HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

 Toh fa ganin nasamu dukiya said harka ta bud'e nazama babbar Y'ar kasuwa wadda batadamu da mijinta ko yaranta ba ....banida lokacin mijina balle na yarana ,kullum INA yawon bin kasashen duniya Dan na bunk'asa business d'ina ....wani zubin ne nake kulawa da sageer saboda son da nake masa...yaro kyakkyawa me hak'uri da kamala ,sai dai damam sageer tun yana yaro miskili ne sosai ko magana bats dameshi bama ....Makaranta ta y'ay'an masu kud'i ko k'usoshin gwamnati ita nasa Nafeesa da sageer tun daga nursery har zuwa secondary me suna (matrix international school).

Har sanda yarana suka girma bandena halaye na ba saima abinda ya k’aru ….ba k’aramin hak’uri mustafa keyi daniba ….ko agaban y’ay’ansa idan naso cin mutuncinsa nakeyi ba ruwana ,wataran yana kuka suna tayashi ,said naga sageer na kuka hankali na yake tashi sannan ,saboda banason damuwar sageer ko kad’an …. A lokacin da sageer ya shiga babbar jami’ar garin nan wato Gombe state university (G S U ) Na aurar da Nafeesa ga wani babban lawyer …inda yatafi da ita k’asar waje domin harkarsa ta shari’a ….a can suka zauna kafin ya kammala komai suka dawo k’asar nan ,suka tare a gidansu dake nan unguwar .

Sageer bayajin dad’in abinda nakewa mahaifinsu ….kullum zaka sameshi cikin tunani da rashin walwala ,tausayin mahaifinsa na damunsa ,wani zubin daddy d’in nasa ke bashi haushi ma ganin yadda yake rawar jiki a kaina ….yawan bak’incikin da mustafa ke shak’a a kaina ya haifar masa da ciwon zuciya me tsanani …amma duk da hakan mustafa sona yakeyi bayason b’acin raina ko kad’an ….ganin hakan yasa sageer yafara tsanar mata ,yana ganin ai duk mata haka suke gallazawa maza ….ga sageer da bala’in farinjini gun y’ammata hard a samari ma ….kodan kyakkyawar surar da Allah yabashi …kallon sageer kad’ai na susuta zuciyar y’ammata.

Tafiye tafiye na ya k'aru ,sai nayi wata uku bana gari ,ban damu in zauna da mustafa ba ,a lokacin shi kuma mustafa bashida buri sai yaganni kusa dashi ...nikuma nak'i yard da hakan ko bai saniba tafiya nake na barshi ...sageer yasha  yimin kuka da magiyar  indena wulak'anta mahaifinsa ...nakan bashi hak'uri da alk'awarin denawa amma kuma na kasa dainawar .

Wata mummunar rana da bazan manta da itaba wadda ta kasance itace silar fad’awar sageer wannan halin ….ranar da nayi nadamar munanan halayen da nake aikatawa….ranar da tazamemin bak’ar rana ….ranar da nasan Ashe inason mustafa da gaske ….

Nayi tafiya tsawon wata Biyar ban dawoba ….ran da nadawo na tarar duk mustafa ya rame Ashe yasha cuta bananan …sageer ne yake kulawa dashi …kwana biyu da dawowata ina zaune a falo ina kallo mustafa yashigo ,yazo ya zauna gefena ya k’uramin idanunsa yanata kallona kamar ya lasheni Dan so ,Yakama hannuna yarik’e yace “don Allah my lubna kidena tafiya kina dad’ewa haka kina barinmu ,wallahi muna buk’atarki a kusa damu nida sageer …ki daure kid’an dinga bamu lokacinki ko yayane kinji my lubna ….”

Wannan magana da mustafa yayi kawai sainaji raina yab’aci ,a kanme zaice na zauna nadena tafiye tafiye na ,aikuwa a harzuk’e natashi nakamai masa masifa da bala’i ….lokacin sageer yazo zai shigo falon yaji ruwan masifar da nakewa mahaifinsa sai ya kasa shigowa …ya tsaya a cikin corridor yana sauraren muryata dake tashi da hargowa ….runtse idanunsa yayi hawaye na kwararowa kamar anbud’e fanfo.

