HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page5⃣5⃣to5⃣6⃣

WATTPAD:hassana3329

® PEN : WRITERS ASSOCIATION


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

TUNASARWA????

GADA

MANZON ALLAH (S A W) YACE “MUMINAI ZASU TSIRA DAGA WUTA,SAI ADAKATAR DASU A WATA GADA TSAKANIN WUTA DA ALJANNA ,SAI AMAYARWA DA KOWA ABINDA D’AN UWANSA YA ZALUNCESHI A DUNIYA HAR SAI AN TSARKAKESU SAI AYIMUSU IZNIN SHIGA ALJANNA.NA RANTSE DA WANDA RAN MUHAMMADU YAKE HANNUNSA ,KOWANNENSU YAFI GANE GIDANSA A ALJANNA FIYE DA GIDANSA NA DUNIYA” BUKHARI NE YA RAWAITO

AIKI ME FALALA????

MANZON ALLAH (S A W)YACE”LALLAI WAD’ANDA ALLAH TA’ALA YAKE JIN K’ANSU KAD’AI SUNE WAD’ANDA SUKE MASU JIN K’AI ,(ATSAKANIN SU DA KUMA SAURAN HALITTUN ALLAH),SABODA HAKA KUJIK’AN WAD’ANDA SUKE A BAYAN K’ASA(TAUSAYI)KUMA WANDA YAKE SAMA ZAI JIK’ANKU

DEDITED TO ALL MY FAN’S ,INA K’AUNARKU KUMA INAJIN DAD’IN ADDU’AR KU GARENI ,NAGODE ANA KYAWUN TARE MASOYANA,MASUYIN KUKA ????KUMA SUYI HAK’URI HAKA YANAYIN LABARIN YAZO DASHI,NAGODE.

***A motar Hamma Sulaiman za’a tafi airport d’in ,bayan an saka kayan a boot d’in motar sai Hamma Aminu yashiga mazaunin driver ya zauna ,Hamma Sulaiman kuma yashiga baya shida Hussaina tana rungume ajikinsa yayinda Hamma Sageer zai zauna a gaba kusada Hamma Aminu ,Hamma sageer yak’araso gaban Baba ya tsuguna kansa a k’asa yace “Baba zamu wuce …ayi mana addu’a ” Baba yayi murmushi yace “addu’ata tana tare da Ku Muhammad …Allah ya kiyaye hanya ya saukeku lafiya ,kayi hak’uri da Hussaina Sageer ….Allah yabaku zaman lafiya ” ya amsa da Ameen sannan ya mik’e ya tsaya gaban Abdurrahman ya k’uramasa idanu yana kallonsa a hankali ya sunkuyarda kai yace “Abdul zamu tafi ….kayi mana addu’a domin kai aminine nagari ” Abdurrahman yayi murmushi yana maida hawayensa ,Yakama hannun Sageer sukai musabaha sannan yace “na yarda a zuciya ta cewar Sageer zai kula da sadaukarwata tamkar sweetynsa ….domin dukansu Abu d’ayane ya samar dasu…. Allah ya sanya alkairi a tsakaninku ya dawwamarda zaman lafiya da k’aunar juna ” sai Sageer Yakama hawaye ,cikin raunin zuciya ya rungume Abdul a k’irjinsa ,a kunnensa ya rad’amasa cewa “babu wani amini ko aboki da yakaika a fad’in duniya ,ka hak’ura da farincikin ka domin ka sanya abokinka cikin farinciki ….lallai kayi koyi da sayyadina Abubakar( assidiq ) sahabin annabi kuma masoyin Annabi ,sannan Abokin Annabi ta wajan nuna soyayya ga abokinka da nuna cewar gara abokinka yaji dad’i akan kaji dad’i …..Abdurrahman irinku bakuda yawa a duniya ,kuma sakamakon ka yana gurin Allah …..” Yana fad’in haka ya sakeshi ya mik’awa ya safwan hannu sukayi musabaha sannan da hanzari ya shige mota ya rufe k’ofa ,yasa kansa cikin cinyoyinsa hawaye na zarya bisa kuncinsa.

