HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yana tsaye cikin d’akin me d’auke da fallow da bedroom guda d’aya tal ,sai toilet acikin bedroom d’in ,falon akwai wata irin doguwar kujera me lank’wasa tamkar ta sarakai ,sai kayan kallo da center table a tsakiyar falon ,bawasu tarkace bane aciki amma ya tsaru sosai ,yana nan tsaye yaji shiru Hussaina bata shigo ba ,wani haushi yakuma kamashi aransa yana tunanin meta tsaya yi awaje …!?a hankali yatako k’afafunsa yazo bakin k’ofar ya tsaya …..zuba mata idanu yayi ganin yadda ta rakub’e a bakin d’akin tana hawaye ,cikin cusasshiyar murya yacemata “me kika tsaya yi anan da bazaki shigo ba ….!?ta kalleshi sai ta sunkuyar da kai tana kuka, ya D’an runtse idanu gabansa na fad’uwa (kar kabarta tayi kuka )kalamin Hamma Sulaiman yafad’o masa a ransa ,sai ya D’an matsa mata kad’an yana nuna mata hanya yace ” shige muje ….”sum sum ta rab’ashi ta wuce tana goge fuskarta da hijabin jikinta ,suna shiga falon ta nemi guri ta tsaya ,ransa ya kuma b’aci wato ita zaman ma sai ance tayi zatayi ,to kuwa sai dai ta shekara a tsaye ,d’an tsaki yaja sannan yajawo jakarsa guda d’aya yafad’a bedroom d’in yabarta tsaye a falon ,yana shiga yaga d’akin tsaf …angyara bed d’in da shimfid’a me kyau ko ina k’amshi ke tashi ,ajiye jakar yayi agefe sannan yabud’eta ya zaro towel na wanka ya fad’a toilet ,wanka yayi da ruwa me zafi sannan ya d’aura alwala ,d’aura towel d’in yayi a k’ugunsa sannan yafito daga toilet d’in ,bayan ya fito ya tsane ruwan jikinsa yad’an Shafa mai da turare kad’an ya taje sumar kansa, boxer yad’auko a jakarsa yasaka tare da wata jallabiyya me tsananin kyau ta maza ,ya d’auki daddumar da yagani akan bedside ya shimfid’a yatada sallar azahar ,bayan ya idar yayi karatun alk’ur’ani ,ya dad’e zaune yanaiwa Hassana addu’a da hawayensa ,dai dai da minti d’aya baitab’a mantawa da yimata addu’a ba ,ko zaune yake shiru to addu’a yakemata azuciyar sa.
Bayan ya kammala yamik’e yafito falon ,ganin Hussaina zaune a k’asa tana gyangyad’i sai yatuna ashefa tare suke, danshi gabad’aya ma ya manta da ita ,kauda kansa yayi daga gareta yazo zai giftata sai k’afarsa tabugi center table d’in dake tsakiyar falon ,k’arar tasa Hussaina ta farka a razane tana shirin kurma ihu ,yayi hanzarin isa gabanta yana tsareta da idanu yace “karki sake kimin ihu anan ….kewai bakida aiki sai ihu ne …!?baki iyayin addu’a ba sai ihu kika iya ko …!?
Tayi shiru jikinta na rawa, yad’an kauda idanunsa daga kanta yace ” wuce ciki kiyi wanka da sallah kin tsaya kinaiwa mutane shirme da shiririta ….”sum sum tawuce cikin d’akin ,tsayawa tayi tana kallon yadda d’akin ya tsaru sosai ko’ina tsaf sai k’amshin turaren da Hamma Sageer yayi amfani dashi ke tashi ,k’ofar da tagani a d’akin ya tabbatar mata band’aki ne shiyasa tanufi k’ofar tana tangad’i saboda wani irin bacci ne a idanunta ,da tashiga ruwa ta had’a me zafi sosai tagasa jikinta sannan ta d’aura alwala ,bataga towel a toilet d’in ba saita d’auro zaninta a k’irjinta tafito ,a hankali take takowa zuwa cikin d’akin sai kuma ta tuna kayan ta suna cikin jaka a falow ,tilas haka ta zura hijabinta da tacire ta nufi falon k’afafunta na sark’ewa kanta a sunkuye ,wayam ta tarar da falon babu Hamma Sageer aciki shiyasa taji dad’i sosai tajawo Jakarta guda d’aya da k’er tana nishi zuwa cikin bedroom d’in ….bud’ewa tayi tazaro wasu Pakistan Riga da wando da k’aton mayafinsu ,wandon irin me fad’in nanne sai rigar me dogon hannu daga saman k’irjin ta matse sosai sai kuma k’asanta da yabud’e ,ko mai bata Shafa ba illah turare da sure da ta goga sannan ta zura kayanta ,duk tanayin hakan ne cikin matuk’ar k’arfin hali da dauriya ,bayan tasaka kayan ta nad’e kanta da mayafin Pakistan d’in ta hau kan daddumar da tagani shimfid’e ta kabbara sallarta ,bayan ta idar tayi addu’o’i sosai ,saida tazo yiwa Hassana addu’a sannan zuciyarta ta karye takama kuka da shesshek’a ,hawaye ya wanke mata fuska tanajin zuciyarta na matuk’ar zafi ,gawata kewar gida da ta mamaye ruhinta jitake tamkar tayi tsuntsuwa ta ganta ajikin ummanta ,akan daddumar tazame ta kwanta tana cigaba da kuka tamkar ranta zai fita ,a haka bacci ya salallab’o ya saceta tana kukan..