Cikin masifa nake fad’in “yanzu kai har kayi kaurin wuyan da zakazao ka tareni da cewar indena barinka gida ina tafiya ta …..da sunan wai kana buk’ata ta kusa da kai ….!?na rantse mustafa kama gama rainamin hankali da yawa …..toh me kake nufi ….kana nufin kafara hajiya da nine ko kuwa …!?

   Da sauri shima mustafa ya mik'e jikinsa na rawa yana k'ok'arin kamoni jikinsa ,nayi maza na kufce inai masa wani mugun kallo Dan alokacin jinayi kwata kwata yafice min a rai kawai ,wani haushinsa nakeji shed'an nayi min zuga a kunnena ......banji tausayinsa ba duk da uban kukan da yakemin ganin irin b'acin ran da yasani ...ganin nak'i amincewa ya kamani yasa ya durk'ushe a k'asa ya kama k'afafuna yana kuka yana cewa " kiyu hak'uri lubna na ba nufina kenan ba ...don Allah kiyi hak'uri bazan kuma furtawa ba tunda bakyaso ko da kuwa shekara biyu zakiyi baki dawoba ....daman sageer nafi tausayawa ganin yanason ya dinga ganinki ko yaushe amma baya samun hakan ....wani zubin haka kawai zai zauna yaita tunani sai dai kiga yana hawaye ....amma koyi hak'uri zan dinga k'ok'arin d'aukemasa kewar rashinki idan bakya nan duk da yaci ace yasaba da hakan tunda ya girma .....amma kuma hakan bai samu ba ganin cewar k'ulafucin uwa daban yake a gun yaranta ....kidena furta cewar nagaji dake ...wallahi lubna na ina sonki ...kuma ko da zan guji kowa a duniya bazan iya rabuwa dake ba ...idan narabu dake zan iya mutuwa saboda tsananin sonki da ke tafarfasa k'irjina ....."

Wata irin hamb’arewa nayi masa da k’afata da yake rik’e da ita…. A fusace nabud’e baki nace “Ashe kuwa zaka mutun Dan wallahi a yau kuma a yanzunnan saika SAKENI nagaji da kai mustafa bana son k’ara zama da kai ko na minti d’aya ….” Wayyo gigitar da mustafa yayi jin kalamaina bashida misali ….sosai k’irjinsa ke tsananin bugawa tamkar ya fad’o k’asa ….idanuwansa k’ok’arin k’ak’k’afewa sukeyi Dan razanar jin kalamaina …wata irin hajijiya ke kwasarsa duk da yana durk’ushe a k’asa …..ya kasa magana hannunsa dafe da saitin zuciyar sa yana wani irin kuka …..takowa nayi har gabansa na tsuguna dab dashi na ambaci sunansa da kakkausar murya “mustafa” ya kuma d’aga idanuwansa da suka jujjuye tsabar shiga tashin hankali ya dubeni hawaye duk ya b’ata masa fuska ….nace “so nake mustafa ka sakeni yanzun nan ” ya girgizamin kai yana nunamin zuciyarsa da k’yar yake magana yace “bazan iyaba ….zuciya ta zata fashe idan na aikata haka….” Ban San lokacin da naci kwalarsa ba ina zazzaro ido ina jijjigashi nace “wallahi mustafa ko bindiga zuciyar ka zatayi yau saika sakeni ….bana Sonka ni yanzu na tsaneka mustafa ….ka sakeni nace maka …..ban auneba sai ganin mustafa nayi yana wata irin makyarkyata ….nasaki kwalar sa a hankali nima jikin nawa na mugun rawa saboda masifar da ke cina ….ina sakinsa na mik’e tsaye …shikuma idanuwansa suka cigaba da k’afewa …hannunsa akan k’irjinsa yana k’ok’arin fizgo numfashi amma yayi masa wahala …duk da haka idanuwan mustafa na kaina yana wani irin dubana….a k’arshe sai numfashin ma ya d’auke gabad’aya ….zuciyarsa ta buga ….yafad’i kwance a k’asa Tim babu rai a tare da shi .

