HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

       Mamma tasa hannaye ta rufewa Sageer bakinsa da ke sake tana dariya tace "duk mamakin ne yasaka sakin baki haka ...!?to kwantar da hankalinka alk'awari na farko ya ruguje ,kayi murna zaka cika alk'awari na biyu ......" Tana fad'in hakan ta nufi k'ofar fita daga part d'in ....

Cikin tsananin shauk’in k’aunar mahaifiyarsa ya runtse idanu ya furta da k’arfin sauti Dan tajiyo shi yace “I love you Mammahhhhhhhhh……”

“Bata juyo ba ta amsa masa da ” mee to my Muhammad Sageer ,Allah yayi maka albarka ….”

Yafad’a kan kujeran wani farinciki na ratsashi yace “Ameen Mammana…..


Da daddaren da Hamma Sageer yazo wajen Hassana ya gayamata komai ,tayi farinciki matuk’a saboda itama bason zuwa Abujan take ba kawai dai tanason tayashi suyiwa Mamma biyayya ne ,Alokacin ne kuma ya marairaice yana bata hak’uri akan abinda yayi mata d’azu ,sai dai ya jaddada mata cewar yanada tsananin kishi akanta ,da da yadda zaiyi da ya makantar da maza saboda karsu kallemishi ita,yace mata d’azun yaji tamkar ya mutu saboda yadda yaga tanaiwa wani namiji murmushi da kyakkyawar fuskarta .

Itama da sanyin muryarta tak’ara hak’urk’urtar dashi da fad’amasa matsayin Wanda ya gansu tare d’azun ,ta gayamasa irin taimakon da Malam Huzaifan yayi musu musamman ta b’angare karatunsu ,abinda bata fad’amasa ba shine tsananin son da Malam Huzaifan ya Nuna mata duk da itan bata soshi ba ,amma tasan muddin tafad’amasa kishi zai iya sawa Hamma Sageer ya mareta ma ,amma duk da hakan yaji kishin yadda take yabon Malam Huzaifan musamman da ta nuna masa abubuwan da yakawo a matsayin gudummawarsa ,sosai ya fitittike akan shidai bai yadda a rabawa mutane wata kalanda me d’auke da hoton matarsa ba ,bai San iya adadin mazan da zasu kalla ba a cuceshi ,zuba masa ido kawai tayi tana kallon yadda yake rigima hannunta dafe da hab’arta ,da k’yar tayi magana tace “Hamma Sageer mata fa zamu rabawa ba maza ba …” Ya girgiza kai fuska a d’aure yana duban kalandar yace “na rantse nidai ban amince ba ,wallahi tallahi babu Wanda za’a bawa wannan abar …” Dariya takeso tayi ganin yadda yaketa balok’ok’o amma ta kunsheta tace “har da saurin rantsuwa kayi fa ….” Ya d’ago ya lashi lips d’insa yanai mata wani irin duba tamkar ya had’iyeta yace “Dan kisan bazanji kowane rok’o da zakimin akan hakan bane ,
Toh ya za’ayi da ita kenan ….!?ta ambata tana d’auke kanta daga gareshi .

Saida ya kuma lalubo idanunta yasa nasa cikin nata sannan yace ” badan kar nayi almubazzaranci ba k’onasu zanyi ,amma yanzu wannan abar zata zama mallakinmu ne kawai nida Abdurrahman ,zansa almakashi na datsasu gida biyu ya d’auki fuskar matarsa nima na d’auki fuskar matata……

Ajiyar zuciya ta sauke tana murmushi tace “duk yadda kayi zai dai ne Hamma Sageer ,
Sosai ya matso kusa da ita kamar zai had’e jikinsu ya sanyaya murya yace ” kiyi hak’uri idan na b’ata miki rai sweety ,inada tsananin Kishinev a kanki …..

K’amshin jikinsa ya mamayeta gabad’aya tare da matsananinciyar k’aunarsa ,kallon da yake mata yanaso ya kassara gab’ob’inta shiyasa tayi k’asa da kai murya na rawa tace “zuciya ta bata ganin laifin Abokin rayuwarta, a kullum k’ara aminta take dashi da k’addarawa ba za’a samu masoyi irinsa a fad’in duniya ba …….

Ya lumshe idanu jikinsa na wata irin rawa tamkar ya fizgota jikinsa yakeji ,shauk’in so na d’ibansa yace ” wannan rana tayi mini nisa ,don Allah ki gaggauta zuwa ko nasamu na nunawa Sweetyna d’ingimemiyar soyayya ta da godiyata abisa tukuicin biyayyarta a gareni …….


