SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

“Tea” ya furta a hankali sannan ya maida idonsa ya rufe

Kitchen na wuce gabaɗaya jikina a sanyaye, sosai nake jin tausayinsa dan a iya zamana na fahimci cewa duniyarsa shi kaɗai ne a cikinta. Bayan na haɗa ma sa tea, scrambled egg na soya ma sa sannan na fice dan kai ma sa

A ƙudundune na sameshi, a hankali na kira “Prince Sydeek” sai dai shiru bai amsa min ba har sau uku, gabana ne ya faɗi, hannu na ɗora saman wuyansa wani irin sanyi na ji kamar an ciro kifi daga fridge, cikin sauri na janye hannuna sannan nace “ga tea ɗin”

Buɗe idonsa yayi ya kalleni da narkakkun idanunsa sannan ya fara ƙoƙarin miƙewa sai dai ya kasa, saboda he looks so weak

Ƙwalla ce ta cika min ido, sai da na share sannan na fara ƙoƙarin ɗaga sa

Da ƙyar na ta da shi zaune, sannan na fara ba sa tea ɗin, spoon biyar yayi yace “na ƙoshi” ya fara ƙoƙarin kwanciya

Da sauri na tallabosa sannan nace “dan Allah ka ci wannan” na faɗa ina kai ƙwai bakinsa, kauda kansa gefe yayi sannan yace “ba na ci”

Tea ɗin na kuma ɗaukowa nace “tau, ka ƙara shan wannan”

Ɗan yatsina fuska yayi kafin ya karɓa, sai dai bai haɗiya ba ya watso min a fuska sanadiyyar tarin da ya fara yi mai haɗe da jini

Jini sosai ya fitar kafin tarin ya tsagaita, dan har sai da na fara bubbuga bayansa sannan, ɗora kansa kan kafaɗata yayi yana sauke ajiyar zuciya

Cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awon gaba da shi, sai da na kwantar da shi sannan na furta “ya rabbb, seems like wanda nake nema ba Sydeek ba ne, wanda yayi poisoning ɗinsa ne”

Miƙewa nayi na kunna chimney (wuta) sannan na fice dan neman Prince Yar coz a lokacin nan muddin Prince Sydeek bai samu kulawa ba yana daff da rasa ransa, coz yana daff da kaiwa last stage

Ina fita harabar wajen idona ya sauka kan Prince Yar da ke ƙoƙarin fita, da sauri har da gudu na nufesa

Tsayawa yayi da smile a fuskarsa yace “kinyi missing ɗina ne?”

Murmushi na ɗanyi sannan nace “dama akan Prince Sydeek ne, wallahi ba shi da lafiya, almost a week yana kwance and he is very sick and so weak, thou yace kar na faɗamaka, amma gaskiya abin is getting out of hand, he may die in aka bar sa haka” na faɗa cikeda damuwa

Ɗan waiwayawa yayi sannan yace “zo mu je” ya ƙare yana ja na kan wani wooden bench

Kallona yayi sannan yace “kar ki damu, he will overcome it, just stay quiet kamar yanda ya faɗa”

Cikin mamaki nace “kamarya he will overcome it, ina faɗamaka he has been poisoned with a deadly poison kuma yana gaf da kaiwa last stage kana ce min wani zaiyi overcoming, are you dummy or what, mutuwa fa zaiyi!!!”

Murmushin fuskarsa ne ya yaye sannan ya kafeni da idanunsa batareda yace komai ba

Sassauto da murya nayi nace “please save your brother” na ƙare ina riƙe hannunsa

“A ina kika san poison?” Ya faɗa in a serious tune

Gabana ne yayi muguwar faɗuwa coz garin gyara nayi makin blanders, ɗan murmushi nayi sannan nace “kawai ina kallon films ne musamman na korea sannan suna yawan poisoning, so i thought it might be poison” na ƙare a sanyaye

Taɓe baki yayi sannan yace “just ki yi abinda na ce, don’t ever tell anyone about this, ki barshi hakanan”

Cikin fushi dan raina ya gama ɓaci nace “ka na nufin na bar mutum ya mutu inyi folding hands ɗina ina kallo, are you really this heartless?” Na tambaya da tsantsar mamaki

Iska ya furzar sannan yace “Batool be a good girl, ki ji maganata kin ji, after all shi ya ja ma kansa duk abinda ya samesa”

“So you want me to stay calm huhh” na faɗa ina kallonsa

Gyaɗa kai yayi da smile a fuskarsa

Murmushin takaici na saki sannan nace “poison ɗin da ke jikinsa might be RISIN kuma yana 12 days ne yana lalata mutum kafin ya kashesa baki ɗaya, and you want me to stay calm and kill a soul”

