HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA .

DAFATAN KUN FAHIMTA MASU TAMBAYA ,NAGODE ????????????????????????

***Kana son me …….!?me kakeso sulaiman ….!?Baba ya tambayeshi bayan yaji shiru bai k’arasa maganar ba .

           Baba kar kaga kamar nadameka nefa .....daman akan maganar sana'ar kane Baba ......so nake ka canza Sana'a Baba .....yanzun Allah ya rufa mana asiri bamu nemi komai mun rasaba .....wallahi banason sana'ar nan Baba .......don Allah a sauya ta ..  

Inji Hamma sulaiman kenan dake magana cikin matuk’ar raunana murya ,wai ko Baban zaiji tausayinsa ya karb’i batunsa …….

Baba ya girgiza kai yana murmushi ,daman yasan tatsuniyar gizo bata wuce ta k’ok’i ,shiyasa yana murmushin ya ambaci sunansa “sulaiman “

    Hamma sulaiman yad'ago ya dubi Baba tare da amsawa ,"na'am Babana ......."

***Kana kunyar ace mahaifinka na saida kayan miya ko sulaiman ………!?inji Baba har lokacin da murmushi a kan fuskar sa .

Ah ah Babana ....Hamma yayi saurin ambata yana girgiza kai ....."ba nufina kenan ba wallahi ......kawai dai naga a kwanakin nan nasamu kud'i a hannuna da yawa ne shiyasa nake k'ok'arin nabaka don kasamu jari me k'arfi na sauya Sana'a .......amma kayi hak'uri Babana nasan nadameka akan maganar ......



   Baba yadafa kafad'ar Hamma sulaiman sannan yace "sulaiman ba inak'in sauya Sana'a bane don wani abun ,ah ah kawai nasaba da itane ,kuma akwai rufin asirin Allah aciki ,hakanan a yadda nafara manyanta ba lallai nasaba da duk wata Sana'a da zan sauya ba .........sulaiman kayi hak'uri kar kaga nak'i amincewa da batunka ....nasan soyayyarka gareni a matsayina na mahaifinka shiyasaka kake ganin dacewar sauya Sana'a ta .....amma a maimakon haka me zaisa kud'ad'en da kasamu ayi amfani dasu ta wata hanyar ......tunda akwai buk'atu da yawa"



   Hamma sulaiman yace " shikenan Baba nagane na fuskanceka ,Allah ya dafa maka akan sana'ar taka ,na hak'ura Baba ......yanzu abinda nake ganin za'ayi shine .....daman zakka ce mahaifin sakeena ya fitar shine yabani kud'ad'e masu yawa da kuma babbar mota .......to ina ganin zanbawa safwan mashin d'ina ....Aminu zai bawa Babangida mashin d'insa...... Kud'in hannuna zanyi amfani dashi gurin siyawa Aminu mota shima .......ya kake gani Baba .....!?hakan yayi .......?



     Tun kan Baba yayi magana sai ganin Aminu yayi yafad'a kan Hamma sulaiman yana wani irin ruk'unk'umeshi da rungumarsa ,fad'i yake "wayyo d'an uwa Rabin jiki ,Wanda yarasa d'an uwa yayi kuka ........yau ni Hamma zai sayawa mota .......wayyo Baba kanaji fa ......wallahi Baba Hammana daban yake da kowa ....."Aminullah murna ta isheshi sai turmushe Hamma yakeyi .

Da k’yar Hamma sulaiman ya kwaci kansa gurin Aminu ,saboda yadda ya rik’eshi gam kamar yakoma cikinsa ,ya rik’emasa wuya gam.

Baba kuwa godiya me tarin yawa yayiwa sulaiman ,yace ” sulaiman ina alfahari da kai ,na tabbatar ko babu raina zaka kula da y’an uwanka …..sulaiman ka gaji me sunanka ,shima haka yake da yawan alkairi …..ba zan manta dashi ba domin yayi min gatan da a rayuwa ko mahaifina sai haka ……shine yabani abokiyar rayuwar da tazamemin sanyin idaniya …..gashi ta haifamini Ku kunzame min abin gani naji dad’i …….Allah ya jik’ansa da Rahama .

A hankali Hamma sulaiman ya amsa da “Amin ,”yayin da tuni Hamma Aminu ya shige d’akin Umma inda take zaune da sauran ahalin gidan tana karb’an haddarsu ta alk’ur’ani ,da hanzari ya k’arasa gaban Umma ya tsuguna bakinsa dai dai saitin kunnenta yana labarta mata abinda ya faru ……ganin Umma na murmushi yasa HUSSAINA tace “Hamma Aminu gaskiya bamu yadda ba …..babu kyau yin rad’a fa …..tun da naga Umma na murmushi to nasan abin dad’i ne yasamu …..pls Hamma muma Abamu musha ……

Hamma Aminu yana dariya ya mik’o hannunsa yana cewa ” bani goro inbaki albishir k’anwata “…….HUSSAINA tayi duru duru tarasa me zata bashi ……can tace ” wallahi Hamma nabaka autan Umma kayi yadda kakeso dashi …..shine goranka …….

