrahman idanu da mamakin jin menene dalilin dayasa ya had'asu a lokacin ...!?shin wane jawabi ne zaiyi da yasa ya tattarasu dukansu ....!?

Abdurrahman yak’ara gyara zamansa yana kuma damk’e hannun Sageer dake rik’e anasa hannun ,sannan yabud’e bakinsa a hankali cikin matuk’ar nutsuwa da sunkuyarda kai yace ” iyayena ,yayyena k’annena ,abokina kuma D’an uwana ,ina k’ara yimana ta’aziyyar babban rashin da yasamemu …Allah ubangiji yayi mata Rahama …mukuma Allah ya k’aramana hak’uri da juriyar rashinta ….Hassana batayi saurin tafiya ba …mukuma bamuyi jinkiri ba ,dukanmu zamuje Inda taje muma ,ranar zuwan da lokacin ne kawai bamu saniba ,sai dai muna addu’ar Allah yabamu kyakkyawar cikawa da tafiya cikin nasara da imani kamar yadda ya baiwa baiwarsa wato Hassana “ya d’anyi shiru yana sauke ajiyar zuciya yayinda duk suka amsa da Ameen sukacigaba da kallonsa da sauraronsa.

Yaci gaba da cewa ” babban abinda yasa nace inason mu had’u anan shine ,inason kowa da kowa ya shaida SADAUKARWAR DA NAKESO NAYI YAN ZUNNAN “

Duk suka sake zuba masa ido suna kallonsa zuciyoyinsu na bugawa ,musamman Baba da Hamma Sulaiman da suka San komai ,tuni Hamma sulaiman ya runtse idanunsa yana sauke numfashi hawaye naciko idanuwansa …mutuwar nasake dawomasa sabuwa.

Abdurrahman Ya kuma sunkuyar da kai hawaye naciko idanunsa yaci gaba “ranar da Hassana tanemi inshiga zatayi magana dani a asibiti …bayan nashiga na isketa cikin matsanancin ciwo ne amma haka ta daure ta rik’o hannuna nazauna kan kujerar kusa da gadon,ganin tana hawaye sai jikina Yakama rawa azatona ciwo ke damunta …NASA hannuna nashare mata hawayenta inayi mata sannu …sai ta kalleni takuma fashewa da kuka tacemin ” inason in rok’i wata alfarma agunka ya Abdurrahman ,sai dai inajin kunyar ka ,gani nake kamar zan zalunceka “naji tausayinta matuk’a shiyasa nima hawaye ya zubomin naji azuciyata zan iyayi mata dukkan abinda takeso ,cikin hawaye nacemata ” ke Y’ar uwatace …karkiji kunya ko Shakkar tambayata komai ,nikuma nayi alk’awarin zanyi miki matuk’ar bai sab’awa Allah da manzonsa ba “sai tayi wani murmushi tace” ajikina nakejin rayuwata tazo k’arshe …ba lallai intashi inci gaba da rayuwa ba ….kasan rashin jituwar da take tsakanin mutanen da nake so da k’auna a zuciya ta …a yanzu banida wani buri face naga sun dena k’in junansu …..Ya Abdurrahman inason Hamma Sageer ,amma alamu sun nuna bazanyi doguwar rayuwa dashi ba ,alfarmar da nake nema gunka itace ,zaka iya hak’ura da Auren sisina kabarwa Hamma Sageer ya aureta …..!?tabbas gabana ya fad’i a lokacin amma cikin dauriya nacemata “meyasa kikayi wannan tunanin ….!?sai tacemin ” aduniya babu kusanci me girma irinna mata da mijinta ….idan suka auri juna kusancin su zaisa subar duk wata gaba da k’in juna ,k’ila daman Allah yayi nufin k’ulla wata alak’a mai girma a tsakaninsu shiyasa zai d’aukeni Dan ya daidaita tsakaninsu ….Ya Abdurrahman nasan kana matuk’ar son sisina …amma kadaure kabarwa Hamma Sageer ita saboda tacigaba da kulamin da tarbiyyarsa ,Hamma sageer tamkar mace yake gurin rauni …ko babu komai zai dinga ganinta tamkar ni …zanyi farincikin mutanen Dana fiso sun zauna inuwa d’aya …sisina tasan irin son da nakewa Hamma sageer ,nasan zatayi hak’uri ta dinga ganinsa tamkar ni a idanuwanta ….katayani mugina wannan abin alkairin Ya Abdurrahman …kayimin alk’awarin idan har k’asa ta rufe idanuna zaka sadaukar da soyayyar sisina zuwaga Hamma Sageer ….”