Wani irin ɓacin rai ne ya bayyana a fuskarsa sannan ya dubeni yace “you seem well educated, kin sani shiga contemplation kan you aint just a palace maid” ya ƙare da murmushi a fuskarsa

Ɗaure fuska nayi sannan na haɗiyi yawu nace “kawai ina son research ne” cikin ɗan daburcewa

Murmushi yayi sannan ya miƙe tsaye, nima miƙewa nayi ina cewa “please let’s save him”

A fusace ya shaƙeni fuskarsa ɗauke da tsananin ɓacin rai dan har ta canza launi zuwa jaa sannan yace “kar ki taɓa shiga abinda babu ruwanki idan ba haka ba zaki shiga cikin gaggarumar matsala, and mind you idan wani ya ji zancen poison ɗin nan kece kikayi poisoning Sydeek kuma sai kin rasa ranki” ya ƙare yana cillani jikin bench ɗin har ya faɗomin a ƙafa

Ƴar ƙara na saki saboda zafi sannan na fara tari domin shaƙar da yayi min ba ta wasa ba ce

Har tarin ya lafa yana tsaye a kaina sannan ya ce “kiyi hattara dan kina ƙoƙarin fara wasa da ajali ne” ya ƙare yana ficewa

Mamaki na shigayi ina yaba hali irin na Prince Yar, tabbas yanada alaƙa da wanda nake nema tunda har ya san da zaman poison ɗin da ke cin Prince Sydeek, murmushi nayi sannan nace “mission almost about to be accomplished”

Apartment ɗin Prince Sydeek na koma, pumpkin porridge nayi masa sannan na je inda yake kwance idonsa rufe

A hankali nayi tapping ɗinsa, jikinsa yayi ɗumi ba kamar ɗazu ba da yake sanyi kamar ice block probably saboda na kunna wuta a ɗakin

Buɗe idonsa yayi ya saukesu a kaina, murmushi nayi masa yayinda naji dukkan wata gaɓa ta jikina na son taimaka ma sa

“Ka sha porridge” na faɗa ina ɗagasa

Ya karɓi spoon goma sannan ya kauda kansa

Cikin tausayawa nace “na sanarma Madam halinda kake ciki?, dan bakada lafiya sosai” na ƙare idona na kawo ruwa

Girgiza kai yayi kaɗan sannan ya maida idonsa ya rufe

Cikin tausayawa nace “kana buƙatar wani abun?”

Girgiza kai yayi

Kwantar da shi nayi sannan na fice nayi apartment ɗinmu, ban tadda kowa ba dan haka na tura information kan anyi poisoning one of the prince da same poison da nake neman mai shigar da shi ƙasarmu sannan na kashe komai na kira Mom

Mom sosai tayi farinciki da na faɗamata ina gaf da completing, bamu ɗauki lokaci ba na kashe na koma sashensa dan yanzu kusan ko yaushe ina chan wani zubin har chan nake kwana

Ko da na je tari naga yakeyi sosai kamar ransa zai fita ga jini da ya ɓata gaban farar jallabiyar jikinsa, wasu hawaye ne suka saukomin sannan na ƙarasa wajensa da sauri na shiga tapping bayansa sai da tarin ya lafa sannan na cire hannuna

A haka yayi dukkan sallolinsa a kwance, sai after magrib nayi masa wani porridge ɗin na ganyayyaki, kama daga bitter leaf, water leaf da dai ganye da nasan yana ƙara jini

Spoon ɗaya yayi ya yamutsa fuska ya kauda kai, da ƙyar nasamu ya cigaba da amsa

Sai da ya shanye duka sannan nayi murmushi nace “sannu”

Taimaka masa nayi na rakasa ƙofar toilet, sannan na nufi sashenmu dan shirin bacci

Ina kaiwa ƙofa gabana ne yayi muguwar faɗuwar da sai da na dafe ƙirjina, innalillahi wa’ina ilaihi raji’un na furta sannan na shiga

Gabaɗaya kayayyakina nagani a watse alamun anyi mugun bincike an gano, innalillahi na fara maimaitawa zuciyata ta fara gudu da ƙarfin gaske

Salamat da ke zaune kan gado tace “mai ya haɗo ki da Prince Yar?, kuma mai kikeyi da su computer a wajen aiki?”

Tsura mata ido nayi ba dan ban ji mai tace ba, sai dan ruɗun da ƙwalwata ta shiga na ganin asirina ya tonu an kuma kwashemin kayan aikina

Toilet na faɗa tareda latsa agogon da ke ɗaure a hannuna na sanar da headquarter kan su yi shuttening duk wasu bayanai an kama ni…….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button