Wata irin dariya Babangida ya kwashe da ita yana rufe baki ,duk suka bishi da kallo ,yana dariyar yake cewa “Amma Hamma Aminu baka dace da goro ba ,a rasa me za’a baka sai kayan kashi …….!?wallahi babu abinda Usman zai maka idan ba yacikawa Aunty Sadiya Masai ba “

Sosai suka kama dariya banda Usman da ya matsa jikin Umma yana kwanciya kan kafad’arta ,cikin shagwab’a yace “ummana kinji Yaya Babangida ko ……!?wai nine kayan kashi …..!?Umma tace ” rabu dashi autana shima ai yanayi …..to ai duk Wanda bayayin wannan abun ma ai bashida cikakkiyar lafiya “Hassana na dariya tace ” Allah Umman mu shidai autanki nasa yafi nakowa ,kamar fara yake gurin yin bayan gida …..”

         Au yau har dake akewa autana tsiya ....!?inji Umma kenan tana Shafa kan Usman .....

Hamma Aminu ne yake gaya musu abinda ke faruwa ,da abinda suka tattauna shi da Hamma sulaiman da Baba .

Gaba d’ayansu suka mik’e da murna suna hamdala ,Babangida kamar ya kifa Dan murnar zai mallaki mashin ,suka fito daga d’akin zuwa gurinsu Baba ………suna zuwa duk suka tsuguna gaban Baba da Hamma sulaiman ….safwan ya zagaya bayan Hamma ya sak’alo hannunsa ta wuyansa ya rungumeshi ,yayinda Babangida ya rungume Hamman ta gaba ,suka sa Hamma a tsakiya suka wani matseshi waisu murna …

Da k’aramar murya Hamma yake cewa “wai Ku karyani zakuyi ne …..!?Aminu yagama tumurmusheni kuma kunzo kun d’ora ……?nidai Allah Ku d’agani murnar ta isa haka ” da k’yar suka cikashi sunata murna ,Babangida fad’i yake “wato zan kankaro wulak’anci a unguwar nan ….da gayya zan dinga hawa mashin d’ina ina tadawa samarin layin nan k’ura ……

 Umma tace " subhanallah ..!au burinka kenan Babangida ....!?zansa a fasa baka fa ..."kamar an wuntsuloshi gaban Umma sai gashi gabanta Yakama kunne yana fad'in "haba Umma ,haba Umman mu ....wasane fa ....Allah ba gaske bane Umma ......idan naga samu naga rashi ai nakad'e har ganye na " yawani langab'e da cilla hanaye yana kwatanta yadda zai kad'e d'in .

Suka tuntsure da dariya ,Usman harda rik’e ciki .

Hussaina ta dubi Hamma tana Sosa k’eya tace “Abban sadauki mu to meye namu kason….. !?Naga anata rabo banji sunanmu ba nida Rabin raina …..” Usman yayi wuf yace “nima Hamma banji nawa ba “

Allah Hamma ka k’yale yarinyar nan ….Dan wani iyayi tanaso ta wanke ka harda cewa Abban sadauki …..to ai da bakya kiransa haka …..da Hamma bakinki ya saba …..”inji safwan kenan yana hararar Hussaina .

Hamma sulaiman yayi murmushi yace “ah ah safwan barta …zan iya da ita ai ……me kike so …..!?Hamma ya tambayi Hussaina yana kallonta .

Saida ta matso jikinsa sosai sannan takama hannunsa d’aya ta rik’e tace ” Hamma kasiya mana babbar waya mana …….nagaji da rik’e k’arama wallahi …k’awayenmu duk sunada babbar harka ……kum …tun kan ta k’arasa Umma ta katse maganar da cewa “ah ah ban amince asiya muku waya babba ba saboda lalacewar zamani ,kudai fad’i wani abun .

Hamma Aminu ne yatari zancen da cewa ” hakane Umma ,amma wani hanzari ba gudu ba ,akwai yara da yawa da waya bata lalatasu ba ,sunyi amfani da ita wajen tsare mutuncinsu ,kuma Umma na yadda da yaran nan ,nasan hankalinsu da tarbiyyarsu bazata saka su kauce hanya Dan anbasu waya ba ….zamani ne yazo da hakan wani abun yanzu tilas saida babbar waya ,kinga Adda Nabeela tuni taso siya musu kika hana …Dan Allah Umma kibari Asiya musu insha Allah ba matsala kuma za’a dinga bibiyar lamarin wayar aga Yaya suke sarrafata da amfani da ita “

Bayanin Aminu yasa Umma ta amince ,nan Hamma sulaiman yace zai siya musu ,shikuma autan Umma akace za’a siya masa keke ….Aikuwa yaita murna .

