HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

A sashen Mamma sukayi masauki gabad’ayansu ,tuni Mamma tasa anyo musu order d’in abinci a wani had’ad’d’en restaurant ,sukaci sukayi k’at ,kowa yayi sallah yayinda Hamma Sulaiman da Hamma Sageer suka tafi masallaci sukayi tasu sallar ,inda a hanyar dawowarsu Hamma Sulaiman cikin k’warewa yake k’ara tausar zuciyar Sageer akan hak’uri da fallawa Allah al’amura ,yacigaba da bashi baki akan yadda da k’addara da amincewa da Hussaina a matsayin matarsa duk da ba itace zab’in zuciyarsa ba ,Hamma Sageer gyad’a kai kurum yakeyi yana tabbatarwa da Hamma Sulaiman ya karb’i batunsa kuma zaiyi aiki da shi insha Allah .

    A can ma haka Adda Nabeela taja Hussaina gefe tadinga yimata nasiha da rarrashi ,ayoyi da hadisai tadinga janyo mata tana buga mata misali dasu, a k'arshe tace "k'anwata babu ruwan Allah da rashin son da kikewa Sageer ,Allah zai kamaki ya tuhumeki idan har kika kasayi masa biyayyar aure, dagake harshi yakamata Ku tausayawa junanku kurik'e junanku da  gaskiya da amana ,wadda kuke abin dominta babu ita a fad'in duniya kuma ita tabar wasiyyar kuzama ma'aurata duk da daman Allah yatsara hakan ,ko yanzu tadawo duniya bazata tab'ajin dad'i ba idan zamantakewarku bata kasance kyakkyawa ba ...." Haka Adda Nabeela tai tai mata nasiha da kwantar da hankalinta har saida Hussaina tadinga hawayen tuna rabin ranta, haka nan tayiwa Adda Nabeela alk'awarin yin biyayya ga Sageer iya iyawarta .

Adda Nabeela da Aunty Nafeesa ne sukaje suka k’ara gyarawa Hussaina part d’inta ,ko’ina k’al k’al suka turare shi da turaren wuta me k’amshi ,kayansu duk suka jeramusu a wardrobe tsaf tsaf ,suna jiran dare yayi domin su raka Hussaina b’angarenta a matsayinta na amarya ,wasu had’e had’en magunguna masu kyau Adda Nabeela da Nafeesa suka bawa Hussaina a wannan ranar Wanda ita kanta Hussaina saida tadinga jin wani bak’on yanayi a tare da ita duk inda ta zauna sai taga lema agun saboda jik’ewar da pant d’inta yakeyi .

Bata k’ara sa su Hamma Sulaiman da Sageer a idanunta ba har zuwa dare da Adda Nabeela tayi mata wankan turare ta gyare mata jikinta tsaf da kwalliya ta garari ,Mamma ce tabada kaya masu tsananin kyau da d’aukar hankali tace asakamata ,Adda Nabeela da Nafeesa ne sukayi mata shiri na musamman tamkar yadda zata gasar sarauniyar kyau ,Hussaina dai gabanta fad’uwa yakeyi sosai tamkar k’irjinta zai ruguzo takeji Dan bugawar da yakeyi ga kuka da takeso tayi amma Adda Nabeela tak’i bata damar hakan .

Da Kansu suka rakata har sashenta suna k’ara jadaddamata abubuwan da yakamata ta rik’a a matsayinta na matar aure yanzu ,Mamma ma tayi mata nasiha sosai da alk’awarin rik’eta amana tamkar Sageer ,haka suka mik’ata sashenta tana hawaye suka barota ita kad’ai zuciyarta cikeda tunani iri iri .

  Hamma Sulaiman shine ya rako Sageer har k'ofar part d'insu inda ya kalli Sageer d'in yace "ka karanta takardar da nabaka randa zaku tawo Abuja a airport ...!?kan Sageer a sunkuye saboda shi gabad'aya ma yamanta da batun takardar ,shiyasa ya girgiza kai yad'ago yadubi Hamma Sulaiman yace " ban karanta ba wallahi na mance da itane "sai Hamma Sulaiman yayi k'aramin murmushi yadafa kafad'ar Hamma Sageer yace " idan babu damuwa kayimin alfarmar karanta ta yau mana ....."ya jijjiga kai da fad'in "insha Allah " anan Hamma Sulaiman yayiwa Sageer sallama da fad'in "gobe insha Allah zamu koma Gombe saboda akwai ayyuka dayawa da nabari natawo ,Zamu juya nida Adda Nabeela ,amma zamu bar Nafeesa anan sai bayan kwana biyu zata koma ita .