K’arar fad’uwar sa tasa sageer da ke lab’e yanajin duk abinda ke faruwa yashigo da wani irin gudu ….ina k’ok’arin tsugunawa gaban mustafa amma sageer har ya rigani …ya d’ago mahaifinsa ya rungume a jikinsa yana Koran sunansa yana kuka ….ganin ko motsi bayayi sai hankalinsa yayi masifar tashi ya tabbatar zuciyar mahaifinsa tabuga ya mutu….sageer ya d’ago kyawawan idanunsa yayimin wani kallo me cike da tsantsar tsana da fushi …idanunsa a jujjuye …yayinda nikuma gabad’aya jikina yayi sanyi tuni nima hawayen ya wanken fuskata kallon mustafa nake kawai a gaba na wai yazama gawa ….kuma dalilin nice sila….sageer cikin kuka yace dani “shikenan mamma kinji dad’i kin kashemin daddy na …..daddy ya mutu ta sanadiyyarki …..bazan tab’a yafemiki ba mamma” yana kukan ya kife kan gawar mahaifinsa da wata irin murya yake fad’in “wayyo daddy don Allah katashi ni ina sonka wallahi ……pls daddy na ka tashi karka tafi ka barni …….DADDYYYYYYYYYY….sageer ya k’wala kiran mahaifinsa yayinda ya zube ajikin mahaifin nasa sumamme shima …….

Mamma ta dakata da bawa Hassana labarin saboda kukan da yaci k’arfinta ….yayinda Aunty Nafeesa ma ke kukan tunowa da baya … Hassana ma hawaye ne a fuskarta faca faca tana wani irin kallon mamma da mamakin duk wad’annan abubuwan da take fad’a itace ta aikata su ………..

Comments
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

TYPING

???????? HASSANA ????????

              *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TARE DA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page 1⃣7⃣to1⃣8⃣

WATTPAD:hassana3329

ROK’ONA ZUWA GAREKU MASOYA NA????

INA NEMAN ADDU’AR KU MASOYA NA DA BAKUNAN KU MASU ALBARKA ,ZA’A YIMIN AIKI NE RANAR TALATA INSHA ALLAH ,SHIYASA NAKE BARAR ADDUAR KU GA DUK WANDA YA KARANTA WANNAN FEJIN YA TAIMAKENI DA ADDU’A ,ALLAH YASA AYI AIKIN CIKIN NASARA ,ALLAH YABANI LAFIYA TARE DA SAURAN MUSULMIN DA BASU DA LAFIYA ,MASU LAFIYAR KUMA ALLAH YA K’ARA MUSU LAFIYA

TUNASARWA????

MANZON ALLAH (S A W )YACE “LALLAI WANDA YAFI KOWA SHARRIN WAJEN ZAMA A WURIN ALLAH (S W A )RANAR TASHIN K’IYAMA DAGA CIKIN MUTANE SHINE WANDA MUTANE SUKA GUJESHI SABODA TSORAN ALFASHANSA
MAFI LAIFUKAN D’AN ADAM YAKAN KASANCE NE DAGA HARSHENSA

AIKI ME FALALA????

MANZON ALLAH (S A W )YACE “DUK WANDA YA KARANTA K’UL HUWALLAHU AHAD SAU GOMA ALLAH ZAI GINA MASA GIDA A CIKIN ALJANNA ,KUMA WANNAN SURAR TAYI DAI DAI DA D’AYA BISA UKUN ALK’UR’ANI

TALLA TALLA TALLA????

????????????????????????
????????????????????????
MUWADDAT
????????????????????????

ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATUL ALLAH , INA MIQA D’INBIN GAISUWATA GAREKU MASOYANA MASOYA LITTAIFAINA,TARE DA YI MUKU FATAN ALKAIRI A DUK INDA KUKE ACIKIN FAD’IN DUNIYAR NAN .

A YAU NI AYSHA A BAGUDO MARUBUCIYAR AUREN SIRRI NAKE SON ISAR MUKU DA SOKON CEWAR LABARIN MUWADDAT
YA DAWO NA KUDI GA DUK WANDA ALLAH YA HOREWA ABUN BIYA , LABARIN MUWADDAT LABARI NE WANDA YA SAKANCE TRUE LIFE STORY.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button