Haka Baba da Ya Abdurrahman da Ya safwan suka dinga d’agawa Hussaina hannu har Hamma Aminu ya tashi motar ….yayinda idanunta suke kan mahaifinta da y’an uwanta tanata zubda hawaye akan k’irjin Hamma Sulaiman ,hannunta tad’ago a hankali itama tana d’agawa su Baba ,har Hamma Aminu yatashi motar suka fara tafiya Hussaina batabar kallon k’ofar gidansu ba ,haka su Baba basu bar gurinba saida motar ta k’ule sannan Baba yajuya yajawo Abdurrahman k’irjinsa ya rungumeshi ,yashafa kansa yace “Allah yayimaka Albarka Abdurrahman …Allah yabaka ladan hak’uri da sadaukarwa.

      A airport suka tarar da Mamma da Aunty Nafeesa na jiran zuwansu ,Mamma ta tarbi Hussaina ta karb'eta daga jikin Hamma Sulaiman ta rungumeta tana share mata hawayen fuskarta ...sannan tad'agota ta kalleta tace" kiyi shiru kidena kuka ,Dan kin bar gida bawai kin tafi kenan ba ...nima inanan zuwa nanda kwana uku masu zuwa insha Allah ....alokacin ne zakisan baki rasa kowaba ,zan zamemiki madadin Umma da Baba ,Muhammad Sageer zai zame miki madadin Hassana da sauran y'an uwanki ,zai zame miki miji nagari me farantawa matarsa ...."haka Mamma da Aunty Nafeesa sukaita bata baki da rarrashi .




      Anfara kiran passenger don hawa jirgi ,lokacin ne Hamma Sulaiman yasa hannunsa a aljihu ya d'auko wasu takardu guda biyu ya tsura musu idanu yana tuna ranar da Hassana take rubutasu hawayenta nad'iga ajikin takardar ,shima idanunsa suka kawo k'walla ,yayi hanzarin mayarwa saboda nasihar da Sakeenan sa tayi masa da safe kan yafito ,har tarako shi bakin mota sai takama hannayensa tarik'e idanunta cikin nasa tana murmushi tace "Abban sadauki kar kayi kuka idan kaje airport d'innan ...kayi k'ok'arin jarumta saboda ganin hawayenka zai dad'a dagula lissafin Hussaina ,shawarata gareka kenan " sannan takai bakinta kan nasa bakin ta sumbata ,idanunsa a lumshe tagama bidirinta cikin bakinsa sannan tasakeshi takoma cikin gida.