  Alokacin da Hamma Sageer yashiga sashensu bai nufi ko inaba sai bedroom domin dai ya d'auko wannan takarda yaduba abinda yake cikinta ,yana shiga Hussaina ya tarar zaune a gefen gadonsu na alfarma kanta k'unshe cikin mayafi tana y'an koke kokenta ,ya D'an tab'e baki yawuce ya bud'e wardrobe da yaga anshirya kayansa ya zaro wandon da yake tunanin anan ya cusa takardar randa Hamma Sulaiman yabashi ita ,wato wandon da yake jikinsa a ranar kenan ,yana sa hannunsa kuwa yaci karo da ita da azama ya zarota ya maida wandon yazo yak'ara wucewa ta gabanta ko kallon inda take baiyi ba , yana zuwa falon ya tsaya ya warfare takardar yafara karantawa cikin azama da rud'ewar k'wak'walwa .

Takardar ta k’unshi batutuwa da dama fiye da abinda Hussaina tagani a tata takardar ,kamar yadda ta rubutawa Hussaina kudirinta akan ita da Sageer d’in shima haka ta rubuta masa ,ta rok’i alfarmar yaso Hussainanta ya kulamata da ita tayimasa zantuka masu tsananin rauni Wanda rubutasu zaisa masu karatu k’ara zubarda hawaye ????,ak’arshe ta nanata masa tana sonsa sau ba adadi kuma zata mutu da k’aunarsa da tacika k’irjinta babu masaka tsinke ,ta tabbatar masa da cewar batasan yawan adadin k’aunarsa azuciyar ta ba ,itadai kawai tasan tana sonsa da gasken gaske,sannan ta rok’i alfarmar ya tattara duk wani so da yakemata ya mik’ashi ga sisinta ko zata samu salama ta wani b’angare saboda tasan sisinta zata tsinci kanta cikin d’ingimemiyar damuwa da rashin da zatayi na mutane biyu wato Abdurrahman da ita kanta Hassanar ,sannan ta jaddada masa cewar yatuna da alk’awarinsu ko babu ranta afilin duniya kar Yakoma shaye shaye ,kuma yacigaba da girmama Mamma a matsayinta na mahaifiyarsa kuma yak’ara yafewa Mamma d’in akan dukkan abinda yafaru baya,k’arshen takardar ta rubuta ,
bissalam ina k’aunarka matuk’ar k’auna Hamma Sageer

Wani irin kuka me tsananin k’arfi ne ya kufcewa Hamma Sageer ,yafad’i a wajen yana buga kansa ajikin kujera yana faman kiran sweetyn sa ????tamkar mahaukaci haka yadinga bige bige yana zuba ihu da kuka ,abinda ya razana Hussaina tafito da gudu falon Dan ganin meke faruwa sai ta tarar da mijinta cikin tsananin tashin hankali ,kasa k’arasawa tayi gareshi jikinta na tsananin rawa ta jingina da k’ofar bedroom d’in tafashe da kuka itama tana ambatar “innalillahi wa inna ilaihir raji’un ,allahumma ajirni fi musibaty waklifny khairan minha,hasbunallahu wani’imal wakeel ,La haula wala quwata illah billahil aliyul azeem….” Ta dad’e a hakan tana kuka da addu’a zuciyarta nafad’amata Cewar”yau d’aya dai kije ki rarrashi mijinki ,kisama masa kwanciyar hankali ki tarairayeshi ki share masa hawayensa ki rungumeshi ajikinki ….”

Zuciyarta na bugawa haka ta mik’e ta nufeshi tana takawa a hankali yayinda kukansa ke k’ara yawa ,addu’a ce a bakinta yayinda ta tsuguna gefensa ta dafa kafad’arsa cikin kyarmar murya ta ambaci “Hamma Sageer…” Cak kukansa ya tsaya sannan yajuyo a razane yanai mata wani irin kallo ,idanunsa jajawur fuska sharkaf da hawaye ya zaro mata idanu cikin tsananin masifa ya tureta yana fad’in “menene ….!?menene zakizo ki dameni bayan rabon aurenki ya kashemin sweetyna ….kitashi agabana banason ganinki ….nace kitashi ko ….” Yafad’a da hargowa kamar zai cinyeta .

