SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

“Batool kinsan meyasa na dinga bin diddiƙi, na gano an kama ki, na kuma kiraki dan taimaka miki, dalilin shine ke kaɗai zan iya yadda da ita akan Prince Sydeek, na tabbata ya aminta dake ne shiyasa har kikayi aiki a ɓangarensa, inada yaƙinin zaki iya taimakonsa da mu baki ɗaya” ta faɗa

“Zan taimaka muku, da dukkan iyawata” na faɗa a sanyaye

“Yawwa, Allah ya saka miki da alkhairi, amma ka da ki taɓa nunawa Prince Yar kin dawo hayyacinki” ta faɗa

Gyaɗa kai nayi sannan nayi ɗan murmushi nace “i will never”

Murmushin itama tayi sannan tace “ki kwana a nan, bari zanyi magana a nuna miki ɗaki, nagode sosai” ta ƙare tana miƙewa

Murmushi nayi nace “my pleasure”

Bayan fitarta tariyo irin cin mutuncin da Prince Yar yayi min, ɗaureni kamar rago tareda kashe jama’ar ƙasata masu adalci da yayi, murmushi na saki sannan nace “yanzu muka fara wasan!!!”

READ FREE NOW AND PAY HEREAFTER LATER
[11/12, 5:15 PM] Muslima????: ???? S A R K I

ABU-DHABI PALACE

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, a yanzu babu abinda ke damuna domin na daƙile matsalar Prince Yameen tun randa na gurji ubansa, hakanan wajen Salamat ma na samu sauƙi domin ta shafamin lafiya sai ya zamana ma ko magana batayi min hakan kuwa sai yafi min daɗi

Wajen Princess Zairah itama ta shafamin lafiya duk da ma dai ranar da muka rabu tsiya tsiya bamu kuma haɗuwa da ita, ta wajen Prince Yar ina tafiyar da shine kamar yanda yakeso, dukkan abinda yace hakanne, abinda yace ba haka ba, tau nima wurina nuna masa nake ba hakan bane

Yanzu damuwata ɗaya shine dawowar Prince Sydeek ayi ayi a gama nakoma inda na fito domin dukka ji na nake a takure

Ina kwance ina wannan tunanin Junnut ta shigo tana faɗin “ke tashi yanzu naji ƙusƙus” ta faɗa cikeda ɗaukin min gulmar

Miƙewa zaune nayi nace “ina jinki”

“Ina kitchen sai masu girkin Big Madam suka zo ɗaukar wasu kayan masarufi da suka ƙare musu a chan, nan naji ƙus ƙus ɗinsu cewar Prince Sydeek na gaf da dawowa”

Wata zaburar farinciki nayi ina faɗin “ke dan Allah?”

“Tau, ba fa tabbatarwa nayi ba, ji nayi dai kuma ba wai sun faɗi lokaci ba ne” ta faɗa tana min kallon tuhuma

“Alhamdulillah!!” Na faɗa cikin jindaɗi

“Wai rawar jikin me kikeyi hakane, hutun ya isheki ne haka?” Ta tambaya

Murmushi nayi nace “dole nayi murna ubangidana zai dawo mana Junnut” na faɗa

“Allah ya kaimu” ta faɗa tana miƙewa

Bayan fitarta Qur’ani na ɗauka nayi tilawa, na jima sannan na jima dan har akayi magrib sannan na miƙe

Bayan nayi sallar isha’i wanka na faɗa sannan nayi shafa na shirya na fita dan yawatawa

Yau canza wajen zama nayi niyyar yi saboda ko kusa bani son abinda zai haɗani da Prince Yar

Flower garden ɗin da ya kaini na je, bakin pond ɗin na tsaya bayan na tsinci ƴan ƙananan duwatsu ina jefawa cikin ɗan nishaɗi

Tsakuwa nake cillawa ina faɗin “Prince Sydeek ya warke”, sai na kuma cilla wata nace “bai warke ba”, ina ɗan enjoying ne da nufin abinda tsakuwar ƙarshe ta bani itace gaskiya

Ina jefa ta ƙarshe wadda ta bani ba zai dawo ba, sai na linke hannayena haɗe da turo baki duk da nasan wasa ne amma hakan bai min daɗi ba

Saukar numfashi naji haɗa kwanciya bisa kafaɗata, sannan ya zuro hannunsa ya zagaye cikina

“Ɓata ran mai kikeyi” cewar Prince Yar yana shanshanar wuyana

Wani irin tulun baƙin ciki ne ya tokaremin dan sosai nake jin haushinsa ga kuma ya wani ruƙunƙumeni

Hannu na sanya na fara ƙoƙarin cire hannunsa daga jikina

Matseni ya kuma yi sannan yace “Batool please stay calm” cikin raɗa yana hura min iskar bakinsa cikin kunnena

Ba dan naso ba haka na tsaya hawaye suka fara kwararomin dan na kasa jure yanayin, tsanarsa nakeji amma banida ikon hanasa raɓar jikina