Bata dad'e da fara barci ba Hamma Sageer ya turo k'ofar bedroom d'in yashigo ,Leda ce a hannunsa me tambarin wani hamshak'in restaurant dake cikin hotel d'in ,k'arasowa yayi ya ajiye ledar akan bedside drawer ,sannan yadubi Hussaina dake kwance tana sharar bacci kan sallaya ....a hankali take sauke numfashi da ajiyar zuciya fuskarta duk jirwayen hawaye ,sosai yaga kamarta da sweetynsa alokacin yadda fuskarta tayi fayau ,ya runtse idanunsa yana dafe kansa da fad'in subhanallah ....!Allah yajik'anki sweety na ...."sai yafad'a kan bed d'in yana dafe kansa saboda wani irin juyawa da yakeyi ,k'ok'ari yakeyi domin yamik'e yatashi Hussaina Dan taci abinci ,yasan dole zataji yunwa ,shikuma yayi alk'awarin kulawa da ita kodan alk'awarin amanarta da ya d'auka ,amma gabad'aya yakasa tashi kamar an sassage masa gab'ob'in jikinsa yakeji ,motsi ma kasawa yayi sai nishi da yake saki a hankali ,ahaka shima barci b'arawo yayi nasarar kwasheshi .....
Can cikin barcinsa yaji tamkar ana kakarin amai ,yafara bud’e idanunsa a hankali kansa na sarawa yadubi agogon bangon d’akin sai yaga har k’arfe 4:30pm kenan har anyi sallar la’asar ,da hanzari yamik’e zaune daga kwanciyar da yayi sai kunnuwansa sukacigaba da jiyo kakarin amai daga cikin toilet ….yadubi inda yaga Hussaina a kwance sai yaga bata wajen …da Sauri yak’arasa wartsakewa yanufi toilet d’in sai yaganshi a bud’e tana durk’ushe sai kakarin amai takeyi babu komai acikinta duk k’arfinta ya k’are ,yana zuwa ya tsuguna gefenta jikinsa na rawa, tad’ago kanta ta kalleshi idanuwanta ajuye hawayen wahala nafitowa ,shima kallonta yakeyi k’irjinsa ba bugawa yace”wane irin amai kikeyi hakane wai ….!?me kikaci kafin mu tawo ne ?kinci wani abun ne …!?tabud’e baki zatayi magana cikinta tayi wani irin murd’awa wani aman yasake yunk’urowa gashi babu komai acikinta da zai zuba ,cikin azaba ta yunk’uro hannunta dafe da cikinta tana zufar wahala ta afka k’irjinsa da k’arfi har yana shirin fad’uwa k’asa yayi saurin rik’eta a jikinsa hankalinsa atashe ganin yadda tafara wani irin nishi k’irjinta na sama da k’asa ,cikin wata irin murya da bata fita sosai tace “wayyo ummana wayyo Babana,…. Wayyo cikina zan mutu nabi Hassanata …wayyooohhh Hamma Sageerrrrrrrrr …..” Kawai sai idanunta ya k’ak’k’afe ta sandare ajikinsa babu numfashi atare da ita.
Wani mugun tashin hankali ne yashiga jikinsa ,tsoro yakamashi kar yarinyar mutane ta mace masa ,hannunsa na karkarwa yak’ara had’ata da jikinsa yasa hannu biyu ya tallabo fuskarta yana girgiza ta muryarsa na carkewa yace “kehhhh wai yazakimin hakane ….!?menene hakane kikeyi so kike ki zautani ne….!?bud’e idanunki ki kalleni nan ….nace ki dubeni nan ko ….” Ganin yadda ta langab’e ajikinsa baisan sanda ya sauke fuskarsa akan tata fuskar yana ajiyar zuciya ajere ba ,hannunsa guda d’aya akan NATA hannun datake dafe da lak’umammen cikinta da tamkar bata tab’a zubamasa abinci ba ,muryarsa na rawa yana fesa mata numfashin hancinsa da bakinsa a fuskarta ,hawayensa nad’iga akan idanuwanta yace “Husainahhhhhhhhhhhhh…………..!
comments
Share
Vote
Pls
HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍
TYPING????
???????? HASSANA ????????
*DA*
❣???? HUSSAINA ????❣
TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍
page6⃣1⃣to6⃣2⃣
WATTPAD:hassana3329
® PEN : WRITERS ASSOCIATION
~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~
TUNASARWA????
DAD’IN ALJANNA
ACIKINTA AKWAI RUMFAR LU’U LU’U FAFAFFE FAD’INTA MIL SITTIN NE YANA DA IYALI A KOWANE LOKO ,ZASU SHIGA SUNA SAMARI Y’AN BANA BAKWAI BABU GASU AJIKINSU DA KWALLI A IDONSU ,SAMARTAKAR SU BATA K’AREWA TUFAFINSU BASA LALACEWA ,BA’A FITSARI KO KASHI A CIKINTA BABU K’AZANTA,MATAJIN KANSU NA AZURFA NE ,GUMINSU NA ALMISKI NE ,MATAN CIKINTA KYAWAWA NE BUDURWAI FARARE,FARKON WANDA ZAI FARA SHIGA SHINE ANNABI MUHAMMAD (S A W ) SANNAN ANNABAWA ,MAFI K’ARANCIN DARAJA ACIKINTA SHINE WANDA IDAN YANEMI ABU ZA’A BASHI NUNKINSA GOMA ,MA’AIKATAN CIKINTA YARANE ABABAN DAWWAMARWA ACIKINTA MASU KAMA DA LU’U LU’UN DA AKA BAZASHI ,DAGA CIKIN NI’IMOMIN DA SUKA FI GIRMA ACIKINTA AKWAI GANIN ALLAH (S W A )DA SAMUN YARDARSA,DA KUMA DAWWAMA