HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

AIKI ME FALALA????

DUK WANDA BURINSA SHINE LAHIRA ,TO ALLAH ZAI SANYA MASA WADATARSA A ZUCIYARSA ,KUMA SAI (ALLAH)YA TARA MASA K’ARFINSA A WURI GUDA ,KUMA DUNIYA ZATA ZOMASA ALHALI TANA K’ASK’ANTACCIYA ,ABISA DOLENTA

SADAUKARWA GAREKU ????

Hassan (A T K)

Hussain (80k)

kamal (no love)

ALLAH YASAKA MUKU DA ALKAIRI YABIYAKU DA ALJANNA ABISA K’OK’ARINKU GAREMU.

INA TAYAKI MURNAR KAMMALA LITTAFINKI SISTER NABEELA DIKKO ,ME SUNA (TARBIYYA)ALLAH YABAKI LADAN FAD’AKARWA ,ALLAH KUMA YA YAFE KURA KURAN CIKINSA????????????????

***Ana saura kwana d’aya tafiyar tasu duk shirye shirye sun kammala ,Hamma Sageer da Hussaina zasu fara yin gaba su sauka a hotel ,yayinda bayan kwana uku mamma zata bisu saboda ragowar shirin da bata k’arasa ba …inyaso ranar da tabisu sai su tare agidan ta dake unguwar maitama a babban birnin tarayya Abuja .

Ranar gidan acike yake ,Adda Nabeela tazo ,ga sakeena da Sadiya ma sunzo ,hatta mummy Aisha da Ya Abdurrahman duk suna gidan ,Abdurrahman yana d’akin su safwan suna D’an tab’a hira dasu Babangida …duk da bayajin dad’in zuciyarsa sosai ….amma yana yawaita addu’a shiyasa yasamu sauk’in damuwarsa.

Cikin gida kuwa sun taru akan Hussaina gabad’ayansu sunayi mata nasiha da fad’an zaman gidan aure, kowa yatofa albarkacin bakinsa sunata lallab’ata ,yayinda Hussaina ke kuka tamkar ranta zai fita …duk wani kayanta da zata buk’ata an had’asu waje d’aya ,bawasu kayane masu yawa ba tunda Mamma tace akwai komai a can basai and’ibi kaya da yawa ba .

Magunguna iri iri masu kyau na gyaran jiki Aunty Sakeena tasa ta a gaba tana d’uramata amma Hussaina tak’isha ,ga garwashi a gefe anzuba wani turaren tsuguno me masifar k’amshi anyi anyi da ita ta zauna akan wata kujera ZA’A saka turaren k’ark’ashin kujerar yadda zai ratsata amma tak’i ,saida Aunty Sadiya taje takirawo Abdurrahman ,suka dawo d’akin tare ,yana shiga ya kalli Hussaina daketa shirgar kuka idanuwanta har sun nutse ciki Dan azabar kuka, matsanancin tausayinta ya kamashi,yasan tana cikin jarrabawa ,yaji tamkar ya rungumeta ya lallasheta …amma yayi saurin tsarkake zuciyarsa da tunawa cewa yanzun tazama matar Amininsa tayi masa nisa na har abada ….

     Har gabanta yaje ya tsuguna ,sannan ya ambaci sunanta a hankali yace "Hussaina " ta k'uramasa ido tana hawaye ,sai kuma ta girgiza kai murya ashak'e tace "ba haka kake kirana ba Ya Abdurrahman ,Dan Allah kacemin tawan yadda kasaba kirana " yayi wani irin murmushi ya sunkuyar da kansa yace "kin tashi daga tawan ,kin zama ta Sageer yanzu" saita kuma fashewa da kuka tarik'o hannunsa tace "Ya Abdurrahman narasa komai ,na rasa Hassanata ....narasa ka amatsayin miji kuma masoyi ,yanzu kuma anata shirin rabani da ahalina gabad'aya ....????"

Ya D’an kawar da kansa yana zame hannunsa data rik’e yace “yadda nakeda tsananin kishi da nine na aureki naga kin kama hannun wani kin rik’e zan iya d’aukar mataki babba ,kidena k’ok’arin tab’ani yanzu tunda kinada aure, ayanzu Sageer ne kawai keda ikon tab’a jikinki akan kowane d’a namiji ,sai kuma Baba da su Hamma Sulaiman saboda sun kasance muharramanki ,Dan haka abinda bazanso ayimin ba nima bazanyiwa waniba ” yad’anyi shiru yanajin yadda kukanta ke hautsina masa kai ,sannan yacigaba da cewa “kiyi hak’uri da jarrabawarki ,kowa da yadda tasa take zuwa ,idan kuma kayi hak’uri da k’addararka Kanada babban kyakkyawan sakamako agurin Allah ,ni daman tuni Allah yarubuta ba mijinki bane ,to idan so cutane ai hak’uri maganine, baki rasa komai ba Hussaina…insha Allahu Sageer zai maye miki madadin kowa da komai a rayuwa ,ammafa sai kinyi hak’uri da jarrabawarki da k’addararki ,kin San wani Abu ….!?ta girgiza kai tana shesshek’ar kuka ,yasaki ajiyar zuciya yana D’an runtse ido yace ” naji labarin wasu masoya wad’anda suka tashi cikin tsananin son junansu da k’aunar junansu tundaga yarinta, basu tab’a tunanin wani Abu zaiyi sanadin rabuwar suba, sai gashi dalilin sanadin hoto da kuma k’addararsu Allah yaraba tsakaninsu ,tsananin soyayyartasu bata kaisu ga aure ba ,sukayi hak’uri sukayi tawakkali ,suka rungumi k’addararsu hannu bibiyu …a k’arshe suka samu ribar hakan suna masu godiya ga ubangijinsu tunda sun San komai nufinsa ne “