Sosai Hassana da Hussaina ke murna ,Har saida Hassana ta furta abinda ke zuciyarta tace “kanada kirki Hamman mu “

Hamma sulaiman baicika dariya ba sai dai murmushi ,amma maganar Hassana tabashi dariya ,shiyasa yakamo hancinta yarik’e yaja yace “duk kirkina ai ban kai ki ba …….Baba ai Hassana tafini kirki ko…..!?ya juya yana tambayar Baban da tund’azu yayi shiru yana sauraren iyalin nasa suna shaftarsu.

     Baba yayi murmushi yace " ba don kar duniya taga nayi ba daidai ba da sai nace kaf yarana masu kirki ne ,to sai dai kar duniyar taga na soku ita kuma ta k'iku ,kun San ance kaso naka duniya tak'ishi ,kak'i naka duniya taso shi "

Dukansu sukayi dariya jin maganar Baban nasu, har da Umma da take fad’in “Malam kenan”


              Ranar juma'a da misalin k'arfe 12:00am muka kammala shirinmu tsaf domin tafiya gidan Hamma sulaiman ,autan Umma yace zai bimu ,sisina tace "wato Dan muje Ku had'u kaida sadauki kucika mana kunne da ball ko ...?

Yace ” ah ah Adda Hussaina bazamu dameku bafa “tace ” to maza jeka ka sauya kayan jikinka ,da gudunsa yayi waje Dan zuwa sauya kaya “

Bayan ya sauya yafito ,muma muka fito cikin shigar atamfarmu me kyau wadda Hamma sulaiman ya d’inka mana da sallah ,na d’auko mana hijab da nik’ab d’inmu sai sisina ta fizge ta mayar tana cewa “in zamu Makaranta kice sai mun rufe fuska ,yanzu ma gidan Hamman sai mun saka nik’ab kenan…..!?ah ah wallahi ai Allah ma baice a rufe fuska ba ,fuskokinmu basa cikin al’aurarmu Rabin raina……. Kuma gaskiya niyau gyale nake sha’awar sakawa ma gabad’aya …..nagaji da hijab d’in .

Hassana tilas ta hak’ura da saka hijab da nik’ab ,sisinta ta d’akko musu mayafai masu yalwa kalar atamfarsu ,suka yane jikinsu dashi tsab ba tare da bayyana jiki ba ,kwalliyar su tayi kyau sosai ta yadda bazaka tab’a bambamce suba, saboda hatta yarin kunnensu iri d’ayane .

Umma tabasu kayan miya da manshanu da zasu kaiwa Aunty sakeena ,sukai mata sallama don tafiya ,tabasu kud’in napep da zasu hau ,su Hamma a unguwar Arawa suke da zama shida Hamma Aminu ,gidajensu basuda nisa da juna.

          Suna tafe ajere yayinda Usman ke gaba rik'eda ledar sak'on Aunty sakeena a hannunsa zasu isa titi Dan samun me napep ,sun iso dab da gidan Nafeesa Hassana nata kallon gidan ko zatayi katari da ganin sageer ......ilai kuwa suna zuwa dai dai get d'in gidan sukaga anturo k'ofar da k'arfi an bud'eta har saida suka firgita .

Sageer ne yafito daga gidan ,dagashi sai wata Riga Mara hannu da wando tiri quater a jikinsa ,inda hakan ya bayyana zatin surarsa me tsananin kyau da haiba …..gashin kansa kwance lub lub irinna fulanin asali ,ga wata irin gira da Allah ya zanamasa cikakkiya tamkar ta mata ,idanunsa dukansu a shanye suke ….duk da Hussaina tace shaye shaye ne ya maidasu haka ????.

Wata mata dattijuwa ce ke biye dashi ,wadda tsananin gayu da kwalliyar jikinta da kyau ya b’oye yawan shekarunta ,sai Nafeesa a bayanta suna biye dashi ,matar nata faman rik’o hannunsa yana faman fizgewa da cin magani ……cewa take “Muhammad pls ka tsaya ka saurareni ….Dan Allah Muhammad ka tsaya …..kaji tausayi na mana …..ina kakeso nasaka kaina Muhammad …..!?Dan Allah ka tsaya muyi magana nagaji da fushin da kake min …….Nafeesa rik’o minshi karki barshi ya fice Dan Allah ……ganin zai tsere musu yasaka matar nan d’aga murya tana nunawa su Hassana shi fad’i take ” y’an mata don Allah Ku taremin shi ,karku barshi ya wuce ….pls Ku taimaka min …..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button