Ta tsorata sosai amma haka ta dake kunsan Hussainar daman jarumace ,kanta a sunkuye amma tad’ago kai ta kalleshi ido cikin ido tace “kayi hak’uri Hamma Sageer bazan iya barinka a wannan halin ba ,nima yau zuwa nayi na aikata umarnin sweetynka ,tace in share maka hawaye aduk sanda ya zubo ,kuma yau zan share makasu kamar yadda kake sharemin” binta da kallo yayi cikin kad’uwar zuciya yana kallon yadda take matsowa da rarrafe zuwa gareshi ,hannayenta masu tsananin taushi tad’ora akan fuskarsa, wani irin lumshe idanu yayi lokacin da yaji saukar halshenta akan fuskarsa tana lasar hawayensa ,ya saki ajiyar zuciya a sanda ya afka k’irjinta yana wani irin nishi da zubda hawaye ,k’ank’ameshi tayi sosai suka rungume juna tanata shafa masa bayansa Dan ta Samar masa da nutsuwa ,haka yayi luf ajikinta yana sauke ajiyar zuciya har bacci yayi nasarar saceshi a jikinta, tunda taji yayi barci sai nata hawayen ya b’alle ,taita kuka kamar bazata bariba tana tausayawa rayuwarsu ak’arshe itama baccin ya saceta tana rungume dashi.


Washe gari Aunty Nafeesa da Adda Nabeela sukaje kasuwar Abuja yin siyayya ,sunata tattaunawa akan zamantakewar su Hamma Sageer da Hussaina yanda zata kasance ,anan Aunty Nafeesa tajawo kunnen Adda Nabeela ta rad’amata mafitar da take ganin idan sukayi amfani da ita toh komai zaizo k’arshe ,sosai Adda Nabeela taji dad’i sukayi farinciki da samun wannan mafita.

 Wani shago suka tsaya suka sayi wani Abu Wanda nima ban San ko menene ba ,sannan suka zarto gida da tarin siyayyar da sukayi ,anan Adda Nabeela ta tarar da Hamma Sulaiman na zaman jiranta Dan su tafi ,sosai suka k'arayiwa Hussaina da Sageer nasiha Wanda shi tun jiya jikinsa a matuk'ar sanyaye yake, tunda Hussaina taga sun shirya take kuka me tada hankali ,da k'er Hamma Sulaiman ya rarrasheta sannan suka tafi suka bar ta cikin kewa da kukan zuciya .

Hamma Sageer ne ya kaisu airport sukayi sallama yajuyo gida kamar Mara lafiya ,abinci ma ranar dukansu da Hamma Sageer d’in da Hussaina duk kasaci sukayi ,da wannan damar Aunty Nafeesa tayi amfani ta dama furar da babangida ya bayar akawowa Hussaina tasaka abinda sukasiyo acikin furar ahad’a ta dama, sai da ta tabbatar taraka Hussaina part d’inta tasata tayi wanka ,ta temaka mata wajan gyara jikinta da turare kala kala ,sannan tabata rigar bacci me D’an kauri tasaka gudun kar tabata Sahara shara tagano shirinta ,falon ta jawota ta kunna mata kallo ,taje ktcheen ta d’auko cup ta tsiyaya mata furar da tayi sanyi sosai ,sannan tabata tace “tunda kink’i cin abinci ga furar da Babangida yakawomiki kisha zakiji dad’inta ” karb’a tayi duk da batason cin komai haka ta kai furar bakinta tadinga kurb’a tana lumshe idanu ,Nafeesa ganin hak’anta yacimma ruwa bata zaunaba saita d’auki kwanon furarta Taiwa Hussaina sallama tanufi sashen Mamma Dan tasan Sageer na can ,
A can kuwa ta iskeshi kansa kan cinyar Mamma sai shagwab’a yakeyi ,Mamma na fama dashi akan yaci abinci shikuma yak’i ,Nafeesa tasan Sageer da jarabar son fura shiyasa ta zauna wajan k’afafunsa tace “k’anina ga fura tashi kasha zakaji dad’inta nice na dama da kaina ” mik’ewa yayi a hankali yana yatsuna fuska ya amshi kwanon dake hannunta bai tsaya jiran cup ba yakafa kai ya shanye furar tas yana lumshe idanu ,yana gama Sha yafara k’ok’arin komawa cinyar Mamma ya kwanta ,da Sauri Mammar ta rik’eshi da fad’in “haba Muhammad ,tashi katafi gurin matarka mana anbarta ita kad’ai fa …” Mik’ewa yayi yana mik’a saboda yadda yaji jikinsa yafara sauyawa yayi musu sallama yafice .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button