SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

CONTACT 08167888934 TO SUBSCRIBE

S A R K I IS NOT FOR FREE
[11/9, 06:05] Mss Flower: ???? S A R K I

By Mss Flower????

SIMILARITIES OR RESEMBLANCE OF STORY/LIFESTYLE IS COINCIDENTAL

PLEASE IDAN BA KI SHIRYA PAYMENT BA KAR KI BIYONI, DON’T WASTE OUR PRECIOUS TIME IDAN KUMA KUƊIN NE YA MIKI TSAURI KI NEMI RAGI BUT KAR KI BIYONI DAN KI MIN ASARAR LOKACI NA ROƘEKI????

          *19&20*

A ɗaki na taradda Salamat tana shan ice cream, kallo ɗaya nayi mata na kauda kaina na cigaba da harkokin gabana

Bayan na shirya holy book na ɗauko na fara karantawa, ba ni na tashi ba sai after magrib, bayan nayi isha’i na wuce dining room na ci abinci

Fita nayi walk zuwa wajen da ke min daɗi, na zauna kenan da mintina sai ga Salamat tazo wucewa cikin kwalliya sai ƙamshin perf take

Taɓe baki nayi cikin rai na nace “you have downgrade yourself to the lowest level”

Harara ta watsamin sannan ta wuce tana juya jiki, actually tanada diri sosai and she is plumpy so in tana tafiya jikinta na karkaɗawa hakan yasanya ta zama very sexy

Na jima a wajen inata saƙa da warwara, nayi nisa cikin kogin tunani naji an dafa kafaɗata tareda cewa “Mss Batool”

Ɗago kai nayi na sauke kan Prince Yar da smile a fuskarsa, maida masa nayi nace “barka da dare”

Zama yayi kusada ni sosai sannan ya kamo hannuna yace “tunanin mai kikeyi?”

Ɗan langaɓar da kai nayi nace “bakomai” ina ƙoƙarin janye hannuna da ga nasa

Ƙara riƙe hannun yayi yace “please let me, hannunki da ɗumi and i want to hold them”

Gyaɗa kai nayi na bar masa ba dan raina ya so ba

Matsa hannuna yake cikin salon kashe jiki, mun jima a haka kafin yace “Batool ina jin ki a raina”

Ɗago kai nayi na kallesa nace “kamarya?”

Murmushi ya saki sannan yace “nima bansan yanda zan miki bayani ba, but actually kin tsayamin a rai, ba kallon maid nake miki ba ina kallonki ne as a woman”

Shiru nayi dan sai na rasa abin faɗa, shima bai kuma cewa komai ba

Mun ɗauki lokaci kafin na ɗago kai na kallesa nace “dan Allah mai ka sani gameda Prince Sydeek na kasa fahimtarsa”

Shiru yayi sanan ya nisa yace “meyasa kike son ki fahimcesa?”

“Da wahala kayima wanda baka san halinsa ka fahimcesa aiki ba, ko bakomai ina tunanin zai rage min wani abun” na faɗa sounding innocent

Gyaɗa kai yayi sannan yace “he is selfish, duk wani abu mai kyau na sa ne, bashida kirki ko kaɗan sannan azzalumi ne, beware of him please Batool” ya faɗa yana ɗan matsa hannuna da ƙarfi

Ɗago kai nayi na kallesa nace “yayi kama da mutum mai tarikan ɓoyayyun sirri

“Ƙazaman ɓoyayyun sirrika ne, actually Batool yana bani tausayi, kowani lokaci ɓata ni yake da ɗan uwana wajen Emir just because yana son rising to throne, zaki ga bai cika magana ba kuma kamar babu ruwansa amma ba ƙaramin mugu ba ne, shiyasa nake yawan cewa ki kula, tausayin da yake ba ni kuma duk kuɗinsa bai gani yana hangen na wani ne” ya faɗa cikin damuwa

Jimm nayi sannan nace “Allah ya shiryesa”

“Ameen ya rabb” ya faɗa in low tune

Mun ɗauki lokaci mai yawa babu wanda ya kuma magana kafin yace “Batool na tambayeki?”

Gyaɗa kai nayi nace “Eh”

“Misali nace ina son muyi dating will you accept me?” Ya faɗa his eyes fixed and focused on me

Wani yawu na haɗiya sannan nace “ehm, i will love to but bazan iya ba” na faɗa

“Why?” Ya tambaya

“Ka fi ƙarfina” na faɗa ina kauda kai

“Look at me Batool” ya faɗa

A hankali na ɗaga kai na kallesa

“Love knows no boundary, please be my woman” ya faɗa yana ƙureni da idanu

Janye hannuna nayi daga riƙonsa da yake sannan nace “dan Allah ka daina maganar nan, kana magana ne akan abinda ba zai taɓa yiwuwa ba” na ƙare ina miƙewa