    Zuciya ta bugawa takeyi tamkar tafad'o k'asa ,na dinga Jan addu'a a zuciyata ...take naji wani k'arfin hak'uri da yadda da k'addara yashigeni ,na tabbatarda cewar k'ila jarrabawata ce tazo ,shiyasa NASA hannuna nagoge mata hawayen fuskarta ,cikin murmushi me tafiya da hawaye nacemata"ki shaida ,nima na shaida ,Allah ne shaidarmu domin shi kad'aine yake kallonmu da jinmu a halin yanzu ....ni Abdurrahman nayi alk'awarin zancika miki burinki muddin bakya raye.... Zan sadaukarwa da Aminina masoyiyata ...zan tsaya tsayin Daka domin naga na tabbatar da wannan Abu ....babu abinda bazanwa sageer ba arayuwa ta ....tabbas inason Hussaina... Amma a halin yanzu Sageer yafini cancantar samunta idan har bakya raye "



   Hannayena duka ta rik'o tacemin "kai mutum ne nagari me k'ok'arin yarda da k'addara aduk Sanda ta riskeshi(tamkar ya Abbas d'in cikin SANADIN HOTO????) ,kacika me imani tunda kasowa D'an uwanka musulmi abinda kasowa kanka...Ya Abdurrahman nagode sosai ,Allah ya musanya maka da mafificin alkairi Wanda baka tab'a tsammani ba ,aduk lokacin da kasamu dama ka Isar da wannan sak'o da buri nawa ,sannan kafad'awa Hamma Sageer da sisina cewa " ina sonsu ,ina k'aunarsu ,abinda zasuyi min su sakamin wannan soyayya shine ,su auri junansu ,sukula da junansu ,sannan su dingayi min add'a aduk lokacin da suka tunani "tasaki hannuna ta runtse idanunta tacemin " shikenan jeka Ya Abdurrahman ,alkairin Allah yana tare da kai insha Allah,kacewa Baba da Hamma Sulaiman inason ganinsu su shigo su biyu "alokacin ne zuciya ta tayi matuk'ar rauni nafito ina kuka, Dan kar Ku tambayeni dalilin kukana shiyasa nafice nabar asibin ma gabad'aya " kunji abinda muka tattauna nida marigayiya Hassana.



   Kowa dake zaune a falon hawaye yakeyi ,musamman Hussaina da tamkar tashid'e don kuka ,Hamma sageer kuwa tamkar saukar aradu yakejin maganar Abdurrahman a kunnensa ,Kansa na tsakanin cinyoyinsa ya matse zufa na yanko masa,ji yake tamkar yamace agun ya huta da rayuwar da babu masoyiyarsa cikinta .

Abdurrahman yakalli Hussaina dake faman kuka ya d’aga mata hannu yace “zo nan ” da rarrafe tak’araso gabansa ta rik’e k’afafunsa hawayenta da majina na sauka akan cinyarsa ,yasa hannu ya d’ago kan Hamma Sageer dake sunkuye ya tsura masa idanu ganin tamkar baya cikin hayyacinsa …sai Yakama hannun Hussaina d’aya ,ya had’a da hannun Sageer guda d’aya ya runtse anasa hannun ,ya d’ago Kansa yadubi mutanen dake zaune ya girgza kansa,yayi namijin k’ok’arin mayarda hawayensa yace “Ku shaida ni Abdurrahman na sadaukarwa Abokina Aminina masoyiyata Hussaina ….gobe idan Allah ya kaimu bayan kammala addu’ar sadakar bakwai za’a d’aura aurensu bisa sadaki dubu hamsin ….” Ya zaro kud’i a aljihunsa ya mik’awa Hamma Sulaiman sadakin Hussaina Wanda yabiyawa Sageer da kansa. Hamma Sulaiman ya karb’a yana zubda hawaye a idanunsa .

Abdurrahman ya d’ago fuskar Hussaina datake ta girgiza masa kai takasa magana sai kuka mai cin rai da takeyi ,yasa hannayensa yana gogemata hawayenta da majinarta da sukaimata kaca kaca a fuskarta ,ya tsura mata idanu a hankali yace mata “sorry tawan …..please sacrifice the love you have for me to my friend ………”

Comments
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍


TYPING????

???????? HASSANA ????????

            *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page5⃣1⃣to5⃣2⃣

WATTPAD:hassana3329

® PEN : WRITERS ASSOCIATION


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

TUNASARWA????

HISABI

ZA’A BIJIRO DA MUTANE SAHU SAHU GA UBANGIJINSU ,SAI YA NUNA MUSU AYYUKANSU ,YAKUMA TAMBAYESU GAME DA SU DA RAYUWARSU ,DA DUKIYOYINSU DA ILIMINSU DA ALK’AWURAN DA SUKA D’AUKA DA DUKKANIN NI’IMOMI ,JINSU DA GANINSU DA ZUKATANSU ,KAFIRAI DA MUNAFUKAI ZA’AYI MUSU HISABI AGABAN HALITTU DAN A WULAK’ANTASU ,KUMA A TSAYAR DA HUJJA AKANSU ,KUMA ASANYA MUTANE DA K’ASA DA YINI DA DARARE DA DUKIYA DA MALA’IKU DA GAB’B’AI SUYI SHAIDA AKANSU ,HAR SAI LAIFIN YA TABBATA SUN AMSA LAIFINSU ,MUMINI KUMA ALLAH ZAI KEB’ESHI YAGAYA MASA LAIFINSA HAR SAI YAZACI CEWA YA HALAKA ,SAI UBANGIJI YACE DASHI “NA SUTURTA MAKASU A DUNIYA KUMA NA GAFARTA MAKASU A YAU
KUMA FARKON WAD’ANDA ZA’A FARA YIWA HISABI SUNE AL’UMMAR ANNABI MUHAMMAD (S A W)KUMA FARKON AIKIN DA ZA’A FARA AUNAWA SHINE SALLAH DA KUMA JINI

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button