“Batool ina sonki” ya furta cikin narkakkiyar murya

Ban iya cewa komai ba dan zuciyata tafasa takeyi

“Ki bani zuciyarki dan Allah” ya faɗa yana matseni gam a jikinsa

Maida ƙwallar idona nayi sannan nace “yaushe zaka fahimci cewa bazamu taɓa rayuwa waje guda ba, ni da kai sam bamu cancanci juna ba, ka taɓa ganin inda haske da duhu suka haɗu?” Zancen nan yana fitowa ne daga zuciyata

Juyoni yayi muna kallon juna sannan yace “mai yasa kike ƙoƙarin nesanta kanki da ni, soyayya babu ruwanta da mai kuɗi ko talaka, babu ruwanta da sarauta ko bauta, tana shiga zukata ne batareda an ankare ba, haƙiƙa a baya ba sonki nake ba amma lokaci guda naji kin zama wani ɓangare na zuciyata, ki ajiye batun dacewa ni kin min kuma a haka nake sonki” ya faɗa yana shafa fuskata

Hannunsa na zare daga fuskata sannan nace “kayi min afuwa ni bazan amince da kai ba dan nasan ƙarshe wahala kawai zan sha, kana da mata dan haka ka jingine zancen soyayya da ni”

“Matata muhallinta daban naki daban, bazan taɓa haƙura dake ba, muddin ba kin amince da soyayyata ba bazan taɓa samun kwanciyar hankalin kasancewarki kusada Sydeek ba” ya faɗa yana riƙo hannayena gamida cewa “ki amince min”

Janye hannayena nayi sannan nace “ka sakani komai zan aikata, zanyi dukkan abinda kace na bar abinda ka hana amma ka daina zancen soyayyata domin bazaka taɓa samu ba” na faɗa ina juyawa dan tafiya

A fusace ya fizgoni haɗe da kwantar da kaina bisa damtsen hannunsa ina kallon sama (bridal style) sannan yace “ke tawa ce Batool, ke tawa ce!!!” Ya ƙare haɗe ɗora bakinsa bisa nawa ya shiga tsotsa da zafi zafi, duk mutsu mutsun da nakeyi da neman ƙwatar kaina gazawa nayi domin shima ɗin namijin gaske ne

Babu yanda na iya haka yayita shan lips ɗina sai aukin zubar hawaye kawai nakeyi, sosai ya fara fita daga hayyacinsa dan har ya zubar damu ƙasa tareda ɗorani bisan cinyarsa batareda ya raba kiss ɗin ba, hannunsa ya ɗora bisan ƙirjina

Wata zabura nayi tareda raba kiss ɗin sannan na fara girgiza kai alamar ya bari dan kukan da nake na baƙincikin karɓar first kiss ɗina da yayi alhalin bani ƙaunarsa na gaza samun jarumta

“Ke tawa ce!!!” Ya faɗa da ƙarfin gaske haɗe da kuma fizgoni ya haɗe bakinmu waje guda

Hannuwana biyu na ɗora bisan dukiyar fulanina dan karesu daga hannunsa

Mun jima a wannan yanayi kafin ya zare bakinsa ya fara maida numfashi, sai da ya huta sannan yace “Batool haƙurina na gaf da ƙarewa gameda ke, ke shaida ce nayi juriya, dan Allah ki aminta dani ba sai na miki ta ƙarfi ba” ya faɗa yana zareni daga jikinsa

Wani irin haushinsa nakeji haka na share hawayena tareda goge bakina sannan na miƙe na fara karkaɗe jikina

Juyawa nayi dan tafiya sai ya fizgoni ya haɗeni da ƙirjinsa, ina jin yanda yake goga ƙirjinsa bisan nawa na rintse ido dan zuciyata ji take kamar an shararamata ruwan zafi

A kunnena ya raɗamin “Batool ina sonki”

Ban tanka ba dan a halin da nake ciki idan nace zanyi reacting toh ba zai wuce na fashe da kuka ba, domin ƙarshen tozarci nake fuskanta a halin yanzu

“Prince Sydeek ya kirani, ya sanar min this week zai dawo, naga bai fuskanci komai ba, i’m grateful da baki faɗa masa ba” ya ƙare yana pecking gashina

Wani irin ajiyar zuciya na saki da naji batun dan ko bakomai tunda yayi zancen dawowa nasan ya samu lafiya ne

“Batool duk abinda nace kiyi, kiyi shi cikin kulawa coz bana son a samu matsala kinji” ya faɗa yana shafa bayana

Ban iya tanka masa ba har sai da ya raba hug ɗin ya kuma cewa “kinji?”

Gyaɗa kai nayi kawai idona na ƙasa

Murmushi yayi tareda matseni jikinsa ya ja ni muka bar wajen, har bakin gate ɗinmu ya rakani sannan yayi pecking goshina yace “go in, have a nice night”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button