Janyoni yayi muna facing juna sannan yace “think about it” ya ƙare yana juyawa

Ko da ya wuce zama nayi nace “bazaku barni nayi aikina cikin salama ba, daga issues ɗin wannan sai na wannan” na ƙare ina dafa kaina da furta ya rabbb

I took few more minutes kafin na koma ɗaki, hira kaɗan mukayi da Junnut sannan muka kwanta har lokacin Salamat bata dawo ba

Knocking ɗin Salamat ne ya farkar da ni da asuba, Junnut ce ta buɗe mata, tsaki na ja na miƙe na nufi toilet

Cikin sauri Salamat ta riƙoni tace “please bari nayi fitsari a matse nake”

Hanya na bata ta shiga, tun ina tsaye zaman jiranta har na haƙura na zauna, ta jima kafin ta fito jikinta ɗaure da towel alamun wanka tayi

Ban ko kuma kallonta ba na shiga nayi alwala, bayan na gabatar da sallah wanka na shiga sannan na koma bacci

Bani na farka ba sai misalin tara, shima Junnut ce ta tasheni

Cikin bacci na zauna ina miƙa sannan na dubi Junnut nace “kin dawo”

Gyaɗa kai tayi tace “ya kamata dai ki tafi aikinki, it’s pass 9”

Miƙewa nayi ina faɗin “har tara tayi”

“Eh, ga abinci nan kici ki wuce tunda kinyi wanka” ta ƙare tana komawa gadonta

“Thank you Habeebty, sannu da aiki” na faɗa ina nufar toilet

Kafin na gama cin abinci har tayi bacci, murmushi nayi nace “you are such a kind person”

Bayan nagama shirina na wuce side ɗin Prince Sydeek, banyi knocking ba dan nasan da wuya yana parlor, so kawai na tura ƙofar

Tsaye yake cikin ash ƙananun kaya wanda sukayi matuƙar masa kyau yana waya, kallo ɗaya yayi min ya wuce bedroom yana wayar ƙasa ƙasa

Taɓe baki nayi nace “da sannu zaka shigo hannu”

Dining area na nufa, komai yana nan yanda na ajiye dan ko alamun taɓa wani abu ba’ayi ba

Wani malolon haushi ne ya tsaya min, duk baƙar wahalar da na sha ace ko duba abincinma bai yi ba, ƙwafa nayi sannan na kwashe nayi kitchen da su

A nylon na juye na zubar sannan na wanke kayan, pancake nayi masa na zuba honey sannan nayi masa Loomi tea (dried lime tea)

Bayan na ajiye na koma na ƙara gyagyara parlorn duk da babu abinda yayi

Chan ya fito, fridge da ke kusa da dining ɗin ya nufa ya ɗauko drink sannan ya zauna a dining

Sai kallonsa nake naga ya buɗe ya fara ci, har na sare ganin bai tanka ba sai naga ya yaye white sheet ɗin, taɓe baki yayi ya cigaba da shan drink ɗin, sai da ya gama ya miƙe

Cikin sauri nace “dan Allah ko ɗanɗanawa ne kayi”

Kallona yayi sai ya ɗauke kansa yayi hanyar fita

“Dan Al….”, ban kai ga ƙarasawa ba ya ɗagamin hannu sannan ya juyo ya. ……

TO SUBSCRIBE, CONTACT 08167888934

S A R K I IS NOT FOR FREE
[11/9, 06:05] Mss Flower: ???? S A R K I

By Mss Flower????

SIMILARITIES OR RESEMBLANCE OF STORY/LIFESTYLE IS COINCIDENTAL

☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSO….

????????????????????????????

IF YOU LOVE THE BOOK SUBSCRIBE, KO BAKI DA KUƊI YI RANCE COZ IT’S GOING TO BE AN AMAZING JOURNEY. DON’T MISS OUT!!!

           *21&22*

Ɗagamin hannu yayi ya juyo tareda watsamin kallon banza sannan ya fice

Taɓe baki nayi nace “kai ka jiyo”

Zama nayi akan carpet ina ta saƙa da warwara, na rasa yanda zanyi Prince Sydeek atleast ya daina nuna min tsana, i just want us to be okay ko nasamu wani abun daga wajenasa

Knocking naji a ƙofa, miƙewa nayi na buɗe ƙofar, ganin Prince Yar ya sanya nayi smiling nace “sannu da zuwa”

Murmushi yayi yace “kina lafiya, ya aikin?”

Kaina a ƙasa dan kallon da yake aikomin dole nai ƙasa da kaina sannan nace “Alhamdulillah sai dai ka zo baya nan”

Murmushi yayi yana shigowa ciki sannan yace “dama ba wajensa zanje ba, yau munada family dinner by 9, tare zaku taho da shi coz ke zaki yi serving ɗinsa, nazo na faɗa miki hakan ne”

Gyaɗa kai nayi nace “toh”

Ƙureni da ido yayi yana kallona, ya jima yana ƙaremin kallo sannan yace “mene amsata?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button