Tuno hakan da yayi shiyasa yayi jarumtar maida hawayensa yasa hannu yakamo hannun Sageer yad’an jashi gefe ,yabud’e tafin hannun Sageer d’in yasa masa farar takarda guda d’aya sannan ya runtse hannun ,ya kalli Sageer yace “wannan takarda Amanace agareni zuwa gareka ,nakuma godewa Allah da yabani ikon isar da wannan sak’o zuwa gareka …aduk sanda kasamu dama ka karanta wannan takarda Sageer ” yayi shiru yayinda Sageer d’in yake kallonsa da fuskar kyautatawa yace “Nagode Hamma Sulaiman ….Allah yak’ara girma yabiya buk’atu na alkairi ” Hamma Sulaiman ya amsa sannan yace “an dank’amin amanar mutane biyu abisa inkula dasu da rayuwarsu ,in hanasu kuka aduk sanda naga zasu zubda hawaye ,nayi k’ok’arin karesu aduk lokacin da naga wani Abu zai cutar dasu …nazame musu duk wata Garkuwa domin suji dad’i ,to amma gashi amanar tawa zasuyi nisa dani ,bazan dinga yawan ganinsu ba balle nakula da lamarinsu …mezai hana ka taimakamin akan kulawa da d’aya daga cikin Amanata Sageer ” Hamma Sageer kansa a sunkuye saboda yana tsananin ganin girman Hamma Sulaiman ,Dan ba zai manta ba sweetynsa tana yawan yimasa zancen sa ,wataran ma sai suna cikin hira sai tace “Hamma Sageer ina k’aunar Hamma Sulaiman ,saboda shi mutum ne nagari me k’aunar ahalinsa da danginsa ” tasha nanata masa wannan maganar sau ba adadi ,shiyasa shima yakejin k’aunar Sulaiman tamkar Nafeesa yakejinsa a zuciyarsa ,ya d’ago kai yakalli Hamma Sulaiman yace “zan tayaka rik’on amanarka Hamma Sulaiman da ikon Allah …mecece amanar taka…!?sai Hamma Sulaiman yayi murmushin jin dad’i ya kamo Hussaina dake jikin Aunty Nafeesa ,ya dank’a hannunta guda d’aya a hannun Sageer yace ” ga amanar da zaka tayani rik’ewa ,don Allah Sageer ka kulamin da amanata ,kar kabarta tadinga yawan zubda hawaye ,ka tausayamata ka rungumeta amatsayin matarka kuma amana agareka “ya waiwaya yadubi Hussaina yace ” mijinki zai taimakeni wajan tayani rik’on amanata guda d’aya ,kuma amanonin biyu ne ,ko kema zaki tallafamin wajen rik’on d’aya amanar ….!?Hussaina ta tsurawa Hamma Sulaiman idanu yayinda jikinta yayi sanyi jin hannunta cikin tattausan hannun Sageer ,sai tad’agawa Hamma Sulaiman kai saboda bazata iya magana ba ,tana bud’e baki kukane zai fito ,ganin ta amsa zata tayashi rik’ewa shiyasa murmushin farinciki ya sub’ucewa Hamma Sulaiman ya dafa kafad’ar Sageer yace “ga amanar da zaki tayani rik’ewa ….karki barshi yayi kuka ,idan kikaga wani Abu zai cutar dashi kizama Garkuwa agareshi …kinuna masa kulawa fiyeda kulawar da zaki bawa kanki …….

Yasaki hannun su yajuya musu baya saboda zazzafan hawayen da yaratso idanuwansa ????,cikin raunin murya yace ” kar Ku manta kunmin alk’awarin rik’emin amanar da nabaku ,kuma duk Wanda yaci amana to amana zata cishi “yana fad’in haka yayi saurin yin gaba zuwa bakin mota inda su Hamma Aminu ke jiransa bai k’ara waiwayo ba ….takardar Hussaina kuwa gefen hijabinta Yakama ya d’aure mata tata aciki ba tare da tasani ba.

  Kiran sunansu da ake tayi shiyabawa Hamma Sageer damar fara tafiya hannunsa rik'eda na Hussaina yanaja ,a hankali yake taka matattakalar jirgin yana sauke ajiyar zuciya duk jikinsa a sanyaye ,binsa take abaya hannunta cikin nasa idanunta kan k'eyarsa tana kallon kwantacciyar sumarsa da ta kwanta lamb'am sai k'yalli takeyi .

Wajan zamansu d’ayane acikin jirgi ,da kansa ya taimaka mata ta zauna cikin kujerarta ,shima ya zauna akan tasa kujerar ,kowannensu zuciyarsa cikeda tunani iri iri …Hussaina dai tayi tsuru tsuru jinta cikin jirgi tunda bata tab’a hawaba ,shikuwa Hamma Sageer yasaba .

Bayan passengers sun gama hawa flight yayi lebir aka sanarda cewa jirgi zai tashi kowa ya shirya ya d’aura belt ,Hussaina tana kallo kowa yanaja yana d’aurawa ajikinsa amma ita bata iya d’aurawa ba ,kuma bazata iya tambayar Hamma Sageer yadda ake d’aurawa ba ,tana kallonsa yaja nasa ya d’aura ya dai daita zamansa ko kallon inda take baiyi ba ,tunani a ransa fal… Yana tunanin yadda zai zauna da macen da ta tsaneshi a rayuwa a matsayin matarsa .