Wani hawayen Yakuma zubomata ,tabarsu suna zuba ba tare da yunk’urin gogewa ba tace “su waye wad’annan Ya Abdurrahman …!?ya ware idanunsa ya kalleta yace ” Abbas da Aysha (safah)kenan….masoyan da tarihin soyayyarsu yasakani kuka da hawayena ????….nima inason nayi koyi da abinda Abbas yayi na d’aukar k’addara da yadda da jarrabawar ubangijinsa ,hakanan kema inason kiyi koyi da safah wajen mik’a wuya ga ubangiji cikin jarabtar da yayi miki ,kiyi biyayyar aure ki yadda da nufin ubangiji …. Zanso ki karanta labarinsu Wanda wannan marubuciyar me suna HASSANA D’AN LARABAWA ta rubuta me suna SANADIN HOTO ,zanyi k’ok’ari nasamomiki domin ki karanta kiji tarihin wannan soyayya “

Tun kafin ma ta karanta labarin taji tafara tausaya musu, idanunta na zubda hawaye take kallonsa ,yakuma sunkuyarda kansa yace “idan nace kimin wani Abu zakimin …!?da rawar murya tace ” zan maka ya Abdurrahman ….kafi k’arfin komai awajena “sai yace ” inason duk abinda akace kiyi yanzu to kiyishi …kidena yimusu gardama akan duk abinda suka saki ,sannan kirage yawan kuka domin bashida amfani sai dai ma ya cutar dake don Allah ….”ta d’aga kanta sama tana kallon fankar dake juyawa ,haka takejin nata kan na juyawa tamkar fankar tace “zanyi maka abinda kakeso Ya Abdurrahman ….bazan k’ara yiwa kowa gardama ba insha Allah …amma kayimin hak’uri akan zubar hawayena banida ikon hanasu zuba ne …nasan kuma bazasu tab’a daina zuba ba har randa zan koma ga mahallici na ” sai ya tsurawa fuskarta idanu na minti d’aya sannan yace “kowace irin damuwa kikeji ki yawaita addu’a Allah zai miki maganinta ,domin duk inda tsanani yake akwai sauk’i agabansa ….inai miki fatan alkairi da nasiha akan hak’uri ,domin shi hak’uri mataki ne na nasara a rayuwa ” yana fad’in haka yamik’e yayi hanyar fita ,sannan ya waiwayo yana duban su sakeena dake gefe a zaune kowacce tazuba tagumi suna tausayin Hussaina da Abdurrahman d’in ,ya sanyaya murya yace “Aunty kuyi mata duk abinda yadace …….” Yasa kai yafice yana goge hawayen da ke k’ok’arin fitowa…….

Hussaina batakuma gardama ba ,duk abinda sukace tayi yi takeyi ,haka komai suka bata tasha Sha takeyi babu gardama ko sa’insa ,sai dai fa hawaye bai bar zuba a idanunta ba ,su Aunty sakeena mamakin yawan hawayen datake fitarwa sukeyi ….saboda yawansu ,duk wani gyara sun mata shi a ranar. Zarah da Asma’u sunzo sunyi sallama da juna ,dukansu sunsha kuka suna tuna rayuwarsu da Hassana ,yanzu gashi tatafi ta barsu ,da daddare kuma Hamma Sulaiman da Aminu sukazo Dan d’aukar matansu , inda sukayi sallama da Hussaina ,sallamar bankwana saboda gobe bazasu zo ganin tafiyarsu ba ,Hussaina ta rungumesu tanata kuka har suma tasasu kukan ,da k’yar suka rabu kowa yana tuna Hassana dayi mata addu’a ,Abdurrahman ma saida yayi nasa kukan shida mummy ….mummy kukanta harda na tausayin d’anta Abdurrahman ,taga matuk’ar k’ok’arinsa akan sadaukarwar da yayi ….kuma kullum addu’a takemasa akan Allah yayi masa tukuici da samun mace tagari zab’ab’b’iya daga Allah .

A daren Umma a d’akin Hussaina ta kwana ,basuyi wani barci sosai ba illah nasiha da maganganu masu dad’i da Umma tadinga gayawa Hussaina ,tayi mata nasiha akan zaman aure da kyautatawa miji da mahaifiyarsa ,Hussaina dai tana cikin tashin hankali Mara misaltuwa ,kwance take kawai ajikin Umma tana shatatar hawaye masu zafi ,gabad’aya ahalin gidan jikinsu a sanyaye yake da tafiyar Hussaina ,Babangida da Usman kuka kawai sukeyi ,har gara safwan yafisu k’arfin zuciya .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button