Babu Wanda yakai Hussaina farincikin jin rabin ranta ba zata Abuja ba ,tayi tsalle tayi rawa tayi juyi ta fad’a jikin Ya Safwan da ke dab da ita ta k’ank’ameshi tana tsalle da k’yar ya k’waci kansa yana mitar ta yamutsa masa shaddarsa da tasha karin guga ,ta nufi Babangida da niyyar rungumeshi Dan murna ya kauce yana Nuna mata farcensa yana dariya yace “na rantse bazaki wujijjigani ki taramin gajiya ba ,kina matsowa zan gallara miki mintsini me Shiga k’wak’walwa Dan natara farce,jin abinda yace ta kauce ta nufi Hamma Sulaiman ,harara kawai ya zubamata ta kauce ta tsaya tayi cirko cirko ,Hassana ce tabud’e hannayenta da fad’in ” tunda kowa yak’i tarbanki tawo na rungumeki sisina…..daman nice mahad’inki tunda tun a cikin Umma muke tare ….”

Da gudu Hussaina tatawo tafad’a jikin Hassana suka k’ank’ame junansu suna dariya .

Hamma Sulaiman ya tab’e bakinsa yana duban ummansu da fad’in “wad’annan yaran k’ila sai sunyi auren zasu daina shashanci ……

       Hussaina sosai tashiga walwala da k'ara karrama Hamma Sageer a zuciyarta ,tayi masa godiya mai tarin yawa kamar zata ari baki,shikuwa dariya yakemata kawai.

Aunty Sakeena ce ta kaisu gurin k’unshi da saloon akayi musu gyara na musamman ,Sageer da Abdurrahman tamkar su zauce ganin yadda amaren su sukayi tsananin kyau da had’uwa .

A gidan Adda Nabeela sukayi kamu da walima saboda harabar gidan Nada girma sosai ,fad’ar had’uwar amaren b’ata bakine ,komai ya k’ayatar akayi lafiya aka gama lafiya cike da farinciki ,
Basu tsara cewar angwaye zasu zo ba amma saida sukazo saboda baza su iya nisa da amarensu ba ,Hussaina dai shagalinta kawai takesha tunda komai ya warware mata ,yayinda Hassana sai a lokacin tsoran Hamma Sageer ke shigarta ganin rawar k’afar da yakeyi da zumud’i baya barin kallonta ko na Minti d’aya in suna tare……

Washegari Aunty Nafeesa ta shirya musu had’ad’d’iyar dinner a COSTODIAN HOTEL da misalin k’arfe takwas na dare……………..”

Comment
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍


TYPING????

???????? HASSANA ????????

            *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page7⃣7⃣to7⃣8⃣

WATTPAD:hassana3329

® PEN : WRITERS ASSOCIATION


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

TUNASARWA????

MANZON ALLAH (S A W) YACE “MUTUM YAYI ZINA DA MATA GOMA SHI YAFI SAUK’I GARESHI AKAN YAYI ZINA DA MATAR MAK’WABCINSA ,HAKA NAN YIN SATA A GIDAJE GOMA SHI YAFI SAUK’I DAGA SATA A GIDAN MAK’WABCI

AIKI ME FALALA????

MANZON ALLAH (S A W ) YACE ” IDAN MACE TA SALLACI SALLOLINTA BIYAR ,KUMA TA AZUMCI WATAN RAMADAN ,KUMA TA TSARE FARJINTA ,KUMA TAYIWA MIJINTA BIYAYYA ,TO SAI ACE MATA :KISHIGA ALJANNA TA KO WACE K’OFA KIKAGA DAMA ,AWANI HADISIN KUMA :”DUK MACEN DA TA MUTU MIJINTA YANA MAI YARDA DA ITA ,TO ZATA SHIGA ALJANNA

SADAUKARWA GA :

MASOYIYATA ,ABAR K’AUNATA ,JININ JIKINA ,Y’AR UWATA DA BAN DA KAMARTA A FAD’IN DUNIYA WATO HUSSAINA D’AN LARABAWA ,BAKINA YAYI KAD’AN WAJEN FURTA MIKI KALAMAN YABO SISINA , KI K’ARA SAWA A ZUCIYARKI HASSANARKI NA SONKI MATUK’AR SO ,WANNAN SHAFIN DUKANSA NAKINE KIYI YADDA KIKESO DASHI ????????IN KINGA DAMA ZAKI IYA SANWA HANAN TSIGALA????????????????