Yanayin yadda jirgi yafara motsawa a hankali yana k’ok’arin tashi sai tsoro Yakama Hussaina, ji takeyi tamkar kifewa zaiyi dasu saboda wani irin sama da k’asa da taji yanayi …tuni taji kanta yana matsanancin juyawa tamkar zai bar gangar jikinta ,ta runtse idanunta tarik’e kanta da hannuwa biyu amma batadena jin abinda takeji ba saima k’aruwa da yayi ,tabud’e baki da dasasshiyar muryarta da bata fita sosai saboda Kuka ta k’wala k’ara da fad’in “wayyoni wayyohhhh Allahhhhh na ,Hamma Sulaiman kazo kacireni daga jirginnan kaina juyawa yakeyi ,wayyohhhhhhh Allahhhh na Hamma……” A matuk’ar razane Hamma Sageer ya kalleta jin ihunta Dan har hankalin mutanen dake dab dasu yayo Kansu ,ganin takuma kwaye baki zata zunduma ihu cikin zafin nama da rashin Sanin abinyi yamatsa dab da ita yasa hannayensa ya rufe bakinta ruf,yayi k’asa da murya yana kallon fuskarta yace “ke lafiya kuwa ….!?me kikeyi hakane …!?me yashiga kanki kikema mutane ihu eyehhhhh” idanunta a runtse jikinta narawa sosai tabud’e baki hawaye naratso idanunta tace “kainane yake juyawa …wayyo kaina zai cirene fahhhhhhhhh” wani haushi yakamashi yayi niyyar rabuwa da ita sai zuciyarsa ta tunamasa Maganar Hamma Sulaiman da yayi wucewar mintunan da suka shud’e ….(duk Wanda yaci amana to amana zata cishi),kawai sai ya lumshe idanunsa yana fesar da numfashi akan fuskarta ,yasa hannu yajawo kafad’unta ya matso da ita jikinsa ,kanta ya kwantar akan k’irjinsa yana runtse idanu da cije lips d’insa ,da wata irin murya yace mata “ki kwanta ahaka karki motsa kirufe idanunki zuwa anjima zaki dena jin abinda kikeji ..rashin Sabone kawai ” Hussaina jinta a k’irjin Sageer kwance sai jikinta Yakama rawa kar kar kar ,wani irin d’umin jikin Sageer na ratsa jikinta ,shikuma rawar da jikinta keyine yakeson haifar masa da matsala saboda yadda tudun breast d’inta ke zungurin k’irjinsa ,da rawar murya yace mata “ke wai wannan rawar jikin namaye haka ….!?na rantse inbaki nutsu ba zaki tashi ajikina …” Tanajinsa saita cusa kanta acikin k’irjinsa wani Abu na tasomata da yunk’uro mata ,da k’yar takuma magana tace “amai ne yake tasomin …jinakeyi tamkar zanyi amai …” Yad’an zaro idanu yana hararan kanta dake kan k’irjinsa yace “kika kuskura kikaimin amai ajikina yaseen sai ranki yab’aci ….ki had’iye amanki idan muka sauka sai kiyi abinki ” yanajin yadda hawayenta ke jik’a k’irjinsa yayi shiru yanajin tamkar shima yayi kukan ,wata gingimemiyar kewa yakeji yanajin Kansa tamkar maraya a soyayya ,idanunsa a runtse fuskar sweetynsa na gilmawa a idanuwansa da murmushi akan fuskarta tana nanata masa kalaman soyayya ,a hankali cikin k’aramar murya yace “wayyohhhhh nayi rashin masoyiya ta .. Sweety na kin barni da k’uncin zuciya …..” Saukar numfashin Hussaina ne ya tabbatar masa da tayi barci akan k’irjinsa .(su hussy anji k’irji me dad’i da laushi an lafe harda bacci????????).

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button