HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tunda sadauki ya d’auki yaran yak’ura musu idanu yahana kowa d’auka ,har Sageer yakula dashi yayi murmushi yace”meyasa kaketa kallonsu haka …!?sai yayi murmushi idonsa akan macen yace”ina son su uncle Sageer”wani murmushi Sageer d’in yayi yace”dole kaso babanka da matarka ai….”kowa yabishi da kallo basu gane maganarba ,sai yayi nuni ga namijin yace”wannan Hamma Sulaiman ne”ya Nuna macen yace “wannan kuma Umma ce”
Kawai sai sadauki ya kuma rungume macen ya kalli Hassana yace”Aunty Hassana nidai inason fad’ima ….kibani ita na aureta idan na girma….”kowa yayi mamakin maganarsa sunata dariya ,Hassana ce tace “daman tun can fad’ima mallakin Abubakar ce….Dan haka ko bayan raina nabaka ita sadauki” sosai yadinga murna yana rik’e da babyn a hannunsa .
Shikuwa Hamma Sulaiman Hussaina ya kalla yace “tunda Y’ar uwarki ta haifi Sulaiman kawai kema kiyi k’ok’ari ki haifo sakeenan Sulaiman ….in ba hakaba hukuncin ki yana wajen Babangida mintsini talatin sau talatin zansa yayi miki …” Kowa ya kama dariya Hussaina na rik’o hannunsa tana dariya tace”menene tukuicina idan na haifi sakeenan Sulaiman ….!?ya kwace hannunsa yana dariya yace”daga gani so kike ki k’wak’uleni wani abun…to nak’i wayon….!? Takuma dariya tace “umara zaka kuma biyamin Hamma Sulaiman d’ina ,idan na haihu sai na tafi” ya mik’e yana cewa “ahaf ai nasani ,kinyi kad’an kidaki hancina Yarinya ,mijinki yafini kud’i yanzu ya biya miki.

Sai dare sannan Hassana tasamu sukunin tambayar Sageer menene dalilinsa nasawa yaran Sulaiman da fad’ima….!?

Ya rungumeta jikinsa yana shak’ar k’amshin jikinta yace” saboda nasan bakida buri illa ki haifi namiji kisa masa Sulaiman,fad’ima kuma nasane saboda it’s ta haifamin ke har nasamu nasarar aurenki …..”

Ta k’ura masa idanu tanajin sonsa na katantanwa da ita, shikuma hankalinsa nakan baby’s d’in yana shafa Kansu ,yad’ago yaga kallon da take masa sai ya hire idanunta yace “wannan kallonfa …!?
” meyasa bakasa sunan Mamma ba ?abinda ta ambata kenan …!
Ya sumbaceta yace “inda rai da lafiya ina fatan wata shekarar ki haifo Mamma d’in ….” Ta zaro idanu tana janye jikinta daga nasa Dan ji tayi tamkar wani cikin zai d’irka mata a lokacin ,ya k’yalk’yale da dariya yabita ya rungumeta ya kwantar da Kansa k’irjinta hawaye naciko idanuwansa ,cikin murya me dad’i yace “kece fitilar da ta haskaka rayuwata alokacin da rayuwar tawa tafad’a cikin duhu da barazana ,a kullum zuciya ta tana wayar gari da sababbin so da k’aunarki …..na rantse da Wanda raina da numfashina ke hannunsa ina sonki Sweety na….”
“Nima ina sonka Hamma Sageer ,bayan mahaifina Kaine mutum na farko da banda kamarsa a rayuwata” tafad’a Rana k’ara shigewa jikinsa itama har idanunta sun fara hawayen k’auna.


Kwana biyu da haihuwar Hassana itama Hussaina ta haifi zankad’a zankad’an yaranta biyu duk maza, farinciki Yakuma cika iyalan da zuri’ar ,sai aka had’a sunan gabad’aya akayi k’ayatacciyar walima me ban sha’awa da burgewa ,
Hamma Sulaiman kuwa har rank’washin Hussaina yayi wai bata Haifa masa sakeena ba …..yaran sukaci sunan Baba da Aliyu mahaifin ya Abdurrahman,
Tuni soyayya ta k’ullu tsakanin Malam Huzaifa da Asma’u ,Ya safwan da Zahra ,anata shirye shiryen biki.

Haka rayuwar wad’annan bayin Allah tacigaba da samun d’aukaka da zaman lafiya da juna ,tare da samun k’aruwa ta hanyar haife haifen da ake tayi………….!

K’ARSHEN WANNAN LITTAFI KENAN NA HASSANA DA HUSSAINA,INA ROK’ON UBANGIJI SARKIN SARAKUNA YA YAFEMIN KURA KURAN CIKI ,SANNAN YABANI LADAN FAD’AKARWAR DA KE CIKI,ALLAH YABAMU LAFIYA DA ZAMAN LAFIYA A RAYUWAR MU,NASO LITTAFIN YAFI HAKA YAWA AMMA ABUBUWA SUNYI MIN YAWA SHIYASA NA TAK’AITASHI A HAKA,ZANYI KEWARKU MASOYANA KAMAR YADDA NAYI LOKACIN DA NA KAMMALA SANADIN HOTO,SANNAN INA MAI SANARDAKU CEWA ACIKIN ABUBUWA UKU ZAN AIKATA ABU GUDA D’AYA DA IZININ ALLAH ,KODAI NADENA RUBUTU GABAD’AYA SABODA YADDA DUNIYAR MARUBUTAN TA CAKUD’E,KO KUMA ZAKU DAD’E BAKU SAKE JINA A DUNIYAR RUBUTU BA,KO KUMA LITTAFINA NAGABA ZAI KASANCE NA KUD’I AMMA BAZAN TSAWWALA BA ZANYI YADDA KOWA ZAI IYA BIYA YA KARANTA,DOMIN LABARIN DA ZANYI INAI MUKU ALBISHIR DA CEWA ZAIFI SANADIN HOTO DA HASSANA DA HUSSAINA DAD’I DA FAD’AKARWA,SAI NAJI RA’AYINKU AKAN HAKAN MASOYANA ,ALLAH YABARMU TARE DANI DAKU ,NAGODE AKAN FATAN ALKAIRI DA ADDU’A DA NAKE SAMU DAGA GAREKU,HASSANA D’AN LARABAWA NA GAIDAKU ADUK INDA KUKE????????????????????????

Comment
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46

Leave a Reply

Back to top button