misalin k’arfe takwas na Daren ranar asabar d’in harabar hotel d’in COSTODIAN HOTEL cike take da zafafan motoci masu kyau da d’aukar ido ,manyan mata k’awayen Aunty Nafeesa da Adda Nabeela da Aunty sakeena duk sun hallara a gurin dinner d’in y’an biyu kyautar Allah , tuni hall d’in yacika da mutane sai kid’a me dad’i ne yake tashi ,kowa kagani ya k’ure adakarsa wajen kwaliyya da d’aukar ado ,babu wad’anda ake zaman jira sai am are da angwaye .

     Can gida kuwa Hassana ce durk'ushe gaban Hamma Sulaiman fuskarta babu walwala duk da tsananin kyawun da tayi, kwalliya tagani tafad'a a yaba akayi musu cikin wasu irin kaya Wanda bazaka tab'a banbance lace ne ko material ba ,har gida Aunty Sadiya ta d'auko me kwalliyar aka rangad'a musu ,tuni Hussaina tana tare da angonta a waje Hamma Aminu zai jasu a motarsa da amsad d'insa kusa dashi , sai Hamma Sageer da ke gefe a tsaye yana duba had'ad'd'en agogon dake d'aure a hannunsa ganin har takwas da rabi nadare tayi amma Sweetynsa tak'i fitowa ,in kaga Hamma Sageer da ya Abdurrahman sai kaji kamar ka sacesu ka gudu Dan kyawun da sukayi ,kayansu iri d'aya komai nasu iri d'aya ,kamar yadda amaren ma ba'a bambantasu a komai ba ,

Hamma Sulaiman ne yakuma d’ago kansa yadubi Hassana yace “bakisan kina b’ata musu lokaci bane kika barsu a waje …!?kitashi kutafi mana …” Ta kuma marairaicewa tana rik’o hannunsa tace “don Allah Hammana kazo mutafi ,bazamuji dad’i ba ace bikinmu guda baka halarci wajen ba ,ga Hamma Aminu canfa shinema zai tuk’a su Ya Abdurrahman …”

Ya D’an karkata kai yana gyarawa k’aramar y’arsa Maryam kwanciya akan cinyansa wadda bata jima da fara bacci ba ,yace “kibar batun Aminu shi wannan daman dagashi har matarsa y’an bidi’a ne ,nikuwa ko banjeba sakeenan Sulaiman zata wakilceni …..” Ganin tanata fama dashi yak’i yarda tafara matso hawaye tana k’ok’arin cire gwargwaron kanta tana cewa “nima nafasa zuwa Hamma tunda bazaka ba ,aje agayawa Hamma Sageer suyi tafiyarsu kawai nafasa zuwa …” Da sauri ya rik’e hannunta da take k’ok’arin tumb’uke d’aurin kanta ya k’ank’ance idanu yana fad’in “ke ,wannan kwalliyar banaji ance kud’i me yawa ake biya ayi ba ?shine zaki b’ata abarki tun kafin kije gun … .!
Ta kyab’e baki cikin shagwab’a tace ” ai nafasa zuwa tunda bazaka ba …”hararanta yayi ya d’auke Maryam daga jikinsa yana mik’awa Umma ita, ya suri makullin motarsa yana cewa “Umma in banjeba yarinyar nan bazata k’yaleni ba ,gabad’aya ta koyi rigima irinna Y’ar uwarta ….mtswww ,ya D’an ja k’aramin tsaki ,
Dariya Umma tayi tana kwantar da Maryam kusa da zuhuriyya d’iyar Hamma Aminu ,tace” ai gara kaje d’in tunda sun damu da zuwan “cikin murna Hassana tamik’e tana murmushi tace” kumafa ummanmu Hamma Sulaiman shi na rubuta a matsayin babbar k’awata ,in ana Neman babbar k’awata a gurin shi za’a kirawo ,
Komawa yayi yana Neman gurin zama da fad’in “kinma rainamin hankali …yaseen kama gabanki nafasa zuwa ” da wani irin sauri ta rik’oshi tana dariya da fad’in “yi Hak’uri Hammanmu na rantse wasa nakeyi ” kad’a kai yayi yana nuna mata hanya yace “wuce mujeto ….”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button